Skip to content
Part 14 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir Takori

Littafi Na Biyu

Ameenu kishingide cikin lallausar kujerar asibitin Saudi-German, nadama goma da ashirin ji yake kamar ya farkewa Daddyn shi komai, in ya so ya nemi gafarar shi, ko ya samu saukin wannan dumbin hakki da ya dauka na rayukan al’umma da dama, na kuma yarinyar da ba ta ji ba ba ta gani ba, ba ta kuma tsare masa komai a rayuwa ba.

Lokaci daya ya ji ya tsani kan sa kai da duk ‘ya’ya masu irin halin shi na taya iyayensu mata kishi. Amma tsoron hukuncin da Daddyn zai dauka a kan shi ya hana shi, gani yake kamar ma ya san shi ne sanadiyyar shigar diyar shi cikin wannan azaba shiru kawai ya yi masa, watakila ma kuma idan ya fada masa shi din ne ya tsane shi, hakan kuma ya yi sanadiyyar jawo masa bacin ran Hajiyar shi.

Ya yi tunani iyaka tunani, ya rasa mafita cikin al’amarinsa, tunda kuwa ya zama fitina kenan ga iyayen shi? Daga karshe ya yanke abinda yake ganin shi ne mafi dacewa a gareshi shi ne ya bar su kwata-kwata ya fita daga tsakanin su, ya yi nisa da rayuwar su, ya bar masu kasar baki daya ya je ya ginawa kansa sabuwar rayuwa mai amfani. Me ye amfanin ‘ya’ya irin sa masu sanya iyayensu cikin halin ha’u’la’i? Babu.

Kada ma ya je Hajiya ta angiza shi ga kisan kai, don ma abin ya zo da sauki? Da ta mutu fa me zai ce da Ubangijinsa? A kan wani kishin su na mata wanda shi bai shafe shi ba.

Tunaninikan da yake ta yi kenan har aka fiddo Intisar daga dakin tiyatar da karfe biyu da rabi na sulusin dare agogon su na can. Ya tsaya a kan ta yana ta muzurai ganin yadda aka nannade dukkan idanunta da bandeji, jikinsa ya saki gaba daya.

Washe gari likita Doctor Khair ya tabbatar wa Daddy Saratu za ta gani da taimakon medical glasses kanana da za su yi mata. Bayan sati biyu da yin aikin aka cire bandejin da addu’o’i na musamman a bakunansu don Daddy har Dawafi na musamman ya yi a kan lafiyar Intisar kadai.

To Alhamdulillahi Saratu na gani daga kusa-kusa, sai dai ba ta iya gane abin da ke nesa da ita tangaran abinda a turance suke kira short eye-sight.

A ranar Dr. Khair ya manna mata farin siririn medical glasses tamkar gidan biro don siranta garai-garai da shi kamar na ado, wallahi kada ki so ki ga yadda ya karawa yarinyar nan wani irin kyau da kwarjini, da aka sa mata sai ta kama dariya.

Daddy ya kashe kudi ba kadan ba, amma wannan ba shi ne damuwarsa ba shi dai burinsa kada a ce Saratu ta rasa ganin ta kwata-kwata. Don haka da ya tabbatar tana gani tar da gilashin in an cire ne take gani dusu-dusu sai ya gode Allah.

A ranar da suka cika sati na biyar suka dawo. Anti Saratu duk ta rame ta yi duhu saboda zullumi. A guje Intisar ta rungume Mamarta suka shiga juyi a tsakar gidan har suka bai wa kowa da ke wajen tausayi.

Tana gaya mata labarin Daddy ya saya mata gilas mai kyau, za ta ke ba ta aro tana danawa, yaya Aminu yana ba ta abinci a baki baya tsula mata carbi a unguwar da suka je. Yayin da Ameenun ya yi tsaye harde da hannunsa bisa kirji yana kallon su cike da jin nauyi ko kadan bai bari sun hada idanu da Antin ba, tunda suka dawo. Antin ta dube si ta watsar ta ce, ‘Al’ameen kenan. Kai ma sannu da kokari.’

Yanayin yadda ta fadi maganar cikin gatse, dole ta sa shi ya yi murmushin dole har cleft din ya lotsa, ya kuma sha jinin jikin sa, ji yake kamar ya ce da kasar ta tsage ya shige, ji yake kamar Anti Saratu ta san shi ne sanadiyyar nakasar diyar ta.

Haka kurum Daddy ya aika takardun retire (murabus daga soja) Abuja. Ko kadan Al’ameen bai so ba, domin yana tunanin Daddyn ya yi hakan ne domin ya yi joining su Benga Delsu da ke son yin juyin mulki cikin ‘yan shekaru kalilan. Bakin ciki biyu kenan ya hadu ya tarar masa. Ga nadamar abin da ya aikata, wadda ta sa har ya tsani kansa da kasar haihuwar shi baki daya, ga kuma bakin cikin Daddyn su zai zubar da mutuncin su a idon duniya.

Ran shi a masifar bace ya sake bijiro da bukatar shi na tuntuni, wato na son tafiya karatu Miami, ba tare da ya tambayi Daddyn dalilin shi na yin ritaya ba. Daddyn ya ce ya je duk abin da suka shawarta da mahaifiyarsa shi ba shi da ta cewa. Da kyar Al’ameen ya shawo kan Hajiyar ta amince da tafiyar shi sai dai ba ta amince mai zuwa America ba, duk wani Musulmi na kwarai yana neman tsari daga sharrin wannan kasa, amma ba wai ya yi marmarin kai kansa ba, ba mamamki ya mance kasar haihuwar shi Nigeria ce, birni irin Miami?

Birni ne na hutu zallah, yana daya daga cikin biranen da kasar Amurka ke takama da su, saboda kasancewar shi wani bangare na kara bunkasar tattalin arzikinta (tourist attraction) sabida yadda al’ummar duniya suka zabeshi a matsayin wajen hutun su (Miami resort) ga kuma kashe Musulmi da kasar Amurka ke yi a lokacin.

Ta ce ko dai (ELT Banbury) wato Ealing Tertiary da ke England ko Hull Unibersity (duka Britain ne), hankalinta zai fi kwanciya, in kuma duk ba su yi masa ba to ya tafi jami’ar Abuja. Ya amince zai tafi Hull ne kawai a fatar baki amma can a karkashin zuciyar shi ya kudurce a Miami zai karaci gaba dayan sauran rayuwar shi har mutuwa, ba don jin dadin da ke cikin birnin ba sai don wani specific reason (kayyadadden kuduri) nashi na daban.

Duk wasu shirye-shirye na tafiyar Al’ameen, shugaban kasa na lokacin wanda aminin Daddy ne na kut da kut tun suna NDA shi ya yi wa Al’ameen, ga inda Daddy ya ce a kai shi, amma Al’ameen ya zage ya ce da shugaban Miami ne. Akwai kudi na musamman da kasa za ta ke tura masu duk shekara a matsayin su na ‘yan kasa masu karatu a waje da alkawarin dawowa su yi wa kasar su aiki.

Ran Al’ameen a masifar bace ya bar Nigeria zuwa U.S inda daga nan ya nemi hanyar birnin Florida, a inda ya sami gurbi a babbar jami’ar Miami inda aka yi admitting din shi into lebel 1 Medicine.

A shekarar shi ta biyu a Miami rannan ya ji a tashar BBC cewa an yi juyin mulki a Nigeria. Tunanin Al’ameen kawai shi ne har da Daddy din shi wanda yana ganin wannan karshe zubar masu da martaba da daraja ne Daddyn ya yi tunda har abada ya bar masu abin fadi, ba kuma ya cikin tsari na abin da ya koyar da su.

Aminu ya yi kuka ya yi kuka har ya gode Allah, kukan da bai taba tsamamnin zai taba yi ba a rayuwarshi. Ya alkawartawa ransa shi da gida Nigeria har abada! Ko ya gama karatun shi nan zai nemi aiki ya yi aure ya yi zamansa.

Ya manta Allahu shi ne mai juya al’amura yadda ya so. Ya je ga kwamfuta ya zanowa mahaifin shi sako yana fitar da zafafan hawaye (sanda na rubuta wannan littafi ilmin yanar gizo bai yi sauki da yaduwar da yayi a yanzu ba haka sadarwa ta kwamfuta ba kowa ke yin ta ba) na dalilin da yasa ya bar Europe zuwa U.S shine don kar suke samun koda labarinsa, a ganin sa ba shi da sauran amfani a gare su. Ya yi matukar nadamar wani gagarumin laifi da ya yi wa Daddyn shi ne zamowar shi sanadiyar nakasar Inteesar diyar Anti amarya.

Ya kuma nuna karin dalilin shi na yin nisa da su saboda bakin cikin abin kunyar da yake tunanin Daddyn ya jawo masu. (Kaico! ‘Ya’yan yanzu har mun fi iyayen mu tunani da sanin abin da ya dace su yi? Mun fi su sanin abin da yake mai kyau a gare su? Anya Aminu bai yi kuskure ba?) A karshen sakon sa ga abin da ya ce duk dai mai nuna tsantsar nadamar sa kan abin da ya aikatawa Intisar ko ko nadamar shi da ya kira mara amfani.

“Now, plz, don’t think I feel I’ve overcome all these regrets, I’ve not. I am one of those people that have to-day-to-day job on myself. But gradually, by trying to follow your teachings, I’m learning to control myself and be less critical of my fellow human being. And, it’s like being released from a prison. I just never dream that life could be so full and wonderful as earlier. Sincerely. (Sai ya yi signing din shi a kasan signing din ne ya rubuta).

Mohammad Al’ameen Bello.

Ma’ana: A yanzun haka kada ku dauka ko na yi nasara ne a kan dumbin nadamar da na yi, ban yi ba. Ina daya daga cikin mutanen da ke duba rayuwar su ta yau da kullum a kan-kan su. Amma a hankali, nan gaba ina kokarin in bi koyarwarka, ina koyon yadda zan ke sarrafa rayuwata in kuma zamo mara kushe da hassada ga kowanne dan adam dan uwana. Sai kuma hakan ya zamto tamkar fita ne daga kurkuku. Na san dai rayuwa ba za ta taba zama cikakka kuma mai dadi ba kamar da.

A ranar Anti ke da Daddy, yana bisa kwamfuta yana duba sakonnin shi, yawanci abokan aikin shi ne ke yi masa korafi da nuna rashin jin dadin su na ritaya da ya yi da wurwuri, da sauran karfin sa da komai ga wadatacciyar lafiya. A kuma lokacin da ake mai hangen isowa matakin General, cikin ‘yan shekaru kalilan.

Shi ko Brigadier Makarfi ko kadan ba su san tsarinsa ba, baya da wani nufi illa ya samu lokacin kula da iyalin shi da sa ido sosai a kan tarbiyyar su, tare da fantsamawa mahaukacin kasuwanci don neman abinci, wannan shi ne kadai dalilin shi na yin ritaya, amma ba wai don wani dalili na daban ba.

Kwatsam sakon Al’ameen ya bayyana jikin screen , ya karanta ya maimaita fiye da cikin carbi amma bai fahimci abin da yaron ke shirin bayyana masa ba.

Ba inda suka ce ya je ba ya je, kuma shi ya yi sanadiyyar nakasar idanun Saratu? Ya kai duban sa ga sashen da Aunty ke kwance tana karatun littafin addu’o’i na Al’ma’asurat da take karantawa duk dare kafin kwanciyar barci, ta kare tana kishingide jikin tuntu da alama cikin dogon tunani take, ya ce, ‘Saratu kin yi barci ne?’

Ta muskuta kadan don ta gyara jin dadin kwanciyar ta ta ce, “No, ina tunanin secondary din da ya dace a kai Saratu ne. Sanin kan ku ne Brigadier dole Saratu ta ci gaba da samun ingantaccen ilimin da ta faro da shi, to makarantun nan na Lagos duka babu na yarwa, amma tarbiyyar Saratu nake ji.

Duka makarantun cakude suke maza da mata kenan hakan nan za ta tashi girman Lagos? Abin nufi, ba tarbiyyar Musulunci ba tsarin Addini balle al’adun mu na Hausa?”

Ta yi shiru kadan ba tare da ta dube shi ba, can kuma ta ce,

“Brigadier, ni dai don Allah ina neman alfarma, ina da account mai nauyi, amma dole sai da taimakon ku. So nake in kai Saratu makarantar kimiyyah ta harshen Larabci da ke Riydh ne.”

Daddy ya yi shiru bai amsa ba, tsawon lokaci yana nazarin zancenta, ya kama kan shi da ke faman sarawa tamkar ya rabe gida biyu ya ce, ‘Zo nan Saratu, ki karanta min abin da Al’ameen ke cewa da kan ki watakila na fi fahimta.”

Jikinta ya yi mugun sanyi da ganin Brigadier hawaye yake fitarwa, ita ma ta karanta sakon Ameenu a fili cikin nau’in turancinta (British accent) da ta samu a shekarunta hudu a Edeter, ita ma ta kasa cewa komai, sai dai bata dimauta ba kamar mijinta. Daddy ya share hawayen da ke bin kwarmin idon shi, tausayin Intisar ne kurum da karin kaunar ta tattare da shi.

Tun da yake da ‘yar yarinyar nan babu abinda ba ta gaya masa, amma ko sau daya ba ta taba budar baki ta ce da shi Aminu ya ko dungure mata kai ba. A tun ranar da ya dauko ta, ya ga alamun hakuri a tare da ita, yatsun hannayenta duka cikin bakinta tana tsotso, irin su ne ake kira ‘damo sarkin hakuri.’ Hakuri ne da ita tun tana tsumman goyon ta.

‘Anya zan taba yafewa Aminu? Mene ne dalilin kashe Saratu da ya so ya yi? Me yake nufi da kin bin umarnin mu ya tafi inda ransa yake so? Anya Al’ameen jini na ne kuwa? Yau dan cikina ke zargina da abin da ya san ko a mafarki ba zan taba aikatawa ba?

Duk kaunar da nake masa a yau sakayyata kenan, ai shi kenan in dai duniya ce ya je ga shi nan ga ta, wanda bai zo ba ma tana nan tana jiran shi. Allah idan har akwai hakkina akan Al….”

Aunty Saratu ta yi sulu ta rufe mai baki da tausasan yatsun ta, ‘Kada ka yi haka Baban su Khalil, kada kai ma ka yi abin nadamar. Ni dama tuni na san Ameemnu ne ya yi kwallo da Saratu a bakin Emma, lokacin Aminun bai san yana durkushe yana wanke tayoyin mota ba, amman ban ce komai ba.

Ba don komai ba sai don na san komai Al’ameen ya yi sa shi aka yi, kome ya yi, ya yi ne a dalilin son Mamarsa, a kuma cikin taya mamarsa kishi, amma ba halin shi ba ne.

Ba tun yau ba na san Al’ameen shi kadai ne ya gado Babansa a wurin tausayi da jin kai. Tun da har ya yi nadama da ta dame shi irin haka baka yafe masa?

Mu fa iyaye har kullum da afuwa aka san mu ga ‘ya’yanmu, domin fushin mu a gare su ba karamin nakasu ne ga rayuwar su ba. Lallai ne a yau Ameenu ya nuna ya cika Al’ameen trustworthy, wato (Mai gaskiya).

Kuma tafiyar shi Miami ni a ganina ba wani abu ba ne, abu ne na kuruciya. Ina da yakinin cewa Ameenu zai dawo a lokacin da ka ke tsananin bukatarsa. Dama can Allah ya rubuta Aminu zai gama da kiyayyar Saratu a rayuwarsa, za kuma ta hadu da lalurar ido ta dalilinsa.

Amma ka sani, sai dai in tunatar da kai, Daddyn Ameenu, wani baya dorawa wata rai abin da Allah bai daura mata ba.”

Ta yi shiru, don ganin irin tasirin da maganganun ta suka haifar, ba shakka ta ga tasirin su sosai a tare da shi. Kanta ta daura bisa kafadun shi ta ce cikin ‘yar karamar murya,

“Brigadier, me ka ce game da karatun Saratu a Riyadh?”

Budar bakinsa sai ya ce,

“Ai ni kin gama da ni Saratu, banida wani tunani sai naki, ba ni da wani hukunci sai wanda ki ka zartar don nasan ba za ki taba yanken gurbatacce ba. Ba ni da wani buri sai na yau a ce Saratu ta yi ilimin da al’umma za ta amfana da ita, ba don komai ba sai don in nunawa wadanda suka yasar da ita a daji muhimmanci da darajar da Allah ya yi wa dan adam, amma suka wulakanta shi. Fatana, Allah ya ba ni tsawon rai, ba ni son ku wahala ko kadan a rayuwa.”

Ita kam Antin ba ta ga dalilin maganar da Daddyn yake yawan yi mata ba, na baya son su wahala, tana ji a jikin ta har su mutu ba za su taba wahala ba, to me ma zai wahalar da su?

Kudi, suna da su kamar su tada kai da kafa da su, kwanciyar hankali kuwa sai dai su samma wani. Saratu ta yi kuskure, komai na rayuwa mai canzawa ne, akwai wanda ya wuce jarrabawar Ubangiji a wannan duniyar? A kuma cikin wannan rayuwar mai siradi iri-iri? To bari mu bi su mu gani, don kuwa an ce ‘gaba ta fi baya yawa.” 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.6 / 5. Rating: 24

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siradin Rayuwa 13Siradin Rayuwa 15 >>

8 thoughts on “Siradin Rayuwa 14”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×