Skip to content

Siradin Rayuwa | Babi Na Sha Daya

3.4
(21)

<< Previous

Wane Ne Brigadier Bello Makarfi?

Bello Isyaku Makarfi, mutumin garin Makarfi ne ta jihar Kaduna, Bello ya tashi maraya gaba da baya hannun Baffan shi Mal. Sani ya girma. Lokacin da aka tura shi NDA garin Jos, shekarun shi ba su fi ashirin da biyar ba. Kwazo, himma da sadaukar da kai irin nasa ya kai shi matsayi iri-iri a soja cikin ‘yan shekaru kalilan.

Ya auri Nafisa diyar wani shahararren dan siyasa mai neman kujerar gwamnatin Kaduna na lokacin wai shi Magaji Doller ne tun auren saurayi da budurwa, don dukkansu so ne ya hada su lokacin tana ajin karshe a sakandire, sai bayan auren ne ya fahimci Nafi watsatstsiya ce, irin ‘ya’yan nan da iyaye suka jika da naira, babu kwaba babu hantara kasancewar ita kadai suka Haifa, sai daga baya ne Allah ya nufa ta zauna gidan auren, da taimakon kaunar da take masa.

Gidan iyayen ta yana nan a unguwar Kabala Cutain, cikin garin Kaduna wanda a halin yanzu mahaifiyar ta ce kadai a ciki (shekarun baya ne mahaifin ta ya rasu a hatsarin jirgin sama a kan hanyarsa ta zuwa birnin New York).

Wannan ya ba ta damar zama millionnaire domin daga ita sai mahaifiyar ta kadai suka gaje mahaukaciyar dukiyar da ya bari. Kusan Nafisa ta fi mijin ta kudi don shi ma’aikacin gwamnati ne na kasa, sai dai za a kira irin su top-millitary a yayin da ita kuma ke harkar cinikayyar gwalagwalai daga kasashen Africa daban-ban da sauran kasashen da ke ketaren mu.

Akwai babban shagon sayar da gwalagwalai nata na kashin kanta da ta bude a babbar kasuwar Kaduna, wanda ta sanya wa sunan first born din ta Al’ameen Jewellaries.

Akwai matsananciyar kauna tsakanin ta da babban danta Al’ameen wanda ya ci sunan marigayin mahaifinta ne. Hakan nan sun bude wani a Lagos sai dai na hadin gwiwa ne tsakanin ta da aminan ta Haj. Suwaiba matar gwamnan Kaduna na lokacin da Haj. Badi’a ministar kudi ta lokacin. Sun yi aure yana matsayin Laftanal-kanal a shekarar da suka haifi Mohd. Al’ameen, yana major din shi ta haifi Najib, Faisal da Yasir. Shekarar da mahaifin ta ya rasu ne ta haifi Nasir da Bello mai sunan Daddy da suke kira (Daddy Karami).

Daga Bello ta haifi Faruk sai ‘yan biyu duk maza Idris da Furkan. Dan ta na karshe shi ne Ibrahim Khalil da bai fi shekaru uku ba a lokacin. Kusan duk yaran sun fi shakuwa da Hajiya Saratu fiye da ita ba don komai ba sai don ba ta da lokacin su, harkar kasuwancin ta ya fiye mata komai muhimmanci, ke dai bar ta masifar son ‘ya’ya da kashe masu kudi, amma babu lokacin kula da tarbiyyantar da su.

Duk wata kulawa da ta dace uwa ta kwarai ta bai wa ‘ya’yanta yaran nan sun same ta ne daga Aunty Saratu, tana iya kokarin ta kwarai wajen ba su kulawa ta musamman da ingantacciyar tarbiyya, kai ba ka ce ba ita ta haife su ba, ba ta ko damuwa da habaicin da Hajiyar ke yada mata na “a ci a yi kashi kadai.’

Ita ko rurrutsa ma take wato kwanika, don duk shekara take haihuwa, sai daga kan Khalil ne haihuwar ta yanke mata, don haka kusan gaba daya yaran dukkansu daya, ba za ka iya bambance wa ko kani ba in har ba su suka gaya ma ba da bakin su.

Brigadier Bello kakkarfan mutum ne na sosai, wankan tarwada mai kyakkyawar sura. Da wuya ka yi masa kallo daya ba ka maimaita ba saboda cikar zati da kamala. Mutum ne mai tausayi da jin kai, ya sha fadawa hadarurruka iri-iri a zamanin kuruciyarsa irin dai na kowanne soja, amma juriya da maida kai irin nasa yasa har kullum cikin promotion kan promotion yake.

Bai damu ba don ya sadaukar da ransa kan cigaban kasar shi, Nigeria. Jaridu da mujallun Kaduna kan so buga abin da ya shafe shi saboda yadda jama’ar Kaduna da kewayen ta ke son shi. Ba shi Kaduna, ba shi a Lagos, kuma ba shi Abuja inda duk aiki ya wulla shi anan yake shi da iyalin sa, ayi ta famabn canjin makarantar yara.

Rayuwar su abin sha’awa ce ga kowa barin ‘yan mazan ‘ya’yansu masu tsabar kama da juna. Duk da kasancewarsa ba mazauni ba baya sake da tarbiyyar ‘ya’yan shi. Islamiyya dole ne su je ta da yamma haka da dare ya aje masu malamin Addini da ke karantar da su littattafan Addini irin su Kawa’idi, Ishmawi, Sirah, Arba’una Hadith, Nurul-Mubeen da sauran su. Idan kuma sun tafi makarantar boko ba su dawowa sai karfe hudu na yamma, domin akwai special edtra lesson da yasa ake masu after school hours. Don haka duk cikin yaran Hajiya Nafi kaf babu dakiki kowanne kwaro ne wajen karatu, idan har ka ji su suna tafka musu to a kan karatun su ne, don kowanne ji yake ya doke dan uwansa a hazaka. Haka lafazin da ke fita bakin su a shekarun su zai ya ba ka mamaki, babu wanda ba za ka ji shi da ma’ana ba. Ga hadin kai, ga baiwa babba girmansa koda shi ke binsa a haihuwa.

‘Ya’yan Brigadier ba su san wani abu wai shi yawo ba ko raini ga na gaba. Basu iya zagi ba, basu iya karya ba, basu san yaya ake yin su ba. Haka idan sun dawo daga lesson din dare, kafin su kwanta karatun su ya koma wuyan Anti Saratu.

Saratu, diyar Baffan Brigadier ce, auren zumunci ne a tsakanin su, zumuncin ma irin wanda aka zama daya din nan kamar wa da kanwa na ciki daya.

Ta kammala digirin ta na farko daga Jami’ar (Edeter) da ke U.K, inda ta karanci Insurance zallah. Wannan kuwa daurin gindi ta samu daga murdadden dan boko dan uwan ta Bello, wanda ya dauki nauyin komai na karatun ta shekaru hudu cif a matsayinta na kanwarsa wadda nauyin komi nata ke kansa tunda ba’a yi mata aure ba.

Ta dawo gida tana da shekaru ashirin da hudu da haihuwa. Rikicin auren ta da Alhazai biyu shi ya yi sanadiyar auren ta da yayanta, ko ko in ce daga gatse.

Da fari Baffan su ya kira Brigadier ne ya ce,

‘Ka ga karatun nan dai kai ka daurewa Saratu gindin yinsa, ga shi ta dawo kowa ya zo ta ce ba ta so ga illar shi, kana nufin auren ma ka daure mata gindi ta ki yi?’

Ya ce, ‘A’a Baffa, Saratu na son yin aure, ba ta samu wanda ya kwanta mata ba ne har yanzu. A yi hakuri a kara mata lokaci.”

Baffan ya yi salati ya ce, “Shekaru ashirin da hudun za a karawa lokaci? To wallahi ba a gidana ba sai dai ka dauke ta ka kai can gabanka ta zauna. Duk kun ja min surutu a gari, ban isa in je wajen daurin aure ba sai an nuna ni ana zundena ga wanda ya aje uwar mata a gida wai boko. Idan ba kya son shi Alhaji Saminu saboda mata uku, shi wannan ministan fa mai mata daya saboda Alah me ye laifin sa?”

‘Yar auta Saratu sai ta kwabe fuska, ‘Gaskiya Baffa ya fiya tumbi, rundumi, ina zan kai wannan kayan jigida?”

Brigadier ya yi dariya shi ko Baffan sandarsa ya dauka zai buge ta Bello ya tare, ya ce,

“Ni za ki kawowa fitsara don ki nuna min ke kin je turai kin fetsare? In gaya miki Mungo-Park ma kakan-kakan ku mun ga iyakar sa balle ke, kuma tunda ba kya son Alh. Aliyu sai ki tattara ki bar min gida ko a daina ganin ki a garin nan ana nuna ni a wajen daurin aure.” Ya soma kuka.

Brigadier ya ce, “Baffa duk abin bai yi kamarin haka ba, kash…”

‘To, to na ji bai yi zafin haka ba, ai sai ka gaya min me kuma ku ke nufi? Ka ce karatu, an kare, sai kuma me? A sani a bakin duniya ko me? Ba kwa auren junan ku kowa ya huta? In kuma shi ma tumbin gare shi to don uban ki zo ki fice min a gida ki koma can turan ki auro bature sardidi sannan ne ki ka burge ni.”

Dariya ce ta kama su dukkan su, ya yi murmushi ya tausasa murya cikin rarrashi, ‘Allah ya ba Baffa hakuri, abin bai yi zafin haka ba sam, Saratu kin ji me Baffa ya ce? Me zai hana ni ki aure ni?”

Kunya ta kama ta, ta sunkuyar da kai ba ta ce komai ba. Sai dai a ranta hakika ta yi na’am da auren Yayan ta, don dama tuni ta dade tana sha’awar yiwuwar hakan, don duk duniya ba ta ga namijin da ke burge ta kamar shi ba. Sai dai me? Tana masifar tsoron Hajiya Nafi, don ta san ta kwarai kamar yunwar cikin ta kan azababben kishi a kan mijinta da suma da suke dangin sa balle sun aure shi? Baffan ya ce,

“Za ki amsa ko sai na yi kwallo da ke?”

Ta zabura ta fake a bayan Yayanta, cikin tsoro ta ce, “Baffa to Hajiyar su Aminu fa?”

Brigadier ya yi murmushi, “Ke manta da ita, ba abin da za ta yi miki, kin amince ko Saratuna?”

Duka suka yi wa juna lallausan murmushi har suka bai wa Baffan kunya, ya mike yana karkade buzun shi ya yi cikin gida.

Ba karamar badakala aka kwasa da Hajiya Nafi ba kan auren Saratu, don cewa ta yi munafurci ne su Baffan suka kulla mata don dama sun tsane ta, amma in ban da haka a rasa wadda za a kakaba masa duk cikin dangin nashi sai yarinyar da suka tashi gida daya?

Kwanan ta goma a yaji babu wanda ya je bikonta da ta ga abin ba na wasa ba ne, dolen ta ta dawo ta tadda amarya a rufaffen sashin da ba kowa, kamar ta yi hauka, ta hana kanta ta hana kowa a gidan nan sakat da bala’i.

Da ta ga wannan ba zai mata ba, domin kamar tana zuga su ne su kara likewa juna sai ta koma bin malamai da ‘yan tsibbu, ta mance Saratu kanta ‘yar malam ce, ba kowanne karabitin asiri ke kama su ba.

‘Ya’yanta ke ta tausar ta da cewa ta kwantar da hankalin ta har Najib na cewa,

“Maman mu in ta zo me za ta yi miki? Maman mu ba a kan ki za ta zauna ba.”

Shi ko Faisal cewa ya yi, ‘In dukan ki ta yi Ya Aminu zai rama miki.”

To sai ya kasance ita Saratun mace ce mai ilmi na zaman duniya ta san yadda take tafi da abokiyar zaman ta cikin lumana. Amma har inda nan ke motsi, Hajiya Nafi kafarta ba ta bar gidan ‘yan tsibbu ba da ‘yan bori ba a hana Saratu haihuwa.

To sun ci nasarar wannan kam, tunda ance abin gaskiyar mai shi ne. Amma kullum mijin su kara son ta yake saboda hankalin ta da tunani.

Rashin haihuwar ta ba su danganta shi da kowa ba face Allah. Su kan ce lokaci ne har yanzu bai zo ba. Shekarun ta biyar a gidan wadanda in kin dube ta ba za ki ce ta hada ashirin da taran ba. Tana aiki da Insurance Company na Kaduna.

Haj. Saratu baka ce bakin da akan kira black beauty. Mace ce da ta lakanci kalmar ‘gayu’ duk da shekarun ta still ita ‘yar gayu ce komai kuma cikin gayun da bokon take yin sa. Rakiyar Brigadier aiki duk ita ce haka in za shi abroad domin hutu ko aiki duka Aunty Saratu ce mai rakiya. Ita Hajiya son ‘ya’yanta ta sani sai maida kobo ya koma dari.

*****

Ta sanya baby a ruwa ta yi mata kyakkyawan wanka, tana mai tazbihi ga Al-Khaliku Sarkin kaga halitta ta yadda ya suranta wannan yarinya tamkar diyar Larabawan Masar. Wani irin so ne ke huda bargo da tsokar jikin ta na ‘yar da ba ta san ko ta wa ye ba!

Ta ciro bebin daga ruwan tana nannadewa a tawul kenan su Khalil suka shigo, wani na ture wani, kowannensu na cewa shi zai fara goyon bebin da Daddy ya ce ta haifa suna makaranta. Dadi ne ya kamata ta ce, Najib ne zai fara goyawa tunda duk ya fi su karfi.

Najib shi ne da na uku a ‘ya’yan Hajiya, yaro ne mai kunya sai ya sadda kai a ransa yana cewa yaya ma za ai ya goya mace? Ya ce, ‘A’a Anti ai mace ce, da dai namiji ne sai in goya.”

Faisal da tun shigowar su yana durkushe gaban jaririyar ya yi farat ya ce, ‘Gafaracan da Allah malam ni in goya, anti ni za ki na goyawa baby kullum.”

Ta sa masa bebin a baya tasa zani ta kulle masa. Najib da yake duk ya fi su wayo har Faisal din da ya girme shi ya dubi bebin sosai ya ce,

“Antin mu a haka wani sai ya ce bebin nan ta yi wata uku?”

Gaban Antin ya bada dam! Sai kuma ta yi dan jim, kafin ta ce,

“Ai su dama lafiyayyun babies haka ake haifan su da girman su.”

A ranar kwata-kwata Faisal bai bar Anti da raino ba, shi ya zabi kaya overall na babies masu kyau cikin kayan da Daddy ya jibge mata ya sanya mata ya shafe mata jiki da olive oil.

Haka Antin ta ce da su nonon ta ba ya da lafiya don haka doctor ya ce a dinga shayar da baby da madarar NAN. Faisal shi ya sanyawa babyn feeder  a baki yana ta zuga ta wai ta yi sauri ta shanye ko ta yi saurin girma su dinga tafiya makaranta tare.

In sun dawo ta bi su Islamiyya kafin su kwanta ya koya mata ABCD. Su kuwa sauran sun zagaye ta in ka dauke Al’ameen da ke makarantar kwana, suna ta yaba kyawun kanwar su, a cewar su ba su taba ganin baby mai kyawu kamar ta ba, ji suke tamkar su lashe ta don so, babu kamar Faisal, da kyar suka bar ta gun uwarta, don sun dage sashin su za ta kwana ko sauro ba za su bari ya taba ta ba, sai da Antin ta ce da su cikin dare za ta yi masu kuka sannan suka hakura.

A daren Hajiya Saratu kwana ta yi rikon Allah ya raya mata bebin ta, ya kare ta sharrin dukkan abin ki, ya rufe bakin Hajiya Nafi kada ta fadawa ‘ya’yanta bebin ‘yar tsintuwa ce.

Da sati ya zagayo raguna har biyu Brigadier ya kayar a kofar gidan si ya radawa yarinya suna Saratu, don kawai ya nuna mata godiyar shi kan karamcin da ta yimasa da kuma matsayinta a zuciyar shi ya zarce na kowa. Domin shi kan son bebin nan yake bilhakki, son da yake jin baya yi wa wani cikin ‘ya’yan shi bayan Al-Ameen.

Unguwar Gwamna Road irin unguwar nan ce ta masu fadi ajin garin Kaduna da babu ruwan kowa da rayuwar kowa, balle har tsegumi ya bullo, don haka Brigadier ya yi wa yaran shi kawai Walima wadda ya hada da birthday din Khalil na 3 years.

Da alama jinin Faisal da babyn Saratu zai fi haduwa, don kacokan Faisal ya tare a sashin Antin yana taya ta rainion babyn da yake kira Intisar. Shi dai haka nan yake son sunan, tuni duk yaran suka kama Intisar, Intisar. Antin kadai ke kiran ta da Saratun ta sak.

Tun Hajiyar su na duka da zagi kan ya fita hanyar su har ta gaji ta zubawa sarautar Allah ido ta yi watsi da al’amarin su kamar ba ta san Allah ya yi ruwan tsirar su cikin gidan ba ma, ta rungumi kasuwancin ta kadai. Kuma dama yanayin sashin su sai mutum ya yi wata guda bai ga dan uwan sa ba in har ba shi ne ya neme shi ba (tamkar tafiya ce ta layi guda).

Babbansu Al’ameen dama tun da fari bai kaunar Anti Amarya, a dalilin yana ganin a kan me Daddyn baya shawara da mahaifiyar shi akan komai na gidan dama rayuwar shi gaba daya sai ita da ta zo daga baya?

Don haka ko da ya dawo ya tadda haihuwar Anti amarya bakin ciki bai sai an fada ba. Aminu kawai masifar jin kai da takama sabanin su Faisal da suke friendly ga kowa, ga miskilanci kamar tsohon kuturu, sai dai fa natural brain wannan shi ne nick name din shi a makaranta, Aminu yaro ne mai kwakwalwa a karatun lissafi tun yana karami.

Sun dauki Intisar sun kai Makarfi sun warwarewa Baffan su da ya rage masu a duniya da Goggo Jummai mahaifiyar Anti Saratu komai. Abin da suka ce shi ne Allah yasa Saratu ta yo halin mai sunan ta kuma mai amfani ga al’umma.

Baffa ne dai ya ce mai ya sa bai tuntubi hukuma ba tun da fari? Ya manta Bellon kansa hukuma ne tunda kuwa babban kusa ne a soja, sai ya ce kawai shi dai hakan nan Allah ya daura mai kaunar Saratu har bai jin dadai duniya zai taba rabuwa da ita.

Malam ya ce,

“hakika Ubangiji Yana jin kan bayin sa masu jin kai. Allah yasa Saratu ta yo halin mai sunan ta, ta kuma zamo ‘ya abin alfahari a gare su”, yadda kuma abin yake sirri a tsakanin su haka suma za su rike.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

8 thoughts on “Siradin Rayuwa | Babi Na Sha Daya”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×