Skip to content
Part 33 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir Takori

A kalaminshi na karshe, wadanda kuma suke kalmomi na karshe a littafin da alama ma yanzun ya rubuta;

‘To in haka ne shi meye ribar sa a rayuwa? Da me ya yi riba da me ya tsira? Bai gani ba! Bai ci riba da son Intisar ba, bai ga amfanin ilmin daya nema don ta huta da shi ba, tunda Al’ameen billonnaire ne, baya bukatar a agaza masa, bai ga ranar da son da ya shekara yi mata yai masa ba. He is but a real loser! To amma tunda don ita ya nema, shi mai mallaka mata duk abinda ya mallaka a duniya ne koda kuwa ta auri Aminu ne ko waninsa, tunda dama tunda fari ya alkawartawa ransa hakan.” Ragowar bata iya ta karasa ba, saboda kwakwalwar ba zata iya ganewa ba…….balle ta fassarawa zuciyar ta!

Inteesar ta daga ido sama tamkar mai kididdiga adadin juyawar fanka, wasu irin hawaye ne marasa dandano bare launi ke tsere ‘one after the other’ (bi-da-bi) kan kyakkyawar farar fuskar ta. Abubuwa da dama ta tuna a wannan lokacin, wato kuruciyarsu da Faisal can baya.

Ashe dama abinda take ji game da shi a lokacin itama ‘son’ ne? Gaba daya jikinta ba inda bai diba ba cikin kaduwa, dimuwa da razana, a take zazzabi mai zafi ya soma kokarin rufeta, saboda karkarwa da ilahirin jikin ta ke yi littafin ya zame ya fadi kan kafarta, dai-dai lokacin da Faisal ya murda kofar bandakin ya fito gabadayan sa.

Daure da towel faffada iya kungushi yana ‘combing’ sumar kanshi sai ya daskare cikin matsanancin mamaki, suka dubi juna a gaggauce idanunta face-face da hawaye, tayi saurin juya mai baya, kana ta doshi kofa tana cewa.

“Dama Daddy ne yace in kirawo ka, kada a kara zama cin abinci kana gida baka zo ba” ta sheka da gudu zata bar dakin abin tsautsayi, sai gilashin ya fado ta kuma taka shi da kafarta hannun ya lankwashe amma saboda quality  (karkon) gilashin bai fashe ba, kamin ta russuna ya isa gareshi sai suka russuna a tare, hannunshi ya riga isa bisa gilashin don haka natan sai ya sauka akan nashin, shi yai nasarar daukowa, yasa karfi wajen gyara lankwashewar da yayi, a yayin da ta jingina da bango idanunta a runtse, hakannan hawayen basu fasa kwarara ba kamar an sunce fanfo. 

Ba komi take tunawa ba a lokacin face ranar da ya cire mata gilashi ta baya, lokacin ana shirye-shiryen tafiyarsu Riyadh ita da Khaleel, ta dinga bin inuwarsa a hasale tana “bani gilas dina Ya Faisal, kaga bana so” haka dukan da ya sha da filo da wakokin da ya kanyi mata na “come on beautiful Babe, Maman?”

Cikin nutsuwa ya maida mata gilashinta, suka sake dubar juna a susuce sai ta kara da gudu.

Ya dade anan tsaye yana tunanin me ta gani ya sata kuka? Me ta gani ya gigita ta haka? Bai yi tsammanin zata sake kulawa da al’amarinsa ba a yanzun dai da ta ke cikin son Yayan shi Ameenu?

Intisar dakinta ta nufa agigicenta ta maida kofar ta rufe ta murza key. Ta jigina da kofar ta sake runtse idonta da karfi, tamkar mai son farkawa daga mafarki. Abubuwanne ke tariyo mata can baya tamkar a majigi. Ta tabbatar Faisal shine mutumin da ta fara so a rayuwarta kuma mutumin da bazata taba samun mai kaunarta a duniya tamkar shi ba. Tausayinshi, yagama narkar da duk wani tunani da ta mallaka. Ta zargi kanta da cin amana ta kuma kirayi kanta da ‘butulu’ dan adam mai manta alkhairi.

To amma wani bangare na zuciyarta ya kalubalanci hakan da hujjar cewa, a lokacinta da Faisal tsammani suke su ‘yan uwan junane sabanin haduwarta da Al’ameen. Hakannan Al’ameen shi ya koyar dai ta son shi, shi ya kimsa mata son shi karfi da yaji, bata san so na soyayya ba sai akan shi, don haka bata jin Allah zai kamata da wannan hakkin na Faisal sai dai kaso mafi rinjaye na zuciyarta na karfafata da cewa, yanzu ne ya dace tayi wani abu, yanzu ne ya dace ta sadaukar da kanta da soyayyarta (son da takewa Al’ameen) don nunawa Faisal wannan kaunar da ya wanzar da rayuwarshi nuna mata, tun tana a tsumman goyo. To wai ma ya akai ta so Al’ameen? Bata sani ba, illa may be because he is unikue (watakila don shi din na daban ne).

Ta yaya? Ta yaya zata nunawa Faisal din kauna bayan a yanzun ya nuna baya da lokacinta ma? Ta tambayi kanta, lokaci guda ta bawa kanta amsa da cewa ta hanyar auren shi mana Intisar? Amsar tayi mata nauyi a baka da zuci, wai Intisar matar Faisal in banda Allah mai juya al’amura ina wannan abu zai taba zuwa masu a rai?

A lokacin ne kuma ta tuna shima fa Faisal dan Hajiya ne! Wannan zuri’ar da tayi alkawarin ba zata sake kulawa ba!  Wannan zuri’ar data nuna mata kiyayyar da ba wani mahaluki a doron kasa da ya taba nuna mata! Wannan zuri’ar da idan ta aura, ta sake jefa kanta cikin bala’I da masifa ne watakila ma fiye da na baya. Bayan yanzun da cikakken gatanta, ga Aunty, Daddy, uwa-uba dangi da uwa mahaifiya masu so da kaunarta. Zuri’ar Haj. Nafi? Ta girgiza kai da karfi, ire-iren maganganun Haj. kadai ke dawo mata wasu na bin wasu.

“Wai me yasa kike son ‘ya’yana ne, bayan ni na tsaneki? Har kullum mutum kanyi nisa ne da jinin makiyin shi, Saratu banda ke! Don naji ance komi Faisal kike ambato, har kuka kika yi da ya bar kasar, yayi maki kama da ‘ya’yan mutsiyatan kauye ne?

So nake bandakin nan ya fiki fari, ya kuma fi Faisal di na kamshi… Faisal ne ya sa miki suna Intisar, kuma da na ne, mallakina ne, don haka daga yau na kwace…. Ke Jikar Jummai ce, Jummai uwar Saratu…. Daga yau kika sake koda kallar min ‘ya’ya, sai na sa wuka na tsokale wadanna makafin idanun munafurcin, kina jina? Ta tuna amsar da ta baiwa Hajiyar a lokacin. A yau ma sai ta samu kanta da nanata su, sai dai sabanin sunayen da ta kira a wancen lokacin a yau cewa tayi…ba Faisal ba, ba Aminu ba… duk wani jininki ma idan na sake daga ido na dubeshi ba da kiyayya ba, ki ce ni shegiya ce na amince!

Ta kudurce a ranta daga yau dukkansu ko gaisuwar dayansu bata so. Aure kuma in har sai da ‘ya’yan Haj. Nafi ne, to ita Saratu ta yafe!

Ba irin bugun da su Hunainah da Anti ba suyi ba amma Intisar bata bude ba. Wuni tayi cin kuka da nadama mara amfani. Ta rasa meyasa rayuwar ta ke da matsaloli iri-iri tun tana jaririyarta. Dagabaya kuma tayi tunanin akan me zata bari soyayyar ‘ya’yan Hajiya ya wargaza mata rayuwa? Komi fa mutum ke daurama kansa don Allah baya daurawa rai sai abinda zata iya.

Ta yankewa kanta ‘solution’ na karshe tayi murmushi ita kadai. Ta san cikin Iyayenta kakaf, babu mai matsa mata akan wannan kudurin nata. Sai ko Mamarsu Hunainah ita ko bata jin ta don ta tabbata Daddynta zai bata goyon baya dari bisa dari.

Ba ita ta fito ba sai karfe hudu na yamma, shi din ma azababbiyar yunwa ta fiddota. Su Hunainah na magana da Anti Hajjo a waya ta ce,

“Gata nan ma ta fito” ta mika mata wayan ta ce,

‘Hello Aunty” Hajjo ta ce,

“Ba wani Yello Aunty, nikan baki dauke ni Antin ba, da ko menene ke damunki da kin kira ni kin gaya mini, Saratu shin me yayi zafi ne haka? Na ji an ce tun safe kin rufe kanki a daki kina kuka.

Na dauka kasancewar mu kusa da ke, da tabbacin da kike da shi na iyayen kwarai ya isa ya sanyaya maki zuciya?  Wannan kuntata duk na menene?”

Tayi shiru, Idanuwan ta sunyi rau-rau kaman ta saki kuka. In da Anti Hajjo ta san yadda take jin zuciyar nan tata, da bata zargeta da kuntatawa kanta ba.

Ita ba sauyin Iyaye ya dameta ba, damuwarta daban ne, daga ita sai Ubangijin ta suka santa. Hajjo ta ce,

“Koda bakya kaunar mu Saratu, mu ne dai iyayenki, kuma ba’a sake iyaye sai iyayen daki. Wannan rashin sakin jikin da kike damu ban sani ba ko don ki na ganin bamu isa mu zamo iyayen ki ne ba?” (Aunty Saratu ce ta koya mata, ba’a jin damuwan ta sai da dabara) Ta sa kuka da karfi tace “Aunty Hajjo me ya kawo wannan maganar?

Na rantse da Allah ba haka bane, ni abinda ke damuna daban ne.”

Hajjo ta ce, “Don kin ce kin fasa auren Al’ameen? Ke, yarinyar ki da ke kar ki bari ciwon hawan jini ya kamaki akan soyayya. Shi Al’ameen din yace dake ya damu? Yana can tare da matarshi Allah kadai yasan farin-cikin da suke ciki sai ke ki bi ki kuntatawa ranki?”

Ta share hawayen da ke zuba mata da bayan hannu, dai-dai sanda dan halak din ya yiwa falon tsinke, matarsa na biye da shi tamkar ta shige jikinshi don tsatsiba, ya zarce kai tsaye har inda take, ya ja tebur inda take ya daura kafa daya, dayar kuwa na kasa tamkar mai son jin kwakkwafin abinda ke sata kuka a waya.

Ihsan ta bisu da kallo kana tabi bayan su Hunainah da sukayi cikin dakin Anti. Intisar ta bude baki domin ta bawa Antinta amsar da tai niyya amma kwarjinin Al’ameen ya katse komi. So ta ke tace har wata tsiyace Al’ameen din da zata kuntatawa kanta akansa? Ita ba shine damuwanta ba.

Hajjo ta ji tayi shiru ta cigaba da cewa, “Ni dai shawarata a gareki Intisar, ki fidda damuwar komi a ranki, ki koma makaranta. A shirye muke damu nuna maki kauna ta kowanne fanni. Na san kina son Al’ameen, so bana wasa ba. Tunda har kika kusa salwantar da rayuwar ki akan tunanin bazaku iya auren juna ba.

Amma abinda na ke so ki gane shine, ki yi tunani, ke yarinya ce karama har yanzu cikin shekarun (teenage), wannan gigin son duk na dan lokaci ne, da anyi auren an haihu shikenan ya zama tarihi sai zaman hakuri da juna.

Abinda nake so da ke shine ki tsaya ki gina rayuwarki a bisa tubala na kwarai, in ba hakaba ba mamaki bada jimawa ba soyayya ta ruguzata. Al’ameen ya fiki wayo, daga shi har matarshi ba tsaranki bane a budewar kai da ilmi.

Don haka ki tsaya ki nemawa kanki madogara mai kyau tukunna, wanda shine wannan ilimin mai matukar wuya.  Idan kika sameshi samun Aminu ba zai maki wuya ba haka in kika barshi ke da banza a cikin su daya kuke, don sai kin raina kan ki a cikinsu.

Ni in son raina ne ma Allah bana son ki auri mai mata irin Ihsan, ki dubi yadda take hauka akan mijinta fa, ke ‘yar nan, mind yourself (ki shiga taitayinki)”. Ahaf! Ai kamar Antin ta shiga ranta taga abinda take shiri komawa makaranta, tayi murmushi tare da saurin rufe ido, maganganun Antin take aunawa abisa sikeli daya bayan daya, wanda dama duk tayi tunaninsu, babu wanda bata ga gaskiya a ciki ba, ta ce a raunane.

“Na gode Aunty.”

Ta rufe wayar, sai yanzu ya fuskanci da wa take magana, bata ko dubeshi ba ta murda kofar da zata hadaka da dakin ta daga falon Anti, yayi hamzarin murda keys ya zare ya tura aljihun bayan wandon ‘basachi’ dake jikinsa ya ce.

“Me Anti Hajjo ke gaya maki a waya, kike godewa kina kuma kara yi mun asaran hawayen da nake ganin daraja da kimar su fiye da na kowa?”

Wasu ubansu harara da ta watso mai ya bashi mamaki don bai taba ganin tayi ba, ga idanun sunyi jawur sai ta kara kyau a idon shi, ko da yake so ne hana ganin aibi, ya ce, “Inteesar” da muryar nan da ke karya lagonta, ta kassara kuzarin ta, amma a yau ko gezau, har yanzu hararar shi ta ke ba kakkautawa. 

Ya soma taki har inda take tsaye tamkar sassakakken gunki, ta soma ja da baya kamar wadda taga abin tsoro da kyama, ta san ba karamin aikin shi ba ne ya kamata da kokawa kawai don ya sata yin magana, cikin tsiwa da yatsina ta bude dan bakinta tana mai nunashi da dan manuninta ta ce,

“Wallahi Al’ameen ka sake ka tabani yau zan fasa ma kaine, in bar inyamurar matarka da jiyyar da baka taba yi ba.” Bai fasa dosarta ba ya ce,

“Jinya kuma wacce ce ba’ayi ba? Sai dai kar a kuma, idan jinya ta ciwon son halimah ce, to ayi ta yi kar a tashi. Kar ki kara kira mun mata inyamura, yadda kike musulma diyar musulmi, haka itama take.” dai-dai lokacin da ta dangana da bangon karshe na falon, shi kuma bai fasa bin ta ba, ta ce,

“Wallahi zan kirawo Anti, tayi ma kashedin shiga harkana, ka nemo Halimar ka can amma ni Intisar ce, ka manta ka taba sanina a rayuwarka, ina gaya maka, ina kara gaya maka” ya toshe mata baki. Ya ja hannunta na dama da karfi har bisa seater dake tsakiyar falon, ta karfin tsiya ya zaunarta ya ce,

“Ke in ma Daddy zaki kirawo babu laifi. Amma sai na gama maganar da zan yi. Kin san me ya kawo ni? 

Zuwa nayi in gaya maki ranar da duk wannan maganannen bakin ya kara kuskuren cewa bazai aureni ba don uwata, wallahi sai na kakkarya ki.”

Cikin tsiwar da bai san ta iya ba ta ce,

‘Ka karya ni? To ka ji ka sani ko da can da ka makantani, don ban da wayo ne, amma yanzu wallahi sai dai ayi ‘yar bibbiyu” saura kadan da dariya ta kwace masa, to amma shi kansa yasan bai kyauta ba, jiya ya mareta yau ya gaya mata kakkausar magana, shi da ke neman wanke dattin da Hajiya ta yayyaba masu daga idanunta.

Ya dire gwiwoyinsa bisa carpet abinda bai taba yiwa wata ‘ya mace a rayuwarsa ba, a yayinda ita kuma take zaune cikin kujera ta cika fam, kiris take jira ta fashe.

Ya langabe kai gefe guda gwanin ban tausayi, yayi kamar ya share mata hawayen da suka soma surtu, sai kuma yafasa. Ya ce,

“Inteesarr!”

Yadda ya kira sunan cikin murya mai karkarwa da kauri (husky) kadai ya birkita Saratun, bata jin ko dan yatsanta zata iya motsawa. Ya ce,

“I ‘am sorry, terribly sorry! Wallahi ni, wasa nake maki, in karya ki in ce na karya wa kenan?

Jiya kuma zuciya ce ta debe ni, kin san bata da kashi, abinda kika fadi cikin mutane ya bata mun kwarai. Ni kaina ban san ya akai ba, Pls, 4 give me…” Ya karasa a raunane, kana ya matso ‘yar kwallah, ya maida ta bisa kujerar ya ce,

“Wallahi Intisar nasan Hajiya ta bata miki, to amma ni meye laifina? Ni ban ji tsoron abinda hakan zai janyo man ba daga gareta na furta ina sonki? Sannan kuma bakya tausaya mun halinda zan shiga in na rasa ki kwata-kwata, ki tuna baya?”

Ta sadda kai kawai, bata son jin wannan abun da take ji game da Aminu, bata son wadannan ‘feelings’ din da take ji game da shi masu tada tsigogin jikinta a duk lokacin da suke tare, to amma Al’ameen din kamar wani mayen karfe ne, wuyarta yayi mata magana da wannan muryan nashi mai jan mutum uwa lantarki duk wani ‘weakness’ din ta ya gama samunshi.

Ta tabbata nisa da shi shine abu mafi a’ala a gareta in har tana son cimma kudurirrikanta akan Haj. Nafi, wadanda daga ita sai zuciyarta sai mahaliccinta suka san na mene, amma ba don bata son shi ba.

Karya ne ko fatar bakinta ta fada, to bacin rai ne. Shi kadai take so har cikin tsokar zuciyarta, har gangar jiki zuwa kwakwalwarta babu inda baya girgiza da kaunar Al’ameen da sha’awar komi nashi, ita kadai ta san me take ji da yakin da take yi da zuciyarvta a duk lokacin da yai kuskuren kai hannunshi gareta koda yatsar hannunta ne kuwa amma ta rantse, ta kuma ta rantse ko son sa zai kasheta, ko duk duniya zata taru a kanta, bazata aure shi ba!

A ganinta ta hakanne kadai zata rama abinda sukai mata shi da mahaifiyarsa wanda har abada bazata manta ba, ba zata yafe mata ba kuma ba zata daina tunawa ba.

Bata san wannan hukuncin da ta yanke yai tsauri ba, domin son da Al’ameen ke mata Allah kadai ya san iyakarsa; ba na wasa bane, ya wuce ayi ramuwar gayya akansa yayi masa tsauri bazai iya dauka ba. Da kyar in bata yi kuskure ba, da kyar in hukuncinta ba zai zamo nadama  mara amfani  a gareta ba.

Ya cira hannunta ya aza bisa kirjinshi, tana iya jin nannauyan bugun da zuciyarsa ke yi akai-akai, jikinta ya soma sanyi, ya ce,

“Ki ji Intisar, kiji irin bugun da  zuciyar nan ke yi a domin ki, saboda ke ne take ciwon da har abada bazata daina ba, ba kya tausayi na Intisar ba kya sona yanzun? Allah na rantse, in muka cigaba da tafiya a haka wata rana…. Wata rana bugawa zatayi gabadaya ta fashe kowa ya huta, ki taimake ni ki agaje ni, ki daina la’akari da laifin da ba nawa ba kina hukunta ni dashi don Allah?”

Ita dai ta zamo ‘pale’ ko motsi ta kasa balle tayi kokarin yin wani abu, ta rasa abinda ke mata dadi shi kuma bakinshi bai yi shiru ba da gaya mata irin halin da zai shiga in ya rasata. Har ya kai ga kwantar da kansa bisa kafadunta.

Cikin wannan halin Faisal ya turo kofar falon ya shigo, fes idon shi a kan su, ya juya da sauri yana cewa, “Excuse me plz. Ya Aminu ban sani ba!”.

Ta mike a gigice ta banka dakin Anti, ta kifa kai bisa gado ta soma rera kuka sabo fil. Ina rowan mai neman kuka an jefeshi da dunkulen kashi.

Gabadaya suka zubo mata ido Anti da Ihsan suka yo kanta Anti ta ce,

“To kin gani Ihsan mijinki kullum sai yasa min ‘ya kuka, don haka ki je ki ja kayan ki ku tafi.” Ta sake kuluwa ta shaka ance Al’amin mijin Ihsan, ta sake tsugewa da kuka.

Ihsan ta matsa jikin gadon ta dago kanta ta aza bisa cinyarta tana murmushi tace “Haba little sister na, kin hana mun miji sakat ko tausayinshi ba kya ji, jiya saura kadan ya sakeni, don Allah kiyi hakuri ki bamu hadin kai ko na samu kan Al’ameen nima…”

Ta soma fidda kwalla itama, wani tukuki na cinta a rai, wai yau itace da kanta ke rokon wata ‘yar ficikar yarinya ta so mijin ta, Aminunta data gama shan bakar wahala a kansa, ta sadaukar da komi nata dominsa, take son sa tamkar ta fidda zuciyarta, ayya rayuwa!

Ta daure ta share wasu azababbun hawaye da suka biyo kumatun ta a guje ta ce, “Intisar, Al’ameen ya gaya mun bazamu taba samun kwanciyar hankali ba in har baki yarda da maganar auren ku ba. Don Allah Intisar ki taimake ni.”

Aunty ta juya ta fita, bata iya jure ganin wannan abin tausayi. Ita Ihsan din ce ta ke bata tausayi, ta tabbata ba karamin so takewa mijinta ba, abinda tayi mata da yawa baza su iya ba, dazu akan idonta Aminu ya turo kofa ya rufesu har da mukulli amma sai cewa tayi.

“Allah dai yasa ya shawo kanta. Don na lura Intissar akwai zucciya.”

Intisar ta dago don babatun Ihsan ya isheta, fuskar nan jike sharab da hawaye ta dubeta sosai ta ce,

“Ina ganin mutuncin ki, don haka don Allah don Annabi Anti Ihsan ba ruwan ki, ki rabu da Al’ameen kawai, shi bai ji tausayi na ba sadda yake kwallo dani har na zamo  nakasashshiya? Hajiyarsa bata ji tausayi na ba a sadda Daddy ke kwallo da ni ba a gabanta, da sadda take fyaula mun kebur? Take sa min shocking? Ke har da kan ki kike son in auri mijin ki ashe karya kike ba son shi kike ba.

Baki sani ba, ni fa tunda fari ba son mijinki nake ba, kaddarar Allah ta hada mu a kichin kuma kaddarar ta raba, don haka ki tafi don Allah ina bukatar hutu, ina maku addu’a Allah ya baku kwanciyar hankalin ba sai tare da ni ba,  ke ni ba wani aure da zan yi, da din ma dana amsa masa rashin galihu ne da rashin abin yi, yanzu kuwa ina da abinyi ina da galihu, ba wanda ya isa yayi kwallo da ni ban yi karar sa an fitar mun hakki na ba, ki je ki lallashi abinki ke daya ko ke ba mace bace baki ishe shi ba?”

Ta fiddo mata ido cikin barazana kamar gaske, bayan a zahiri ji take kamar ta makureta ta huce.

Ihsan tayi murmushi ta mike, a ranta ko cewa take lallai wannan yarinyace, danya (fresh), kalaminta kadai zaka ji ka tabbatar kurucci dangin hauka na dawainiya da ita, har akwai wata ‘ya mace mai cikakken hankali ta kuma san abinda takeyi da zata budi baki tace wai bata son Al’ameen Bello?

Ta mike ta na rataya jakarta ta nufi kofa ta ce,

“Ki dai kara baiwa zuciyar ki shawara Intisar, Al’ameen mai matukar son ki ne tsakani da Allah. Ba fata nake miki ba, amma ba zaki samu miji da ke son ki tamkar yadda ya ke son ki ba.”

Intisar ta bita da hararar haushi, kar ta samu din, wannan dan iskan mijin nata? Yau kam kunya da tozarci tagama jin shi a rayuwar ta. Da wane ido zata dubi Faisal?

Wane kalami gareta na wanke kanta daga sunan mayaudariya, maciyiya amana, butulu kuma mai manta alkhairi a idon Faisal? Sai ta kara jin tsanar Al’ameen ninkin baninkin na da, dubi yadda yake wa matarshi don wai kurum tana sonshi. Itama idan ya aureta wata rana ya sami wadda ya fiso fiye da ita ba mamaki ya turota lallasar yarinyar da yake son, tab! In ita ce ai za’a yi kata’i. Bata san wannan duk yana cikin wayewar Ihsan da duniya ne ba, ko ba komi zata sayo ma kanta daraja da soyayya a zuciyar mijinta, gaskiyar Hajjo ne Ihsan da Aminu sun fita wayo, ba kuma tsaranta bane a budewar kai da Ilmi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2.9 / 5. Rating: 23

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siradin Rayuwa 32Siradin Rayuwa 34 >>

9 thoughts on “Siradin Rayuwa 33”

  1. Da kyau diyar daddy makarfi da aunty Saratu! Gara ki nuna musu kema kin girma but billah ina tausayin faisal takori

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×