Skip to content
Part 42 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir Takori

Da gudu ta fada kitchen din ta kankame yar uwar ta, ta daga ta cancaras tana juyi da ita a kitchen din ta ce,

“Aunty Intisar sunan ki daga yau, kin yi mun abinda har abada bazan manta ba, me kike so in miki nima in faranta miki don Allah?” Ta ce,

“To aje ni in gaya miki, kada kirjin ki ya bude?” Ta dire ta tana dariya ta ce,

“Wallahi baki da nauyi, shafal kamar na dauki bokitin ruwa.” Ta bita da kallon mamaki ta ce,

“Hunainah, dama kina da karfi haka?” Ta juya mata baya cikin jin kunyar abinda ta yi, ita kanta bata san inda karfin nan ya fito ba, karfin soyayya kenan?

Ta dafa kafadarta ta ce, “Me ya faru ne sister, you look so happy than ever, whats the matter? (Da alama kina cikin, farin  ciki fiye da koyaushe, me ya faru?) Ta juyo ta koma cikin nutsuwarta ta ce,

“Ke share kawai, nayi passing papers dina in ji Saajid Marwan (abokin karatun ta).” Ta san halin Intisar sarai, yanzu idan ta ji zancen nan sai kowa a gidan ya ji, tsiya kuwa da zasu yi mata ita da Hidaya, sai ta kasa kurbar ruwa a gidan don ta sha ce musu ba wanda ya isa ta bata muhimmin lokacin ta a kansa, sabida duk mazan mayaudara ne balle Hidaya da tayi saurin yarda da Najib bata ko tunanin karatun ta, gata nan har yau ta kasa komawa karatun, Najib sama- Najib-kasa bata da wani aiki sai nasa ga tsohon ciki tun bata cimma komi a rayuwa ba (a tunanin ta fa).

Intisar ta yi murmushi don ta sunsuno yar uwarta ta amma sai itama ta bagarar ta ce,

“Shine kuma sai ka ce yau kika fara cin jarrabawa, idiot” Ta sa hannu ta lakace mata hanci ta cigaba da kwabin da ta ke cikin mider, ta ce,

“Je ki daki ki cigaba da hirar ki da Saajid Marwan din naki, ko dai da shi zaa yi ne?”

Ta kyalkyale da dariya tace amman kin yanke ni, wannan abu dan kutuf ya kuttun tofa miyau? Ta ce,

“Yi a hankali dai ke mace ce, kada ki haifo irin sa ko wanda ya fi shi muni.”

Ta dubi yawan aikin da Intisar ta yi cikin dan lokaci tana can tana soyayya, ta jinjina kai ta ce,

“Amma ni a ganina Hajiyar su Najib ba karamin taimakon rayuwar ki tayi ba, tayi miki horo na ya mace, abinda kike yi ni ko rabin rabin sa bazan iya ba, ke ko cake wannan wallahi ganin wahalar in zauna in kwaba na ke.”

Ta yi murmushi ta ce,

“Nima na sha tunanin haka, in banda dukan da take mun da kebur, da shocking din da take jona mini kamar wata barauniya, da zagin da take mun na fitar hankali da ni da Anti Saratu, da gorin da take mun a kan son yayanta, wallahi da na gode mata.”

Hunainah ta fiddo ido ta ce, “Shocking fa kika ce? Ta girgiza kai cikin tuno tsohon bakin ciki ta ce,

“Shi fa, ke dai kawai a share, ban taba gayawa kowa ba ko Antina sai Alamin, na barwa raina, na barwa Allah ya saka min abinda matar nan ta wanzar da rayuwanta a yi mun, na barta da fitowar rana da faduwarta, na bar ta da duniya da abinda ke cikinta, na bar ta da Allah!”

Hawaye suka ciko idon ta, Hunainah ta ce, “Menene kebur? Ta ce,

“Wani siririn karfe ne da ake daure itace da shi, yafi bulala zafi, ya fi kututturen ice shiga jikin dan adam, kada Allah yasa a doke ki da shi Hunainah. Ta janye rigar ta sama ta nuna mata gadon bayan ta ta ce,

“Duba nan ki ga, wannan tabon har abada ba zai goge daga kafafuna da gadon baya na ba, kamar yadda har abada bazan yafe mata ba.”

Hunainah ta dubi zanen da ke gadon bayan ta wani a kan wani, sai dai yabi lafiyar jikin ta ya fara bacewa, ta share kwallar idon ta tace ido na idon matar nan Unh! Intisar ta yi murmushi ta ce,

“Kada ma ki fara wannan tunanin, don a yanzu ta zame maki dole, kakar dan ki da Hidayah zata Haifa, ni kuwa ta gama mun komi tunda ta haifa mun Alameen ta shayar da shi, ta so shi, ta kauna ce shi fiye da komai a rayuwar ta, ta haifa mun Faisal daya zamo ginshiki kuma tushen duk wani mataki da na taka a rayuwa.

Ya so ni, ya kaunace ni yayi duk iya kokarin sa wurin gina mun rayuwa mai inganci. Ina tabbatar miki duk wani hakilon Faisal na rayuwa domina ne, ni yake nemawa, bai damu da kansa ba tunda yana daga tsatson Hajiya, bana jin ko jikokin jikokin su zasu taba wahala a rayuwa.

Tana da arzikin da hankalin ki ba zai taba baki ba don haka ni yakema tanadin rayuwa amma ba shi ba. To don ta ki ni bata yi laifi ba, don ita zuciya an halicce ta da kishi a kan abinda ta ke so, ta na son yayan ta, su kuma suna so na, dole ta yi kishi dani.”

Hunainah ta yi ajiyar zuciya ta ce,

“Allah ya saka miki.”

Ta ce, “Wannan kawai itace magana Hunainah, A bar wa Allah ya fi a ja Yasin. Yanzu me ta isa ta yi mun a duniya sai dai in mata in kwana lafiya, to amma ba zan yin ba, ko gobe na gan ta durkusawa zan yi har kasa in gaishe ta, don na san Alameen ko a ina ya ga Mamata ba zai yi mata kallon banza ba, zai tsuguna da guiwoyin sa ya gaisheta cike da girmamawa. Ya gaya mun cewa kiyayyar da take min bata da dalili Allah ne ya daura mata, ba don kuma wani aibu na ta ke ki na ba, illa kawai ta samu kanta a mai ki na. Sai in fidda ta cikin masoyana in rungumi masu so na.

Bai yiwuwa mu samu soyyaya daga kowa don ko Annabin rahma Allah bai bar shi ba makiya ba. Kenan ya dace na yi mata uzuri. Uwa- uba tana auren mutuminda bani da kamar sa a duniya, tana auren Daddy Makarfi, da dadi ba dadi ta yi hakuri ta zauna da shi cikin kowanne hali. Ni kuma duk mai kaunar sa abin girmamawa ne a gareni.

Don haka a ranar da kika yiwa Babar Alameen rashn kunya, a ranar zan lakada miki dukan da baa taba yi miki ba!”

Ta rungumeta tana dariya ta ce, “Allah ya sauwake ki doke ni dukan haushi sai dai ki yi mini dukan kauna.”

Ta ce, “To ko ke fa?”

Cikin dan lokaci sun kammala aikin su mai ban shaawa, abinci kala-kala har kala bakwai Intisar ta shiryawa bakin ta da bata san ko su wanene ba, abin sha kala hudu, (snacks) kuwa baa maganar su kala-daban  daban mai ban shaawa. Gabadaya abincin ta babu irin namu daga na Masar sai na Korea. Sai da kasusuwan bayanta suka amsa kas! Kana ta shiga wanka.

Ta dade tana gyaran fatar jikinta da mayuka masu gyara fata da sanya taushin fata, irin su aveeno E45 da norwegian formula kamin ta shirya cikin wani tattausan lesi (cotton) baki mai kananan duwarwatsu, ta killace gashin kanta cikin hair bound ta mulke siraran labbanta da lip-balm mai sanyin kamshi, ta kuma feshe jikin ta da turaren cKIn2U. Iyakacin kwaliyar ta kenan a kullum cool don ko kwalli bata damu da ta sanya ba sai Anti Saratu ta matsa mata.

Hunainah na gefen gado can a makure tana amsa waya cikin yar karamar murya don bata son Intisar din ta ji, da ganin yadda take kashe murya kasan da masoyin da a ke matukar so ake magana. Intisar ta yi biris da ita kaman bata san me take ba amma a ranta tayi dariya tayi har ta gaji.

Ta na zaune a gaban mudubin bata mike ba tana fesa turare wani dan yaro da bai fi shekaru biyu ba ya yane labulen dakin ya shigo yana zare kyawawan idanun shi alamun bakunta, yatsun shi biyu duka a baki yana tsotso, sanye yake cikin caftan na purple shadda rini me tsadar, kafar sa daure cikin farin kambas.

Da farko dai zuciyar ta ce tayi wani irin mummunan bugu kafin hawaye su biyo baya su bata mata kwalliyar fuskar ta, kirjin ta yana harbawa da sauri da sauri ta karasa ga yaron, ta zube ragwaf a gaban sa ta kama hannuwan shi da ke cikin bakin sa ta rungume shi sosai a kirjin ta, hawayen ta na zuba a gadon bayan sa.

Ganin babba tana kuka shima sai yasa kuka, ta yi saurin share idon ta tana dariya ta cira shi zuwa gefen gado ta zaunar da shi a kan cinyoyinta ta jawo jakar Hunainah da bata rabo da choculate ta dauko kit-kat ta bare ta bashi, ta ce,

Alameen  Alameen Bello, suna na Aunty Intisar, ka na so na? Ya gyada mata ka kawai cikin halin ko in kula, ta ce wa ya kawo ka? Yace Uncle dina da Baba na.

To ai uncle din nashi da Babannin nashi suna da yawa, don haka bazata ce wanne ne ba wanne ne ba. Ta ce ka ga shi wancan Alameen din yana sona, yana yi mun murmushi, kaima kayi mun murmushi don Allah?

Gaba daya ya bude bakin yana yi mata dariya da kyawawan hakoran shi, beauty point din da cleave suka lotsa a tare, tayi saurin juyawa tana share hawaye.

Hunainah ta kashe wayarta ta dauki yaron a cinyar ta, itama kwalla ta cika idonta tace Allah da girma yake, Intisar ashe akwai irin wannan kama ta da da uban sa? Intisar ba baki, tace Alameen ka ga ka sa Aunty Intisar kuka, ka bata hakuri ya kai dan hannunshi ya shafo hawayen ta, ya sauka daga cinyar Hunainah da gudunsa yayi waje, a hausar shi wai Baban shi zai je ya nunawa Antin tana kuka.

Hidayah ce ta shigo Najib na biye da ita kaman jela, kafin ka ganta sai ka fara ganin tulelen cikin ta sabida girman sa, kafafunta sun kunbura haka ita kanta ta zama katuwa basu san sanda suka fashe da dariya ba. Ta juya cikin shagwaba, hannunta a ido tana kai karar su ga Najib. Ya ce,

“Kyale su honey, shekara mai zuwa duk haka zasu koma suma, gara ke tare zamu yi nakudar mu mu biyu mu haife kayan mu.”

Hunainah ta ce, “Tab! Allah ya nuna mun wannan rana, wallahi bayan taga zai koma ya na leken ki, ki na wayyo Allah Najib, ba ka ce tare zamu yi nakudar ba, ya zaka tafi ka barni ni daya? Tana yi tana gwada irin rike kwankwason da Hidayar zata yi gaba daya suka sa dariya har ita.”

Najib ya ce, “A bar zancen wasa, ke Intisar bakuwa kika yi tana falo, Maman Hunainah ta ce ku je dukkan ku. Kin ga dan ki ko? Ta sukuyar da kai a hankali ta ce, “Eh, Alameen ya girma fiye da yadda na zace shi, kamannun shi da Baban shi har sun yi yawa.”

Ya yi murmushi ya ce, “Kowa haka ya ke cewa.”

Duk sai suka yi shiru dukkansu, babu shakka kowa Alameen din ya tuna. Najib ya bagarar ya dubi Hidayah yace zani cikin gari honey, take kia of yourself, pls, me kike son in taho miki da shi? Ta yamutsa fuska tace kafafunnan sun matsa mun Najib, ko asibitin zamu koma? Ya ce yana karasowa inda take kwance a gafen Hunainah,

“Aah bari in gani, I can deal with them, messaging din su zan cigaba da yi zasu sace yanzun nan.”

Gaba daya ya manta da su Intisar da ke wajen, ya debi kafafun ya aza a cinyar shi yana matsawa sannu a hankali. Cikin matsananciyar kunya suka zame daya bayan daya suka bar masu dakin zuciyar su cike fal da shaawar su, barin Hunainah da a take ta rinka kissima wai inama ita ce da Hashim din ta, ita kuwa Intisar tunanin ta shine Allah ya bata mai son ta kamar yadda Najib ke son Hidayah, har baya iya jurewa a gaban kowa nunawa yake bashi da abu mafi muhimmanci kamarta.

Ta shiga falon da sallama, amma sai tayi turus, a bakin kofar bata karasa ba. Zuciyar ta na harbawa, kafafuwanta suka sage, jikin ta yayi sanyi; Hajiya Nafi ce, a zaune a falon mahaifiyar ta sai Khaleel da ke shan lemun Ribena. Ta juya da niyyar komawa cikin gigicewa amma muryar da ta ji daga can kofar shigowa ta katse gudun jinni a cikin jikin ta, ta warware tunanin ta kaf ta kasa koda motsa kafar ta balle ta idasa yunkurinta na komawa inda ta fito, muryar Faisal.

Ya ce Intisar! Bata amsa ba, amma ta dakata kuma bata juyo ba, shima bai shigo cikin falon ba, daga can bakin kofa yake maganar kamar baya so, da gani don ta zame masa dole ne amma da ba zai yi ba.

Ba kuma tare da ya kalli sashen da take ba ya ce (cikin murya ta girma da bada umarni).

A matsayin Yayan ki, baa matsayin dan ta ba, ina ganin ya dace ki saurareta. Ba lallai ne ki yarda da abinda zata ce da ke ba, amma a kalla tunda gaba take da ke, ta kuma taso gari-ya-gari domin ki, ta kashe muhimmin lokacin ta tazo gareki, duk da kike kasa da ita, ta zo neman wata alfarma a gareki.

Ashe kenan ta san cewa ke wata aba ce mai daraja da zata nemi wani abu daga gareki. Bai dace ki wulakantata ba tunda Manzon Allah (SAW) ya ce bakon ka annabin ka ne. Kuma ko a lahira wani kan ci albarkacin wani.

Da haka ya juya yayi ficewar sa. Ya bar mata permanent (tabbataccen) kamshinsa na (5,000 Doller perfume) da har a mafarkin ta jinsa take yi. Hawayen suka idasa zubowa bisa kundukukinta.

Cikin dauriya da jarumtaka ta juya ta isa gabanta, ta zube guiwoyinta a kasa hawaye na zuba a idon ta tace Hajiya ina wuni?

Ita kanta Hajiyar kuka take yi, haka bata ji dadin kalaman da Faisal yayi amfani da su wajen yi mata magana ba, tamkar ya goranta mata kaunar da suke mata ne, su da suke nema. Ta kai hannu ta dafa kan yarinyar tana share mata hawaye da hannunta, ta kuma sauko daga kujerar da take zaune ta zube gwiwoyinta a gaban Intisar din kamar yadda ta yi, ta ce,

“Ki yafe min don Allah Saratu, ki yafe ni Saratu, bani da kalaman da zan yi amfani da su wajen nuna miki dimbin nadamata kan abinda na yi miki. Abinda zan iya cewa kawai shine kiyi hakuri ki yafe min hakika nayi nadama, na yi nadama mara amfani a kan ki Intisar. Kada ki dubi tsakanin ki da yaya na ko abinda suke miki, wannan hakkin ki ne. Ki dubi girman Allah da manzon sa ki yafe mini. Kuskure ne nayi, nasan kuma babu wanda yake sama da shi. Kiyi hakuri da abinda Faisal ya ce da ke, ban san me ye ke damun sa ba.

Hajiya Hadiza ta shigo, tana tura troller kwandon kayan abinci zuwa dining da ke gefe guda a falon ta ce wane irin abu ne haka Hajiya? Don Allah ki koma ki zauna.

Ta ce, “Aah Hadiza, ki bar ni in roki gafarar Intisar kawai, ko kwanta mata ne sai in yi, in ba haka ba hakkin ta ba zai bar ni kwanciyar kabari ba.

Intisar ta kama hannun ta ta maida ta bisa kijerar ta ce shikenan Hajiya, Allah ya yafe mana gaba daya.”

Shiru ta yi tana mamakin sanyin zuciya irin na yarinyar, tana mamakin kaunar da take wa yayanta. Ta na mamakin hakuri da yakanar ta da daukar alamuran duniya da sauki.

Bata zaci ko a mafarkin ta yarinyar zata taba yafe mata ba. Ta tabbata ko don wannan halayyar tata dole kowa ya sota, dole alumma su kaunace ta, dole ta zamo a bar so ga duk wani da muamala ta hadata da shi koda na second guda ne, hakika a yau ta kara tabbatar wa da cewa da a ke ita din yar baiwa ce.

Ita kuwa Intisar ta yi laakari ne da fadar Ubangiji (SWA) mai cewa hakikah Ubangiji mai afuwa ne, kuma ya na son bayin sa masu afuwa. Bata duba Alameen ko Faisal ba, ta yafe mata saboda Allah. Ta yi tunanin to me ya sameta bayan kiyayyar da ta ke nuna matan? Babu komi sai alheri. Ita ce dai har ta dangana da asibitin masu hankali. Amma ita ai gata da lafiyar ta sumul kalau a gaban iyayen da aka tsaneta don bata da su.

Sun hadu suna cin abinci gaba dayan su har Abban Hunainah, Najib da Hidayah da kuma Khalil da suka zo tare da shi. Hajiya Hadiza tace wai ina Faisal ne a gidannan?

Hajiya tace rabu da shi mutumin banza, na rasa inda ya dauko wannan bakar zuciyar kamar tsohon kuturu, ni wallahi har fargaba nake Jumaar sa ta zo ya zo garin Abuja, ya zama wani masifaffen karfi da yaji, abu kadan su Furkan zasu yi ya rufe su da fada in banda Alameen karami babu wanda ya ke ragamawa a gidannan, ban sani ba ko gamo yayi cikin kabilun nan na Lagos don ba kyau ne da su ba.

Hidayah ta tuntsire da dariya har tana kwarewa, Najib yayi saurin cika ruwa a kofi ya mika mata yace kin gani ko? Hajiya shiyasa baa son magana in ana cin abinci. Baban Hidayah ya dago ya dube shi yayi murmushi ya ce Najib ka na ji da matar nan ta ka, baka san tafi kowa fitina a gidan nan ba. Ka rage rawar kan nan da kake a kan mace, in ba haka ba zata raina ka.

Daga shi har Hidayan sun ji matukar kunya Hajiya ta ce,

“Umh-umh, kyale sa ya kula da matar sa, dubi halin da ta ke ciki fa ai dole a kula da lafiyar ta.”

Hajiya Hadiza da bata san tsamar da ke tsakanin. Faisal da Intisar ba ta dube ta ta ce, “Ke tashi maza ki je waje ki nemo man Faisal, ya zo ya ci abinci.”

Hajiya ta ce, “Ba zai wuce bencinnan na wurin masu gadi ba, ki ce da shi ya zo ina kira yanzun nan.”

Sai da kirjinta ya harba kamar ta ce wayyo Allah! Ta mike talau! Juwa ta kwasheta saura kadan ta kai kas, Hunainah ta tallafe ta tace yi a hankali, kujerar nan zata tade ki Najib ya dago ya dubesu yayi murmushi kawai ya dauke ido a kan su.

Ta fita cikin kasala da rashin kuzari amma sai ta labe a hanyar zuwa wajen bata je din ba, a ranta cewa take lallai ma ya Faisal! Har yau bai gama sani na ba, ba dai ni ce baya son gani ba, ni mujiyar sa ajalin sa to nima bana son ganin sa ko hanyar daya bi nima na daina bi. Hawayan da basa wuya a idanunta suka zubo.

Ta sa gefen rigar ta ta share ta dawo falon ta zauna a mazaunin ta tace yace ya na zuwa. Shiru shiru babu shi babu alamar sa har suka kare cin abincin. 

Abinda kunnuwanta suke jiyo mata Hajiya na baiwa mamarta labari ta kasa gasgata shi, hakan nan ta kasa amincewa da abinda ta ke jin. Wai Faisal ya kawo wa Baban shi mata Bayarabiya kuma bazawara mai yaya uku da suke aiki tare a NNPC wai ita Ronke yace nan duniya ita ya ke so, su kuma sun ce wannan auren sai bayan ran su.

Hajiya Hadiza ta yi dariya ta ce,

“Ina ruwan kurucci dangin hauka. Kin san idan Allah yayi ma wata baiwa baka gani, sai dai wani ya gane maka. Amma ina mutum kaman Faisal ina auren bayerabiya?”

Najib ya ce, “To yaya zai yi Hajiya? Wadda ya ke so bata son shi, ba sai ya je inda ake son shi ba?” Ya fada ne kamar da biyu, idanun shi a kan Intisar, wadda cikin sanyin jiki ta aje cokalin da ke hannunta ta tashi ta yi dakin su da ke saman bene.

Ta sa mukulli ta rufe kofa ta tafi gaban taga ta tsaya kawai, hannayenta sarke a bayanta, wasu irin zafafan hawaye suka zubo a kumatun ta. Kamar an ce da ita juya nan; ta kalli harabar gidan ta tagar.

Daga can ta hango shi cikin motar sa porsche kafarsa daya a motar daya a waje, sanye cikin lallausar shadda yar Indonesia ruwan kasa-kasa dinkin Tazarce, fatar agogon roled da ke hannunshi ma ruwan kasa  kasar ce haka takalmin fata na kasar Italy dake kafarsa ruwan kasa ne mai duhu. Ya rame ainun hakannan kyawawan idanunshi masu narkar da zuciyar ta sunyi ciki sosai ya kara fari, haka lallausan fatar shi ta kara gogewa sosai fiye da sanin da ta yi masa a baya.

Waya ce yake amsawa cikin lumshe ido, da gani zaka san kalaman da a ke gaya mai cikin wayar ba karamin dadi su ke mai ba, don har kwantar da kujerar motar yayi da alama dai cikin matsanancin nishadi yake. Zuciyar ta ce ta shiga harbawa da sauri da sauri don tuni ta fassarawa kanta koda wa yake maganar kawai Ronke Adeyemi.

Ta ja murfin tagar da karfi ta rufe garam, tare da zuge labulen gaba daya, ta durkushe a nan ta yi kukan ta mai isar ta. Ta tabbata a yanzun kam Faisal ya daina son ta! Duk wani so, duk wata kauna daya ke mata ya zagwanye sakamakon rashin maida mishi martanin dimbin soyyayar da ya shekara yi mata.

Ronke yake so tun-tuni har yanzu kuma bai daina ba, har ta zama bazawara uwar yaya uku still ya na son kayar sa. Ita kuma haka Allah ya so da rayuwar ta? Ba zata taba cin riba a soyayya ba. Allah Sarki!

Wai yau ita Intisar ce Faisal ya ke neman maraba da ita. Ita din da a da, baya da abin so da gani tamkar ta. Ita din da a da, in bai gani ba baya iya nutsuwa amma a yau rashin ganin ta shine nutsuwar sa, kwanciyar hankalin sa kuma abinda yake matukar so.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.6 / 5. Rating: 17

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siradin Rayuwa 41Siradin Rayuwa 43 >>

5 thoughts on “Siradin Rayuwa 42”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×