Skip to content
Part 36 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir Takori

Tafe yake a mota amma hankalin sa baya jikin sa. Kuka yake kashirban kaman karamin yaro. Duk da zuciyar sa tayi sanyi da yafiyar da ya samu daga gareta wannan bai hanashi kukan tashin hankalin da kalamanta suka tsomashi ba. Wane alkawari ne yai mata? Ya kasa tunawa.

Hajiya kin ce in koma ga matata, to ai gara in dawwama a nan kina azabtar dani daga hukunce-hukuncen ki, domin in na koma gareta bani da wani sauran amfani a gareta, me zan yi mata? Me zan ce mata? Rayuwata ta zamo impotent ba zata kara moruwa da ni ba, kowa ma ba zai kara moruwa da ni ba including Inteesar!

Na dauka zaki fahimce ni, na dauka zaki ji kai na ki ji tausayi na, na dauka zakiyi tunanin soyayyar da nake yi mata bata shafi kiyayyar da kike mata ba, na dauka zaki yi min alfarma irin wadda ba ki taba yi mun ba, na dauka zaki ce je ka Aminu ka auri Intisar, Allah yayi maku albarka, ya sa hakan shine mafi alkhairi a gare mu bakidaya., amma kamar ba kya tausayi na, me zan yi miki ki fahimci ni mai gudun bacin ran ki da fushin ki ne? Ban zaci zaki yafe mun ba tunda na yi sanadiyyar zubar hawaye daga idanuwanki.

Bana nufin in tursasa ka bisa raayi na, illa in tserar da kai daga tozarta alkawari ya tuno kalamanta na karshe. A lokacin zuciyarsa ta tariyo masa ranar da ya dawo, da kuma maganganun da sukayi shi da ita a dakin Faisal. “alkawari daya zan iya yi miki hajiya na, ba zan taba son ta irin son da Faisal ke mata ba!”

Amsar da ya bata kenan a wancan lokacin, maganar ta cigaba da amo har cikin kwakwalwarsa, ta bi har cikin jijiyoyi da tsokar jikin sa, ta zagayo ta fito daga bakin sa. Eh nayi maki wannan alkawarin kam, nayi Hajiya na, kina da hujjar hukuntani da alkawari na. na gode. To amma ba kiyi tunanin komi ya faru a bisa rashin sani ne ba? Ban san Intisar ce diyar Anti Amarya ba. Na so ta a Halimar ta, baa Inteesar ba, Ban san san sanda zuciya ta rinjayeni ga son nata ba.

Karar karon motoci sama da goma, tare da wuntsilawar da motar Alameen ta yi ta shiga katantanwa bisa titin, haka murje ta da wata kotuwar DAF mai cike da Hatsi tayi bisa titin da zai shiga da kai garin Minna kafin ya sadaka da Abuja, ya janyo hankalin alummar da ke wajen bakidaya suka ambaci. Inna lillahi wa inna ilaihi  raji oun!

Cikin dan lokaci jamian tsaro suka cika wajen tare da motocin ambulance abin dai babu kyawun gani.

*****

UWA, MAHAIFIYA!!!

Tunda ya fita ta kasa sukuni, ta rasa me ke mata dadi, ta rasa inda zata tsoma ran ta ta ji sanyi. Ta kai gwauro ta kai mari a tsakiyar kayataccen falon, can kuma ta isa ga taga tana lekensa, har ya tada mota ya fita daga harabar gidan idanuwan sa basu bar tsiyayar da hawaye ba.

Ta koma cikin kujera ta zauna cikin mutuwa jiki, ji tayi tamkar ta zauna a cikin kaya, ta yi tagumi, zuciyar uwa! Haka kawai taji hawaye na zuba mata sharr-sharr. Ta san duk cikin yayanta babu mai son ta tare da yi mata biyyayyah tamkar Alameen, anya hukuncinda ta yanke a kansa tayi masa adalci?

Gaskiyar Innar ta ne son kanta yayi yawa, kuma wannan ba so bane! Ita uwa kullum hakuri take da abu koda tana so ta barwa danta, ya roke ta, ya kaskantar da kansa gareta irin yadda wani cikin yayanta bai taba yi mata ba.

Ya nuna mata fifiko akan bukatar shi. Ya ce alfarma ce ya ke nema irin wadda bai taba nema daga gareta ba! Ya zubar da hawaye irin wanda bai taba zubarwa a duniya ba, sabida tashin hankalin fushinta a gareshi. Koda sanda yake kankani bata taba ganin shi yayi kuka haka ba.

Ya nemi jin kanta da tausayi amma bata nuna ko daya ba, duk da cewa ba hakan ba ne zahiri a zuciyarta.

Ta nuna masa damuwar shi bata dameta ba, kiyayyar da ke zuciyar ta kadai ta sani, koda hakan zai zama ajalinsa bata amince masa ba, shin ita din wace irin mahaifiya ce?

Ta kai tunaninta ga yarinyarda aka kira da suna Saratu-Intisar. A iya saninta da yarinyar, shekaru goma sha takwas da suka gabata, tun tana jaririya kawo girmanta, bata taba daga ido ta yi mata koda kallon banza ba, bata taba bude dukkan idanun ta tangaras ta dubeta ba, sabida tsananin girman ta da kimar ta da take gani. Bata taba fada mata abu tace da ita ba haka ba. Bata taba yin musu da ita ba balle ta kai ga zaginta, duk kuwa da irin kyara, tsangwama, ukuba da rashin kyautatawar da take mata.

Ta dauki yayanta tamkar yan uwanta na jini, bata kula yayan kowa a duniya sai nata, sune ta mayar abokanta, yayyunta, kawayenta, abin gani ta ji farin-ciki kuma abin alfaharinta. Bata hada kaunar yayan ta da na kowa a zuciyarta. Bata dauki kanta a bakin komi ba face kaskantacciyar baiwa a gareta, duk da yakinin da ta ke da shi na cewa ita din diya ce ga Bello Makarfi.

A duk iya fadin tunaninta, ta kasa tuno ranar da yarinyar ta kuskurota ko da sau daya, ta kasa tuno ranar da yarinyar ta yi mata ba dai-dai ba. Ta kasa tuno ranar da yarinyar ta hantari ko daya cikin yayanta, duk da fada mata da take tayi da babbar murya cewa ta fita harkar yayanta, domin ita din ta tsane ta. Ta kasa tuno inda yarinyar ta taba gayama wani abinda take mata koda da subutar baki ne kuwa, har kuwa mahaifiyar ta, bata jin ta gayawa Saratu irin rikon da tayi mata a bayan ta. Kai iyaka tunanin ta bata taba ganin yarinya mai hakuri da yakanah kamarta ba, shin maye laifinta don Aminu ya so ta?

A kan me bazai so ta ba? Tana da qualities da dama da zaa so ta a kan su, me tayi mata ta tsaneta?

Rashin iyaye? To ai kowa ma zai iya rasa iyayen sa, ko ita a yanzu mhaifinta ya rasu, da uwar ta take zaune, sai a tsaneta?

Shegiya ce? To in shegiyar ce ma ai ba ita tayi wa kanta ba, ba ita ta jawa kanta ba, itama hakan ta budi ido ta tsinci kanta, kuma ko yau ta mutu zata shiga Aljannah kamar sauran halattattun yaya in har ta yi aiki na kwarai. Ko a yanzu ta tabbata da yarinyar zata fadi ta mutu, to bata da kaico a rayuwa!

Uwar rikonta da uban rikon ta kullum cikin shi mata albarka suke, bata wasa da lokacin sallolinta guda biyar duk rintsi, duk gajiya, duk sanyi, duk ciwo sai ta ganta tana sallah da asubahi, sai ta ganta tana sallah akan lokaci har wani mulmule ne baki wuluk bisa goshinta sabida tsabar sujjadah, kullum Kaman ana kara tisa shi ya fito radas.

Bata taba jin ranar da harshen yariyar yayi ashar irin na su Khaleel ba koda da kuskure ne kuwa. Bata taba jin ranar da wani ya budi baki ya furta wani kalami ga yarinyar, wanda ba na yabo da alheri bane.

Zata rantse wannan yarinyar bata san meye iskanci da shaidanci na wannan zamanin ba, da yammata suka sa a gaba, batasan kallace- kallace da karance  karancen banza na zamani ba, bata san bata lokacin ta a abinda bazai amfane ta ba, to meye laifin ta? Me ta yi mata?

Ta tsaneta domin Daddy Makarfi na son ta fiye da kowa cikin yayan sa? To amma in tayi tunani duk wani da mai hakuri da biyayyah ya kan samu mafificiyar kauna a zuciyar iyayen shi. Idan Bello Makarfi bai tausasa mata ba, ina zata je ta a tausasa mata? Ina zata je ta ji dadin rayuwar ta? Bata da kowa, sai su sai Allah da ya halicce ta, ya dace tayi wa Makarfi uzuri akan wannan, in haka ne to meye hujjar ta na tsana da tsangwamar wannan baiwar Allah?

Babu! Illa ita din mutum ce mai son kanta da yawa, mai biyewa sharrin shaidan da rudin zuciya, abinda Allah ya hore mata bai sa ta gode masa ta fuskanci abinda zai anfaneta ba, aah, ta wanzar da muhimmin lokacin ta wajen nuna tsana da kyara ga wata kankanuwar halittar Ubangiji da bata tare mata komi a rayuwa ba, ta biyewa sharrin kawaye da dukiyar da Allah ya hore mata, maimakon tayi aikin lada da su ko sadakatul  jariyah, aah, sai ta bata su ga tsafe-tsafen banza, wanda aka ce gaskiyar mai shi ne domin a yau, babu ya wargaje! Ba abinda hakan ya kare su da shi, Allah ma kadai ya san irin farin cikin da Saratu da Saratu da Bello Makarfi suke ciki a yanzun.

Ga dai gidan tana gani, ta sha wucewa ba sau daya ba ba sau biyu ba ta gabansa, amma ya gagareta shiga. Bai sake ta ba. Ta tabbata a zahiri ba kishi ko zafin ranta ne ya hanata komawa gidan ba, illa ita din ji ta ke ta kaskanta, ta wulakanta, hakannan bata da idon da zata dubesu, ko ma tace kwata-kwata ji take gidan yafi karfinta. (To tun a duniya kenan wata shariar, sai a lahira)!

Shin ma anya ba hakkin su ne ya rikide ya dawo kan yayanta ba? Wannan soyayyah da Faisal da Ameenu ke wa Intisar, ta tabbata ba kadan ba ce, kwayar idanun su ya nuna, komai na jikin su ya nuna, ta tuna Almeen magana yake amma a zahiri fatar bakin shi ce kawai ke motsi, a sanda ya ke cewa zai daina sonta zai daina kaunarta, in har hakan zai sa ta yafe masa

Wasu hawaye suka kara zubo mata, wannan shi ake kira nadama mara amfani. Inama ba tayi ba, inama bata aikata duk wannan ba!

Wani bangare na zuciyarta ne ya tunatar da ita cewa ai akwai sauran lokaci, lokaci bai kure ba, da zaki gyara bayan ki, ki nemi gafarar kowannen su, dukkanninsu masu sanyi ne (musamman Alameen) tabbas zasu yafe miki, ba tare da wani jan rai ko bata lokaci ba, kuma hakika zasu yi farinciki dukkanin su, idan kika nemi afuwar Intisar din nasa zai yi farin ciki da hakan.

Wannan tunanin ne ya dan sanyaya mata, ta mike domin dauko wayar ta, ba wanda tayi tunanin fara kira sai Almeen tana mai saka irin tausasan kalaman da zata yi amfani dasu wajen bashi hakuri, tare da tabbatar masa da amincewarta 100% kan bukatarsa.

Kuma tace da shi a washagari yazo ya dauke ta ya maida ta dakin ta, ya danganata ga Intisar ta nemi gafararta ta sa mata albarka, ta nemi gafarar mijinta da abokiyar zamanta su koma zama na amana da aminci kamar yadda tun farko Saratu babba ke so su yi.

A yayinda ta kai hannunta ga wayar, a yayin ne zuciyarta ta yi wani irin mummunan bugu irin wanda bata taba yi ba a rayuwar ta. Lokaci guda yawun bakinta ya tsinke, hakannan tsigar jikin ta ya tashi yarrr! Dai-dai sanda agogon dake makale a bango ya ke kada karfe biyu na rana, cikin daddadan sautin da yafi mata kama da wakar Bankwana!

A Gidan Bello Makarfi

Dawowarsa kenan daga sallar Jumaa da sassarfar shi, cikin takun sa mai karfi ya doshi sassansa, to amma tun safe yau haka yake sukuku ba kuzari. Aunty Saratu ta karaso ta amshi brief-case daga hannun shi da bakar suit da ya ratayo a kafadun shi, lokaci guda kuma tana loosing tie din shi tare da yi mai sannu da zuwa.

Bai amsa ba hakannan dai ya wuce zuwa toilet, tayi zugudiii a falo da taguni da hannuwa bibbiyu, cike da tunanin me ke damun Daddy a yau ne?

Daga can gefe wayar shi dake cikin aljihun suit din shi da ta aje ke ta tsuwwa, ta fiddota da nufin mika masa toilet amma ganin sunan mutumin da ke kiran ya dan kadata, Commissioner of Police Adams Stacy, kawai sai ta amsa ba tare da wani tunani ba.

Ya fara ne da magana cikin nutsuwa cewa ta sada shi da Markarfi direct wato kai tsaye inda ita kuma ta nuna baya kusa, ya fada mata ko minene in ya fito zata fada masa, shi kuma ya dage kawai ta bashi Makarfi har ranta ya baci ta kashe wayar, ta cillata bisa kujera.

A dai-dai lokacin daya fito daga toilet din, ba kuma tare da ya tambaye ta ita da wa take magana a waya ba kawai ya hau darduma ya zauna, can kuma ya mike ya fuskanci gabas ya tada sallah da ba zata ce azahar ce ko laasar ce ba, don kuwa dawowarshi kenan daga sallahr jumaa, kai da alama bama ya son magana kwata-kwata kuma baya cikin hayyacin sa, ta tambayi kanta ko rashin nutsuwar sa na da alaka da kiran da aka yi masa yanzun? Oho!

A irin wadannan lokutan itama bata faya takura masa ba, baya-baya take da shi har zuwa lokacin da shi da kansa zai ware ya kulata, sai ta maida hankali bisa jera abinci bisa tebur.

A sannan ne wayar ta cigaba da kara ba kakkautawa amma bata ko dube ta ba, ta tabbata mutumin dazu ne, ta tsani mutum mara yarda da kafiya.

Sai da ya sallame sallar a lokacin wayar tayi burarin ta har ta gaji ta katse ta kama wani, ya mika hannu ya dauki wayar ya ce,

Hello?

Daga can bangaren mutumin ya ce,

Your excellency, Stacy Adams ke magana daga ofishin yan sanda da ke Minna yace na gane ai, akwai lambar ka a waje na, ina fatan dai lafiya?

Yayi dan jim, yayinda zuciyar Daddyn ta shiga harbawa da sauri da-sauri, ya tabbatar wannan shine sakamakon mugayen mafarke mafarken sa a dan tsukin, sai dai ya ambaci (Innalillahi) a zuciyar sa yafi sau talatin tun ma kafin ya ji mabbabin kiran. Yayi karfin hali ya ce ina sauraronka. Mutumin ya ce cikin tattausar murya

Your edcellency, muna tare da gawar dan ka Dr. Alameen Bello Makarfi, ya yi mummunan accident akan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Kaduna, wanda bincike ya nuna yafi minti talatin da sakin sityarin motar shi wanda hakan ya janyo hatsarin motoci fiye da goma akan titin, babu wanda ya tsira a cikinsu.

So ku zo babban asibitin Minna ku karbe shi da kayayyakin da ke cikin motarsa da ke tare damu. Ina mai yi maka taaziyya, hakika rasa mutane irin su M.A.B, ba karamar asara ba ce, ba ga iyayen su kadai ba har ma ga alummar Nigeria bakidaya.

Hawaye na kwarara daga idanunsa, irin wadanda bai taba zubarwa ba, har kuwa lokacin da aka yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai da san da ya rasa iyayen sa! Ya ce,

“Daga Allah muke, kuma gareshi zamu koma. Alameen Allah ya ji kan ka, ya sa mutuwar ta zamo hutu a gareka, ya baka Aljannar Firdausi madaukakiya, ya yafe maka kurakuranka, ya inganta aiyukan ka na kwarai, ya shafe zunubanka, ya sa ka zamo Da mai ceto ga iyayen sa.”

Na yafe maka duniya da lahira. Ina rokon Allah yayi maka rahmah da gafara!. Wasu hawayen suka zubo, irin wadanda basa saukaka kunci da radadin mutuwar da a zuciyar mahaifansa! Balle da irin Alameen Bello! Ba iyayen sa kadai ba, duk ma wanda wata muamala ta taba hada shi da shi koda sau daya ne, dole ya girgiza da gushewar sa a doron kasa.

A lokacin ne ye tuna wannan ba lokacin kuka bane, lokaci ne na karfafa zuciya, lokaci ne na nunawa Alameen din sa gata na karshe a rayuwarsa, wanda ba komi bane illa Addua da nema masa rahmar Ubangiji.

Wani Imani ya zo masa. Ya yunkura ya mike ya doshi kofa ya manta babu ko kwakkwarar suttura a jikin sa. Aunty Saratu ta mike bata ko ganin abinda yake gabanta illa ta mika masa babbar riga da takalmi, suka fito harabar gidan a tare.

Har zuwa sanda Daddy da mukarrabansa suka shiga mota suka bar gidan, bata ko motsa daga inda take tsaye ba, hakannan hawaye ko digo daya bai fito daga idanuwan ta ba. Ta kasa gasgata alamarin, ta kasa gaskata abinda kunnuwan ta suka jiyo mata, ta kasa amincewa da wai Alameen ya rasu! Ta dauki alamarin a matsayin irin mugayen mafarke mafarken nan da dan adam ke yi ya farka cikin dan lokaci.

Allah kadai yasan tsawon awonnin da ta yi a tsaye a wajen tamkar sassakakken gunki ko gungumen itace. Har zuwa lokacin da motar da ke dauke da gawar Alameen tare da motocin da ke biye da ita suka cika harabar gidan. Ta daga ido taga wai yau Alameen ne ake fiddowa da sunan babu wata gaba dake motsi a jikinsa kuma babu numfashi. Abin mamaki, babu ko kwarzane a jikin sa, babu ko digon jinni a jikinsa tamkar mai barci kai baka ce accident yayi ba. Fuskarsa da a kullum ke cike da ilhama da cikar zati, tare da kwarjini na musamman a yau ma hakan ta ke, baya ga wani haske da annuri da ya kara tamkar a ce Alameen ya bude kyawawan idanuwan sa ya amsa.

Ta dai tabbatar wannan zahiri ne ba mafarki ba ne sai ta yanke jiki ta fadi, yayin da jinni ya soma bin kafafunta ba kakkautawa. Babu ko tantama dan yaron cikin da take dauke da shi ne ya bi dan uwan sa nan take.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.8 / 5. Rating: 24

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siradin Rayuwa 35            Siradin Rayuwa 37 >>

8 thoughts on “Siradin Rayuwa 36”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×