Skip to content
Part 4 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir Takori

Ta bi cake samosa spring-rolls da doughnuts din da ta shafe awanni hudu cur tana aikinsu tun karfe shidda na safe da kallo rugurguje a kasa, tare da kiyasta irin azabobin da za a gana mata a kan wannan snacks, amma wannan ba karamin mugu ba ne, sai hawaye sharrr! To saime? Kafin ta gama tantance what will happen nedt (Me kuma zai faru?) Al’ameen ya kai mata wawura yana kokarin lalubar cikin ta tamkar mai shirin kwashe mata ‘ya’yan hanji da kayan ciki gaba daya cikin gigita, mamaki da tashin hankali ta ce.

“Wayyo Dela, na shiga uku zai kashe ni.”

Ya ce, “A’a ba kashe ki zan yi ba, cikin na ke so in duba in ji ko saurayin banza ne ya yi miki ciki, ki ka gudo daga gidan iyayenki, ki ka kama wannan aikin wahalar don cikin ya bare, ki ka kuma tsani duk maza ta kai ga ko sallamar su ba kya amsawa saboda shi wancan din? To ni na iya zubar da ciki ta hanya mai sauki ba ta wannan aikatau din da ki ke ba.”

Ta zaro ido abin dariya abin tausayi ta ce, “Don girman Allah ka sake ni, wallahi ni ba ni da wani ciki ban ma taba yin wani saurayi ba a rayuwata.”

Ya sake ta tare da maida hannuwansa baya ya sarke su cikin murmushinsa mai kyau ya ce,

“Munafuka, ashe kina magana?”

Ta sha kunu ta cika ta yi fam, kiris take jira ta fashe ta ce, “Shin don Allah ina ruwan ka da ni? Wane irin bako ne kai mai shishshigi ga rayuwar mutum da yawa? Ba ka san masifar da ka janyo min yanzun ba? Ba ka san in Hajiya ta san kana shigowa nan sai ta kusan kashe ni ba?” Sai ta sa kukan da ya karyar da zuciyar Al’ameen gaba daya.

Ya ja kujera kwaya daya tal da ke cikin kicin din ya zauna dab da ita ya cure hannuwan shi wuri daya ya ce,

“Ba abin da ya hada ni da Hajiya, ni dan uwan su mai gidan nan ne a Kaduna nake, halin rayuwa ya sa muka bacewa juna tun tuni sai yanzu suka gan ni muka gane juna. Hajiya ba abin da za ta yi miki tun da kuwa ni na kawo kaina ba ke ki ka janyo ni ba ko ke ki ka kirawo ni?”

Shi kansa ya yi mamakin kansa kan karyar da ya samu kansa yana mai sharawa, a take ya soma Istigfari a zuci. Ta share hawayen ta da bayan hannu duk sai ta kara ba shi tausayi, ya ce,

“Don Allah ki yi min wata alfarma guda daya, ni kuma zan taimake ki ki samu ‘yancin kan ki, in dai kudi ne daga naira daya zuwa million zan baki, ki koma gaban iyayen ki, ki je makaranta ko ki yi aure, ya fiye miki wannan wahalar wadda kwata-kwata ba ta dace da mace mai darajjah da kima kamar ki ba!.”

Maganar shi ta karshe ta bata matukar haushi, ita nan har wata daraja gare ta? Shin ‘ya mace na da wata daraja ne ma? Ita da ubanta ke bal (bull) da ita? Yana cewa in aka tausasa mata bai yafe ma? To me ye amfanin rayuwarta tunda kuwa bata da wata daraja yanzun a wajen uban da bata da kamarsa?

An yi wa uwar ta sakin wulakanci, an daidaita matsayinta da na ‘yar aikin gida mafi kaskanci, to me ye amfanin rayuwar ta in ba ta yi bauta ba?

Wasu sababbin hawayen suka kwararo mata sharrr! Ta ce, ‘Ni ba ni da wata daraja ‘yar aikin Hajiya ce!”

Ta tsugunna bisa gwiwoyinta a gaban sa ta ce, ‘Don Allah Yaya na kada ka kara zuwa nan, Hajiya har shocking take sa mini, ta sa kebur ta farfasa min jiki, ta sa kafa ta taka fuskata ta ce wai ni ba ni da amfani tunda ubana da kansa ya bata ni in yi mata bauta. Idan ta ji kana zuwa nan Allah shocking za ta sa min…”

Ta kai hannu ta dan janye doguwar rigarta sama zuwa gwiwar kafarta, me zai gani? Jini ne kwance yarab-yarab lub-lub da shi abin ki da farar fata, zanen kebur birda-birda wani a kan wani, ya kau da kai da karfi ya juya mata baya.

Ya ji idanunsa sun ciko da kwallah. Wai Hajiyarsa? Ita ce mai ganawa dan adam irin wannan rahsin imani, su ko ko mari wannan bai taba hada ta da su ba.

Kenan ‘ya’yan ta kadai take so, ba ta yarda da na kowa ne ba? A yau kam ya yi nadamar kasancewarsa (Al’ameen dan Haj. Nafi). Ina ma shi dan Aunty Saratu ne? Yanzu ne ya godewa dabarar shi na boye mata ainahin ko shi wane ne, zai kuma ci gaba da boye matan.

Ya tabbata da ba za ta kula shi ba, ko yanzu ma don ta ji ba abinda ya hada shi da Hajiyar ne, to ai ko shi ne, to wanda ke gana maka irin wannan azaba ina za ka daga ido ka dubi wani da ya shafe shi ma balle dansa na cikin sa?

Ya zaro handkerchief din sa mai kamshi cikin aljihunsa ya mika mata ya ce, yana mai kawar da fuska daga gare ta, ‘Share hawayen nan maza-maza bana son in ga mace tana kuka, zan tafin yanzu, amma ki yi min alfarma daya ki gaya min me ki ka yi wa baban nan naki haka da zafi?”

Ta sunkuyar da kai, ta rasa me yasa zuciyarta ta amince da Al’ameen haka farat daya, ba ta san me yasa ya shiga ran ta haka da sauri ba. Babu abin da take jin za ta iya boye masa a game da ita ban da abu daya, shi ne ba za ta taba tonawa wani cewa ita ‘yar daddy ba ce, kuma take cikin irin wannan kaskanci da rashin galihu a gidansa, wannan zai zubar mai da mutunci ne a idon dan uwansa da sauran jama’ar da ke ganin kima da mutuncinsa. Tunda shi Daddyn ya san da ita, amma bai gaya masa yana da ‘ya ba a gidan ita a kan me za ta fadi? Ita fa tana da zuciya, ba kuma ta tura kan ta inda ba a kai ta ba, bari kawai ta kara wulakanta kanta, tunda ita dama wulakantacciyar ce a gidan.

Ta ce cikin wata irin sassanyar murya da ta kassara gabobin shi baki daya.

“Ni ban san abinda na yi masa ba, kawai dai talauci ne ya ishe shi shi ne ya sayarwa da Hajiya ni.”

Al’ameen ya sa hannu ya dafe kansa da ke sarawa tamkar ya rabe gida biyu, bai taba jin inda aka sayar da dan mutum ba a wannan zamanin dai da muke ciki kamar wani zamanin cinikin bayi?

Da kyar ya samu kalma ta fito daga bakinsa ya ce, “Yanzu ina baban naki yake?’

Ta ce, ‘Ai yana fita daga nan ranar da ya kawo ni mota ta kade shi ya mutu, uwata kuma tun muna kanana dama ya sake ta ban san inda take ba yanzun, dama kuma an ce ba ‘yar kasar nan ba ce.’

Ta yi hakan ne don ma kada ya ce zai kai ta wani wuri, ita wannan rayuwar ta fiye mata duk wata rayuwar jin dadi da za ta yi a wani wuri, a gidan da ba na Daddy da ya nuna mata ingantaccen so da kauna a baya ba. Ba ta san hakan da ta yi kuskure ne babba ba, domin tausayi kan taimaka wurin kimsa ‘so’ na hakika.

Ta ce, ‘Na rasa me yasa Hajiya ta tsane ni? Na dade ina yi wa kaina wannan tambayar, iyakacin biyayya ina kokarin in ga na yi mata tamkar Mama ta. Tunda nake a duniya babu wanda ya taba budar baki ko da wasa, ya gaya min ya tsane ni gaba da gaba tamkar mutuwar sa ba sai Hajiyar nan gidan, I don’t know why?”

Al’ameen sai ya samu kansa a rashin yarda da abin da ta gaya masa na cewa wai talauci ne yasa ubanta sayarwa da Hajiya ita, to amma wacce hujja gare sa da zai karyata ta? Shi kam ko za a tsaida shi gaban alkali ko a ritsa shi da bindiga ba zai yarda ba ‘yar manya ba ce. Kai ba alamun ta taba kasancewa cikin talauci a rayuwarta.

Muryar ta kadai ya ji ya san tana da ingantaccen ilimi, magana take a nutse, cikin sassanyar murya ta da ke sanya gabobin dan adam su yi sanyi, kai, unblievable.”  Ya ce,

“Kin san wani abu ne?”

Haka kawai Allah kan halicci mutum ya kimsa kiyayyarsa a zuciyar wani, ba tare da wani dalili ba. Bai yiwuwa musamu soyayya daga kowa don ko Annabin Rahma Allah bai bar shi ba makiya ba. Idan har ba ki da makiyi, to ki binciki aikin ki.

Dole wani ya so ka wani ya ki ka a duniya. Akwai wani shahararren (popular and famous American doctor) wai shi Dr. Fell da aka yi a kasar Amurka tun 19th Century (Karni na goma sha tara), wanda kasar ke ji da shi saboda fasahar shi, kowa na son shi saboda dumbin taimakon shi ga al’umma, ba shi da wani aiki sai na ceton rai, ba shi da wani buri sai na ya ceci rai a gaba dayan tsayin rayuwarsa, ba tareda ya karbi ko kwabo ba, amma sai wani mawaki makocinsa yake waka a cikin wani baiti da yake cewa:

I don’t like thee, Dr. Fell

I don’t like thee.

I don’t like thee, Dr. Fell

The reason why? I can not tell.

A nan shi mai wannan wakar ya san dai ba ya son Dr. Fell duk da farin jininsa da da irin taimakon da yake wa al’ummarsa kuwa, amma bai san me ya hana shi son sh ba. To haka tsananin ki da Hajiya, ba wai sai da wani dalili ko wani abin ka wa mutum zai ji ya tsane ka ba. Don haka kar ki sa wannan a ranki har ya dame ki.

Duk wani matsayi da ki ka ga dan adam a ciki to haka Allah ya rigaya ya tsara masa rayuwa sai ya rungume ta hakan nan ya kuma zamo mai godiya a gare si. Idan ya aiko mai da sauki, ana son ya yi farin ciki, ya rungumi wannan saukin, ya dauka cewa daga Allah ne. Don haka ni taimakon ki nake son in yi tsakani na da Mahalicci na, idan kin amince da ni.”

Ya sunkuya ya dago habar ta, ya dubi yadda hawaye ke rolling one after the other (gudu bi-da-bi), a irin wannan fuska mai zati. Yasa hankici yana share mata sai ta runtse ido ta girgiza kai alamar ba ta so. Ya sakar mata fuska ya ce, ‘Ha-di-rah.” Idonta a rintsen ta ce, ‘Ni ba sunana Hadirah ba.”

Ya ce, ‘To Halimah dube ni.”

Ina! Al’ameen bai sani ba, muryarsa kamar wani maganadisu ne (magnet) mai jan zuciya tamkar jan wutar lantarki ta ce,

‘Ina ji.”

Cikin wata raunanniyar murya, ta rasa me yasa idanun ta ke kasa dubar wannan mutum, wala Allah kwarjin shi ne? Ya tabbata ba za ta taba iya kallon shi ido cikin ido kamar yadda yake so ba, sai dai in su kwana a hakan sai ya ce, “Kin amince da taimakon da nake son yi mikin?” Ta yi shiru na ‘yan dakikai.

In dai barin gidan Daddy ne ba za ta taba iyawa ba. Ta gwammace Allah ya dauki ranta a nan ta huta, to ma sace ta zai yi? Ko ko Hajiyar zai roka ta ba shi ita? To ya kai ta ina?

Sam, ita ba ta son wani taimako, ba kuma ta son watsawa mutumin da ya taba nuna kulawa da rayuwar ta bayan Faisal kasa a ido. Ba shakka ta ji dadin maganganunsa, ta tabbatar shi mutum ne mai wadataccen ilmin kwakwalwar dan adam da aiki da shi, har take jin zuciyarta na yaudarar ta da gaya mata wai ta sami makwafin Faisal wurin kulawa da nuna kauna.

Bai kuma zugata ta ki babanta da ta ce ya bada ta bauta ba, haka bai zuga ta da ta yi izgili ga Hajiyar da ta tagayyara masu rayuwa ba. Ya nuna mata yi wa kowanne dan adam uzuri komai abu ne mai matukar muhimmanci. Ga kuma hikimar kwantarwa da mai matsala hankali, cikin fasaha da ingantacciyar kulawa, she enjoyed meeting him hakika (ta ji dadin haduwa da shi).

Da ya ga ba ta ce komai ba duk sai ya damu, ya karkatar da kai ya ce,

“Halimah, ba ki amince ba ko? Na rantse da Allah ba ni da niyar cutar ki, hakan nan na samu kaina da son taimakon rayuwar ki da tausayin ki, amma ban sani ba ko ke har yanzun tsoro na ki ke ji amma….”

Ta katse shi, “By the way, in na amince ka taimake nin, ta wacce hanya ka ke ganin za ka taimake nin?”

Ya yi shiru, shi kansa bai sani ba, amma can a karkashin zuciyarsa wani sako ne mai nauyi da ba zai iya fadi yanzun ba, in ya yi hakan ya yi garaje, akwai bukatar yin dogon nazari a kan al’amarin, ya binciki Addinin ta, usli, halayyar ta da iyayen ta don kar a kuma komawa ‘yar gidan jiya. Ya ce,

“Nan da jibi ni da matata za mu koma gidan mu da ke nan garin, zan roki Hajiya ta ba ni ke a zuwan za ki ke taimakawa Ihsan a kicin, sai in maida ke makaranta, don zuciya ta na ba ni yakinin cewa kina da ingantaccen ilimin da ki ka fara ba ki kai karshensa ba, haka ne?”

Ta yi murmushi kawai, sai dai tsarin sa kwata-kwatan bai yi mata ba. So take ta ce ya kai ta Makarfi, ta ga mahaifiyar ta ko da sau daya ne ya fiye mata duk wani taimamko da za a yi mata a duniya, ko da kuwa shugabancin kasar za a bata baki daya.

Amma in ta fadi abin da ke zuciyarta ba mamaki ya dago ainahin ko ita wace ce? Wanda ita ba ta fatan hakan, ba don komai ba sai don mutuncin Daddy din ta.

Za ta ci gaba da hakuri, har zuwa ranar da wannan ‘daukin’ na Ubangiji da aka kwadaitar da ita zai zo daga Allah, a lokacin da bata zata ba. Ta daga kai ta  dubi angogon kicin din ta ga tsawon awoyin da suka share a zaune. A firgice ta mike ta soma hada kayan girki duk jikinta rawa yake ta ce,

‘Ka ga ka sa na yi lattin abincin rana, ka yi hakuri don Allah, na gode kwarai da kulawarka, amma bana bukatar kowanne taimako rather than in ga Mamana da ban san inda take ba.”

Ta dauki bokiti ta fita.

Dr. M.A.B ya dade yana kallon ta har ta kule cikin store yana kallon inda Ubangiji ke yin halittar mace har mace, wai a matsayin ‘yar aiki? Irin su sun fi dacewa da gidan auren so da kauna, inda za a so su a tarairaye su a kuma kula da su cikin tsantsar soyayya da jin dadi.

Tafiya take illahirin jikin ta na rangaji tamkar reshen bishiyar da iska ke kadawa. Bai taba ganin macen da ta sa shi jan ido kamar wannan ba, bai taba katari da macen da ke burge shi ta kowacce siga, magana, tafiya, nutsuwa, murya da yauki na halitta kamar wannan ba. To ko dai idon shi ne shi kadai? Dole ya kara likewa matar har sai ay ginawa kansa matsayin da ita ma za ta ji shi har bargo da kasusuwan ta tamkr yadda yake ji game da ita a yanzun.

Abin da ya lura da shi shi ne yarinyar wata irin murdaddiya ce hakan nan maza ba sa gabanta sam-sam, kai da alama ba ta san ma mene ne son ba; naive and innocent.

Tabbas wannan wata kyauta ce daga Indallahi a dirowar shi Nijeriya kuma rabon soyayyar ta ya tunkudo ruhin shi gida. Bai taba tsintar kansa a irin wannan yanayin ba, wai son mace? Har cikin bargo da kasusuwan sa? Jin sa ya yi duk ya wani yamutse, wani sabon nishadi na bi shi (ya ma manta ya taba aure kuma yana da shi din). To bari mu bi su mu gani.

A Makarfi ya yi sallar Azuhur shi da Daddy da Baffansu, kuma Al’ameen shi ya yi wa mahaifin shi bikon Antin shi. Kar ki so ki ga farin cikin da Baffan su Malam Sani ya yi, domin dama chairman din su na nan Makarfi ya matsa mai da maganar Saratun. Ba su baro Makarfi ba sai karfe hudu na yamma bayan komai ya daidaita.

Ita kanta Antin ta amincewa ranta gidan su Zarah ne kadai za ta iya zaman aure. Babban farin cikin ta ma tarbiyyar Intisar din ta ya dawo hanunn ta kenan. Sai dai ta ce tana bukatar lokaci a kalla wata guda domin ta kimtsa a hankali, wannan ko odar Sharifi Mal. Sidi ne, domin ya ce sai ya shirya su sosai domin kishiyar ta hatsabibiya ce, kuma ya ce yana kokarin karya na Saratun ta da ya ce har ya fi nata tsauri da wahalar karyuwa, amma Alhamdulillah ya san ko a lokacin Daddyn na cike da tunanin, ko a wane hali take ne?

Don haka Al’ameen sai karfe tara na dare ya shigo gida a gajiye lis don sai da ya gama da ministry tukunna, an amshe shi da dukkan yabo da izinin yin aiki tare da su ma idan yana so, gami da izinin gina asibitocin duba lafiyar kwakwalwa a ko’ina ya so a Nijeriya.

Bai samu zuwa Garki wurin su Ihsan ba, wannan ya masifar kara fusata Ann, don yau kwana uku kenan suna zuba idonsa su kafa masa dokokin rikon Ihsan, amma ko wayar sa babu balle kafar sa. Ita Ihsan din ta neme shi ta tarar kwata-kwata ya rufe wayarsa ma.

Baya jin gajiyar da ya yi da yunwar da ke tare da shi za su hana shi neman Halimah, (sunan da ya rada mata kenan bai kuma damu da sai ya ji sunan ta na hakika ba, tunda ba ta son fadi ai dole wata rana zai ji ne). Ba ya jin zai iya barci bai yi tozali da wannan fuskar mai zati ba, baya jin zai iya barci bai ji wannan muryar mai katse duk wasu jijiyoyi masu gudanar da jini a jikin sa ba.

Shi kadai ya san me yake ji game da ita. Hakan nan ya wuni zungur da tunanin da baya da makama, ya tabbata son Halima ne ke spreading all over his body (Kurdawa cikin kowanne sako a jikinsa).

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.2 / 5. Rating: 24

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siradin Rayuwa 3Siradin Rayuwa 5 >>

24 thoughts on “Siradin Rayuwa 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×