Skip to content
Part 6 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir Takori

Tsaye yake kikam, ya hade hannuwan shi a kirji yana kallon tangama-tangaman hotunan ta kamar ta fito ta yi magana da aka manna a kusurwa biyu na falon tabbacin ana ji da Ihsan kenan, kuma ita daya kenan a gidan tamfar rai ga iyayenta. Ko bude abubuwan da aka jera masa bai yi ba balle ya kai ga ci.

Ta samu kujera can nesa da shi ta harde, ta dauki remote control ta karo karfin A.C ko sannu da zuwa ba ta ce masa ba balle ci kan ka. Shi ne ya gaji da shirun ya bara, ya dubi agogon hannun shi Jovial ya ce,

“Saboda Allah Ihsan haka ake karbar baki ku a gidan ku?”

Ta sake tunzura ta ce, ‘Da aka yi me?’

Ya ce, “Kin san awanni biyu kenan kwarara, ina zaman jiran fitowar wani a cikin ku, amma shi ne sai yanzu ki ka ga damar fitowa?”

Ta yamutsa fuska ta ce a zafafe,

“Aminu, har kana da bakin gaya min haka? For God’s sake, yau kwanakin mu nawa a garin nan amma ka nuna wa iyayena ba ni da wata daraja a idon ka ba ka kuma damu da ni ba, shi ne kuma har za ka nemi gayan magana? Wai haka muke karbar baki, to ni ko iyayena da wa ka ke?” Ta tsatstsare shi da ido.

Al’ameen ya san ba shi da gaskiya, kuma ko a wurin Allah ne ba shi da ita. Dole ya sauke nashi temper n ya samu masangalin kujera ya rage tsawo, ya sanya hannu cikin aljihu ya zaro wayar shi da ke ta tsuwwa a cikin aljihun kaftanin shi, ya dade yana magana da aminin shi Rehab wato babban likitan Meritime yana gaya masa irin muhimman ayyukan da suka gabatar ne a kwanakin, ya ce ya yi kyau ya kuma yaba komai, ya gaya masa akwai motocin sa har yanzu suna port bai san ba a auno su ba, sai jiya ya je da kansa ya auno masa ta jirgin ruwa, amma ta Nijar za su biyo don ba jirgin kaya tun bayan da suka taso, don haka ya je ya fiddo su a Yamai. Suka yi sallama ya maida wayar shi aljihu.

Ya dubi Ihsan da sassanyan kallo ya ga ko kallon shi bata yi, ta maida fuskar ta can wani gefen daban bayan ta daure ta iya daurewa kamar bata san Allah ya yi ruwan tsirar shi ba ma, ransa ya sosu, amma sai ya yi murmushi ya ce,

“Ihsan kenan, dadi na da ke ba kya tsayawa ki ji uzurin mutum sai kawai ki kama fushi, amma ai ke ma dai kin san I missed you very-very much…” 

Ya kira kalaman cikin tattausar muryar da ta kusa sa ta gyangyadi, amma da yake tana son ta nuna fushin nata sai ta cije ta kyabe baki a lokaci guda kuma tana girgiza kafa daya kan daya ita ala dole fushi take, duk sai ta ba shi dariya, ya mike har inda take ya mika mata hannuwan shi masu matukar taushi alamar ta tashi su yi sulhu, amman sai ta noke cikin jan aji irin nata, sai ya russuna ya kama hannayen ta duka biyun ya mikar da ita tsaye, suka fuskanci juna cikin ido, ita kallon haushi take masa shi kuma kallon I beg your pardon.

Ta ce, “Me ye haka?”

Amman can karkashin zuciyar ta hucewa take yi, tana kuma kara son mijinta a kowanne dakika, duk wata hanya da ya san zai bi ya wanke laifin shi a zuciyar ta ya san shi, duk da ta san kaunar da ita take masa ta rinjayi wadda yake mata, amma yana kokari a koyaushe ya nuna shi din mai son ta ne, mai gudun bacin ran ta ne.

Bare yanzun da ta yi kewarsa, fiye da yadda bakin ta zai iya fassarawa, sai ta bada kai bori ya hau. Sun dade cikin farantawa junansu tamkar suna gidan su koko bakin beaches na Miami, kafin su zauna su fuskanci juna, jikin ta a barin kafadun shi na dama, ta soma share hawaye da bayan hannu duk ya bi ya rikice ya ce,

“Me ye kuma?”

Ta ce, “Anya Al’ameen ba ka gamu da wata kana so ba a dawowar mu? Wace ce Halimah da ka ke kirana da sunan ta yanzun?”

Ya ji gabansa ya fadi damm! Kwata-kwata ya manta da wa yake tare, ya mance a inda yake, ya mance abin da yake yi, ita kadai ke yawo a ransa, ita kadai ke yi masa gizo a kowanne kiftawar ido. Amma ai namiji ne, tuni ya waske ya sha kunu ya ce, “Da aka yi me fa?”

Ta yi tsaki ta ce, “Nufin ka ba na ji sosai ko me? You ‘ve both changed, u ren’t my real Ameenu (Gaba daya ka canza kai ba Aminuna da na sani ba ne).

Ya ce, ‘Ashe? Baki na yi ko fari?”

Ta ga yana neman ya raina mata hankali, sai ta yi murmusin takaici ta ce, “Man, kada ka yi fooling dina man? Be frank, duk ka canza, ka yarda ko kada ka yarda, na ji ka ba a yadda na saba jin ka ba, na rantse I’m smelling something trouble (Ina sunsunar wani abu mara dadi a tare da kai).

Inda Allah ya cece shi shi ne kafin ya motsa bakin shi don shirya amsar da zai ba ta, Ann ta yaye labule ta shigo, shi ne ya matsa gefe cike da haushi, me ake da kafiri? Babu ko sallama balle neman aminci ga wanda ka taras? Ita ko Ihsan ba ta ko motsa daga yadda ta ke ba don ita kanta ba ta ji dadin abin da mahaifiyarta ta yi ba, ai ko bature yana kwankwasa kofa, ta san halin Al’ameen din ta sarai daga yau baya kara girmama ta, don ya sha ce mata babu dabba kamar mai shiga waje babu sallama.

Ann ta dade tana kallon su cike da haushi kaman ta rufe Ihsan da duka ta ce, ‘Get out stupid.” Sum-sum-sum ta fice tana sharar hawaye, ita fa tana son Aminu, ba kuma za ta yarda a kashe mata aure ba, ita kadai ta san wahalar da ta sha kafin ta same shi. Sai dai a yau ma kamar kullum tana shakkar kaunarsa gare ta, amma na yau ya fi na kullum.

Duk da cewa bai nuna mata wani abu ba ita dai zuciyar ta na ba ta yakinin a lokacin da suke tare hankalin shi baya tare da ita, musamman saboda sunan da ta ji ya fito cikin kuskure daga bakinsa, da kyar in ba wata ya gano yana so ba, sai ta kara barkewa da kuka.

Ta samu kujerar da ke fuskantar shi ta zauna ta ce, “I’m sorry, na dauka wajena ka zo da babanta?”

Ya ce, ‘Oh yes, Ma’ama, me too, am sorry, ni da Ihsan mun yi missing juna ne sosai.”

Ta dube shi a lalace, sai dai fa ita kanta na mamakin wai wannan tsalelen ne mijin Ihsan din ta? Ko ita ta samu miji kamar shi ba haukan da ba za ta yi ba a kansa, sai ba ta ga laifin Ihsan ba ko kadan, amma Addinin shi ne ba ta ra’ayi, kuma tana son Ihsan da auren manyan mutane ne irin baban ta ba wai yara professionals irin su Aminu ba, yo me na sama ya ci bare ya bai wa na kasa?

Ta zuki iska ta fesar ta ce, ‘Haka ne? Ni ko sai na dauka ba ka son ta ne.”

Ya ce, “Ki yi hakuri Ma’ama, na dade ne rabona da gida, shekaru goma sha biyar, na dawo na tarar da uzururruka da yawa da suka sha gaban kaina, in kin duba fa kwata-kwata ko sati biyu kwarara ba mu hada ba a kasar, ita kan ta Ihsan ta sani ni ne babba a gidanmu, so kin ga ko family dina bai isa a ce na gama da su within a week ba, ku yi mun uzuri, rashin zuwana baya nufin tozarci ko izgili a gare ku don ko jiya babana ya samu Dr. A ofis, so ki yi hakuri.’

Ta gyada kai cikin gamsuwa da wannan ta ce, “Na lura dai kana son ci gaba da zama da Ihsan bayan wanda ku ka yi a Miami bai isa ba, to ina da wasu sharudda da zan gindaya maka a gaba, idan har ka amince da su to ko a yanzu sai in kira Ihsan ku tafi.”

Ya ce, ‘Ina jin ki Ma’ama.”

Aminu fa daurewa kawai yake yana bin ta da yadda take so, ba don komai ba sai don nuna yes, yana son Ihsan, ya kuma san bai kyauta masu ba, amma shi ne za su gara shi kamar wata taya don kurum ya ce yana son ‘yarsu, su din banza?

Ya dai kanne bai nuna ba a fuska. Ann ta gyara zama ta dube shi sosai ta ce,

“Da farko dai ni Christian ce, karewa ma Babana Pastor (priest) ne babba a sanda yake raye. To a bisa tsarin mu tun Ihsan na karama tana bina church kuma har ta tafi America ba ta daina ba, ba zan ce Ihsan Kirista ba ce tun da kuwa baban ta ya dage ta yi Addininku, kuma nima na ga tana so sosai, don haka ba ruwana da wannan.

To yanzu da ta dawo ma lallai ne duk Lahadi kabar ta ta je chochi ta ji wa’azi, ba zan ce kada ta yi sallar ku ba, wannan bai shafe ni ba, amma chochi dole ne ta je duk ranar Sunday.

Abu na biyu kuma shi ne na san ku Hausawa ba ku dauki mace da wata daraja ba, da kun yi ‘yan shekaru da ita shi kenan ta gama amfani, sai a auro wata a wulakanta ta, to Ihsan ita kadai ce da mu, ba mu da wani kwai a duniya sai ita, kenan ba za mu zuba ido mu bari a wulakanta ta ba a ko’ina, dole mu kula da farin cikin ta, don sai tana farin ciki ne mu ma za mu kasance cikin dawwamammen farin ciki da kwanciyar hankali.

Don haka in har kana son ci gaba da zama da Ihsan sai ka rubuta min a rubuce ka yi alkawari tsakaninka da Allahn ka daya cewa ba za ka kara auren wata mace bayan ita ba, ban hana ka harka da mata ba don na san matashi kamar ka ga sura uwa-uba naira, ba za ka lamunci rayuwa da mace guda ba.

Sharadi na karshe shi ne ban yarda ka hana Ihsan yin duk abin da take so ba, don tana son ka, tunda mu ma ba ma hana ta yin son ranta, idan har ka amince yanzu rubuta min in kira ta ku tafi. Ganin baban ta bai zama lallai ba, don bai isa komai ba.”

Al’ameen na zaune tamkar sassakakken gunki yana sauraron yadda ake tsara mai rayuwar kafirci ziryan a gidan auren shi. Tab, ba zai taba amincewa ba, don bai tashi ya ga ana hakan a gidansu ba, bai ga inda Daddy bai isa komai ba a gidansu, au shi ne shi ma za a nuna mai bai isa komen ba don kawai ya ce yana son ‘yar su?

Niyyar shi da kawai ya mike ya tafi ya kyale ta sai sun neme shi don kan su, sai kuma ya yi tunanin ai kunyar marar kunya asara ce.

Ya ce, “Am, Ma’ma, bana nufin izgili, raini ko kaskanci ga maganarku, illa ina son in miki bayanin da maybe, ita Ihsan ba ta yi miki ba.

Da ni da Ihsan, duk mun hadu a Jami’ar Miami ne ko kuma na hadu da Ihsan na karuwancin ta ne ko ko in ce, dukkanin mu watsewar rayuwar turai ta hada mu, ba wai cikin mutunci na aure ta ba a hannun iyayenta da za’a kafa min wasu sharudda marassa madafa bayan auren da muka yi ba da sanin ku ba ko wasu specific hujjoji, da abin mu ku ka gan mu.

Zan iya cewa ma na taimaki Ihsan ne daga gurbatacciyar rayuwar da ta jefa kanta a Florida, ashe in ba a gode min ba, ba za a wulakanta ni ba, a kan me yanzu don mun dawo cikin ku za a nunan iko da matar da na biya sadaki, a gaban shaidu?

Maganar zuwa church ma kwata-kwata ban amince ba, yaya tana sallah za a ce min ta je chochi yin wa’azi, sai dai in itama Ihsan Kiristar ce short and simple, amma ba a hada Addinin mu da kowanne addini sai dai in completely ta koma addinin ki ne?

Sai maganar aure. Ni dai Aminu Bello Makarfi, Musulmi ne gaba da baya, Addinin mu ya ba mu damar auren mata daidai har hudu in har muna da hali za kuma mu iya adalci a tsakanin su, domin kare kan mu daga dattin zina.

Don haka ba zan iya wannan alkawarin ba, idan na yi niyyar in kara aure zan yi.

Na ji kina cewa wai ina da chance na neman mata a waje alhalin ina da aure, to a Addininmu babu wannan damar, ko na Kiristan ba san inda ya baku wannan damar ba. Na karanta bible din ku ciki da bai din sa ban ji wannan nassin ba, (adultery)?

Wancan ma da muka yi a turai mun tuba, duk rudin kuruciya ne da rudin shaitan, amma a yanzu dube ni am a perfect gentleman (cikakken mutum ne) na wuce stage na wannan shedanar.

Maganar in bar Ihsan ta yi son ran ta? Like how? (Ta yaya?) Ban gane ba! Kada ki manta ina auren Ihsan ne fa ba fa ita ke aurena ba, don haka tilas in ta yi ba daidai ba in gyara mata. Mu a Musulince namiji ke ruling matar shi ba wai matar ke ruling din shi ba.”

Ya yi shiru idon sa ya kada ya yi jazur alamun bacin rai. Ta ce, “To who ‘re you telling all these rubbish? (Wa ka ke gayawa wannan maganar banzar?).”

Cikin bacin rai ya ce, “Am not talking rubbish, I only told you the fact (Ba maganar banza nake ba, gaskiya kawai na gaya miki).”

Ta ce, ‘Sai ka sake ta kuwa, yanzun nan kafin ka bar falon nan, ana aure dole ne?”

Ya yi murmushin takaici ya ce,

“Bana jin kaina sai ‘yar ki, idan na sake ta sai kin gwammace mutuwar ta da rayuwar ta.”

Ta ce, ‘Then divorce her and see (ka sake ta ka gani), me zai same ta?”

Ya ce, a yayin da yake mikewa tsaye,

“The worst thing you‘ve never imagine.”  Wato abin da ba ta taba tsamamni ba. Ita ma ta mike ta ce,           “Tun da na ce ka sake ta ta ruwan sanyi ka ki, to ka je, amma Ihsan ba za ta gidan ka ba.”

Har ya kai bakin kofa sai ya juyo,

“Kada ki kara cewa in sake ta, ba zan taba sakin mace ba a rayuwata. Ba don komai ba sai don daraja da girmanta da nake gani da tausayinta, amma ba wai don son ‘yarki ba.

Da wannan nake cewa, in za ku iya ci gaba da ba ni auren Ihsan, idan na dawo daga tafiyar da zan yi a gobe zan zo in tafi da ita, in kuma kuna ganin akwai cutarwa ko takura a gare ta, duk ya rage na ku, sai in ce da ku, Salam!”

Sai ya russuna mata da hannuwan shi biyu tamkar wani Ba’indiye, alamar girmamawa kenan da ake yi wa iyaye a Miami, ya juya ya yi ficewarsa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.4 / 5. Rating: 19

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siradin Rayuwa 5Siradin Rayuwa 7 >>

9 thoughts on “Siradin Rayuwa 6”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×