Skip to content
Part 22 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir Takori

Abuja, Ranar Litinin

Karfe Hudu Da Rabi Na Yamma

Intisar ta tashi da matsananciyar damuwar da bata san ko ta mece ce ba a safiyar yau Litinin. Wani irin kunci  ke damun ta a zucci da bata san ko na mene ba kamar koyaushe wani sabon al’amari zai faru da ita mai dadi ne ko mara dadi?

Ta rasa meke damun ta kwata-kwata, don haka ne ma ta langabe a gado tun safe har yamma ko falon su bata leko ba,  bata ko so Anti Saratu ta ganta, don ta san muddin ta ganta cikin wannan halin to ita da kwanciyar hankali sun yi hannun riga kenan.

A lokacin ita kuma Antin cike take da farin-cikinn samun ‘appointment’ da ‘Afribank,’ don haka ne ma tun safe bata nemi Intisar din ba tana ta aikin takardun neman akinta, sai da ta gama  tas ta ankara da rashin Intisar din a falon tun bayan da ta karya kumallo. Tasa murya daga falon tace “Saratu!”

Ta yi doguwar mika gami da dan tsaki cike da jin zafi, amma ba da Antin take ba, na damuwar da ta cuzguna rarraunar zuciyarta ne, ta mutstsike ido gami da tattare curarren gashin kanta cikin bakin ‘hair-bound’ ta zura kyawawan kafafun ta cikin farin takalmin bakin gado (bed-side shoe), ta murda marikin kofar dakin cikin matsananciyar kasala ta fito ta tadda Antin, saye da doguwar riga ruwan makuba mai hade da hula, amma bata sanya hular a kanta ba.

Ta dube ta cike da murmushi irin wanda rabon da ta ganta da shi tun kulle Daddyn su tace “kin san meye ne?

Wani abin alheri ne nan ke shirin samun mu, amma na gan ki rather-moody today, wani abu ne ya faru ban sani ba?”

Ta zauna bisa kafafun Mamar ta, ta kwantar da kai bisa gwiwoyin ta tamkar dai zamanin kuruciya, kodayake ita har girman ta baka rabata da yaro dan shekaru uku, son jiki kuwa ko mage haka ta ganta ta kyale. Muryan ta a karye tana dibar bangon dakin tamkar mai tunanin wani abu tace

“nima na kasa gane meke damuna, amma Mamar mu, mafarki fa na yi yau wai an tafi da Daddy za’a harbe…”

Kafin Antin ta samu damar cewa uffan, itama Babyn ta karasa zancen ta sai dirin motoci suka ji, mota ba daya ba babiyu ba, hakannan ba uku ba, Intisar ta nufi bakin taga ta leka da sauri, abinda ta gani ya gigita ta (Daddyn su ne ke fitowa daga mota).

Ta kwalla ihu tace “Daddy!” Anti Saratu ta mike a gaggauce zanin ta na kuncewa tayi sa’ar riko shi, da gudu itama ta leka ta tabbatar Saratun ba karya ta ke ba sai tayi waje.

Ita ko Intisar sai taji hawayen dadi da farin-ciki na kwararo mata, ta jingina bayanta da bangon tagar idanun ta a rufe.

In har tana da wani buri daya saura a rayuwar duniya to a yau, ya cika. Ta daga hannuwanta sama ta shiga kwararo yabo da godiya ga sarki Allah jikin ta na wani irin kyarma da karkarwa tamkar wadda aka sanya cikin sanyin kankara.

Daga bayanta Khalil ya zungureta yana dariya kamar bakin shi ya tsage ya ce,

“To ki je, ke kadai yake nema, ke kadai yake kira, ke kadai yake tambaya Inteesar!”

Ta nufi sassan Daddyn da sauri faram-faram kamar zata tashi sama, Khalil na biye da ita a baya, amma ji ta ke saurin da ta ke dinnan ba zai sadata da Daddyn a yau ba, sai ta kara a guje.

Shima Daddyn ya taso ne ya je nemanta da kansa don yana ganin ta ki zuwa ne sabida tsoron Hajiya Nafi.

A bakin kofar shiga falon sukai karo da juna, a guje ta rungumeshi tana hawaye ta ce,

“Daddy kai ne, ashe dama akwai ranar da zaka dawo?”

Ya kalleta. Ya ce,

“Saratu, ke ce kika lalace haka! Ina Al’amin Hajiya da ya tafi ya bar mun iyali cikin wannan ukuba?”

Ya saki Inteesar ya juya ga Hajiya tamkar ita ce ta boye mai Aminun, ta sunkuyar da kai bata ce komi ba sabida zuciyar ta dake kuna, don ita kanta bakin-cikin da Al’ameen ya kunsa mata yana da yawa amma bai tambaye ta ba sai akan tsinanniyar ’yar sa? Idan ma yana nan din shi bawan su ne da zai nemo masu abincin?

Duka yaran gidan basa nan sai Khalil kadai ya ce,

“Daddy, muma tunda ka tafi, bamu kara jin labarin sa ba. An aika mai cewa an kulle ka amma ya ce wai ba ruwan sa.”

Brigadier ya zame ya zauna akan kilishi yana girgiza kai ya ce, “babu laifi” ya tambayi Anti Saratu su Bappa Sani da su Najib tace kowa yana lafiya, su Najib kuma kowanne yana makaranta. Yace ita Saratu me ta ke a gida bata koma makarantar ba?

Sai kawai Antin ta rufe zancen da cewa ai sun gama makarantar ita da Khalil don bata son zancen yayi tsayin da ran ta zai baci, ya tambayi Hajiya ko ina motocin gidan bai ga ko daya ba? Daga nashi har na amfanin gida? Anti Saratu ta ce,

“Don Allah Babansu Khalil ka tashi ka kintsa ka huta, ba yanzu ne lokacin wadannan kananun maganganun ba.”

Bai ki ta tatan ba, sai ya mike ya nufi sassan shi. Hajiya na jifan ta da harara, lokaci guda kuma tana lallatsa nambobin su Najib tana gaya masu su zo gida ga Baban su Allah ya fito da shi.

Intissar na ganin ita ya dace ta yi wa Faisal wannan muhimmin albishir ko don ta gyara zumuncin su data wargaza. Ita kadai zata iya bada labarin halin kuncin da ta tabbata zuciyar Yayan nata na ciki a dalilin yin biris din da tayi da shi.

A hankali ta shiga danna nambobin shi wadanda suke tamkar karatun sallah a cikin kanta, zuciyar ta cike da farin-ciki maras misaltuwa.

Kai tsaye ta samu bugu daya layin ya shiga to amma me? Muryar mace ce take tambayar ta ko wane ne akan layin? Ta yi dan jim, kirjin ta ya soma harbawa da sauri-sauri, muryar ta wani iri, cike da zargi ta ce,

“Plz, ba layin Faisal Makarfi ne ba?” Ta ce,

“Shine dai, amman ya shiga wanka yanzun nan, ko zaki sake kira anjima?” 

Saratu ta ji wani abu ya zo ya soke ta a kahon zuci, zuciyarta ta cunkushe kwakwalwar ta kasa rungumar abinda kunnen ta ke son ta fahimta. Me kenan Ya Faisal ke yi a kudun? Ba dai neman matan banza ba?

Ta yi jifa da kan wayar ta hadu da garu wanda hakan ya haifar da darewar ta gida biyu, kafin wasu hawaye masu gudun gaske su zubo a kundukukin ta, tayi saurin sanya bayan hannun ta ta goge dai dai lokacin da Anti ta turo kofar dakin ta shigo, ba tare da ta lura da yanayin da Intisar din ke ciki ba tace

“Saratu, Baban ku yace ki hada mai ‘vegetarian-meal’ mai kyau (abinci wanda babu nama a ciki sai ganye) bai son girkin  kowa a yau sai naki, gashi na ganki sai kumburi kike kina neman fashewa?”

Taja wani dogon tsaki, “Tsuuu!” ta girgiza kai ta sunkuyar, Anti Saratu ta kama baki

“Ke Saratu, lafiyar ki kuwa?” Sai ta kara tsuga tsakin, ta mike tana niyyar shiga bayi domin adana hawayenta, bata san me zata ce da Antin ba.

Anti Saratu duk da cewa ranta ya sosu da wannan sabuwar halayya ta Intisar da koda wasa bata taba yi mata ba, wai tsaki? Ta danne nata bacin ran don sanin halin ‘yan kayan nata sarai ba’a jin damuwar ta sai da dabara, don haka Faisal ya sabar mata.

Sai ta kada kai ta juya ta ce,

“Ai sai ki ce in je in ce da Daddyn ba zaki samu damar yi mai girkin ba, sabida wasu can sun bata maki rai, amma ba ki yi ta tsuga masa tsaki ba.” Tasa kai zata fita.

Da sauri ta kamo hannunta, gaba daya ta fiddo abnormal idanunta waje, zaka iya ganin matukar razanar da ta yi cikin kwayar idon ta, ta ce,

“Wallahi-wallahi Mamar mu ba haka bane, kai umh, ni abin ne ma na kasa ganewa Allah.”

“To menene in ba shi kikewa tsakin ba?” Ta ce (kaman za tai kuka),

“Haba Mama, haba don Allah Mamar mu, yaya za’ayi na yiwa Daddy tsaki ‘eben if I run mad (koda na haukace)? Wai Ya Faisal ne ke da budurwa? Kuma ba ki ji ba har tana ce mun ya shiga wanka? Ko a ina suke oho, da har zai shiga wanka a gaban ta?”

Anti tayi jim, ita dai wannan closeness wato (kusancin) na Faisal da Intisar na bata tsoro, na kuma tayar mata da hankali, domin abun har ya so ya zarta na wa da shakikiyar kanwar sa, kar dai Saratu kishin Faisal ta ke?

Ta ja dogon tsaki itama tace,

“To ke ina ruwan ki?

Kina tsammanin Faisal bai isa yin aure bane da zaki ce ba zai yi budurwa ba? Kina nufin ba zai yi aure ba kenan don yana matsayin yayan da ke son ki? To ke din zai aura koko in kin yi naki ne zaki sa shi a gaba ku je gidan mijin tare? Kin ga ni bani cikin shirme, ta so mu je?”

Intisar data auna maganganun Antin cikin ma’auni na hankali da tunani sai ta ji Antin tayi gaskiya. Sai dai ita kam a duniya bata taba kawowa kanta yin aure ba tunda kuwa zai rabata ne da Ya Faisal da Mamarta. Bata kuma jin zata iya har abada! Ita kanta ta rasa maiyasa budurwar Faisal ta tsaya mata a rai ya ciwon makogaro.

Sakwara ta shirywa Daddy da miyar egusi da aka wadatata da ganyen alayyafu sosai da gandar fatar saniya wadda ta dahu tai lugub, sannan da busashshen kifi, ganyen yaji sosai miyar tayi shar gwanin sha’awa musamman da yake da manja tayi amfani, sannan ta shirya faten dankalin turawa shima da ganyen a ciki da ruwan tumatur zalla. A karshe ta shirya  farfesun hanta wanda shima ta wadata da ganyen alayyafun, kana ta shirya salad da ruwan salad cream, heinz-beans da mayonnaise (kalb) wanda ta fara cakudewa da kifin gongoni nikakke na (starkist) da bineger, tabi samanshi da adon cucumber, tomatoes, karas dafaffen kwai da sauransu.

Duk da dai Daddyn ‘vegetarian-meal’ ya ce ta shirya lafiyayyen farfesun macen tolo-tolo mai rai da motsi, irin wanda ya dahu lugub din nan har tsokar ta salibe da kanta, tace a ranta in Daddyn bai son wannan ai Mamarmu zata so, har ila yau, tayi dafa-dukar spaghetti wadda carrot, greanbeans, kabeji da hanta yafi taliyar fitowa sannan ta matse mai ruwan guava kamar yadda ya fi so a kullum ta sanya a firji.

Tayi wanka ta shirya cikin atamfa (exclusive) fara mai ratsin shudi kinsan irin wannan ‘colour’ a jikin farar mace karkiso kiga yadda ta kara haskaka ta, ta nannade gashin kanta kamar kullum cikin shudin ribbon ta jerawa Daddyn abincin a inda ya saba cin abinci.

Saratu ba sangartacciya ba ce, ta iya komi a wurin Mamar ta, don tun tana shekaru sha biyu suke shiga kichin tare tana kallon yadda Mamar ke hadawa Daddy ‘delicious’ don haka ne in ta tsaya ta tsarama abinci ko na Nicon-Noga albarka.

Daddy na cin abinci suna mai hirar abubuwan da suka faru baya nan amma ba su gaya mai me sosa ran ba. Hajiya ta tashi fuuu ta fice da ta ji Daddyn na tambayar Saratu ‘glasses’ dinta sun tsufa ya dace a je Jidda sabon wata mai kamawa a canzo wasu.

Ya tabbatar Hajiya ta saida gabadayan motocin sa da yayi magana tace lalurorin karatun yara ne, yace amma larurorin har sun kai na wadannan miliyoyin nairori sai cewa tayi itama gani tayi an fara shiyasa ta bi layi (tana nufin Anti Saratu da ta saida ‘yar motar ta bayan kuma tana da masaniyar cewa shi Daddyn ne ya mallaka mata da kansa), bawan Allah, bai son maganar tayi tsayin da har zata janyo bacin rai, sai ya ce Allah ya mayar masa da alkhairi.

Kan ka ce meye wannan gida ya cika da jama’a masu taya Daddy murnar kubuta, wani abu da ya basu mamaki duk wasu tsofaffin abokan sa na nesa dana kusa wadanda rabon su da kofar gidan tun ranar da aka ce an kulle Makarfin sai gasu wai duk sun zo taya murna, dan adam kenan.

Malam Sani da Goggo Jummai ma da yamma suka iso garin, kada ki so ki tona zuciyoyin wadannan dattijai, su Najib ma duk sun iso ana ta hamdala.

Nasir ne ya gayawa Faisal ta waya shima yace Insha Allah gashi nan tahowa. Daddy bai samu kubuta daga mutane ‘yan taya murna ba sai karfe goma na dare, don haka bai samu damar fayyacewa iyalin shi komai ba na daga zargin da ake mishi Allah ya kubutar da shi sai ko Allah ya kai mu wayewar garin.

Washegari da safe kuma sai ga ‘yan aikin gidan da suka gudu suna dawowa daya bayan daya suna aikowa wai a gayawa ranshi ya dade ga mai ban ruwa da mai tada inji nan sun dawo bakin aikin su, Aunty Saratu na jin sanda ya leka yace a gaya masu wanda suka yiwa iyalin shi da baya nan ma ya isa ya gode sai tayi dariya.

Da aka taru ana karin kumallo kamar yadda ya ke a tsarin gidan kowannen su matse ya ke da son jin yadda wannan ijaba ta Ubangiji ta sauka kan mahaifin su, zuciyar kowanne fari kal kamar an mai bushara da Aljannah.

Furkan ne ya kasa hakuri ya bara, “Wai Dad, ya aka yi ne?”

Brigadier yayi murmushi, ya san abinda suka matsu da son ji kenan musaman Saratu karama da ta kura mai ido kamar mai gadin sa kada a sake kame masu Daddy a kulle. Fuskar shi ta yi fayau don duk wata kasimbar wahala ya shareta tas da kyakkyawan saisaye, sai dai ba karamar rama yayi ba tabbacin ya wahala kwarai da gaske.

Ya dubi iyalin shi daya bayan daya kana tsoffin shi Baffa Sani da Goggo Jummai, sannan agogon da ke manne a falon, ya ce,

“Ya isa a ce Faisal ya iso, don ya gaya mun ya biyo jirgin kasa tun daren jiya sabida tafiyar dare tafi dadi a jirgin kasa sai dai bata lokaci.” Ya kai duban sa ga Hajiya ya yi murmushi ya ce,

“Dan ki, naso a ce yana nan.”

Ta sunkuyar da kai kawai don tasan Al’amin yake nufi, ita kanta a yau tayi kewar shi ba kadan ba, tuni idanun ta suka ciko da hawaye.

Abubuwa da yawa na faruwa a bayan Al’ameen masu dadi da marassa dadi. Taso a ce yana tare da su a yanzun tamkar sauran ‘yan uwan shi, ta tambayi kan ta ko maiyasa Al’ameen ya gujesu, baya ko tuna su?

Bata sani ba, duk a kan nadamar abinda ya aikata ne ga ‘yar da ta tsana fiye da kowa Al’meen ya guje su, har kullum har kuma zuwa lokacin ya kasa daina ganin kansa a matsayin azzalumi akan Saratou.

Ya cigaba da cewa, “Don abinda zan fada ya zamo darasi a gare su.

Bana nadamar zamowana soja mai kare kasarshi takowannne fanni, kamar yadda har gobe ba zan yi ba.

Abinda zan fadi muku yanzun ina so ne ku dau darasi kan cewa a wannan zamanin da muke ciki, babu aboki nagari, babu wanda zaka amincemawa, abokai sai su kai ka su baro ga fitinar da bazaka iya fidda kanka ba, su tsundumaka cikin masifar da baka san farko balle karshenta ba.”

Ya mike tsaye, hannuwan shi ya sarke a bayan shi ya juya masu baya cikin tuno tsohon bacin rai na wani abu daya taba ma mutum zuciya matuka, dukkannin su sun yi tsit ko tari kwakkwara babu wanda yayi, su dai kawai so suke su ji me ya kai Daddyn su ga abinda suke da tabbacin ba laifinsa bane, to me ya tsunduma shi?

“Rannan ina zaune a falon Janar Benga, ina sauraron fitowar sa a sabili da kiran gaggawa da yayi mani, sai na iso kuma a dai-dai lokacinda aka ce yana ganawa da baki, na kishingida cikin kujerar falon farko da zummar in jira shi, to amma sai na rika jiyo tashin muryar sa yana cewa da bakin sa shifa ya gaji da tsarin mulkin president (mai ci a yanzu) sabida yadda ya hana masu yin yadda suke so kamar yadda suka yi tsammani, suka kuma yi yarjejeniya da shi kafin su tsaya masa ya samu ya haye, su shirya juyin mulki kawai su turani in maye gurbin sa domin ni ina da sanyi, zan bar su su yi yadda suka ga dama da kasar mu, amma muddin suka bijiro min da bukatar su naki basu goyon baya, zasu shirya min tuggun da zan yi nadamar shiga na soja.

A lokacin na fito, ko ganin abinda yake gabana bana yi sabida tashin hankali, don nasan su Benga sarai kamar yadda nasan yunwar cikina, masifaffun sojoji ne da babu abinda bazasu iya ba in har suka sa kansu don su suka san yaddda sukai suka raba president da Marshall Damijo duk irin matsananciyar amintakar dake tsakanin su kuwa, na shiga mota direba ya dawo da ni gida.

Ke Saratu in zaki iya tunawa a ranar babu yaddda ba ki yi ba ki ji abinda ke damuna naki gaya miki har kika yi ta kuka.

Na kwana ina saka yadda zan yi in fidda kaina daga wannan tsaka mai wuya da suke neman turani, wanda a lokcin da za’a rantsar da ni, na yiwa kasata alkawarin bazan taba yin wani abu ba bisa doka ba, ba zan taba cin amanar kasata ba, idan kuma har na nuna hakan na tabbata Benga Delsu da jama’arsa ba zasu kyaleni in zauna lafiya ba, sai na yankewa kaina shawarar yin ‘retire’ in koma kasuwanci cikin ruwan sanyi in barwa Allah al’amura na, na kuma amince cewa duk wata cuta ko daukaka da zata sameni to da sani da yardar sa ne.

A washegari na aika takarduna na yin murabus daga aikin soja  kwata-kwata, ai dai na fita daga kowanne irin shirin suma.

Ashe dai tuya nayi na mance da albasa, don kwata-kwata sati daya a tsakani na ji su Benga ma sun yi ritaya, a dalilin an soke mulkin soja a lokacin, amma manya-manyan su irin su Marshall Shu’aibu Damijo, Shitu Allazi da Janar Delekonkwo duk basu yi ba, ban kawo komai a raina ba, don ban zaci zasu waiwayeni bama tunda sun ji na bar ‘military’ ashe dai kuskure nayi. Don a dai-dai lokacin aka soke ‘military-rule’

Ranar wata asabar ina hutawa a gida aka ce dani Benga da Shitu na son gani na (seriously private) wato cikin tsananin sirri, nayi Addu’a kan Allah ya raba ni da sharrin wadannan miyagu kamin in je.

Bayan mun gaisa, sun kuma gamsu da matakan tsaron da ke falon, suka gaya min bukatar su na cewa su Shittu zasu shirya kashe president ta hanyar sa masa guba a abinci da za’a sa kukun sa ya aiwatar akan wasu adadin biliyoyin nairori, in yaso ni sai su tsaida ni takara a jam’iyyyar da zasu kafa  mai karfin gaske in samu ‘by all means’ (koda ta magudi ne) sai in barsu su tsara min irin mulkin da suke so a yi.

Hankalina ya tashi, cikin zafi na zazzagesu na kuma gargadesu kan cewa wallahi babu ruwana, idan kuma suka sake sako sunana cikin al’amarin su, to kuwa zan tona musu asiri duk da kakkarfar abotar dake tsakanin mu kuwa.

Sai suka yi murmushi suka bani hakuri, tare da tabbatar min zancen ya wuce har abada, suka tafi.

Kawai sai ji nayi har a bakin Faisal wai na tsaya takarar shugaban kasa? Duk an bi an manna posta na a ko’ina, president da kansa ya neme ni a waya yace a she takara na shiga haka ba sanarwa? To yana mun fatar alhairi.  Sai ma na rasa me zance.

Na kira Benga a waya nace ban ji dadin cin mutuncin da su kai min ba, wannan ai kazafine, suna sane da tsakanina da president ya za suyi min kage kan abinda bani da masaniya a kai?

Sai cewa yayi su ba su bane, basu ma san anyi ba, don shi a lokacin ma yana Cameroun, amma inyi hakuri zai bincika ko su Marshall Shu’aibu ne. Abinda yace da ni kenan.

Ranar da suka shirya wanzar da komi sai kukun da suka damkawa amanar abin ya kira president ya tona masu asiri, har kudin da suka bashi ya danka mai da takardun yarjejeniyar cewa ni za’a tsayar. Ni da nake  amininshi tun muna NDA, nida ya taimaka ta kowanne fanni a soji, hatta karatun Al’ameen a turai shi ya dauki nauyi  har yau kwandala ta bata taba yin ciwon kai ba, amma wai dani aka hada baki za’a kasheshi har lahira, (a tunanin shi fa), an ce mun president har kuka yayi kan cin amanar da yake tunanin nayi mishi, a take ya bada oda da shelar a kame mu duka.

Rannan ina magana da Najib a kan hanyata ta dawowa daga Makarfi dibo jikin ka Baffa, motocin soji suka yi mana dabaibayi, nace da direbana ya tsaya amma saboda rudewa sai ya karawa motar wuta, nayi mai tsawa maimakon ya tsaya sai ya kara gigicewa ya kara gudun motar fiye da (300), ba sai suka sakarwa tayoyin motar (bullets) ba, motar ta hantsila ni na fado bisa titi cikin jini, shikuwa tuni ya dagargaje a ciki.

Duk irin rauninnikan da ke jiki na haka suka kakaba min ankwa a ranar suka tafi damu Kiri-kiri.

A Lagos aka kaini asibitin bariki nayi jiyya ta tsayin watanni uku kafafu da hannayena duka daure da ankwa jikin karfen gado, ban taba zaton zan rayuba, sai dai da yake wuya bata kisa sai in kwana ne ya kare.

Bayan na warke aka tafi damu Enugu daga ni har su Benga ba mai ce da kowa uffan don takaici.

A daren ranar abinda ya sani kuka tun farkon al’amarin shine da aka daura min camera daga gidan talbijin na kasa NTA, CNN da BBC domin watsa labarun cewa an kama mu dumu-dumu kan son yiwa kasa juyin mulki, karkashin jagorancina ni Bello Makarfi. Nayi kuka irin wanda ban taba yi ba a rayuwata, sharri ciwo ne da shi balle irin wannan dana tabbatar za’a harbe ni ne a banza a inda ko gawata baza’a yi mata sallah ba, sai dai ta zama ta ungulu da tsintsaye.

Bana kuka don zan mutu, sai don mutuncinku da zai tafi terere, a sanadiyyyar wulakantacciyar mutuwar da nayi! Aka dawo damu (Imo State prison) da abin yayi kamari aka cilla mu South-Africa ta jirgi, inda aka cigaba da bamu tsatstsauran tsaro.

A wannan dan tsukin na fidda rai da rayuwa kwata-kwata sai na maida al’amurana ga Allah, dare da rana ina rokon shi yayi mun rahma ya inganta rayuwar ku bayan raina.

Mun shiga kotu ranar Alhamis inda aka tafka mahaukaciyar shari’a, shaidu suka tabbatr da sa hannun mu duka nan da nan ka yankewa Benga Delsu da su Shitu hukuncin kisa da bindiga.

Ni kuma da babu kwakkwarar shaida a kaina, ban kuma amsa laifina ba, haka shi kansa kukun ya tabbatar babu ni a sanda aka kirawoshi, duk da irin kokarin da lauyana yayi suka san yadda sukai suka zurmani aka yanke min hukuncin life – imprisonment (daurin rai da rai), sai na daga hannu nace Allah yasa hakan shi ya fiye mun alkhairi da ku baki daya.

Shekaranjiya ina kwance aka ce in taso, a gidan gwamnatin Delta, dayake an maido ni jurun din Delta State, President ne na gani tare da mukarrabansa wato gwamnonin Nijeriya gabadaya, ya debo su don su zo su bani hakuri an gane bani da laifi kwata-kwata a yau za’a maido ni gida.

Na tambayi yadda abin ya kasance aka gaya min cewa Shitu da Marshall da za’a harbe su suka roki alfarmar a basu lokaci su farke komi, ba kuma nufin su a yafe musu bane, illa su fadi gaskiyar yadda Benga ya turani cikin al’amarin, don ya nemi hadin kaina na yi mai barazanar tona musu asiri, suka fadi inda za’a samu shaidar komai akan hakan a gidajen su, suka kuma roki da a kyaleni ko hakkin da ke kansu ya ragu, sun tabbatar alhakina ne ya janyo masu tonon asiri. An bani hakuri, an kuma bani tarar bata mini suna da sukai ta biliyoyin nairori tare kuma da sabon albishir din cewa sati mai zuwa in shiga (presidential office) a matsayin mai baiwa Shugaban Kasa shawara kan harkokoin Mulki.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.5 / 5. Rating: 17

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siradin Rayuwa 21Siradin Rayuwa 23 >>

3 thoughts on “Siradin Rayuwa 22”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×