Skip to content
Part 16 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir Takori

Ko kafin a dawo hutu, lokacin aikin su a Riyadh wanda dama na wucin gadi ne ya cika, an cilla Bashir Sambo kasar Korea aikin Jakadanci. Su Hunainah sun yi bakin ciki ba kadan ba na rashin sallama da kawar da suke so kamar ran su ga shi kuma basu taba tunanin yin musayen lambar waya ba.

Hajiya Hadiza, ta roki Allah ya cire mata wannan tunanin da ke addabar zuciyarta yake kuma neman wargaza mata farin ciki, tunanin cewa wai diyar ta Fatimah ta gani. Shi maigidanta ma da ta fada masa dariya ya yi ta yi mata wai tasa abin a ranta ne ba dole ya yi ta yi mata gizo ba?

Dama duk โ€˜yar farar yarinyar da ta gani ta ce tana kama da โ€˜yar ta Fatimah yau kuma kacokan ta ce โ€˜yar ta gani dungurungum.

To amma wane mai hankali ne zai yarda cewa yarinyar da aka rasa shekaru goma a kauyen kayau, ita ce za a ce an gani a babban birni irin Riyadh? Birnin da ya tara alโ€™umma iri daban-daban. Ban da abin Hadiza ai fararen โ€˜yaโ€™ya gidansu ta zo.

Hutunsu Saratu a Abuja suka yi shi inda Daddyn ya komo da zama kwata-kwata. Burin Aunty Saratu kusan ya cika ganin yadda Baby ta kwantar da hankalinta ta tsaya tsayin daka tana karatu.

Babban bakin cikin baby da har za ta koma hutu ba ta sanya Ya Faisal din ta a idanun ta ba.

Aunty Saratu ta yi mai waya cewa ga su Saratu sun zo hutu har za su koma ba ta ga yayan da ba ta da kamar shi ba, lokacin shi Faisal yana tsaka da jarrabawar wucewa (200 lebel), sai ya ce Aunty Saratu ta budewa Baby kwanfutar ta zai turo mata sako ta e-mail din Antin karfe shidda daidai na yamma, don a ayanzun zai shiga dakin jarrabawa ne sai ya fito.

Inteesar na dakin ta a lokacin, komai yana nan yadda yake sai ma gyara na musamman da Daddy ya kara yi mata, saboda ya ce ita yanzun ta tashi daga 0-lebel. Kuka take sosai hawaye ya hade da majina, a kan me Ya Faisal ba zai baro kowane irin karatu ba ne ya zo ya ganta ba?

Tsawon shekara guda basa tare? Amma just once throughout a year?  (Sau daya kacal a shekarar baki dayan ta). Ba yadda Anti ba ta yi da ita ba ta amshi wayar sa su gaisa amma ta ki, me waya za ta yi masu, yadda ta yi kewar shi din nan? Ta kunso labarun su Hunainah fiye da cikin โ€˜yaโ€™yan carbi tana Allah-Allah ta sanya kafa a Nigeria ta ba shi ya sha, shi ne zai yi mata haka, wai ba shi da lokacin zuwa?

Antin ta kara tunzurata ta hanyar yi mata gwalo da fadin wai Faisal bai damu da ita ba, ai kuwa sai ta fashe da kuka na gasken-gaske, ta rungume kugun Mamar tana mata ihu da gunjin kuka ba na wasa ba, a dole tausayin ta ya kamata domin ta damu da Faisal sosai fiye da kowa a duniya haka shi ma, tunda ta tafi bai bar zancenta ba, bai daina tuna ta ba a kowanne dakika, harshensa bai bar ambaton sunan ta ba.

Abu kadan sai ya ce, โ€œAllah Sarki Baby na ana can, ko me ake yi yanzun?โ€

Antyn sai ta yi dariya ta ce, โ€œAi sai ka bar naka karatun ka bi ta can ku yi tare.โ€

Sai ya ce,

โ€œBari in samu hutu ki gani, Aunty nima Riyadh zan tafi.โ€

Ta kamo hannun ta suka zauna cikin kujera ta ce, โ€˜Saratu wai ke ba kya girma ne? Faisal da gaske yake jarrabawa yake yi, kuma ba a barin jarrabawa a jamiโ€™a a fito. Ke in kina taki jarrabawar kin taba tahowa baki gama ba? Idan kin kwantar da hankalin ki da kafafun shi za ki gan shi da zarar kun koma, don ba ki san yadda ya damu da ke ba ne.โ€

Sai tayi murmushin da ba ta shirya ba. Antin ta kara da cewa โ€œโ€˜Taso ma ki ga wani abu.โ€ Tana lalube cikin shafin yahoo-mail wani katon zanen zuciya kalar shi ja mai haske ya bayyana a jikin screen din kwamfutar, a kasan ta wani boyayyen rubutu ne da aka dunkule sa cikin tsari mai kyau da daukar hakali,

Saratu-Intisa!

Drop my picture into your mind Sis, allow it to dissolve in consciousness, and it will spread a healing balm over your entire soul. This is one of the simplest processes to feel me beside you.

Read hard and make us proud.

                                    Faisal Bello Makarfi.

Ba ta san sanda ta yi dariya ba kamar ba ita ce mai kuka wiwi yanzun ba. โ€œShin Mamana ta yaya zan sa hoton Ya Faisal a raina?โ€

โ€œShi ne sai ki dauko fuskar shi a zuciyarki, ki sama ranki cewa wannan Faisal ne ku ke tare, yana kallon ki yana miki hira, yana kuma yi miki wannan kyakkyawan murmushin nan nasa. In kin yi hakan ba za ki ji haushi ba don ba ki gan shi a wannan shekarar ba.โ€

To Saratu ta koma makaranta cike da farin cikin kaunar da Mamar ta da ya Faisal ke mata.

Ba karamin bakin ciki ta taras a makaranta ba da ta ga ta shafe sati daya, biyu har uku su Hunainah ba su dawo hutu ba. A sati na hudu ne ta kasa daurewa ta je ta tambayi malamin da ke kula da shige da ficen hutun dalibai da suke kira Sayyid Ridhwan game da su. Ya dade yana bincike kafin ya samo mata detail din su, cewa ya yi da ita dama aikin jakadanci mahaifin su yake yi, inda kuma duk ya tashi nan suke komawa da karatu, yanzu kuma an yi posting dinsu kasar Korea.

Ta samu wani kututturen icce ta zauna ta yi kukan ta mai isar ta; kukan sabo da kewa, kukan rashin amini, (to lose a friend is the greatest loss of all losses). Sai ta ji rayuwar makarantar ya zamo mata wani irin salam, musamman in ta tuna hirarraki da ban dariya irin na Hunainah masu cike da hikima a ciki, da kuma tonon fada irin na Hidaya da a kullum ke sanya su zama busy wato dai ba za su zauna shiru ba.

Ta yi kuka har idanun ta suka shiga zafi da radadi. Daga baya ta rugnumi kaddara ta sanya wa ranta salama, don malamin Islamiyya ya sha gaya masu imanin mutum ba ya cika har sai ya yarda da kaddara mai dadi ce ko mara dadi?

Kenan Allah ya kaddara iyakacin rayuwar da za ta yi da su kenan, shi yasa har ya nufe ta da zuwa gidansu, ta watsar da komai ta rungumi karatun ta kamar da, barin ma da ta yi sabuwar kawa Raadhah, mutuniyar Jeruslaam, tana fatan wata rana Allah ya kara hada ta da su ko da a mafarki ne.

Sun ci gaba da karatu sosai Saratu Bello na kara yin fice. A wannan shekarar sau biyu ta fita debate a kan lissafi har Abudhabee (Dubai), dayar a Oman dukkansu UAE ne wato United Arab Emirate, ana kuma nunawa a tauraron dan-adam, ta kuma daukowa makarantar su kofin zinare, wannan ya kara bata damar zama โ€˜yar lelen malamai da hukumar makarantar gaba daya. Kingston College, na hangen bata shugabar dalibai in ta iso ajin karhse, wai โ€˜yar Africa! Africar ma kasar da suka fi gani da kaskanci, Nigeria ce?

Wata ranar Litinin ta fito daga library tare da wata yarinya Rabikha, aka ce da ita principal na kiranta. Ta zo shiga kenan suka ci karo da Khalil, tsoro ya kama su, don wannan shi ne karo na farko da wani kira makamancin wannan ya ratsa da su a tare. Tsoron ta Allah, tsoron ta kada ta yi laifin da zai sosa ran Daddy a rayuwar ta. To amma me?

Ta dade da sanin wani kamshi da ba ta jin shi a jikin kowa a duniya sai mutum daya, ba ta jin shi jikin kowa in ba… Ji ta yi an sure ta an yi sama da ita ana juyi da ita tamkar a hadiye ta, sai kuma dariyar mamar ta, ta dubi mai rike da itan, Ya Faisal ne.

Tuni ta saki ihu, ta rukunkume shi tamkar ta sume don dadi ba ta ko ta Mamar ta. Kaunar Faisal da Intisar wannan cikin jininsu ne, kuma daga Indallahi take. A duk san da suke tare da juna, mantawa suke da kowa a duniyar sai junan su.

Da Principle ta ga ofishin ta ya kacame da hayaniyar wannan family masu matukar kaunar junan su sai ta fita ta bar masu ofishin. An yi hira an yi dariya, amma baby magana daya, biyu za ta ce ina Daddy na? Sai Faisal ya ce,

โ€œBa ki san Daddy ya tsaya takarar President ba?โ€ Ba su tafi ba sai yamma lis. Washe gari suka zo suka yi masu sallama suka tafi. Dama sun zo aikin Umrah ne.

To haka karatun ya kasance masu, duk shekara suna zuwa gida su yi wata guda suma kuma mutanen gidan na zuwa masu a kai akai, musamman Faisal, kaโ€™ida ne duk karshen semester Daddy ya biya mai kujerar dubo Intisar.

Wannan wani alkawari ne da ya yi wa rayuwar shi cewa ko Daddyn ba zai biya ba, zai san duk yadda ya yi ya kai wa Intisar ziyara ko da hakan na nufin ya ciyo bashi ne.

Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah, yau ga Saratu Bello ta kammala ajinta biyar na secondary a shekarun ta goma sha biyar a duniya. Shi kuma Khalil ya kammala, don ma sun maida shi baya ne saboda faduwa darasin lissafi da ya yi, amma da tun shekarar baya ya gama, daga wannan hutun shi ba zai koma ba, ita ce dai za ta koma ta yi final year din ta.

An danka mata dankwalin shugabar dalibai. Wayyo! Ashe daga wannan hutun, mafarkai da burirrika ba za su taba zama reality ba.

Saratu ta dawo hutu cike da farin cikin abu biyu, first of all, alkawarin da ta yi wa Daddy na kwato (1st Position) din ta daga hannun Amra Rushd abokiyar takarar ta mutuniyar Katar, da ta kwace mata a zangon baya ta cika shi, ta kwato (1st position) din ta as usual. Sai na biyu za ta ga farin cikin Mamar ta a fili, watakila ma har ta goya ta da zani duk da girman ta kuwa. A wurin Mamar har abada ita BABY ce, ta kan ce, har sai ranar da ta samu kani.
Haka take yi mata duk san da ta yi na daya, wato ta goyata tayi ta zagaye daki da ita, in kuwa na biyu ne ta shiga korafi kenan.

โ€œSaratu kina wasa, Saratu alkawarin mu da ke kenan? Saratu where is your delegence (Ina kwazon ki), I dare you!โ€ 

To yau dai duk ba ko daya, ga na dayan ta ta dauko, saura tukuicin Anty da Daddy.

Ashe labarin bakin ciki da tashin hakali ke nan yana tsimayen su su fito daga jirgi, wanda daga jin sa Saratu sulalewa ta yi nan take a kasa sumammiya.

*****     

Cyril Stober ne tare da sabuwar Newscaster Hawwawu Gebi, ke karanto kanun labarun yau daga gidan talbijin na kasa (NTA Abuja), inda ya ce,

โ€œAn kama wadanda suka shiryawa kasa juyin mulki a ranar 5/5 wanda Benga Delsu da Bello Makarfi ke jagoranta. A yayin da aka shiga hasko fuskokin su daya bayan daya, kafafuwan su da hannaye duka daure cikin ankwa abin babu kyawun gani.

Suka kafawa Daddyn su ido kuriiii, abin tausayi tamkar sa zuko shi daga akwatin talbijin din. Cikin kwanaki biyu kacal ya rame, ya yi baki, ga wata kasumba ta tashin hankali da ta baibaye fuskar shi mai zati da kamala, kan shi a sunkuye, tun suna kuka kasa-kasa har suka rikice gaba daya da kakkarfa, Faisal ne ya mike ya finciko wayar T.B din ya hada ta da garu.

โ€œAllah Daddy ba zai yi haka ba, wannan sharri ne, sharrin..โ€

Ya ma kasa karasawa saboda takaici da kunar zuci. Duk gidan ya koma tamkar gidan mutuwa, Inteesar tun zuwan ta da ta riski labarin, ta fadi ta sume, aka samu ta farfado har lokacin kudundune take cikin bargo tana rawar dari, zazzabi da masassara suka rufe ta, hakoranta sai karo suke da juna kawai ji ka ke kaf-kaf-kaf.

A ranar Najib da Bello suka iso, washe gari sai ga Nasir da Yasir su ma a gigice, Nasir mai raguwar zuciya nan falon Hajiya ya zube yana kuka riris shi da kananan kannen shi, ita kanta Anti ta fita hayyacin ta ba kadan ba, bata ko iya rarrashin su.

Najib ya ce,

โ€˜Me zai sa Daddy ya sanya kan shi cikin wannan balaโ€™i?โ€

Shi ko Faisal rantsewa ya yi da Allah ya tabbata Daddy ba zai taba aikata abinda ake zarginsa da shi ba, saboda president aminin Daddy ne na kut da kut tun suna NDA a Jos suke tare har girman su har tsufan su ba a taba jin kan su ba balle a same su da wani sabanin raโ€™ayi, ya ya za a ce an hada baki da shi a kashe shi? Sun rasa ya za su yi? Sun rasa wa za su kai wa kukan su a yanzu ya dube su, yadda kasa take cike da su Daddy a wannan lokacin.

Sai Saratu ta share hawaye ta ce,

โ€œYa Najib, ni ina ganin mu taru mu yi ta adduโ€™a da kan mu kawai, in Daddy ba laifn shi sai ka ga sun sako shi da kansu a lokacin da ba mu tsammana ba, amma duk inda za ku je a halin yanzun ba wanda zai saurare ku.โ€

Sai a yau Hajiya Nafi ta taba daga ido ta dubi Intisar a rayuwar ta, duba na mutum dan adam, ta ce, โ€œYarinya karama ta fi ku tunani, amma kun tsaya kuna ta koke-koken banza amfanin me ke gare shi?โ€

Washegari Najib ya nemo bisa din mutum biyar da shi da Faisal, Yasir da Hajiya sai Anti, suka dunguma kasa mai tsarki domin yin dawafi na musamman kan Allah ya fiddo mijin su/mahaifinsu cikin ruwan sanyi, suna adduโ€™a fuskokin su jike da hawaye, tuni an manta da wani kishi, to ina wanda ake yin kishin domin shi?

Gidan farin ciki gidan Brigadier Bello Makarfi, komawa ya yi tamkar gidan makoki, dukkan harkoki da walwalar su sun karkatse. A satin Saratu da Nasir suka kamo hanyar kauyen Makarfi. Kallon fuskokin su kawai Baffa Sani ya yi ya tabbatar babu lafiya haka goggo Jimmai.

Nasir ba ya ko iya magana sai Saratu ce ta yi mai bayanin halin da ake ciki hawaye na bulbular mata a guje. Malam ya shiga rarrashin su yana tunatar da su duk wani soja haka ya gada, shiga hadarurruka ba yanzu Babansu ya fara ba, ya ma fi na wannan a baya lokacin da rikicin sojojin Amurka da Saddam Hussaini ya ritsa da shi a Baghdaza, da lokacin da aka kashe Major-General Aguiyi Ironsy ya kuma fito sumul kalau.

Tun a ranar ya tara malamai bila adadin ya raba masu abin sadaka suka dukufa rokon Allah. Duk wani shahararren malami da ya kwana ya tashi a garin Makarfi da wajen ta Malam Sani ya kai abin sadaka a taya su rokon Allah ya fiddo Bello, gudan jinin shi kuma bango abin jinginar su.

Nasir ya bude account din shi ya karowa Baffa kudi masu yawa.

Watan su Hajiya guda a Saudiyyah kafin su dawo. Gidan ya kuma komawa tamkar gidan mutuwa harkokin su suka kara katsewa, na makaranta sun kasa komawa, masu aiki su kasa komawa bakin aikin su, kowa na ji da yadda ya ke ji a zuciyarsa. Najib ya yi trying wayar Aminu, kwata-kwata ya daina amfani da layin, ya aika mai ta e-mail babu amsa. Da yamma ya shiga dakin Hajiya sai ya tarar da ita tafukan ta cikin fuska tana ta razgar kuka. A sanyaye ya zauna ya sunkuyar da kai ya ce.

โ€˜Hajiya duk fa abin da ya yi zafi maganin sa Allah ne.โ€

Hajiya Nafi ta ce, โ€œNa san da haka Najibullahi. Tunanin Alโ€™ameen ke damuna, baya ko tunawa da mu balle halin da muke ciki. Mun yi da za shi Hull Unibersity, cikin ajiyana na banki na tattara na tura Ali dan kanin mahaifina ya binciko min Aminu a England, address din da ya bar mini ka san me ye? An ce kwata-kwata babu mai irin sunan shi a cikin shekarun da muka ambata da ya zo daga Nigeria.

Na rasa inda zan sa kaina in ji sanyi. Idan na rasa Aminu na rasa ubansa ina zan sa kaina?โ€ Sai ta kara tsanannta kukanta.

Najib ya lankwashe kai abin tausayi ya ce, โ€œAmma dai Hajiya kin san dai cikin kowanne hali Ya Aminu zai iya kula da kansa a koโ€™ina.

A ganina bai dace kisa damuwar inda yake a ranki ba har ya zo ya dame ki, hakan yana iya zamo miki illa, kuma a cikin wannan halin da muke ciki na kewar mahaifin mu ke ma mu rasa farin cikin ki akan ya Aminu shi kadai ransa? Tunda dai kin san ko ba dade ko ba jima zai dawo ne?โ€™

Ta ce, โ€œYa kuwa bazan damu da inda Alโ€™ameen yake ba, alhalin duk cikin ku babu mai kauna ta tamkar shi? Babu mai gudun bacin raina tamkar shi? Babu mai son abin da nake so tamkar shi? Ba mai damuwa da bakin cikina tamkar shi? Ya ya kuwa ba zan damu da inda yake ba?โ€ Najib dai ya yi ta lallashin ta har ya samu ta yi shiru.

Washe gari ya zauna ya zanawa Aminu duk halin da suke ciki ta cikin yanar gizo internet yana rokon shi ya zo su taru su san hanyar da za su kubutar da mahaifinsu da ya tabbatar da ba ya da laifi. Ya tunasar da Aminu yanzu ne fa ya dace su nunawa ubansu kaunar da ya wanzar da rayuwar shi a nuna masu. Ya tabbata ya kammala koma wane irin karatu yake yi cikin wadannan dumbin shekaru amsu yawa da suka gabata. To amma me?

Daga Ameenu no reply har tsayin sati guda, wannan ya kara tunzura โ€˜yan uwan. Sai a kwana na takwas ne ya cillo wani matsiyacin rubutu don a ganin sa ai abin da ya jiyewa Daddyn kenan tun farko da ya yi ritaya amma shi bai jiyewa kansa ba.

Rubutun Alโ€™ameen Bello, ya nuna bai damu ba, bai kuma da ranar barin inda yake, domin America, ta zama wani ginshiki na farin ciki da kwanciyar hankali a gare sa, ta yadda har bai jin wani abu da ya shafi gidansu zai sa ya baro ta. A takaice dai ga abinda Ameenu ya rubutowa dan uwansa Najib.

America teaches the cultivation of peace of mind to me, not as an escape from life into protected quiescence, but as a power center of which comes driving energy for constructing personal and social living. One is responsible for the outcome of what would be sealed.

Alโ€™ameen Bello

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.9 / 5. Rating: 17

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siradin Rayuwa 15Siradin Rayuwa 17 >>

5 thoughts on “Siradin Rayuwa 16”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
ร—