Shopping Cart

Close

No products in the cart.

Siradin Rayuwa 2 by Sumayyah Abdulkadir

Siradin Rayuwa 2 | Babi Na Hudu

<< Previous

Najib ya fashe da kuka, ‘Faisal, anya wannan Yayan mu ne da na sani mai so da kaunar Daddy?”

Shi ko Al’ameen ba su san a halin bakin cikin abin da ya ke tunanin mahaifin su ya aikata ne ya furta wadannan kalaman ba, a ganinsa me Daddy ya rasa a rayuwa da zai tsunduma kan shi cikin irin wannan masifa in ban da rashin godiyar Allah? Har nawa duniyar take da zai bari neman mulkin duniya ya rinjayi imanin shi?

Kudi dai na gwamnati albarkacin aikin soja bai san wane iri yake so kuma ya yi ba. Ya manta cewa, “Kalmomi da alkawarirrikan da aka yi su cikin fushi, kamar cin wuta suke, ba za ka taba iya maida barnar su ba.”

Daga Faisal har Najib sun ce a kyale Ya Aminu ya yi yadda yake so. Allah zai fidda Daddy ne ba sai da taimakon sa ba.

Ranar Asabar Baffa na Makarfi ya zo da malamai kimanin guda goma aka bude masu nan sashen baki, sati guda suka share suna saukar Alkur’ani mai tsarki, an yanka raguna har ba iyaka an yi sadaka haka sauran abubuwan sadaka iri-iri iyalin Brigadier ba mai jin kyanshin bada ko mene ne.

Sai da Aunty Saratu ta zamo babu ko sisi a account din ta ta hada da saida bungles din ta na danyar gold. Haka samarin nan na Brigadier ba sa barcin kirki kowannensu kamar bai taba mallakar kwandalar kansa ba, duk sun jeme abin gwanin ban tausayi.

Hakika Bello Makarfi ya gina iyalin shi a bisa tubala na so da shakuwa da shi, ta yadda rashin sa ya zamo masu tamkar rasa rayuwar ne dungurungum. Mutum ne da ya iya zaman duniya kuma mutum mai nuna wa ‘ya’yan shi da matan shi kauna da kobo, lafiya da karfin shi.

Ya tsaya tsayin daka domin iganta rayuwar su ta yadda har sun fi kaunar shi a kan-kan su, dama duk wani abu da suka mallaka a duniya.

Malamai iri-iri na karya da na gaskiya haka suke zuwa suna cin kudin su da sunan wai kafin sati an sako shi, amma shiru ka ke ji wai malam ya ci shirwa, sai ma sabon bakin mummunan labarin an dauke su daga Kiri-kiri Prison zuwa South Africa.

Intisar, dama gwana ce wurin kai wa Sarki Allah kukanta a komai, to balle wannan matsala da ta shafi rabin ranta ‘Daddy Makarfi’. Yarinyar nan ‘Halwa’ ta shiga, idan ka ganta a wancan lokacin sai ka amince ta fi kowa damuwa da Daddynsu.

Jar fatarta ta yi duhu ainun, idanun ta sun fada ciki, sai kwayar idanuwan nan da karan hancin kadai. Ba a zancen komawa makaranta, aljihun kowa ya masifar girgiza, hatta Hajiya Nafi ba karamin faduwa ta yi ba a wannan shekarar, sabida cin kudin kawai ake ba’a inbesting din su, sai da ta kai ta kawo abinci wannan ya soma karanci a gidan Makarfi.

Wani abin mamaki duk wasu abokan arzuka na Brigadier da abokan aiki wadanda cikinsu babu wanda ya taka matsayin da yake kai a soja ba tare da taimakon Makarfin ba, babu wanda ya yi tunanin ya taimaka masu ko da da kwayar shinkafa ne sai jelen jaje da ake ta yi masu ana Allah ya kiyaye gaba amma naira daya wannan babu wanda ya dauka ya ba su da sunan wai yana amintaka da Daddyn su. Ganin haka Faisal ya tara ‘yan uwansa kaf a falo ya ce.

“To Assalamu Alaikum ‘yan uwa. Ku sani fa (La yukallifullahu nafsan illa wus’aha) Ma’ana: Allah baya dorawa wata rai abin da ya san ba za ta iya dauka ba. Saboda haka a abar komai a hannun Allah, mun yi addu’a daidai karfi daidai iko da gwargwado, we’be to wait for the outcome, wato mu jira ijaba a barwa Allah komai, mu koma makaranta masu aiki su koma bakin ayyukan su.

A yau ku duba ku gani yadda aminan Daddy suka watsar da tallafin mu da shiga al’amuran mu bayan cikin su babu wanda ya taka matakin da yake kai ba tare da taimakon Daddyn mu ba. Wannan bai ishe mu ishara ba?

A yau in cewa akai Daddy ya fadi ya mutu, ba za su taimake mu da komai ba haka za su bar mu mu tagayyara, da kyar su ce

‘Allah ya jikan rai.’

Ashe kenan wannan karatun nan namu da ayyukan mu su ne madogarar mu sai kuma Allah gatan kowa? Karatun nan shi ne gatanmu, da shi za mu rufawa iyayenmu da kannin mu asiri. Ga shi kowannen mu ya yi asarar shekara guda wadda da tuni wasu cikinmu sun kammala har sun fara aiki. A gobe kowa ya koma inda ya fito, mu ci gaba da addu’a hakika ita addu’a ba ta faduwa kasa banza, kuma wanda ya fawwalawa Allah lamarinsa ba zai taba tabewa ba.”

To nasihar dan uwansu ta ratsa su dukkan su. Saratu kam sharban kuka kurum take kashirban. Hajiya ta ba kowannen su isassun kudi ya koma makaranta. Ka ji ‘ya’yan Hajiya, to Saratu da diyar ta Saratu fa?

A ranar baby kwana ta yi lallashin Mamar ta ta koma aiki ita ma, don Hajiya tuni ta koma harkokin ta, da yake ba ta son ganin bacin ran Saratun shi yasa kawai a wayewar garin Litinin ta shirya ta tafi. Allah Sarki! Wani ta taras a mazaunin ta, Insurance Company, ba su san wasa da aiki ba.

To su sai abun duniyar ya taru ya yi masu yawa. Ta dai aika da takardun neman aiki kamfanoni da bankuna da dama a nan cikin Abuja, to amma aiki a Abuja sai ga masu uwaye a gindin murhun. Ba abin da ya dame ta kamar yankewar karatun Saratu a shekarar ta ta karshe, dama ta kammala ne da da sauki sai ta nema mata public unibersity wato ta gwamnati,  ta tafi.

Yadda Hajiya ta yi komai nata-ya-nata ta tabbatar ta nuna mata ranar NAIRA ne. Khalil din ta ya gama, to ita yanzun ina za ta nemo makudan kudaden da za ta maida Saratu Kingston College?

Sai ta hada dukkanin gwalgwalan ta na ado gaba daya ta tattara ta sa a kasuwa, an yi masu sayen daraja kuwa. Ta dade da amsar mota cibic hannun Daddy wadda take zuwa aiki a ciki, ita ma ta yi gwanjon ta wani makocin su ya saya a wulakance. Ranar Laraba suka biyo motar haya zuwa Makarfi abin da ba su taba yi ba a rayuwarsu, don direban gidan tuni ya kama gaban sa tunda ya ga an yi watanni har shida ba wanda ya tuna ya ba shi ko sisi, ba shi kadai ba duk ma’aikatan wajen sun gudu in ka dauke maigadi, shi ma tabbas don ba shi da wajen kwana ne in ya tafi watakila shi yasa ya zauna amma hatta ‘yan aikin Anti Saratu sun yi tafiyar su tuntuni, sai ko ma’aikatan cikin gida su Dela da ke bangaren Hajiya da yake ita tana biyan su amma na Anti Saratu ko wata ba a yi ba da kulle Daddyn suka kama gabansu.

Wannan bai damu Hajiya Saratu ba abinda ya dame ta ya dame ta.

Sun iso Makarfi karfe uku da minti ashirin na rana lokacin Malam yana cikin gari, Goggo Jummai ta yi masu kyakkyawar tarba, bayan sun ci abinci sun yi kat, sannan Saratu da Saratu duka suka hada kai da gwiwa suka yi shiru. Goggo, ta ce,

“Ku yaran nan, da kuruciyar ku za ku sanyawa rayukan ku cututtukan zamani masu wuyar magani? Mu ma tsofai-tsofai da mu rashin Bello bai hana mana rayuwa mai kyau ba sai ku? NI na san Bello na sarai tun yana a tsumman goyon sa babu abinda zai sa ya aikata abin da ake tuhumar sa da shi. Kuma ko don albarkacin addu’ar da ake ta yi gaskiya za ta bayyana, ko ba dade ko ba jima.”

Aunty Saratu ta ja numfashi, Intissar kuwa kuri ta yi da jajeyn idanun ta kan tururuwan da ke ta yawo a kan malalen suminti, a ranta ko cewa take su babu abin da ya dame su, yanzu haka suna tare da Daddyn su, sabanin su da aka kame nasu aka garkame a kurkuku! Suka zama matsiyatan karfi da yaji sai tafkeken gida.

A daidai lokacin da Baffa Sani ya shigo, shi ma nasiha ya shiga yi masu mai sanya nutsuwa da kwantar da hankalin mai imani. Har yana gaya masu ya yi Istihara ya ga Bello lafiya lau. Ya kara da cewa.

‘Saratu hakika Ubangiji yana duba izuwa zuciya, daga biyayya tasa, gwargwadon tsarkakewarta ko kebantuwar zuciya zuwa imani da shi, daga ambaton sa Madaukaki. Ki yi duba ga abin da ya cakuda zuciyar ki ki ambaci Allah da shi.

Abu-Yazidal Basdamy ya ce, ‘Madallah da wanda bakin cikinsa ya kasance bakin ciki guda daya, abin da ya gani da idanun sa (na wannan bakin cikin) bai shagaltar da shi daga kai wa Allah kukan sa ba, haka abin da ya ji da kunnuwansa shi ma bai shagaltar da zuciyarsa ba.”

Saratu ki yi tawakkali mana? Duk wani cikakken Musulmi mai imani wanda ya yarda da Allah daya ne, dole ne fa ya yarda da kaddara mai kyau ko akasin haka. Idan har imanin mu ya cika, to bai yiwuwa mu zauna lafiya.

Akwai wata mace a zamanin Annabi (S.A.W) da suke tare da mijin ta lami lafiya, tunda suke tare ko ciwon kai bai taba yi ba. Anan ne take da wasiwasin cikar imanin shi.

Rannan sai ta ce da shi su tashi su je wajen Ma’aiki mai tsira da aminci, ya tambaye ta laifin da ya yi mata ta ce babu, sai ya amince suka tafi, don ya san in har ba ta da wata hujja haka kawai (S.A.W) ba zai raba masu aure ba.

Kafin su kai sai ya yi tuntube danyatsan sa ya fashe jini ya fito, sai ta ce mu koma dama shi kenan.

Musulmi cikakke dole ne ya dinga gamuwa da jarrabawar Ubangiji a cikin al’amuransa na yau da kullum. Bai yiwuwa mu zauna lafiya har karshen rayuwarmu. Saratu da Saratu ku kwantar da hankulan ku da sannu zu ku ga nasibi daga Allah!!!”.

Sai suka share hawayen a tare su ka ce, “Haka ne Baffa.”

Aunty Saratu ta kwashe matsalar karatun Intisar kaf ta fada masa da kuma hukuncin da ta yanke. Baffa Sani dattijo mai zurfin tunani da hangen nesa bai katse ta bar sai da ta dasa aya, ya yi shiru cikin nazarin zancen ta a bisa ma’auni na hankali. Ya ce, ‘Amma Saratu ba ki yi tunani ba, idan kin kadar da dukkan abin da ki ka mallaka Saratu karama ta koma Riyadh, wanda bai zama dole ba, ba kya tunanin halin da za ku iya fadawa a gaba?”

Gaba daya suka yi wa Baffan kallon rashin fahimta, ta ce da mahaifinta, “Uhm, Baffa ban gane ba?”

Ya yi murmushi, “Kai yaro dai yaro ne, kuma tashi kyau take amma ba ta karko. Abin nufi me za ku ci, me za ku daura ke da diyar taki? Da me za ku ije lalurorin ku na yau da kullum? Alhalin babu wanda ya san ranar dawowar Bello sai Lillahi?

Kun saba da ku ci mai kyau ku daura mai kyau, ranar da ku ka wayi gari ba ku da komai ya za ku yi? Kin san dai uwar su Aminu ko za ku mutu ba za ta taba daga ido ta dube ku ba, gamu ni da mahaifiyarki da Allah da taimakon da ku ke mana ke da Bello mu ka dogara, ga shi kin ce ke ba aiki ba to me ki ka gani?”

Daga Inteesar har Mamanta suka yi wa juna kallon gane hangen Baffan su, to amma Saratu ta bar kyakkyawar turbar da ta fara gini a kai na ingantaccen ilimi? Idanuwan Anty Saratu suka ciko da hawaye. A yau kam ta kara tabbatar wa Allah ne gatan su, sai kuma Brigadier Bello Makarfi.

Baffa ya ce, ‘Karatun Saratu abu ne mai kyau da muhimmanci, amma yadda Allah ya tsara al’amari, haka ya kamata bawa ya yi hakuri, ya danne nashi tsarin ya bi shi. Kana naka ne Allah yana nasa, kuma nashin shi ne gaskiya.

A tsahirta da karatun a ga abin da Allah ya shirya a gaba. Ku zauna ku ci abinci, ba tare da kun zubda mutuncinku ta hanyar roko a idon kowa ba, balle a samu abin goranta maku. Na san yanzu an sa ido ne a ga kasawar ku. Amma in kun kame mutuncin ku baku kuma je neman taimako wurin kowa ba, ban da Allah, babu wanda zai wulakanta ku.

A yau neman taimakon ya zamewa talaka abin wulakanci, don haka ku tashi ku je ku kwanta, gobe in Allah ya kai mu ki koma dakin mijin ki, ku ci gaba da addu’a, Allah ya kawo mana dauki da gaggawa.”

Washe gari suka kamo hanyar Abuja cikin bus din haya kamar yadda suka zo, zuciyoyin su cike da taraddadin wannan masifa. Ko a mafarki Saratu ba ta taba kawowa iyayen ta da ita kanta za su taba fadawa irin wannan SIRADIN RAYUWAR ba. Saratu ta yi kuskure, babu wanda ya ke sama da jarrabawar Ubangiji. A yau ta tuno da wata waka da ta kan ji a bakin kawarta Hidayah, da haka kawai in tana wani abun za su ji tana waka tana cewa:

“The rich also cries….”  Ma’ana: ‘Mai kudi ma yana yin kuka.”

Lallai Uba, shi ne jigon rayuwar ‘yan adam. Uba shi ne farin cikin iyali, shi ne bango abin jinginar su, shi ne rufin asirin su, in ba shi rayuwar iyali abin tausayi ne.

Wani abu da ya ba su mamaki da suka iso Khalil ke gaya masu Hajiya da Mama Suwaiba sun tafi Johannesburgh (Saro gold dinsu). Madadin zaman hakan nan ta samawa Intisar makarantar koyon na’ura mai kwakwalwa a layin su inda za ta yi (DIT) ta kuma dauko daya cikin dakin Brigadier ta aje mata bisa tebirin karatun dakin ta sannan ta hada mata Internet, duk don ta debe mata kewa duk da yarinyar ko kadan bata nuna mata wata damuwar ta ba sam. Ita ce ma mai karfafa Antin da ta saki ranta, in don makaranta ne ko nan da shekaru biyar in Allah ya ce za ta koma ne a cikin yardarsa.

Ta dage da fafutukar neman aiki da kafafunta. Saratu ta share komai ta maida hankali kan koyon kwamfutar ta, cikin watan ta na farko da farawar Diplomarta ta kware sosai.

Yammacin wata ranar Juma’a zaune take bisa kujerar na’urar ta, tana zanawa kawarta Raadhah sakon yadda al’amuran rayuwa suka cude mata, suka yi sanadiyar rashin dawowarta makaranta.    

Next >>  

10 thoughts on “Siradin Rayuwa 2 | Babi Na Hudu

  1. Ako yaushe ina mai alfaharin kasancewa daya daga cikin makaranta littafanki,hakika ke yar baiwa ce na karanta tun daga siradin rayuwa har zuwa masarautarmu,Allah yakara maki lfy da Nisan kwana hakika ke yar baiwa ce

Leave a Reply

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.