Skip to content

Siradin Rayuwa 3 | Babi Na Hudu

4
(12)

<< Previous

Lagos/ Talata

25 Ga Watan Shawwal

Dr. Hajjo Hassan Biu, kodayake da yawan dalibanta a LASU sun fi kiranta da Dr. Biu, sunan Biu ta sameshi ne daga mijinta Hassan wanda yake mutumin garin Biu ta jihar Borno. Ta baro ofis da karfe hudu dai-dai na yamma a matukar gajiye cikin motar ta Legend (One Door), sauri take data kai gida ta yi ‘freshen-up’ wannan gajiya da ta kwaso ga Maigidanta da yaranta tasan suna nan suna tsimayen ta ne ita kadai, dai-dai (junction) din da zata dauki titin Victoria Island danja ta tsaidasu, ta yi tsakin takaicin bata mata lokacin da za‘ayi a ranta ko tana tsinewa wannan traffic-congestion na garin Lagos, tsayin minti ashirin ba’a basu hannu ba, ta sake tsuga tsaki ta bugi sityari tace “damn it” kana ta sake duba agogon hannunta dana motar baki daya, yanuna karfe hudu dai dai na yamma dai-dai kokacin da wani Bayerabe ya zuro mata tulin jaridun mako ta tagar motar ta.

Ta harareshi cikin takaici amma me? TELL Magazine ta wannan ranar dauke take da wani ‘headline’ da ya sa jikinta tsuma, da hamzari ta dauka ta bashi kudinsa, tabi rubutun a gurguje da mamaki “INNOCENT-MAKARFI, RELEASED!” Ma’ana “an sake shi a matsayin mara laifi” a shafi na gaba kuma “Makarfi celebrated his sixtieth birthday, at Nicon Noga, on 2/2…… watau Makarfi yayi bikin cikar sa shekaru sittin a hotel din Nicon-Noga dake Birnin Tarayya ranar biyu ga watan biyu, sai kanun labaran yadda kowanne ya kasance.

A dai-dai lokacin da danja ta baiwa bangaren da take hannu, tasa ma motar giya a guje. Ta yi parking a inda suka tanada domin adana motoci kana cikin sassarfa ta fito, bakar ‘after dress’ dinta rataye a kafadunta haka Jakarta na sakale a yatsunta biyu ko file dinta bata tsaya dauka ba tayi cikin gida, karar horn dinta ya fiddo ‘ya’yanta a guje suna “Mummy oyoyo!”

Ta daga karamar ta café ta ce “my dear Dijah, ince ko kinci abinci sosai?” Ta daga mata kai alamar eh, don bata fara magana ba amma tana gane duk abinda aka ce da ita.

Ta kama hannun ‘first born’ dinta Bishir tace,

“Kawu na, Daddyn ku na ciki ko?” Ya ce

“Eh, tun dazu ya dawo, amma yace yau sai anyi miki bulala, kin dade baki dawo ba”

Ta bude baki, “Wayyo ni Hajjo, ka ce yau sai buzu na.” Ya ce,

“Ai boye ki zan yi cikin rigata Mummy.” Tana dariya ta ce,

“To na gode Kawu na, nasan bazaka bari Daddy ya duke ni ba.”

A haka suka karisa falonsu tamkar wadanda suka shekara basu ga juna ba. Da sassarfarta ta tura kofar ‘bed-room’ din shi, baya nan. Tayi murmushi ta dan saurara don ganin ta inda zai bullo, sai ta jiyo karar zubar ruwa a famfo kadan tabbacin yana bandaki, ta karisa jikin kofar ta kasa kunne ta ce “can I come in? “(Na iya ya shigowa?).

Ya ce, “No” Ta yi dariya ta murda kofar tana cewa,

“Ai ni mazaunai ce, dole a zauna da ni.” Ya ce,

“Idan duwawun ya zama kakkausa, sai a yanke shi shi asa na roba.”

Yana tsaye ne jikin ‘sink’ saye da gajeren wando kadai yana wanke hannunshi da kamkamsan sabulun ‘cleopotra’ bai ko juyo ya dubeta ba, ita ko jikinta ba inda baya rawa rike da jarida, ya juya mata baya ya soma cuda farin hankicinsa cikin ruwan da ke zuba daga famfo ta ce,

“Pls, Baban Bashir dubar ni, Allah ba wasa cikin lamarina.” Bai dubetan ba dai ya ce,

“Ni kuma nace bazan dube kinba, tunda kin zama kakkausa ba sai in cire in sa mai laushi ba?” Ta ce kaman zatayi kuka,

“Be serious, don Allah?” Ya ce,

“Idan mutum ya dauki al’amarinki da muhimmanci Hajjo shine gaula, to naji zan dauwama a gaula na bana bukatar zama serious, dubi agogonki karfe nawa?” Awoyi nawa kika kara kika barmu cikin yunwa nida yara bayan na gaya miki a daina basu abincin masu aiki?”

Ta langabar da kai gefe guda, kana ta janyoshi ta baya, fuskar ta bisa kafadunshi ta ce, “To bakwa shiga kitchen din da kanku Baban Bishir?”

Ya dan juyo ya dubeta da wutsiyar ido, Hassan ya san Hajjon shi sarai, har yanzu tana shimfida mai wautarta ne yadda ta ga dama, uwar ‘ya’ya biyar a yanzun amma in ta kwaba mai wani shirmen ko dan ta Bashir baya yi ba, ya juya ya cigaba da abinda yake ba tare da ya ce mata komi ba.

A ran sa ko cewa yake, “Allah dai ya shirya min ke.”

To har gobe haka Dr. Hajjo ta ke, malama a sashen Harsuna a (Lagos State Universisty) tana karantar da harshen Faransa zalla. Ta cigaba da magiyar yayi hakuri ya saurareta, ya fito daga (toilet) din zuwa dakin barcin su inda duk ya aje kafa nan zata mayas, tana tirjiya cike da shagwaba.

A dakin barcin su ne ta russuna ta kama tafin kafarshi ya ce, “Wai ke wace iri ce ne?” Ta kakalo wani guntun hawaye can karshen idonta tace “Allah Babansu Basheer traffic congestion ne ya tare ni, kayi hakuri ka yafe don Allah ?”

Ya tintsire da dariya ya dauki jaridar ta yana dibawa. Dr. Hassan Biu har kullum ba mace a idonsa tamkar Hajjo, wautarta kuwa kullum sai abinda ya karu shi dai hakannan yake son kayar sa.

Daukaka kan daukaka suna gani a rayuwa don a yanzu haka Dr. Hassan Biu shine Ministan Kariya na kasa wato (Defence Minister), ‘ya’yansu biyar cif maza uku da mata biyu, Bashir mai sunan Babansu Hidayah kuma Kawun da bata da ya shi a duniya sai Hakimi (Abubakar) da Hafiz, Hannatu mai sunan mahaifiyarta kuma (name-sake) din Hunainah tana ce mata Maama, Dijah itace auta ta kan ce mata (Yaya Dijah) don sunan Yayar ta Hadiza ne.

Ya zauna bakin katafaren gadonshi ta zauna bisa carpet tace, “don Allah bude jaridar nan mana? Allah na kasa karantawa duk jikina rawa ya ke,”Ya dubeta sosai ya ga yadda ta susuce ya dan dubi shafin jaridar ya ce,

“Shin ina ruwana da (birthday) din Janar Makarfi?” Ta ce,

“Wai wane Makarfin su ke nufi?” “Yace “Tsohon Brigedier General Bello Makarfi, kin san ya fita sharrin ‘coup d’état’ (juyin mulki) da su Janar Delsu suka tura shi, a yanzu shine mai baiwa president (shugaban kasa) shawara kan harkokin Mulki.” Ta ce  wadanda suka zauna nan ‘opposite’ (gida mai kallon) na mu shekarun baya?”

Ya ce” eh, ai tun kan a kamashi suka tashi daga nan, wai ke kin san shi ne? Kin ce don Allah in karanta kuma kin isheni da tambaya kin hanani karantawar, kin san kina son ki karanta ki karanta abunki mana” ta ce “Baban Bashir, be serious don Allah, shin a wane gari Makarfi ya ke yanzun?”

Hassan ya cika da jerin gwanon tambayoyin matarsa kan Janar Makarfi, kishin ‘yan mazan ya motsa ya ce a hasale.

“So what in na gaya maki Abuja ya koma da zama? Sai ki dau mayafi ki yafa ki tafi, isn’t that good?” Hajjo ta kwantar da kai tace “Alasabbinani, maida wukar, ba abinda ya hada ni da shi baya ga Yaya Hadiza da tace diyarta da aka sace tana jaririya, su Hidayah sunyi makaranta daya da yarinyar a Riyadh, har suka kaita gidansu ta ganta ta gane ‘yarta ce Fatima, kuma wai yarinyar ta taba gayama su Hidayah cewa anan Lagos gidansu yake, gidan Bello Makarfi na nan Victoria.

Wancan zuwan da Ambasada dasu Hunainah su kai ai kan maganar ne, muka je gidan a lokacia yana kulle. Ashe iyalinsa sun tashi…” ta kwashe komi dai ta gaya masa tun farkon al’amarin, ta kare zancen ta da cewa,

“Abinda yasa tun tuni ban gaya maka ba, zancen ne naga ba wani ‘logic’ (makama) ba, to amma yadda ta dage ‘yar ta ce ta gani, sai duk nima naji jikina na bani yakinin cewa hakanne, ka san UWA fa a kowanne hali dan ta-dan-ta ne, ba kuma zai taba boyuwa gareta ba walau girma, tsufa ko kuruciya.

Kana sane da cewa har yanzu lafiyarta gata nan ne kurum sabida nasihohin mutane, Hassan ka taimake mu ka kuma ceci rai don Allah?”

Jikinsa yayi sanyi lakwas har bai san abinda zai ce ba. Hajjo ta daura hannayenta bisa kafadunshi tace.

“Baban Bashir, farin-cikin Yaya fa shine nawa, bani da kowa a duniyar nan sai ita, ina boye maku damuwata ne kawai akan lamarin nan don bana son tayar da hankalin ku kamar yadda Yaya ta tayar da na Ambasada, ‘pls do something’ (kayi wani abu) mana”.

Hassan ya dubi matar shi  yana kallon yalwatacciyar sumarta ta filanin usli, idanuwanta duk sun cicciko ya ce,

“Hajjo, ji ni nan don Allah kar ki min kukan nan naki, I’ll try my best (zanyi iya kokori na) amma kin san mutane haka ‘top military’ irin su Makarfi dosar su da wani al’amari makamancin wannan sai anyi kyakkyawan shiri, hakannan uwa-uba shaidu, shin wacce shaida muke da ita na cewa ‘yar shi tamu ce?

Wannan kwata-kwata baya a tsarin shari’ah kuma ya haura doka mai kare ‘yancin dan-adam tunda bamu da wata sahihiyar shaida. Abinda yafi yanzu ni zan fara zuwa Abuja inyi bincike in tabbatar in ma har yana da ‘ya mace a gidan, don a sanin da nayi wa Makarfi sanda suke makotan mu ya’yansa tara ne duk maza ba mace ko daya.

Kai mata ma dai da rigma kuke kuma dole a biku da yadda kuke so ana so ko ba’a so, in ba haka ba yarinyar da aka ce ta bata cikin tsumman goyo, a kauye, itace za’ace an gani a birni irin Riyadh, birnin da ya tara al’ummar cikin duniya, ko dayake kamar yadda kika ce din ne UWA ce bazan musa mata ba.

Amma da wani ne Allah ba ma zan sa bakina ba cikin wannan al’amari mai rikitarwa. Idan na tabbatar da komi zan shirya mana ‘visa’ zuwa Korea sai mu taho tare da su gabadaya, ni ina cikin hutun sati biyu, ke kuma na san kwanannan zaku shiga ‘long-vacation’ (dogon hutu na Jami’a) ko? Sai a shirya mai yiwuwa, hakan ya yi miki?”

Tayi murmushin jin dadi, tabbacin ya faranta mata ta ce “nagode kwarai, Honey. Allah ya kara dankon kauna”.

Minister bai yi sanya ba, a washegari ya bi jirgi zuwa Abuja, saida yasa akai mai kwakkwaran bincike kamin da suyiwa gidan tsohon Brigedier Bello Makarfi tsinke shida ‘yan rakiyarsa, amma cikin sa’a basu sami ganin sa ba yana dakin ‘meeting’ tare da shugaban kasa.

Duk da haka Hassan ya baiwa sakatariyar shi ta gida katin shi wa Advisern, ya kuma bar daya cikin yaranshi yayi masu bincike kan ‘ya’yan Brigedier cikin siyasa irin tasu.

A washegari ya tabbatar mai akwai Inteesar ‘ya mace daya kwal cikin ‘yan mazan ‘ya’yan shi amma a yanzu haka uwarta bata gidan tana hannun kishiyar uwarta ne.

Ya ce shima ya yi nasarar samun wannan cikakken bayanin ne daga bakin Ado direban gidan, ta hanyar hilatar shi da cewa ‘ya’yan Birgediyan ne suke birgeshi da da mace a cikin su da ya aura, shine yake gaya mishi hakan.

A ranar Hassan da jama’arsa suka baro Abuja. Yana cike da dokin ganin farin-cikin Hajjon shi, cikin wautarta watakila tace goyon shi zata yi har da majanyi da juyi.

Ya ko gani, har ya gode Allah.

Da wannan suka durfafi kasar Korea don kulla mai yiwuwa. Zuciyar Hajjo dai bayan farin-ciki cike ta ke da taraddadin kada Allah yasa su je su kwaso mutane kasa-ya-kasa a zo a ce Bello Makarfi ya sake canza garin zama.

Kauyen Makarfi, Cikin Garin Kaduna

Aunty Saratu tun bayan rabuwar su da Daddy tana gidansu a Makarfi, kullum kuma idanunta basa rabuwa da tsiyayar da hawaye duk kuwa da kulawar da lyayenta ke gwada mata. Baffansu cewa yayi Allah yasa hakan shi yafi alkhairi agaresu duka ya kuma kawo mata mijin aure kurkusa, (ya ma manta ciki ne da ita).

Hakan kuma bai bata tsakanin shi da dan dan-uwanshi ba daga matsayin da ya rikeshi watau Da. Duk da cewa shi Makarfin ya watsar dasu gabadaya don ma kar suce ya maida Saratu, don shi yanzu ko mai irin sunanta baya son ji, kafafunshi kuwa rabon da su taka garin Makarfi shekara guda da doriya kenan.

Shi ko Baffan musamman yake nikar gari ya je har offishinsa yace yazo ne su gaisa kurum ya ga lafiyar shi tunda shi ya watsar dashi akan abinda  bai shafeshi ba.

A irin wadannan lokutan Daddy kan ji kunya matuka. Tun yana dari-dari da Baffan har ya dawo ya saki jiki dashi suka koma kamar da, don ya lura Baffan mai kaunar shi ne don Allah ba wai don wata tsiyar hannunshi ba. Don kuwa ko kwandala baya tambayarshi in har bashi ya dauka don kashin kansa ya bashi ba bare har yace ya maida Saratu dakinta.

Daga baya kuma ya wanke kafa ya soma zuwa Makarfin don kansa, amma baya shiga cikin gidan, iyakacin sa falon soro da ya ginawa Baffan don bakin kunya. Hakannan tun bayan fitowarshi yasa an rushe gaban gidan anyi mai zubin zamani an kuma wadatashi da komi na jin dadin rayuwa.

Tun rabuwar shi da Anti ko naira biyar bai taba dauka ya aika mata ba a matsayinta na me dauke da cikinsa. Wannan bai dami Hajiya Saratu ba, don ita kanta mai kudin kanta ce a halin yanzu, a sabili da aikin da ta fara bayan fitowar Daddyn a sanda kuma duniya ta dawo masu sabuwa, sai kawai ta shiga tari, ga wanda Daddyn ke basu ita da Hajiya naira dubu dari-dari duk wata, don haka yanzu ‘account’ din ta cike yake da (millions) gashi kuma ba abinda tsoffinta basa yi mata.

Koda wasa Baffa Sani bai taba daukar carbi da niyyar wai Allah ya gyara auren Saratu da Daddy ba, sai dai Allah ya zaba mata abinda yafi alkhairi a rayuwarta.

To amma Goggo Jummaifa? Kusan kullum sai sun kai ruwa rana da Baffan kan don me ba zai mike ya nema masu makarin asiri ba bayan yana da tabbacin wannan duk aikin tsafin su Hajiya Nafi ne?

To in tsafi suke ita Addu’a ta ke, kuma ko gonakin gadonta zasu kare sai Saratu ta koma dakinta.

A irin wadannan lokutan sai Baffa yace “kema tsafin zaki tafi nena kenan? To ki dinga yi dai kina tunawa duk matar da taje wajen boka ya bayyana mata wani sirri da Allah ya boye ko ya biya mata wata bukata da take ganin Allah ya gaza ko jinkirta biya mata, sai anyi kwana arbain ba’a karbi sallar ta ba, hakannan tayi shirka”.

Goggo Jummai bata tsinkawa don tasan bata nufin kowa da mugun nufi face nemowa diyarta farin-ciki wanda yake a wuyan su iyaye, hakannan ta san boka ta san Malam.

Shi kansa abinda yasa yaki tsoma baki don yana ganin da Saratu da Bello duk daya ne a wajen shi ba wani banbanci, kuma da suyi zaman aure tare da kar su yi, duk sunansu ‘ya’yan sa.

Idan ya yi Addu’ar Saratu ta koma gidan Birgedier yana bukatar abin hannunshi da ya rage basu kenan, wanda shi ba don haka yake kaunarshi ba.

Ya rungumeshi a sanda yake maraya; ba Uwa ba Uba balle dangi, ya zame masa komai nasa a lokacin shi bai taba haihuwa ba, ya wahala ainun wajen daukar nauyin karatunsa. Ya shiga kwanan kurkuku yafi a kirga akan bashi, don Bello ya zama soja, ya sha zagi gun mutanen kauyensu kan ya daurewa dan Wansa gindin zama dan fashi da makami, a lokacin kai bai waye da ilmin zamani ba, to akan me a lokacin bai ki shi ba sai yanzu don ya saki kanwarsa kan ta ci mai mutunci?

Wane irin tallafi da girmamawa ne bai yi masa ba da ya soma daukar albashinsa na farko a soja, tun kafin a haifi wata aba Saratu? Ba zai ki Bello ba cikin kowanne hali, dukkansu kuma bai ga laifin kowanne ba.

Ya san halin Saratu sarai, raina na gaba da ita balle mijin ta ba halinta bane sam tabbas akwai dalilnta na yin hakan, duk kuma dan-adam yana tare da ajizanci, sannan shi aure rai ne da shi, duk ranar da Allah ya kawo karshen sa zai mutu, ana so ko ba’a so.

Hakannan hakuri da wahalar da suka sha ita da diyarta lokacin da yake kulle, sun cancanci mafificiyar kauna daga gareshi ba wulakanci ba. Dole watsar dasu din da yayi yayi mata zafi. Ya san in aka kawota bango kamar mara tunani take.

Ita ko Goggon tunanin ta sabanin na Baffan ne, cewa take so-so-ne, amma son kai yafi. Da yardan Allah sai Daddy yayi nadamar wulakancin da yayi wa diyarta lokacinne ita kuma zata nuna mishi Nairarshi bata da amfani agaresu.

Ta fannin ita Saratun kullum tunaninta na bisa halin da ta baro Intisar a ciki ne. Ta tabbata Allah ne kadai zai ceceta a hannun Hajiya. A duk sanda tayi rin wannan tunanin ta soma kuka kenan har Allah ya gajishsheta.

Sau da dama ta kan yi tunanin kawai taje ta dauko ta shine mafi a’ala amma tunanin barazanar Makarfin da gudun abinda hakan zai haifar, na tonon abin tausayin da ke rufe daga Daddy ko Hajiya game da Intisar din shine ke tsorata ta.

A watan Najib yaje Makarfi, sun jima suna hira da Antin iyakar kokarinsa yayi wurin boye mata zahirin halinda ‘yar ta ke ciki, yace ne kawai tana nan lafiya koda yake shi ba zaman gidan yake ba yana Enugu.

Wannan ya dan kwantar mata da hankali don lafiyar ta tafi ji ba damuwarta ba. Ta tabbata dole ne zata kasance cikin damuwa kamar koma fiye da ita. Amman komi mai wucewa ne da yardan Allah.

Bata tausayin kanta kamar yadda take tausayin Intissar don haka ta dage da Addu’ar Allah ya kawo masu mafita cikin al’amuransu.

A watanninta na biyar da zaman Makarfi, ta haifi sankaceciyar diyarta a safiyar wata litinin. Yarinyar bata debo kamannin kowa ba sai na Faisal. Kamar su daya da faisal a komi. An aikawa Daddy a ranar ba yabo ba fallasa yayi hidima dai-dai gwargwado don Baffa kadai amma ba wai don ya damu ba. Da aka tambayeshi sunan jaririya sai yace su sanya duk wanda yayi masu mana?

A nan ne ran Baffa ya baci yace a sawa yarinya suna Fatima – Zahra. Su yasir duk sun baro Enugu sunzo sunga kanwarsu dukkansu sai kururuta tsabar kamanninta da Faisal ne babu kuma wanda ya leka Abuja a cikinsu har suka koma.

Anti Saratu kanji haushin Goggonta kan yadda taki hutar da kanta ta zauna wuri daya ta dangana da kaddarar rabuwarta da Daddy. Ita a yanzu ma chairman na Makarfi ke son aurenta tun bayan aifuwarta.

A ranar wata alhamis Goggo da aminiyarta Inna Jami suka dawo yawonsu goshin mangariba kafafun su futu-futu da kura duk sai suka bata dariya. Jami tace

“Au, dariya ma kike mana Saratu don muna nema maki ‘yancinki da aka bi aka bibbinne?

Ni bani ruwa inyi alwallah inyi Sallah ki ji labari. Ai dama aka ce mai nema yana tare da samu, in Allah ya yarda nanda sabon wata mai kamawa kina dakin mijinki, kaikayi kuma koma kan mashekiya zamuyi”.

Saratu tayi tsaki, ta mike ta ciccika masu butoci da ruwa a randa a lokacin zarah keta tsala ihu amma ko waiwayon inda take batayi ba. Jami ta dauketa tana cillawa tana cafewa ta ce

“yi shiru ‘yar ikon Allah, daga wannan watan kin bar zafin kauye In sha-Allahu don nasan shi ke damunki sai Habuja, ke da kauyen Makarfi sai ko gaisuwar Sallah”.

Goggo Jummai tayi dariya ta ce” ai gobe har ita zamu tafin ko? “Jami tace “kwarai kuwa, don gara a soma yi mata rigakafi itama, baki ji Malam na Kafanchar yace itama an maida ta kamar mijiya a idon Mahaifin ba?

Tunda aka haifeta kin ji yace a bashi ita ya gani? Ai gobe Saratu da kin ki da kin so kafar mu kafarki bukkar Mallam Sidi Fari”.

Ita kam jinsu kawai take a ranta ko cewa take ko Sidi Baki ne ba inda zata. Haka kawai don B-Bello shine autan maza?

Itama bakikkirin din take ganinshi babu kuma koda birbishin son sake zama dashi ko kankani a kalbinta, zumunci ma don ya zama dole ne.

Har sun kwanta da doddare Goggo ta kasa hakuri ta kirayi sunanta a hankali tace “Saratu, duk fa hakilon nan da muke yi don ke muke yinsa da farin-cikin ki ba don wani abu daban ba.

Amma na lura ke haushin mu ma kike ji bakya godewa. Dazu ina ji Jami na ce miki gobe ki shirya mu tafi Kafanchan kin yi shiru baki amsa ba har da bin ta da tsaki. Shin ko yanzu ba kya son mijin ki ne?”

Aunty Saratu ta gyara kwanciyar Bebinta dake barci tana fidda numfashi sannu a hankali cikin koshin lafiya. Tabbas tambayar Goggo itace amsarta. Ko a lahira bata fatan su hadu da Birgedier yanzu (kaji sharrin kishiya).

Ta muskuta cikin tsananin bacin ran tono ma mutun abin bakin-cikin da ya manta dashi tace “Goggo ni fa tunda na bar gidan ban kara tuna wani Bello da sunan so ba, sai ko Yaya na Uban ‘ya ta. Yadda kika san bakin kumurci haka nake ganin sa ko muryarsa bana son ji wallahi.

Wannan ‘yar ma kan dole nake shayar da ita, amma duk sanda na tuna wai kanwar su Aminu ce kamar in shake shegiya wallahi”.

Goggo ta yi salati ta sanar da Ubangiji tace “Ba zan musa miki ba Saratu don tabbas kema tsafin ya ci ki, amma a kalla gobe ki bimu addu’o’I ne Malam Sidi zai baki na neman zabin Allah ba wai wani abu ba”.

Ta amince zata amma ba don ranta yaso ba sai don bata son yin musu da Goggonta ne kawai.

A soron Sidi Fari wanda Sharifi ne a garin Kafanchan kuma dan uwan Inna Jami, ya amshi Babe-Zarah yana kallonta yace

“Shin Saratu zaki iya bayyana mun yadda kike jin tsohon mijin ki a ranki?” Ta mayar mai kamar yadda ta fadiwa Goggon ta a daren jiya, duk ta matsu ta tafi don ita ba wannan aka ce zai hadasu ba illa Addu’a, ya girgiza kai ya dubi Jami yace

“Hajiya Jamila, a jiya nayi bincike naga duk matsalar yarinyar ku amma Insha-Allahu komi ya zo karshe”.

Ya mika mata Zarah ya umarceta da ta shiga cikin gidan shi ta basu wuri, ita dama so take ta tafin, don haka cikin hamzari ta saba ‘yarta a kafada tayi cikin gidan.

Malam ya ce “Jamila yarinyar nan duk wani mai imani dole ya tausaya mata, kuma ku godewa Allah daya nufe ku da mikewa tsaye kan al’amarinta, don Ubangiji shi yace tashi in taimake ka, kuma a gaskiyance sai mun mike tsaye in ba hakaba itada aure har abada kenan.

Bakin asiri ko ince tsafi ne aka bizne mata a dakin aurenta wanda aka hada da idanu da gangar jikin matacciyar mujiya, da gashin kan ita Saratu d farcenta, shi ko mijin ta firraku a kayi masu ta yadda ba zai taba samun kwanciyar hankalin kanshi ba in har ba gani yayi ya rabu da ita ba.

Akwai wata yarinya ma dana gani a gidan itama abinda aka yiwa Saratun da mijinta shi aka yi mata dashi Maigidan, kodayake na gani tana cikin gidan duk da haka, sai dai Maigidan na ganin ta kamar mujiya ya tsaneta kwata-kwata.

Wannan tsafin a tsibirin Okeremor aka sameshi ta yadda karyashi kadai shine tono abinda aka bizne aka koneshi kurmus. Sabida haka zan tura wani Musulmin aljani dake min aiki wai shi Salmanu ya aiwatar da aikin. Daga wannan zan yiwa Bello kiranye, ai gyaran sunnah ne, shi da kansa zai zo neman a maida mishi matarsa, kada ku tsaya ja masa rai ku maida auren don kwata-kwata baya da laihi”.

Goggo Jummai ta gaya mai yarinyar diyar Saratun ce yace “ba komi, da tsarkin Alkur’ani kamin kwana uku zai warware komi. Itama Saratun ya kirata ya bata addu‘o’I da Nafilfilin da zata rikayi har tsawon kwanaki arba’in, da rubutun da za’a dinga rubutawa suna wanka suna sha ita da Zarah.

To Anti Saratu taji dadin wannan, daga Goggon har Jami babu wanda yai mata zancen da Malam yayi.

Tunda ta fara Addu’ar sai taji zuciyarta na sanyi a kullum. Duk wani kunci dake tattare da ita ya shiga yayewa sannu a hankali. Tabbas babu maganin da Al-Kur’ani ba ya yi kuma lallai shi (Shifa’un-Linnasi) ne wato ceto ga al’ummah. Kaunar diyarta ke shigarta sosai kamar na kowacce uwa ga dan da ta haifa.

Kuna wai har ta sami kanta tana mai tinano irin kyakkyawar rayuwar da sukayi da Bello Makarfi da diyarta Inteesar.

Da Goggon ta fahimci haka sai ta daga hannu tayi godiya ga Allah ta kuma garzaya Kafanchan ta tadda Mallam Sidi tare da abin sadakar da ya nema, harta dada ninka mai amman shi din sai yace ba zai anshi karin ba, yayi masu ne domin Allah da neman ladan gyaran aure da kuma kasancewar Jami kanwa agaresa, sai tayi godiya, ta kuma shiga kara jan hankalin Saratu tana nuna mata gidan Daddy shine kadai kwanciyar hankalinta ita da diyarta da Inteesar. Ko bazata koma don komi ba ta koma don Intisar da Zarah. Don ko tayi wani auren hankalin ta ba zai kwanta ba tunda bazata kasance tare da su ba, ina amfanin badi ba rai?

Sauran abubuwan da suka biyo baya duk kun ji su cikin littafi na daya, wato dawowar Antin da barin garin Hajiyar. Dawowar Faisal da gane ainahin wacece Intissar kuma wanene Al’ameen? Suman da tayi ne har yanzu ban san musabbabinsa ba; na gane hakikanin waye Al’ameen ne? Na bakin-cikin kasancewarta dumu-dumu a soyayyar dan Haj. Nafi ne? Koko na tunanin ta rasa Al’ameen ne shima kaman Faisal tunda yake shima uban su daya? Ban sani ba.

Yau ga likita a gadon likitoci kenan, in ji babban Likita Alfred, don sanin waye Al’ameen?

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

2 thoughts on “Siradin Rayuwa 3 | Babi Na Hudu”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×