Skip to content

Siradin Rayuwa | Babi Na Tara

3.2
(21)

<< Previous

Karya Fure Take

Al’ameen na gidan shi tun jiya bayan ya sauke Faisal yana faman aikin takardun tsare-tsaren ginin asibitocin su da fasalin da yake so a yi wa gidansa, wanda zai kasance cikin asibitin. Wayar Ihsan ta katse shi, da ya duba ya ga lambar ta ne sai kawai ya kashe ya ci gaba da aikinsa.

Karfe shida na yamma ya baro gidan ya biya ya yi wa Halimar shi sayayyar su ice cream da dangin sa kana ya wuce.

A harabar gidan ya ga bakin motoci da dama lambar Enugu tabbacin yau gidan a cike yake da ‘yan uwansa, a ransa ya kudurce yau sai sun gaya masa ko fushin me suke da iyayensu.

Ya ratsa ta lafiyayyen falon Hajiya zuwa babban falon gidan ya shiga da sallama cikin muryar sa ta kasaita nan ya tadda su (complete family as earlier). Ba karamin dadi ne ya ziyarci zuciyarsa ba, domin ganin su a hakan ya tuna masa da abubuwa da dama da suka gabata cikin rayuwarsu.

Najib, Faisal, Bello mai sunan Daddy, Faruk, Yasir, Nasir samarin Daddy da sauran kannen da ke bin su sun cika falon sun kawata shi, kowannen su ji yake da boko wanne-ne-ba-wanne-ne ba! Bai san da ya murmusa ba, sai baiwa Daddy labari suke na abin da ya shafe su, to amma me?

Abin ne ya bala’in daure masa kai, ya rikita kwakwalwarsa, ya kasa tantance me yake gani?

Halimar sa ce kwance rashe-rashe bisa doguwar kujerar da Daddy din shi ke zaune, ta yi matashi da kafafusna yana karanta mata labarin kwallon kafa cikin jaridar Punch da su Najib suka shigo da ita. Kamar sun hada baki suka ce,

“Gaskiya gobe za a je bikon Ihsan wa Dr. Al’ameen, mun matsu da mu ganta.”

Daddy ya aje jaridar bisa ruwan cikin ‘yar lelensa, ya dube shi ya ce,

‘Ku kyale shi dai, nake jin wata ya gano yana so ‘yar doguwa kyakkyawa anan din, don kwanaki har man gashi da ‘dryer’ ta gashin mata na gani a wata leda da ke hannunsa bai san na gani ba.”

Gaba daya suka kwashe da dariya har ita da ba ta san takamaiman da wa ake cikin su ba, don a kwance take, ta juya masa baya tana fuskantar Anti Saratu da ke shayar da baby Zarah.

To amma shi bai yi dariyar ba, maimakon haka da kyar ya iya daga kafa ya karasa har saitin kanta ya ce, “Halimah!” Da wata irin murya mai sanyi da rashin kuzari.

Da sauri ta mike zaune ba tare da ta juyo ba, ta san dai ko ba jima ko ba dade dole zai san matsayin ta na hakika a gidan, kuma dama ita hakan take jira kafin ta iya yarda su yi aure, wato sani da amincewar Daddy da Mamarta!

Ba ta iya ta dube shi ba, amma ta san duk duniyar nan babu mai kiran ta Halimah, sai shi, kuma ko a cikin mafarki ta ji lafiyayyar muryar shi cikin muryoyin maza dubu za ta iya fidda ita. Ta dai sunkuyar da kai kawai (feeling guilty) a ran ta tana cewa, yau dai Daddyn da kansa zai gayawa dan uwan su Al’ameen abin da ya dade yana son ya ji, ba za ta iya hada ido da shi ba, saboda dunguma-dunguman karerayin da ta shishshirga masa, amma ai Allah ya gani kuma shi shaida ne kan cewa ta yi ne don mutuncin Daddyn ta a idon dan uwansa har ga Allah kuma dalilin ta kenan.

Aunty ta watsa masa harara ta ce,

“Yaushe Inteesar din ta koma Halimah?”

Idanun shi suka soma kankancewa su kadai cikin tsananin mamaki, ta’ajjibi da tashin hankali ya ce, “Inteesar kuma?” To wai an ce suna linzami, ba ta san sanda ta ce,

“Na’am” ba.

Ya dubi Daddy gaba daya ya rikice ya ce,

“Don Allah Daddy, wannan ba Halima mai aikin Hajiya ba ce ne?”

Muryar sa kamar an shake shi, Aunty Saratu kallon sa kawai take kamar ta ga mahaukaci sabon kamu, yau ga likitan kwakwalwa ya samu tabi a kwakwalwa, haka Daddyn, ta ce cikin halin ko in kula,

“lallai ai ban san Aminu ya yo guzurin shaye-shaye daga Miami ba.”

Najib mai bin Faisal ya tabbata dan uwansa Al’ameen lafiyar sa kalau, ya kuma yi tsamamnin watakila Al’ameen ya manta Intisar ne yana dai ganin ta a kicin tana girke-girke da rayuwa a sassan ‘yan aiki saboda rashin imani irin na Hajiyarsu, sai ya ga ya dace ya yi mai cikakken bayani. Ai Al’ameen bako ne har yanzun kwata-kwata watannin shi biyu a kasar bayan shekaru goma sha biyar, ya san watakila don yana ganin ta tana jera abinci a dining in an gama ta kwashe ta yi sharar gidan gaba daya ta yi wanke-wanke, ta gyara masu dakuna ta kuma wanke masu bandaki.

Ya dubi dan uwansa da idon rahama ya ce,

“Ya Ameenu wannan Intisar ce fa, da ka ta fi ka bari tana karama. Wani labari mai tsawo ya faru a bayan ka, da ya yi sanadiyyar jawo faruwar al’amura da dama cikin rayuwarmu da har ya hana ta komawa makaranta shekaru biyu cif.

Bayan Daddy ya rabu da Anti Saratu, Hajiyarmu ke sata ayyukan da ka ga tana yi don Daddy ya ce Antin ba za ta tafi da ita Makarfi ba, ka kuma san tsakanin su da Hajiyar tun tuni.”

Al’ameen ya soma fiddo ido da murya ya ce, “C’mmon, wai kana nufin Inteesar diyar Aunty Amarya da na illata wa ido?”

Najib da sauran suka gyada mai kai dukkansu alamar “Eh, ita din ce dai.”

Ita kam girgiza kai kawai take, ta dafe kanta da hannuwan ta biyu tamkar mai ciwon kai,

Shin wa ye ne Al’ameen? Ba dai Aminun Daddy ba? Yayan ta da ke karatu a Miami? Ta dubi mahaifinsu cikin yankewar buri bakinta na rawa ta ce,

‘Daddy wannan shi ne Al’ameen din ka na Miami?”

Tana nuna masa shi da yatsan ta Ibham, ya gyada kai tababcin shi din ne. Ta dubi Al’ameen bakin ta a bude ta kasa cewa komai, shi ma din kallon ta yake haka duk jama’ar da ke falon kallon su suke.

Ya kara matsowa gaban ta sosai cikin shakakkiyar murya ya ce,

“Me yasa ki ka yi min karya?’

Anty Saratu ta dubi Aminu ta ga yadda ya rikice, ta dubi Intisar ta ga yadda ta susuce tamkar wata kwarya-kwaryar drama ake yi a gaban ta, ta yi tsaki cikin takaici da tasowar wani tsohon bakin ciki mai tokarewa mutum a kahon zuci har ya rasa salama sai ya amayar da shi tukunna, irin wanda har abada mutum baya mantawa balle Uwa da ake cewa wai in maye ya manta…

Ta ce, ‘Al’ameen ko? Wannan Intisar ce, Saratu ce, diyata da ka yi ball da ita idon ta ya fashe, ka tuna? In kuma ka manta ne na ke tuna maka. Har yanzu bata gani sosai. Ke kuma Saratu wannan yayanki ne Al’ameen, tun kina karama ya tafi karatu shi yasa ba za ki gane shi ba, ko kuma ba ki san shi ba ma kwata-kwata.”

Intisar ta fasa kara mai firgitarwa ta ce,

“Wayyo Daddy, shi ne har muke shirin aure? Aminu fa har… ya ke yi…” Muryar ta ta kakare, sauran maganar makalewa ta yi a makoshin ta ta kasa fadin abin da ta yi niyya saboda wani makoko da ya zo ya tokare ta a makogaro, sai ta sulale daga kujerar da take kai bisa carpet a sume.

Ba abinda ke yawo a kwanyar Al’ameen kamar abu daya “…alkawari daya zan iya yi miki Hajiya ta, ba zan taba son ta irin son da Faisal ke mata ba!”

Ya kama kansa da hannunwan shi biyu yana girgizawa da karfi, ji yake abin tamkar a mafarki don haka yake fatan Allah ya taimake shi ya farka daga wannan mugun mafarki. Ya kasa daina gano ranar da ya dawo, ga Hajiyarsa a gabansa, yana yi mata wannan alkawarin, kalamun sun ki daina amo cikin kwakwalwarsa da karfi.

“Ba zan taba son ta irin son da faisal ke mata ba!”

Wai me yasa har kullum yake gamuwa da nadama mara amfani ne a kan Intisar? Kafafuwansa sun kasa daukar nauyin gangar jikinsa haka duk wata gaba a jikinsa ta rasa garkuwa, sai ya fada jikin Faisal yana fidda numfashi daidai. Kafin wani dan lokaci ragowar numfashin ya dauke kwata-kwata.

A guje Daddyn ya yi kan shi ya dago shi ya rungume a kirjin shi ya ce, ‘Al’ameen, don Allah kada ka mutu, me ya faru?

Me ke tsakanin ka da Saratu? Eye, ka gaya min mana?” Sai kuma ya sungume shi ya yi waje ‘yan uwan na mara mai baya suka sa shi a mota suka nufi babban asibiti.

In banda Faisal ba wanda ya bi ta kan Intisar. To kowa nasa ya sani, don haka Anti Saratu diyar ta ta dauka tasa a tata motar Faisal ya ja suka nufi wani asibitin daban. Tana rungume da Intisar din ta tana kuka. In dai soyayya ta hada wannan abu, to ta tabbatar rabuwar ta da Intisar din ta ne ya zo! Ta san Daddy ko don kada ya rasa dan da ya fi so a duniya sai ya gaya wa kowa akwai aure tsakaninsu, tsintar ta ya yi a daji ba su san ko ‘yar waye ba.

Ba ta tunanin komai illa rayuwar Intisar a gaba, da ta tabbata za ta kare cikin bakin ciki da takaici. Babu abinda ya kai rashin asali ciwo. Tsoron ta Allah, tsoron ta kada Saratu ta ce za ta tafi neman iyayenta. Tunanin hakan ya sa ta kara rikicewa da kuka.

Likitoci biyar ne a kan Intisar suna kokarin ceto numfashin ta, to haka shi ma Al’ameen oxygen ne makale a fuskar shi ga kuma likitoci rankatakaf a kan shi. “Yau ga likita a gadon likitoci kenan?” In ji babban likita Alfared don sanin waye Al’ameen.   

Farkon Labarin

Brigadier Bello Makarfi, ke kwance a bayan mota ‘Land-cruser’, sanye yake cikin korayen kakin sojoji hakan nan ya saya kwayar idanun shi cikin bakin gilashi mai duhu ainun. Ya bude wayar shi ‘Thuraya’ ya shiga aikawa da sako hedikwatar sojoji da ke Jos, a kan hanyar shi ta zuwa Kano daga Kaduna, domin halartar seminer da karfe uku daidai na yammacin ranar a can Kano din.

Ya kammala maganganun shi ya rufe wayar ya maida aljihu kana ya dubi direban shi ya ce,

“Karo mun karfin A.C Sam.”

Sai da ya kame kana ya karo, can ya kuma cewa, “Sam.”

Direban ya sake kamewa tamkar wanda aka yi wa allurar zuke jini ya ce, “Yes Sir.”

“Idan ka fita kauyen nan ka tsaya a nemi wuri in yi sallahn Azuhur, ga shi har biyu na neman shiga.”

Yana magana cikin harshen Turanci ne a gurguje. Direban da ya kira Sam ya amsa a ladabce, a zuciyar shi yana mai jinjina tsantsenin Addini irin na ubangidansa ko kadan baya wasa da lokacin sallar sa koda a filin daga yake.

Daidai hanyar na fita wani kauyen Fulani wai shi Shanono, direban ya tsayar da motar karkashin wata bishiyar darbejiya sassanya ga ‘ya’yan ta yalo shar duka sun nuna sun zuzzubo kasa abin sha’awa sun cika wajen, sai suka kawata wajen kwarai.

Ya bude but din motar ya fiddo katuwar darduma kana cikin zafin nama ya budewa Ogansa kofar owner side, shi ma ya fito rike da doguwar tazbahar sa koriya. Sam ya nemi wuri zai shimfida dardumar a karkashin bishiyar amma sai me? Tsalle ya buga gefe daya cikin matukar razana a gigice ya ce, “Oga… Oga… na beb… baby.”

Ya ce, “Kai wane irin shashasha ne, me ka ke cewa?”

Ya ware iyakacin katuwar muryarsa ya ce,

“I said there’s baby here, come and see for urself, nawaho!”

Brigadier ya kara taku, ya isa ga yaronsa ya ga yadda ya bi duk ya firgice har ya manta dawa yake magana yake kuma yiwa tsawa.

Kana ya dubi inda ya mannawa ido tamkar sa fado, da gaske yake, jariri ne ko jaririya jazur da shi kwance cikin zanin saki, yatsun shi duka biyun cikin baki yana tsotso tamkar ya samu nonon mamarsa, alamun hakuri kenan, yana wutsil-wutsil da hannayen shi cikin koshin lafiya da gani ka ga haihuwar Fulanin usli, domin ko’ina a jikinsa jawur yake.

Ya kira yi sunan Allah Al’ Aleem kana ya russuna ya dauki jaririn da Bismillah a bakinsa don shi kansa ba karamin kaduwa ya yi ba, don dai jarumin soja ne kawai.

Sam ya kwalla kara don bai ga dalilin da ubangidan sa zai yi wannan kasadar ba, idan kuma dan aljanu ne fa? Karar da ta firgita jaririn ya tsandara kuka mai firgitarwa, cikin tsawa ya ce da Sam.

“Shut up!”

Tuni ya koma cikin nutsuwar shi, ya rungume jaririn tsan-tsan a kirjin shi ya dubi gabas, ya dubi yamma, kana kudu, sannan arewa. Ba motsin wani mahaluki in ka dauke karar tsilli-tsillin motocin da ke giftawa a kan titi jefi-jefi.

Mutanen yanzu, anya suna son gamawa da imani?

A zo dajin Allah, ba gida gaba ba gida baya a ajiye jariri, wanda bai san ma abinda duniyar take nufi ba, a gudu, don kurum son cimma wata manufa ta duniya ko ko don gudun abin kunya? Shin kunyar duniya har ta fi ta lahira?

Ai shi kenan. Da ai na kowa ne, don haka ni ina so, zan kuma rike tsakani da Allah. Kai Sam dauko dardumar nan mu koma Kaduna.”

Magana yake shi daya tamkar zararre, takaicin al’umma ne cike da ransa har bai san yadda zai kwatanta ba.

“Oga da tsintaccen baben?”

‘Yes?”

‘Oga Seminar fa?”

Cikin tsawa da gajiyawa da banzayen tambayoyin da yake ta jero masa ya ce, ‘Na fasa ko dole ne?”

Bai kara magana ba, amma duk jikin sa babu inda baya rawa tamkar ana kada masa gangi. Sam kam ko za a kashe shi ko yana hauka ba zai dauki dan da bai san ko na waye ba!

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

6 thoughts on “Siradin Rayuwa | Babi Na Tara”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×