Skip to content
Part 18 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir Takori

Sanye ta ke cikin danyar atamfa Super English, ruwan kwai da aka yi wa ratsi da shudi da jaja-jaja, atamfar ta yi matukar amsar dan kyakkyawan jikin ta, an yi mata dinki zani da riga fitted kanta babu kallabi, maimakon haka ta daura shi ne a kan cinyar ta, gashin kanta wanda yake curl a sake yake bisa dogon wuyan ta, sanyin air-condition ya kara taimakawa ainun wurin kara kwantar da shi lub-lub a wuyan ta kamar ba abin da ya dame ta.

Sai dai ta yi ‘yar rama wanda hakan ya kara mata kyau, fuskar ta fes, da ruwan hoda chiristian dior da take amfani. Sai kawai ta ji an rufe mata ido daga baya, ta lumshe ido ta yi ajiyar zuciya ba ta bari a kasa ba ta ce,

“Daga jin kamshin 5000 Doller na san Ya Faisal ne, wani Bayarabe mazaunin Illorin.”

Faisal ya yi dariya, ya dube ta gaba daya yana kiyasta adadin ramar da ta yi, hannuwan shi a cikin aljihun wandon shi, ya ajiye gwiwoyinsa a carpet ya zaro hannun shi daga aljihu ya tallabi habar ta ya ce, ‘Baby, are you still… still at home?”

Hawayen da take ta tattali ne suka kubce sharrr! Haushi ya ba ta kamar ta doke shi, ta kai hannu ta sauke hannun shi a habarta ta maida hankali ga abin da takeyi. Ta tabbatar sakon ta ya tafi ga Raadha, tana yi tana share hawayen da suka jika mata kundukuki da yatsun hannun ta.

Ba wanda take tunani a wannan lokacin sai Daddy. To bata san kuma me za ta ce da Faisal ba, ba za ta iya gaya masa mai dadi ba, shirun shi ne mafi amfani.

Ai ko albarkacin makwabtaka, bar ta kasancewar ta kanwar ubansu, ba ma na uban da ya hada su a gidan ba, sa dinga taimakon Aunty Saratu.

Su ‘ya’yan Hajiya uwar su mai gwal, don haka duk suka koma makaranta suna batar da kobo yadda ransu ke so, turaren Faisal kadai ya isa su shekara suna cin abinci ita da uwar ta.

Ba a maganar agogon diamond da ke daure cikin lafiyayyar fatar hannun shi wanda ya isa ya maida ta Riyadh har da canji!

Su ko Allah Sarki, ko abinci sai sun je kasuwa da kansu sun sayo. Amma shi ne wai don rainin hankali yake tambayar ta har yanzu tana gida? To sun ba su wani abu ne ko da cikin dukiyoyin Daddyn da Hajiya ta tattare ta boye?

Tasa dankwalin atamfar da ke bisa cinyar ta ta share ido, a sanda ta jiyo Najib na gaisawa da Aunty, wai ga buhun shinkafa nan za a shigo mata da shi, tana jiyo sanda Antin ta ce cikin fara’a, “Lah! Ku bar shi kawai, don can da yara muku nan mu biyu ne kacal, ba zamu rasa abin da za mu ci ba don ba Alhaji.”

Ta sake tunzura, ta mike ta kashe kwamfutar ta yi daki fuuu! Har tana tuntube da kujera. Ita dukkanin su ba ta son ganin ko daya duk selfishes take ganin su wato masu son kansu kadai. Faisal ya zamo wani irin pale (Mara kuzari) tamkar ya mtu, ya kasa motsa ko da dan yatsansa, da kyar muyarsa ta fita can kasan makoshi.

“Intisar na so ki tsaya ki fahimci ba wai…”

Tuni ta fice. Faisal bai yi wa kowa sallama ba a ranar ya koma Ilorin. Bai ko ji tsoron tafiya mai nisa haka cikin daren ba, a hanya ya kwana, kar ki so ki tona zuciyar wannan aminin Intisar.

An sanar da Anti tana da baki sati biyu bayan faruwar wannan. Ta sha lullubi ta iske su a sassan baki su biyu duka maza, ta sha mamaki da ta ga Larabawa ne na usil bakin nata.

To an yi sa’a ita ma ta dan iya larabcin a bakin Intisar, nan suke gaya mata su shuwagabannin shashen da diyar ta ke karatu ne a Kingston da ke Riyadh.

Sun zo Nigeria ne musamman don abu biyu, na daya kafa reshen makarantar su tare da Jami’ar Bayero da ke Kano, na biyu, sun yi amfani da adireshin su Saratu don su zo su ji ko lafiya, suka katsewa hazikar yarinya kamar Sarah da ake wa hangen great achiever a gaba karatu? Ya kare da cewa.

“Saratu in ta kammala karatu, ba ma nufin kasar Saudiyyah ta amfana da ita, face kasar ku da za ta sami dumbin amfani daga gare ta.”

Aunty Saratu ta gode masu, for their concern kan al’amarin diyar ta, kuma hakika ta ji dadi, sai ta ce, da su ko Saratu za ta koma Riyadh to ba yanzu ba, saboda ba za ta iya affording cost, din ba. Babanta yana kulle. suka nuna matukar juyayi, dayan ya ce shi da Saratu tamkar diya da ubanta suke a makaranta, shi ne Dr. Alhassan As-Sayyid malamin Chemistry din su, don haka zai ci gaba da daukar nauyin karatun Saratu daga sakandire har jami’a amma fa in sun amince.

Aunty Saratu ta dade da daukar wata wasiyya ta mahaifinta kan ‘dogaro da kai, shi ne babbar siyasa’, amma bata nuna masu ba.

A karo na farko ta yi sha’awar gwada hankalin Saratu, sai ta yi ta yi masu godiya ta ce amma bari ta je ta ji ta bakin Saratun tukunna, don bai yiwuwa ta ari bakin ta ta ci mata albasa, suka ce alright.

Inteesar kwance tsakiyar ni’imtaccen gadon ta tana mai fuskantar ceiling idanunta a rufe ruf kamar mai barci, zuciyar ta cike da kuncin Ya Faisal da Najib. Aunty ta tsaya a kanta ta yi murmushi ta ce, “Har yanzun haushin Faisal din ne? Alhalin sam ba shi da laifi Saratu, kudi fa uwarsa ke da su ba shi ba, a kan me za ki dauki laifin duniya ki dora masa? Sata kike so ya je ya yo ya maida ki makarantar ko me? Bayan ma Allah ya yi mana ludufi?”

Ta juyo ta dube ta cikin ido,

“Daddy ya fito?” Ta fadi da wata irin shanyayyar murya.

‘Tukunnah, ki san wani Dr. Alhassan a makarantar ku?’ Ta zabura ta zauna daidai, ‘Chemistry teacher na da nake ba ki labari mai yi min wakar Saratu is doing research, kin tuna? Ya kula da rayuwata sosai a duk zamana na shekaru biyar a Riyadh.”

“To shi ne ya zo yanzu tare da wani Abraham Shaikh, sun ce ki bi su ku koma makarantar zai ci gaba da daukar dawainiyar karatun ki har zuwa mu ga abin da Allah zai yi.”

Saratu ta yamutsa fuska ta ce, ‘Kash! Ya kawo taimako a sanda ba ni da bukatarsa. Dama dai ya ce zai taimaka ne a fiddo mana Daddy, Akbar min zalik (abobe all) Mamar mu ba zan iya tafiya in bar ki lonely cikin irin wannan halin da muke a yanzu ba, ba zan iya karatun ban san halin da Daddy ke ciki ba.

Don Allah Mamar mu ki ba malami na hakuri, ni wallahi ba zan bi su ba……”

Sai tasa mata kuka da baya mata wuya tun farkon faruwar al’amarin kamar sun ce za su ja ta ta karfi ne. Aunty Saratu ko so da kaunar Intisar ke kara tofo a zuci da gangar jikinta. Ta gode Allah da bai ba ta dan kanta ba, mai yiwuwa da ba zai ji kanta kamar ‘yar da ba ta san ko ta waye ba.

Da kyar ta lallabi Dr. Alhassan amma ya ce duk san da suke neman taimako kan karatun Saratu a shirye suke da su taimaka ta kowanne bangare. Har adires din sa ya basu na Riyadh, inda yake aiki da Turkey kasar haihuwar shi inda yake zaune da iyalin shi. Ga yadda Antin ta karanci zuciyar Dr. Alhassan ma kadai ta fahimci matukar kaunar Saratu yake, kauna ta hakika kuwa, ba ta malami da dalibi ba.

Bello ya zo ya yi week-end a Abuja wannan watan. Ya ba baby wasikar Faisal da ya ce shima ta zo mai ne daga post. Da ta ki karantawa, sai da ta ga bacin ran mamar ta tukunna.

“To Mama dauko min gilas dina.” Hajiya Saratu ta yi dariya ganin yadda ta zobara baki gaba (hakan take yi idan Faisal ya ba ta haushi), ta je ta dauko mata gilashin da kanta, ta sa hankici mai tsabta ta goge mata kwarmin ‘yan lumasassun idanun ta, kana gilashin, kafin ta manna mata farin siririn medical glass din ta.

Broken heart!

Na sani, duk bayanin da zan yi ba zai gamsar da ke ba Intisar, amma kafin nan, ina farawa da baki hakuri, Allah shi ne shaida, na fi ki damuwa da rashin komawar ki karatu.

Ni kaina abubuwan da Hajiyar mu ke yi bana son su, to amma kin san ba yadda zan yi, tunda Hajiya mahaifiyata ce. A da ban yi niyyar gaya miki ba, sai don gani da na yi kin yi min wani fassara na daban a zuciyar ki. I try my best (na yi iya kokarina) in samu ko da takardar motar Daddy guda daya in saida, ki koma makaranta. Hajiya ta hana, har tana ikirarin tsine mini, idan na sake sa baki kan harkar karatun ki.

Intisar abin da ban taba tsammani ba (ko a mafarki) wai Baby ki ka ki saurarena a kan wani (matter) da ki ka san ba ni da iko. Amma kin san Allah ko da zan yi yawo ‘in nude’ (tsirara) ne, sati mai zuwa za ki koma makaranta.

Daga Yayan da baya da laifi.

Ta lumshe ido abin tausayi, tausayin kanta ne ko ko Ya Faisal? Ita kadai za ta iya kiyasta halin kuncin da zuciyar Faisal ke ciki a yanzun kan wannan al’amari. Ta sani idan da abin da Faisal ya ki jini a rayuwarsa ba kuma zai iya jurar sa ba. To bacin ranta ne.

Ta san a duniya daga Daddy, Mamar ta, sai Ya Faisal a masu kaunar ta. Ta kai duban ta ga Aunty Saratu da ta yi tagumi tana kallon ta, ta yi murmushin karfin hali.

“Kin ji abin da Ya Faisal ya ce? Cewa ya yi ko da a ce zai yi yawo tsirara ne, wai sati mai zuwa zan koma Riyadh, kuma wai kin ji ashe Hajiya ce ta hana su ba mu komai na gidan nan? Shin Mama me na yi wa Hajiyar su Khalil ne ta tsane ni? Me na ke mata? Kin san Allah tunda nake a rayuwata, ban taba gaishe ta ta amsa ba, ban taba shiga sashin ta ba ta zage ni ba, ban…..” Sai ta sa kuka.

Aunty Saratu ta rasa ma me za ta ce? Tunani goma da ashirin ya yi mata rubdugu. Me za ta ce da Saratu wanda ya jawo mata kiyayyar Hajiya Nafi? Ta tsane ta don tsinto ta aka yi? Ta tsane ta don kaunar da Daddy ke mata sama da ‘ya’yanta? Ina! Ko za a daura mata bindiga a wuya ba za ta taba furtawa Saratu ba ita ta haife ta ba! Ba tun yau ba ta san Saratu tana da zuciya a kan komai.

Da suke yara in Khalil ya ba ta abu, daga baya ya dawo ya ce ta ba shi, sai ta cilla masa ta ce, ‘GA tsiyar ka nan. Ni ma Allah zai ba ni.”

Ba kuma za ta kara duban abin ba ko da ya yar daga baya balle ta dauka.

To haka abin yake har girmanta. Duk wani abu da ta san zai taba mutuncin ta tana gudun shi tana kyamar shi tana yin nesa da shi balle rashin usli? Ta girgiza kai cikin jin wata sabuwar kaunar yarinyar da ta ratsa ta, ta kada harshe ta ce,

‘Saratu in Maman Khalil na bada rahma, don Allah in ta zo kan ki kar ta baki, in ce ko karshen ta kenan?” Ta yi murmushi tana share idon ta da hankici ta ce, “Karshen ta kenan fa Mamar mu.”

Ranar Juma’a bayan an sauko sallar Juma’a, Faisal ya iso Abuja kamar yadda ya saba. Sanye yake cikin ‘yar ciki da wando ga kuma babbar riga ya ratayo a kafadun shi na babbar shadda Wagambari ruwan sararin sama mai haske (sky blue) wadda ta taimaka ainun wurin kara fiddo gogaggiyar choculate colour fatar shi mai sheki. Duk ‘ya’yan Hajiya Nafi haka suke kamar half cast kasancewarta usli Shuwa ce. Kira kamar well-fed Americans ga tsayi ga zati tamkar Babansu.

To shi Faisal karan hancinsa har wani rankwafawa ya yi kadan saboda tsayi. Kowannensu ya mallaki diggunan beauty point biyu in ka dauke Al’ameen mai guda daya a gefen kuncin sa na hagu kawai kuma shi kadai ne da cleabe wannan dan digon na tsakiyar haba yayin magana ko murmsuhi. Faisal akwai son turare (5,000 Doller), inda duk ya yi za ka ji daddadan kamshin na bibiyar shi. To haka yau ma.

Ya kalmashe cikin ‘yar lallausar kujerar computer Intissar yana kallon ta sai fama take da dogon gashinta mai santsi, ita a la dole sai ta yi kalba, ta yi ya warware, ta sa roba ta matse bakin ya sabule kamar ba ta san Allah ya yi halittar shi a dakinta ba ma.

Ba don ta girma ba, da ya amshe ta, don wannan aikin shi ne, tun tana goye, sai da ta kai aji uku shi da kansa ya bari. Ko ta yi ta yi ya gyara mata sai ya ki, ya ce shekarun ta sha biyu ta gyara abun ta. Shi kadai ya san me yake ji tun lokacin game da Baby. To balle a yanzun da ta zama cikakkar budurwa ‘yar sha bakwai, komai ya ji Tubarakallah, komai na ta ya kai ya kawo, ya yi wa fuska da zubin halittar ta daidai.

Ga ta nan dai tamkar kwalbar nan ta coca-cola mai sanya kan duk wani hadadden namiji juyawa.

Kan shi kuwa ke juyawan ta ko’ina, wani irin abu ne ke ratsawa tun daga kwakwalwar shi har yatsan kafar shi game da Saratu a yau, barin yanzun da take sanye cikin wata jar matsatstsiyar riga fara sol da ratsin baki-baki samfurin (Dolce & Gabbana) da bakin dogon siket din jeans, to amma wannan kanwarsa ce fa da suke uba daya? Sai ya yi saurin korar shaidan a zuciyar shi ya rintse ido yana jan Hasbunallahu wa ni’imal wakeel, ni’imal maula wa ni’imal naseer, allahumma ajirni fi musibati hazihi wakhlif ni khairan min ha” har ya samu hakan da zuciyar shi ke yi ya lafa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.6 / 5. Rating: 22

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siradin Rayuwa 17Siradin Rayuwa 19 >>

9 thoughts on “Siradin Rayuwa 18”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×