Skip to content
Part 26 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir Takori

Littafi Na Uku

Lahadi, Jumada-Awwal

Watanni Biyu Bayan Barin Faisal

Satin Daddyn kwata-kwata biyu da fitowa ya shiga sabon ofis din sa a gidan shugaban kasa. Cikin watanni biyu rak arziki ya ci uban nada, rayuwa a gidan Brigadier Makarfi ta dawo sabuwa ful arziki wane shekarun baya.

Sai da hankali ya natsa aka mance komi Aunty Saratu ta farkewa Daddyn gaskiyar Saratu bata kammala karatu ba.

Daddy yayi ta fada  har yana haki kan don me tuntuni bata gaya masa ba, da yanzu bata yi zangon karatun ta na farko a aji shidda ba, gashi shekara ta zo tsakiya tilas abarwa sabuwar shekara mai kamawa in Allah yayi tsawon rai. Amma kam ran shi ya matukar baci inda ya dauki duk laifin ya daura akan Anti Saratu.

Ranar Lahadi, cikin sabon watan Jumada Awwal, ta shirya cikin wani lallausar material baki wuluk mai yarfen jajayen furanni. Curarraren gashin kanta ta nade shi tsaf cikin dankwalin kayan ta yadda baka ganin ko sili daya, kafar ta sanye cikin (bed-shoe) watau takalmin bakin gado, sannu a hankali take sauka daga benen sassansu tana bin matattakala cikin nutsuwa da yaukin ta na musamman da Allah ya hore mata.

Tayi amfani da sassanyan turare (Week-End Burberry) sanyin kamshin na tashi daga jikin ta kadan-kadan inda duk ta gifta har ta iso falon hutawar Daddyn, da yake ranar Lahadi ce, ya kan kasance ne a falon yana ‘browsing’ tun   safe har bayan karfe hudu na yamma baya zuwa ko’ina.

Ta sakko ne musamman da niyyar bashi labarin Hidayah da Hunainah Bashir Sambo, kawayen ta na makaranta da suka shaku, bata taba yi mai zancen su ba, shi ko Daddyn komi nashi ita yake fara gayamawa kafin kowa a gidan har matan sa kuwa, tana ganin Daddyn zai taimaka ya binciko mata inda suka koma a Korea da adireshin su, kullum da tunanin da take kwana take tashi kenan, don dai hankalin su bai kwanta bane sai ko yanzun da take ganin ya dace Daddyn ya san da su Hidayah, har abada bazata taba mancewa da su ba.

Yaran Sun zauna cikin kwakwalwar ta (like the screen saver of her imagination) Musamman Hunainah, kauna ce mai karfi take masu da har ta kan tambayi kanta, da su da Ya Faisal, wa ta fi kauna?

Ta same shi da ‘laptop’ din shi ne kamar yadda tayi tsammani, sai ta ja kujerar da ke fuskantar shi ta zauna, suka dubi juna suka yi murmushi ta ce,

“Daddy an tashi lafiya?”

Ya ce, “Tunda ki ka ganni a nan ai zance ya kare, kin san tambayarki itace amsarki Saratu….”

Magana yake amman hankalinta baya tare da shi, yana ga allon kwamfutar. Wani kayataccen rubutu ne Daddyn yayi, yayi mai ‘design’ mai kyau, da gani yayi ne don ado kawai cikin kwanfutar ba don ya aikawa wani ba, kalolin da aka kawata rubutun da su masu daukar ido ya dubesu ne koda bai yi niyya ba.

A gurguje ta shiga bin rubutun bata sani ba ma a fili takeyi ba.

“Although he refused to assist me when I needed his assistance most, I should, however, forgive him wholeheartedly.”

Ma’ana “Duk da cewa ya ki taimakamin a sanda nake tsananin bukatar taimakon sa, duk da haka zan yafe mai da zuciya daya”.

Cikin ‘yar karamar muryar ta ta ce, “Daddy waye wannan?”

Yace “Yayan ku Al’ameen ko kin manta shi?”

Ta kai hannu ta zare gilashin ta a hankali ta ce, “Al’amin kuma? Waye haka?” Cikin tsananin mamaki, zaka iya karantar hakan karara cikin abnormal (marassa lafiyan) idanun ta.

“Muna da wani Yaya ne Aminu Daddy ko dai cikin dangi ne ta Makarfi?” Mamaki ya kama Daddy, ya ce,

“Sanda Aminu ya bar kasar nan bakiyi wayau ba, Aminu ne ya janyo maki laluran ido, har da shi muka kaiki asibiti a Jeddah ba mamaki da baki san shi ba, abin mamakin shine ko sunan shi baki sani ba?”

Ta ce, “Kwata-kwata ban taba ji a bakin kowa ba, ba wanda yake zancen shi daga Ya Faisal, Ya Najib har su Mamar mu ban taba ji ba.”

Yayi murmushi ya ce,

“Su Najib ai haushin sa suke ji, sunce sun fidda shi a layin ‘yan gidannan.” Abinda ta lura da shi shine idanun Daddynsu cike suke da kaunar dan shi Al’ameen da bege mai tsanani. Ta gyara zama ta ce,

“Daddy a bani labarin Ya Ameenu?” Ai kamar mai jira ta tambaye shi, ya shiga bata labarin Al’ameen tun daga rayuwar shi ta kwaleji, hazakar shi irin nata, da yanayin mu’amalar shi da mutane. Ya ce,

“Mutane da dama na mai mummunar fahimtar girman kai da wulakanci, amma ni nasan Al’ameen dina (gentle) ne kawai. A ‘ya’ya na ba mutun irin Al’ameen Saratu, domin shi din genius ne (mai madaukakiyar iyawa).

Al’ameen nawa, yana kaunata sosai Intisar, ban taba zaton jin dadin turai da kyale-kyalen ta zasu sa ya mance ni ba balle…” Bai iya ya karasa ba sakamakon hawaye da suka shimfido mai a guje.

Ya juyar da kai don bai son Sartun ta gani amma ta ganin.  Tuni itama nata idanun suka cika da kwallah, tayi azamar mai da gilashinta tasa tissue tana share hawaye ta kasan gilashin. Tsana da haushin wannan Yaya Al’ameen ya dirammata tunda kuwa har zai sa Daddy kuka da azabar kewar shi, bata san sanda bakin ta yayi subul da cewa

“Daddy maiyasa kake son Al’amin har haka?”

Yayi murmushi ya ce, “biyayyar sa.

Ban taba ganin yaro mai gudun bacin ran iyaye a duniya  irin Al’ameen ba. Yana jin maganata yana yi mun biyayya, ban taba cewa ya bar abu yaki bari ba sai a kanki.

Ya gaya mun sabida nadamar abinda ya aikata gareki ne ya bar mu kwata-kwata don aganin shi bashi da amfani a gareni…”

Ya kwashe labarin komi ya gaya mata, bata yi wani mamaki ba, tunda kuwa dan Hajiya Nafi ne, ba illata ta ba, ta tabbata ko konata ne Hajiya zata iya sawa a yi.

To amma albarkacin wannan son da ta ga Daddy na yiwa Al’ameen sai taji itama tana son shi, bata kullace shi ba ko kadan.

Tabbas a lokacin zai kasance yana yaro ne cikin gigin kuruciya, tana da tabbacin da zai zo a yanzun he’ll be a caring brother (dan uwa mai nuna kulawa). Tace

“Kaayi hakuri Daddy, ni na tabbata Al’amin zai dawo a lokacin da bamu zata ba.” Ya ce, “Kayya Intisar, Aminu fa har gaya mai akai an kulle ni, akan laifin da ya tabbatar ba zan taba iya aikatawa ba, amman yace wai zaman Amurka ya fiye mai kwanciyar hankali bazai dawo ba.

Koma menene laifi na ne da tun farko na amince mai ya tafi.

Ban taba kuka akan son dan da na haifa ba sai a kan Al’ameen. Ameenu yaro ne mai matukar shiga rai don haka fidda tunanin shi a lokaci guda, abu ne da bazai yiwu ba.

Tunanin sa na azabtar da ni Saratu Ina kokari ina dannewa ne kawai don bana son kuma ku shiga damuwa”.

Inteesar tayi zuruuu tana sauraren Daddyn duk tausayin sa ya nannadeta, amma a ranta cewa take Allah ya isa tsakanin ta da wannan Ameenun, kuma wannan Al’ameen anyi tsinanne, tunda kuwa har zai iya sanya rayuwar Daddyn su a wani hali bayan wanda ya fito, kuma akan sanin kansa, suna murna duk wata matsala ta kare?

Shin shi Ya Al’amin din nan bai tsoron hakkin Daddy ya hana shi kwanciyar kabari?”

Ta tausasa halshen ta ta dukar da kai cikin matsanancin takaici ta ce,

“Ba dai biyayya Al’ameen yake maka ba Daddyn mu?  To na yi alkawari tsakanina da Sarki Allah zanyi ma biyayya Daddy irin wadda Al’ameen bai taba yi maka ba! Zan maye maka gurbin Al’ameen.

Zan wanzar da rayuwa ta a biyayyar ka, zan dauwama a cikin umarnin ka in har bai sabawa mahalicci ba, bazaka taba sani abu in ki yi ba koda ya fi karfin lafiya, rai da abinda na `mallaka; sai dai in mutu a cikin umarnin ka Daddy!”

Kalamun ta sun matukar bashi mamaki, hakannan sun girgiza shi amma bai nuna ba, sai yai murmushi ya shafi kanta da hannun shi na dama. Shi kansa ya san hakan a tun ranar da ya daukota cikin tsumman goyonta a dokar daji. Ya ga alamun hakuri, biyayya, kyautayi da jin kai tattare da ita.

Yana kaunar ta, kaunar da baya yiwa daya cikin ‘ya’yan sa bayan Al’ameen. Ta ce “Wai shin ba’a bin sawun Yaya Aminu ne?”

Ya girgiza kai, “Ba wai kudin ne babu ba Saratu. America kasa ce mai girman gaske, (It’s the greatest country of the world). Abin takaicin shine yana birnin Miami yana buya a cikin Florida kar mu gan shi ko kar mu san inda yake. In banda adireshin sa na e-mail ban san komi game da shi ba a yanzu.

Kuma ke a tunanin ki yaron da ya watsar da iyayen sa akan kansa, bai son ganin su kina ganin ya dace iyayen su zubar da darajar da Allah yai masu ta iyaye su nemeshi?

Ai har kullum da ke neman albarkar iyaye ba iyaye ke neman albarkar da ba.

Yaran yanzu ne ka haife su amma baka haifi halin su ba. Duk in da uba ya kai ga gwada masu kauna da nema masu farin ciki su sai sun sashi kuka. Ba zan nemi Al’amin ba koda zan mutu ne ban gan shi ba, koda na mutu, Saratu ki gayawa Yayanku Aminu, son nan da nake mishi tun yana gudan jininsa, ina zumudin a haife shi in samu magaji, da kasancewar shi buri na ba abin da ya canza har gobe sai ma abinda ya karu.

Kuma har cikin raina na yafe mashi kuncin daya dasa mani na shekara da shekaru.”

Sai ta rufe bakin Baban su da tafukan hannun ta, kamar tace wayyo Allah! Sabida bakin cikin Al’ameen da mutuwa da Daddyn ke ambatawa kansa.

Ta ce, “Insha Allahu Daddy ni da kai, zamu gayawa Ya Ameenu wannan. Daga yau zan fara Addu’a duk inda Al’ameen yake, Allah ya karkato da hankalin shi gida Daddy.”

*****

Wani muhimmin abin farin ciki daya samesu bayan kubutar Daddy da ‘yan watanni shine bayyanar matashin ciki jikin Anty Saratu, farin cikin Inteesar a wannan dan tsukin kema kin san ba sai an fada ba. Daddy don farin-ciki makullin mota KIA ya danka mata fara sol ta fara zuwa sabon aikin da ta samu da (Afri-Bank). Gabadaya sun kirayi shekarar da watan Jumada-Awwal; ‘Cikar Burin Shekara Da Shekaru.’

Dukkan Farin-Ciki Na Tafiya Ne Da Bakin-Ciki

Laraba/Ashirin Ga Watan Jumada-Thani

Ranar wata laraba, da saratu ta kira LARABGANA a gareta, ya kama ranar girkin Antinne don haka tayi mata sallama ta nufi sassan Daddy, duk ranar girkin ta haka suke wa juna, babu zancen kunya tsakanin Saratu da diyarta Saratu.

A lokacin cikin ta ya shiga watanni uku duk wasu alamomin mace mai juna biyu sun gama bayyana a jikin ta. To bayan fitar Antin har goma na dare Inteesar na falo kwance cikin (rest-chair) dake falon tana sauraron labarun ‘network’ daga gwanin ta Cyril Stober da Hawwa Baba Ahmed bata san sanda barci mai nauyi ya dauke ta ba, sabida a yau wuni sukai girke-girken Daddy ita da Mamarta ko na minti biyu ba su huta ba.

Ba ita ta farka ba sai karfe ukku na sulusin dare shima sakamakon masifafffen sanyin da taji yana hurata ne, ta yayibi bargo ta ji wayam. Ta mike taga yadda ta bar komi a kunne ta kashe talbijin da ke ta shuuu!  Da sauran kayan wutar da ke falon.

Ta daga labule da niyyar kashe fitilun falon ta je ta kwanta kenan taji motsin ana taba kofa. Cikin ta ya hautsina ji kake kulululuuuu! Musamman data tuna bata rufe ko kofa daya ba bayan fitar anti, a guje ta shige bayan labule ta sandare ko kwakkwaran numfashi ta kasa shaka balle ta fesar.

Ba abinda ta kawo wa ranta a lokacin face gaggan ‘yan fashi ne suka kawo masu ziyara, amma wannan ba karamin abin mamaki bane in akayi la’akari da irin sojojin da ke gadin gidan Bello Makarfi tuni ta soma hawaye, a lokaci guda kuma fitsari ya kulle mata mara.

Bata san sanda ta sakeshi daga tsayen ba.Tsoron ta Allah, tsoron ta kada su taba lafiyar Daddyn ta. Ko wannan shine dalilin yin zancen mutuwa da Daddyn yayi mata a kwanakin baya?

Daga inda take rakube a bayan labule, tana iya hangen kofar shigowa falon su kasancewar labulen shara-shara, kuma dakin gauraye yake da hasken da Allah  bai bata ikon kashewa ba.  

Tana ganin sanda aka turo kofar falon cikin nutsuwa da sanda, ba abinda ‘yan idanun ta basu gane mata ba kasancewar akwai wadatar hasken kyandir kamar safiya. Sanye da bakar zulumbuwar riga, kanta a tsefe, tana rike da bakar kwarya a hannun ta na dama, wata bakar tsuntsuwa ce da ake kira mujiya matacciya rike a hannunta na hagu; Hajiya Nafi ce.

Kanta tsaye ta murda kofar dakin barcin Antin ta shiga, tafi karfin awa daya kamin ta fito, tuni numfashin Intisar ya dauke. Ashe bata gama razana da mamaki ba?

Da ta fito daga dakin Antin dakin Intisar din ta afka gaba-gadi. Ji tayi kamar tayi ihu amma sautin ya dauke kakaf.

Me wannan baiwar Allah ke yi masu haka a dakuna cikin irin wannan talatainin dare?

Nan ma tafi awa biyu kamin ta fito. Ta diba gabas, yamma, kudu da arewa bata ga kowa ba, sai kurum ta fice ta jawo kofar. Daga kwaryar har tsuntsuwar, sun bace bat.

Wai a wauta irin tata, sai ta sheko da gudu ta lelleka dakunan ko zata ga in da ta aje masu kwaryar da mujiyar? Tunaninnika iri-iri ke shigar ta. Mafi rinjaye shine Hajiya na bakin ciki da cikin da Anty Saratu ke dauke da shi, shine tazo tayi mata wani mugun abu?

Ta sha jin ana cewa Anti Suwaiba aminiyar Hajiya matsafiya ce ta kuma dade tana son sanya Hajiya a turbar tsafe-tsafe Hajiyar na ki, don ita Hajiya na daga cikin irin matan nan da basu yarda cewa asiri shi zai kwato masu miji ba sai power din su da kaifin bakin su.

Wato yanzu cikin Anti yasa ta bi layi kenan? Har aka yi kiran assalatu tana rakabe a bayan labule cike da tunani da tsoro.

Ba ita ta fito ba sai karfe biyar na asuba a lokacin da ta ji masallacin da ke makwabtaka da su ya kira sallah, jikin ta ba inda baya rawa ta shiga toilet din dakinta ta dauro alwalar sallar asuba, ta fara da raka’atainil fajr kamin ta bada farali. Ta kara da nafilfili na musammam tana mai rokon Allah ya kare su daga duk wani mai nufin su da mugun abu. Ta cigaba da karanta Suratul Kahfi har zuwa wayewar gari. Nan akan sallayar barci mai nauyi ya sureta.

Da safe ta fita baiwa ‘yan aikin su umurnin abinda zasu hadawa Daddy da Anti karin kumallo, sai ta jiyo motsin Antin a daki, kamar tace wayyo Allah! Taso ta gayawa Antin abinda ya faru a daren jiya tun kamin ta shiga dakin gashi ta riga ta shiga.

Tayi tunanin fadar ma bashi da amfani tunda yake ita din ma ai ta shiga, ko ta fada sai dai kurum ta tayar mata da hankali a zo a bata tara daya bata gyaru ba, don tasan halin Mamarta sarai cewa za tai sai anyi abinda za’ayi a gidan kuma kenan ita ta tayar da tarzoma ana zaune lafiya?

Ta amince ta kuma hakkake cewa a duniya babu wanda ya isa yayi masu abinda Allah bai masu ba, to akan me zata dami kanta? Sai kawai tayi watsi da al’amarin.

Sati daya da faruwar wannan rannan Daddy na sassan su, a lokacin tana kwance a dakin ta tana nazarin wani tsohon littafin larabci na Alfu-Lailah (Dare Dubu Daya), kamar a mafarki, sai ta jiyo Daddy na zagin Anty Saratu yana cewa,

“Ke har kin isa ki gaya mun magana, naki in maidata makarantar, ko an gaya maku tono kudin nake?

Idan bazaki maidata FGC Kazauren ba da kudin ki, kar Allah ya sa ta je, an gaya maki na damu da harkar ku ne matsiyatan banza da baku san ku taimakawa mutum ba koda kwandala sai dai ya baku, mts!” Ya ja wani dogon tsaki ya fice a fusace.

Kirjin ta ya wani irin buga, jikake dammm! Me kunnen ta ya jiyo mata haka? Daddy ne yake cewa bai damu da su ba balle karatunta? Kai, wannan mafarki ne it’s only a bad dream (mugun mafarki ne kadai) bazata taba amincewa da abinda kunnuwanta suka jiyo mata a yau ba. Tayi saurin yasar da zancen shiyasa akace sauraron hirar mutane ba kyau, don wata rana bazaka jiyo wa kanka alkhairi ba.

To Allah ya gani dai ita ba saurara tayi ba shi Daddyn ne yake yi da karfi. Ta kudurce daga yau koma waye yake magana da karfi, in har ba da ita yake ba to zata toshe kunnuwan tane.

To sai me? Ta hadawa daddy abincin rana na Dolmah Stuff Cabbage, Fried Beef da Stuff Atomy a washegarin ranar. Duk gidan ya karade da kamshi a lokacin yana sassan Hajiya, to ta saba inda duk yake nan take kai mai abincin duk ranar girkin Antin in tayi ko antin tayi.

Daddy da Hajiya na bisa tebur suna cin abinci, tayi sallama amma ba wanda ya amsa bata kawo komi a ranta ba cikin dariya tace “ayya Daddy, nayi latti ko?”

Dai-dai sanda ta aje tray din a gabansa. Wani uban kallon tsiya da ya bi tangarayen da shi ya tsoratata ya ce,

“Ke daga yau ke da uwar ki kada ku sake wahal da kanku wurin dafa min abinci, don na gaji da gishirin da kuke cika min, right?”

Idanun ta suka ciko da kwallah, gwiwoyin ta suka sage, ta tuna tun tashin ta kullum ta yiwa Daddy abinci yabawa yake ya sa mata albarka, haka anti Saratu. Dai-dai da rana daya bai taba cewa ga abinda bai mishi ba a girkin su sai girkin Hajiya.

Rannan ya ce inda ba’a kan idon shi anti Saratu ta karanci ‘Insurance’ ba da ya ce nutritionist ce, ko yaushe suke cika gishirin oho! Abinda ta ji kwanaki ke neman zama gaskiya.

A tsukin ta lura kwata-kwata Daddy ya dauke kafar sa daga sassan su haka Aunty Saratu ta daina girki amma dai-dai da rana daya bata taba nuna mata hakan a fuska ba.

Data gaya mata abinda yace kwanaki game da girkin su sai tace wai itace tayi kuskure ta sanya mishi gishiri (3-spoon) kwanaki a dankali. To amma me?

Kwanaki ta shiga dakin Antin sai ta tadda ta tana wani rubutu da ‘chalk’ a bayan kyauren bandakin ta, tayi abinda ya shigar da ita ta fito. Da ta tabbatar antin ta shiga wanka sai tazo ta karanta, ba komi bane illa (off-duty 29/9) wato Daddy ya dakatar da ita girkin sa a ranar ashirin da tara ga watan tara.

A da, kullum ta Allah masu aikin gidan kan shigo da kayayyakin abinci iri-iri daga katon na juices zuwa na sauran kayayyakin bukatar yau da kullum amma yanzu kwata-kwata ‘store’ din su ba komai duk na Hajiya Daddy ke cewa su kai.

Rannan taga Antin ta debo kudi ta kira direban cefanen gidan tana lissafa mai abubuwan da zai sayo mata. A daren ranar ta shiga dakin Antin ta gaya mata kawar ta Hajiya Zainab na kiran ta a waya, sai ta taddata rub da ciki tsakiyar gadon ta tana girzar kuka.

Tayi saurin komawa da baya ta kife wayar ta kifa kanta a jiki itama tayi ta kuka har Allah ya gajishsheta. Ta tabbatar Anti na cikin matsananciyar damuwar yadda Daddy ya yi watsi da su. To amma maiyasa bazata gaya mata ba su taru suyi ta kukan tare?

A rayuwar ta, bata taba ganin Anti tana kuka ba. Mace ce tamkar da maza; zuciyar ta mai tauri ce, ba kowanne kankanin abu ke sata kuka ba. Shin ko wannan  shine gaskiyar abunda kunnuwan ta suka jiyo mata kwanaki?

Me yasa su basa dauwama a farin-ciki ne? Ta tambayi kanta wai meyasa rayuwar su ke juyawa ne tamkar a majigi?

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.1 / 5. Rating: 17

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siradin Rayuwa 25Siradin Rayuwa 27 >>

3 thoughts on “Siradin Rayuwa 26”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×