Skip to content
Part 40 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir Takori

Bayan Watanni Uku

Lallai babu cutar da Allah ya saukar a doron kasa ba tare da ya saukar da ita tare da maganinta ba. A yau Hajiya Nafisatu Bello Makarfi, ke sauka daga matattakalar jirgin KLM cikin filin jiragen saman da ke garin Kaduna. Dr. Rehab Mohammed tare wasu daga likitocin asibitin meritime su biyu sune suka yo mata rakiya daga Birnin Miami da lafiyarta da hankalin ta sumul kalau, inda yayan ta Faisal da Nasir suka zo taryenta, kar kaso ka tona zuciyar su mai cikke da godiya ga sarki Allah da ya baiwa mahaifiyar su lafiyarta sumul kamar ba ita ce ta tafi bata san abinda take yi ba. Suka rungume juna daya bayan daya cike da kewa da farin ciki, a yayin ne wasu hawaye marassa dandano suka zubo mata.

Ba komi ta tuna a lokacin ba face ranar da Alameen ya zo ya dauketa a air-port zuwa gidan iyayen ta ranar da ta dawo Dubai, kuma ranar da ta kasance ta karshe a tsakanin su. Ashe wani bakin  cikin na nan yana jiran ta, shine rasuwar mahaifiyar ta Hajiya Iyami. A nan kuka ya zamo mata sabo.

Yayan ta sunyi nufin tafiya da ita gidan mahaifinsu inda ita kuma ta nuna aah, suje su fara rokar mata gafararsa tukunna, bazata koma masa gida ba da yawunsa ba, kuma ta san har ga Allah ta zahince shi kwarai da gaske, in bai yafe mata ba ta san hakkin sa kadai bazai barta ba. Baa maganar hakkin Saratu da Saratu da ke kanta.

Ta roke su su nema mata gafarar wadannan bayin Allah kafin ta zo da kanta neman gafarar su. Ta tabbata hakkinsu ke ta dawainiya da rayuwar ta.

Komawarsu gida suka tadda labarin duk suna asibiti, Ihsan ce ke nakuda tun shekaran jiya haihawar ta zo da tangarda, daga karshe dole mahaifinta ya sa hannu aka shiga da ita dakin tiyata bakunan su cike da adduoin samun saa domin hakika ta jigata, duk wani mai imani dole ya tausaya mata.

To alhamdullahi an yi nasarar fiddo jariri katoto da shi lafiyyaye. Daddy ya amshi Babe da niyyar yi mishi addua da lankaya mishi kalmar shahada amma sai zuciyarsa ta buga da karfin gaske! Yayi tazbihi ga Allah ya tsarkake shi a zuciyar sa, ya kara imani da buwayarsa da isar mulkinsa akan komi.

Babu ko tantama wannan Alameen Bello ne yake rike da shi a sanda mahaifiyar shi ta haife shi. In kasan photocophy na Alameen to wannan jaririn ne. A take ya lankaya mai sunan shi cikin kunnuwan shi wato Alameen Alameen Bello.

Sai dare aka fito da Ihsan zuwa dakin hutu, duk tayi wani fiyat ta zabge sabida wahala. A wannan dan tsukin ne kuma taga kauna da karimci daga lyaye da yan uwan Alameen irin wadda bata taba tsammanin zata samu ba. Ta tabbata ita yar gata ce amma Alameen ya fita gata gaba da baya, kuma kaunar da iyaye da yan uwan shi ke mishi, duk dimbin arzikin iyayenta ita bata samu koda kwatankwacin ta ba.

Ashe ba dimbin arziki da dukiya ne gata ba, aah, matsayin da kake da shi a zuciyar iyaye da yan uwan ka. Har aka basu sallama suka dawo gida bata san kukan Baby Alameen ba, koyaushe yana jikin Aunty Saratu da kannen mahaifin sa, iyakacin ta da shi shan nono kadai. Gaba daya sun dauki kaunar duniya sun aza bisan Alameen karami musamman Faisal da Najib da shiga goma fita goma sai sun ce a kawo masu yayansu.

Bayan sunan Alameen ne suka doshi Daddy da alfarmarsu na ya yafewa mahaifiyarsu kurakuranta, domin hakika tayi nadama mara iyaka. Daddy sai ya yi murmushin sa mai nufin alamura da dama kamar koyaushe zai yi wata magana mai muhimmanci. Ya ce,

“In don ni ne ai ba abinda tayi mun, ban da kaunata da take da ku yayan ta. Wadanda ta zalinta kam suna can inda suke, don haka ta je na yafe mata duniya da lahira. Amma maganar wai ta dawo dakinta bata taso ba, domin mai hali baya fasa halin sa.

A yanzu kam girma ya hau ni, ina bukatar hutu, bazan iya jurar tashin hankali ba. Don haka ku je ku tambayeta idan har ta shirya zama na amana da zuciya daya da duk wanda na kawo cikin gidan nan na ajiye, to ana maraba da ita. Idan kuma akasin haka ne a zuciyarta to don Allah ta nemi wani gidan don wallahi a yanzu bazan iya jure halinta ba!

To bayan dogon kai ruwa rana da kyar da sidin goshi Aunty Saratu ta shawo kan Daddyn ya yarda da komen Hajiyar da babu shakka ta darastu da rayuwar duniya. Har kasa ta tsugunna neman gafarar Saratun tare da alkawarta mata tazo ne su yi zama na amana da aminci na har abada. Saratu ta tabbatar mata duniya da lahira ta yafe mata domin yayanta sun gama mata komi a rayuwa. Ta nemi Intisar domin neman gafarar ta, inda ake sanar da ita tana Alkahira tana karatu.

*****

Bayan Shekara Daya

Faisal Bello Makarfi ke taka matattakalar da zata sadashi da falon Daddy Makarfi cikin sassarfa, sanye cikin farar shirt product din DKNY da bakin wandon Tokyo da misalin karfe shidda na yammacin ranar Lahadi. Isowar shi kenan cikin garin, kamar kullum, a yau ma ya saya kwayar idanun shi cikin bakin gilashi domin boye halin da kwayar idon shi ke ciki.

Ya yi sallama a babban falon kana ya jinkirta har ruwa sanda Daddyn yayi masa iznin shigowa. Zaune yake ya tasa allon computer (Laptop) a gabansa bisa tebir inda suke musayen sako da diyarshi Inteesar tana bashi labarin karatun su a makaranta. Ba tare da ya dauke hankalin shi daga computern ba ya amsa sallamarsa tare da nuna masa wajen zama daga gefen sa.

Aunty Saratu ta shigo dauke da babbar warmer da kofunan shan ruwa ta aza daga can kan dining tana murmushi tace aah bakin Ikko ne sai yanzu, kai da tun jiya muke tsammanin ka. Ya ce wallahi kuwa shirye shiryen tafiyana ne ya tsaida ni, kin san babu biza mai wuya irin ta U.K.

A sannan ne Daddy ya cira kai ya bishi da kallo na mamaki. Sannu a hankahi kuma cikin dan kankanin lokacin yayi nazarin wasu muhimman abubuwa da dama a tare da yaron. Ya sa hannu ya fidda mudubin idonsa ya kara duban Faisal sosai. Ta fahimci uban da dan na bukatar privacy domin tattauna matsalolinsu sai bata matsa da tambayar me zai je yi ba ta ce Allah ya shige mana gaba. Daga haka ta ba su waje.

Daddy ya ce cikin wata murya mai kama da umarni.

Faisal ina zaka je?

Yayi dan dawurwura na dabarbarcewa da rashin kwakkwarar hujja ya ce am eh, Daddy, admission dana nema tun shekarar baya a can Birmingham domin karo Ph D dina, har na manta kawai sai shekaranjiya suka aiko min, to shine nazo in yi muku sallama, zan ta fi.

Daddy ya ce Faisal, me ke damun ka? Kana kallon kan ka a mudubi kuwa? Tun bayan rasuwar Alameen na ke lura da kai babu cigaba a alamarinka, kullum kara lalacewa ka ke. Wannan ramar da kake tayi a kullum kamar kudin guzuri ta mece ce?

Yaji idanuwan sa sun ciko taf da hawaye amma yayi kokarin maida su. Cikin jarumtaka yace Allah babu komi Daddy.

Yace to kaima Faisal ko dan uwanka zaka bi ne ku barni ni daya? A wannan lokacin duk jarumtakarsa saida hawayen suka balle. Ya zare gilashin sa a lokacin ne Daddyn ya samu damar ganin yadda idanuwan sa suka fada sosai, baya ga kadawa da suka yi sukayi jawur kamar gauta. Ya ce,

“Ina adduar Allah ya bani tsawo ran da zan kula da kai a gaba dayan ragowar rayuwar ka, kamar yadda ka sadaukar da kuruciyarka wajen kulawa, hidimar mu da tarbiyyantar da mu.”

Ya ce, “In haka ne Faisal me yasa zaka bar ni? Me yasa baka son tsugunawa a waje daya? Yau kana can gobe kana nan kamar wani tsuntsu. Ka kasa tsayawa ka ginawa kanka rayuwa ta da namiji. Ba ka ko tunanin yin aure! Karatu dai karatu kadai Faisal kaman alhuda huda?

Duba kaga kanin bayanka matar sa tsohon ciki gareta, haihuwa yau ko gobe. Dubi Alameen ya tafi, amma ga Alameen Alameen nan na yawo cikin gidan nan yana tuna mana da shi muna yi mishi addua, ko ba zaka yi aure domin bukatar kanka da cikar mutuncika ba, kayi domin shi kansa ibada ce mai zaman kanta.

Ban san me kake nufi da rayuwar ka ba, ban san meye planning dinka a rayuwar nan ba. Ina jiye maka tsoron kazo duniyar a banza ka koma a hofi. In kana ganin bani iya yi maka maganin matsalarka to a kalla zan baka shawara wadda kai a shekarun ka bazaka hangosu ba. Ko kuma mutuwar Alameen ce ta ke nukurkusar ka har yanzun? Take neman kayar da kai tun karfin ka bai kare ba?”

Yasa hankici ya share idonsa ya share dogon karan hancinsa ya ce,

“Aah Daddy, na riga nayi tawakkalin cewa ya tafi, ba kuma zai kara dawowa ba.” Ya ce,

“Madallah, ni dai da zaka bi son raina da ka hakura da tafiyar nan ka rungumi aikin ka an kuma daura maku aure da matar marigayi Ihsan da ka faranta mini, ko ba komai yarinyar ta nuna mana ita mai kaunar mu ce ba wai abinda muka mallaka ba. na dade ina kissima yiwuwar hakan a zuciyata ba tun yau ba..”

Ya dago cikin wani irin yanayi na firgici da tashin hankali ya dubi mahaifinsa, kana cikin nutsuwa yace

“Daddy! Na rokeka alfarma, don girman Allah koda wasa kada ka kara tunanin zancen nan balle ka fada wani ya ji. Kada ka bari alamarin yayi tasiri a zuciyarka don Allah? Yaya ma zaayi ka yi wannan tunanin? Zaka karasani kwanana bai kare ba.

Ka bar ni in ji da ciwon da zuciyata ke yi. Ba matar da Alameen ya aura akan yana so ya tafi ya bari ba don ba ya so ba, ko yarinyar da ya taba nema bazan iya aure ba balle matar sa. Kayi min uziri ka karbi hanzari na, in dai tafiya ce na fasa amma don Allah, kada ka kara ce min wani abu makamancin wannan.

Daddy ya yi murmushi ya ce yaro dai yaro ne. To kaje ka kawo min yarinyar da kake so cikin kwanaki goma rak! Amma in ba haka ba zan daura aurenka da Ihsan a ranar da kwanakin nan suka cika. Na gaya maka na kara gaya maka babu wasa cikin magana ta.

Cikin matsananciyar damuwa ya ce ni bani da wata yarinya da na ke so. Ban taba son wata ya mace a duniya ba. Alameen kadai na ke so!!! Don haka na baka wuka da nama ka zartar da duk hukuncin da ka ga dama a kaina, ka zabamin ko wacece amma ka taimake ni Daddy kada ka aura min matar Alameen. Wallahi zan gudu in bar garin, don ni Ihsan Yaya ta nake ganinta.

Saura kadan dariya ta kwace masa amma ya cije ya daure yace shikenan, tashi je ka sai na neme ka. Sai dai ina mai gargadinka ka cire abinda ke damunka daga zuciyar ka domin tsira da lafiyarka. Babu wata cuta da Allah ya saukar a doron kasa da bai saukar da maganin ta ba. Ka kaiwa Sarki Allah kukan ka amma ba wannan damuwar da ka sawa ran ka ba babu gaira babu dalili.

Ya mike kamar wanda kwai ya fashewa a ciki ya doshi sassan Anti Saratu. Tun daga hangoshi Alameen karami ya watsar da kayan wasan shi ya rarrafo da hamzari ya kama kafafun shi, shi kuma yayi gaggawar russunawa ya daukeshi ya rungume a kirjin shi.

A lokacin ita Ihsan ta tafi asibitin Alameen Memorial da ake canzawa suna maimakon MERITIME. Ko ba don haka bama a dan tsukin bata samun zama sabida shirye  shiryen bude asibitin da ya gabato, tana sa ran yaye Alameen karami ne ma cikin wannan watan mai kamawa domin hidimomin sun mata yawa, ga tafiyar ta karin karatu saura watanni (3) kacal.

A kan Alameen bata da kaico ta san Anti Saratu na iya kokarin ta a kan sa, haka Hajiyar Alameen duk wani buri da tattalinta ya taallaka ne a kan dan yaron da bai ma san ko shi wane ne ba. Motsi kadan zata shigo sassan Antin tana ina maigidana ne? Ban ji duriyar sa ba tun dazu, wane shagalin yake yi ne?

Kayan wasa kuwa na dubban nairori bata jin kyashin saya masa ko na nawa ne har ma wanda yafi karfin shekarun shi irnsu automatic motorbike da kekunan yara musamman take yo odar su daga Germany duk don Maigidannata. Inda shi kuma Daddy bashi da wani aboki kaman wannan Alameen Alameen Bello. In kaji shi yana bashi labari sai ka rantse da wani cikakken mai hankali ne yake magana ba da yaro dan shekaru biyu ba.

Faisal ya zauna ya kifa fuska cikin tafukan sa, yayinda Alameen ke dabdalarsa a dokin wuyansa. Antin ta karaso rike da tambulan cikke da sassanyar madarar shanu fresh ta mika masa. Ba tare da yayi musu ba ya amsa ya shanye wata niima da sanyi suka sauka a zuciyarsa. Jijiyoyin kansa duk sun mike rada-rada a kansa haka tsigar jikinshi sai tashi yake, tabbacin zazzabi ke neman kama shi.

Ba ta katse shi ba har saida ya samu nutsuwa don kansa, kana cikin sanyin murya ya ce,

“Aunty, kin ji abinda Daddy ya yanke a kaina?”

Ta ce, “Ya hanaka tafiyar ba? Ni ma ban ga dalilin tafiyar ba”

Ya ce, “Tafiya ni na fasa da kaina, cewa yayi in kawo matar aure cikin kwanaki goma ko ya aura min maman Alameen karami. Sabida Allah Anti yaya ma Daddy zai yi wannan bahagon tunanin? Sabida Allah an yi mun adalci kenan? Cikin mu wa aka taba zabawa matar aure? Yaya zaayi in iya hada rayuwa da matar da Alameen ya mutu ya bari ba don baya so ba, sai don mutuwa da tayi mishi yankan kauna? Wannan ai cin amana ne da tozartawa.

Wallahi ko yarinyar da Alameen ya furta ya na so, bazan iya aure ba balle matar sa. Komi son da nake mata kuwa zan iya jurewa. Don na tabbata in shine ya san ina son mace, da ko itace autar mata daga ranar bai kara sonta. Zai hakura ya bar mini domin shi dan uwa ne mai dimbin karimci da sadaukarwa.

Na zo ne in roke ki alafarma ki hana Daddy wannan kudurin nasa, ni kuma nayi alkawarin yin biyayya ga duk matar da ya zaba mini matsayin abokiyar rayuwata ta har abada, amma ni ba zan auri Ihsan ba.”

Ta yi murmuishi ta ce, “Na ji uzurinka Faisal, kuma da yardan Allah zanyi kokarin in ganar da shi. Amma da sharadin zaka amsa min wata tambaya guda daya da zan yi maka. Kayi min alkawarin zaka fada min gaskiya ni kuma na yi maka alkawarin ba zaka auri Ihsan ba!”

Cikin sauri ya ce, “Wace tambaya ce Anti? Wallahi zan amsa miki iyakar abinda na sani.”

Ta ce, “Shhhh, ka daina saurin rantsuwa akan abinda baka da tabbas.”

Ya ce, “Wallahi Anti zan gaya miki.”

Rantsuwar da yazo yana dana sanin yinta kamar yadda ta gargadeshi a farko.

Ta tattara hankalinta gabadaya gareshi cikin murryar manyantaka da bada umarni tace menene hakikanin abinda ke damunka, tsakaninka da mahaliccin ka?

Cikin juyayi da dana sanin alkawarinsa ya ce,

“Anti soyayyah ce ta ke azabtar dani. Shekaru dai-dai har goma sha daya. Amma alhamdulillahi a yanzu ta kusa karasani nima in bi dan uwana in huta da azabar ta.

To amma matsalata shine bana so tayi galaba a kaina, kamar yadda tayi galaba akan dan uwana.

So nake in nuna mata banbancin mu na cewa ni mai iya controlling zuciyata ne sabanin shi da zuciyar ke juya alamuransa.

Idan na barta ta yi galaba a kaina sauran yan uwana ma bazata kyalesu ba, haka zatayi ta bin mu daya bayan daya tana kashewa har sai ta karar damu. Don haka bazan barta tayi galaba a kai na ba.”

Murmushi tayi ta ce,

“Wace yarinya ce kake so shekarun da suka wuce, ba kuma zaka taba iya aure ba har ka bar mu domin ta?”

Cikin kaduwa da matsanancin mamaki ya ce, “Anti wa ya gaya miki wannan maganar?”

Ta ce, “Bai zama dole ka sani ba, ka yi alkawarin amsa min tambayata ne kawai amma ba kai ka dinga tambayata ba. Sabida haka ka ji tsoron Allah ka idasa cika alkawarin ka.”

Ya sunkuyar da kansa kasa, in banda zufa ba abinda ke ketowa daga koina a sassan jikin shi, duk kuwa da A/C da fanka da ke ta aiki a falon. Ya yi dana sanin saurin rantsuwar sa. Nauyi da kunyar idanunta duka sun masa mayafi. Muryar sa can kasan makoshin sa tamkar ba tashi ba, ya ce,

“Anti Inteesar din ki ce!”

Ba tare da alamun wani mamaki ko girgiza da furucinsa ba ta ce,

“To yanzun ka daina son nata ne?”

Ya girgiza kai har yanzu bai dago ba, ji yake har abada bazai iya kara hada idanu da ita ba, a sanyaye ya ce,

“Ya zaai na daina sonta? Ita din ce dai har yau bata bar ni na huta ba kuma har gobe ba zan taba iya auren ta ba!”

Ta ce, “Hujjah?”

Ya ce, “Hujjata a da shine kasancewar mu uba daya. Hujjata a yanzu kuwa Alameen ya so ta. Ni kuma bazan taba yin tarayya da shi a son komi ba ban hakura na bar mishi ba. Don na san da a ce ya san ina sonta, da tuni ya hakura ya bar mini.”

Saura kadan dariya ta kwace mata amma ta cije,

“Ta girgiza kai tana murmushi”

Ta ce, “Wannan ba hujja ba ce ba Faisal. Don haka tashi je ka. Cikin kwanaki goma ka yi tunanin abinda ya dace da kai. Ko dai samawa zuciyarka abinda ta dade tana so don dorewa rayuwa mai inganci ko kuma auren matar yayan ka.

Ina mai tabbatar maka har yau, har gobe Saratu na son ka. Soyayyarta da Alameen wata kaddara ce daga Allah amma kai kadai take so tun tana mitsitsiyar ta. Ta damu da kai sosai, zata iya yin komi a domin ka. Gareta duk yadda rayuwa ta zo, a karbeta. Don haka ne ta karbi soyayyar Alameen.” 

Sau da dama tana yiwa komi na rayuwarta uzuri da Faisal da Daddy Makarfi. Ta baka wata daraja da muhimmanci a rayuwarta irin wanda bata baiwa kowa a duniya ba. Duk halin da kake ikrarin ka shiga a wancan lokacin, ina mai tabbatar ma itama ta shiga kwatankwacin sa koma fiye da naka. Ta damu da kai sosai. Ta na matukar kishinka fiye da yadda baka zato.

A duk halin da take ciki, na farin-ciki ne ko na bakin ciki kai take tunawa tace Allah Sarki Ya Faisal! Da yana nan da kaza-da kaza, da kaza bata faru ba, da kaza ta faru. Ta fi kowa bakin ciki da tafiyar ka ni nasan wannan, amma ita tsammani ta ke ban gane ba.

Ya girgiza kai har yanzu kan shi a sadde, ya ce,

“Anti wannan kauna ce ba soyayyah ba. Intisar kauna ta kawai take, amma bata so na!”

Ta ce, “Babban jigon soyayya shine kauna. Kai ba namiji bane? Baka san yadda zaka yi ka gina soyayyar ka a zuciyar matar da kake so ba? Sai ka zuba ido ka zama dan kallo kana muku-muku cikin daki? To zauna nan kallon ruwa har sai kwado yayi maka kafa.

Ina mai tabbatar maka Intisar ta shigo wani matakin da take tsananin bukatar soyayyar da namiji a yanzu, komai na iya faruwa da rayuwar ta balle a inda su ke da babu kowa a tare da su sai Allah da ya halicce su. Bar ganin ta yarinya mai kamun kai, da yawan yaya mata basa iya tsallake wannan stage din (adolcence). A jiya da na lissafa jibi ne zata cika shekaru ashirin da haihuwa. Faisal me kaka jira da rayuwar ka? Ina ganin lokaci yayi da ya kamata ku fuskanci alkibla sahihiya.”

Kwana yayi yana nazarin zantuttukan da suka yi da Anti a daren jiya. Sai dai har zuwa lokacin ya kasa tsayarwa da kansa wata sahihiyar shawara. Ya kasa daina ganin Saratu a matsayin mai dimbin laifi a gare shi. Laifin da yake jin har abada ba zai iya yafe mata ba!

Hakan nan zuciyar ta ki bada goyon baya, ta ki daina bugawa a kowanne second da so da kaunar Inteesar, shi kam ya rasa inda zai tsoma rayuwarshi ya ji sanyi.

Ya kasa zabarwa kansa komi cikin zabin da aka bashi. Abinda yake da tabbaci kawai shine ko zai mutu ba aure, ba zai auri matar Alameen ba, kamar yanda ba zai iya auren yarinyar da Alameen ya furta yana so ba kome zaayi da shi kuwa, balle Intisar din da har abada ba zai daina ganinta a matsayin azzaluma ba a cikin soyayya, mayaudariya mai son kanta da yawa kuma maciyiya amanar kauna.

Laifuffukan ta gareshi basu da iyaka kuma tananinsu ma bata lokaci ne. Ya dai barta da duniya da abinda ke cikin ta kadai sun isa su koya mata hankali.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.6 / 5. Rating: 21

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siradin Rayuwa 39Siradin Rayuwa 41 >>

5 thoughts on “Siradin Rayuwa 40”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×