Skip to content
Part 8 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir Takori

1 Rabi Al-Thani

Wata biyu bayan dawowarsa

Al’ameen da Halimar shi (Kamar yadda ya nace da kiranta) sai aka soma shimfida ingantacciyar soyayya mai ban mamaki da ban sha’awa. Barin yanzu da ba su da shamaki, Hajiya kishi ya kore ta don har kwanaki suka shura tana Dubai ta ki dawowa. Su Khalil tun safe in sun tafi makaranta sai karfe shida na yamma suke dawowa don haka ba su ma san me Al’ameen ke yi a gidan ba, kai ko a mafarkin su ba su kawo ya ma san hanyar kitchen din gidan ba, to ya je ya yi me?

Ita kuwa Dela tsoron shi take, da ta gan shi za ta soma bare-baren jiki ta gaishe shi ta wuce ta bar su. Tana kakabin abin a zuciyarta ita kadai amma ba ta ce da yarinyar komai ba.

To ta ce mata me? Me ke tsakanin ki da Aminu ko me? Ta gaya masa ya ce tasa mai ido a yi mata asarar abincin ta yadda duniyar nan ta zama uhm-uhm, ba ruwanta su karata. Daga ita har Al’amin sun dauka da ba son juna suke ba, sai yanzun. Tun tana jin kunyar sa har ta gaji ta bari, domin ban dariya irin na Al’amin Allah ya yi yawa da shi.

So, shakuwa da yarda da junansu su ne muhimman tubalan da suka gina soyayyar su a kai. Haka amincewa da junan su kullum sai kara karfi yake a zuciyar kowannensu. Ji suke, daya bai iya rayuwa ba tare da dan uwansa ba.

Ba ta san me ye so ba a rayuwar ta amman Al’ameen ya koyar da ita wata irin soyayya mai shiga rai a lokaci daya, ya koyar da ita yadda za ta so shi, ta kaunace shi shi kadai a zuciyarta. Ba ta taba jin son wani da namiji a duniya irin yadda take ji yanzun a kan Ala’meen ba. To haka shi ma, tuni ya mance da Ihsan kwata-kwata a babin rayuwar shi watakila ta zama tarihi. Wadda a lokacin ta rasa nutsuwa kwata-kwata na rashin sanin makomar ta; ‘yar rakiya? Ko matar Al’ameen?

Ita kam da ta san cin amanar da kasar haihuwar ta abin tunkahon ta, Nigeria, za ta yi mata kenan da tun farko ba ta takura su dawo ba. Haka Ann ta ce da ita muddin ta name shi bai kawo kansa ba ta bar ta da Jesus ya bi mata hakkinta na haifar ta da ta yi da wahalar da ta yi ta yi da ita.

Ya tabbatar mata da amaryar Daddy ta tare zai kai masa bukatar su, kasancewar sa gwarzon uba, mai son duk abin da ‘ya’yan shi ke so ko da shi ba ya so in har bai sabawa tarbiyya da Addini ba, ya tabbata ba za a samu wani mushkila daga gare shi ba, sai dai ko daga gare ta, don ya lura son shi take amman auren baya gaban ta sam.

Duk lokacin da ya yi zancen aure ya kan lura ta shiga wani zuzzurfan tunani, sai ya ta’allaka hakan da tunanin mahaifiyar ta da ta ce ta rabu da ita tun tana karama ba ta san inda take ba.

A irin wadannan lokutan ya kan gaya mata zai zamo mata Uwa…, zai zamo Uba a gare ta. ‘Yan uwan shi za su maye mata gurbin nata ‘yan uwan, su nuna mata kauna ta jini da bata samu ba a rayuwar ta. Zai zamo mata miji kuma aboki, zai zama komai nata, zai kauna ce ta muddin ransa…, zai nesanta ta da Hajiyar da ke kin ta…, zai bude mata duk wasu kofofin farin ciki da dan adam ke burin samu!

Ta kasance cike da tunanin wa Daddy zai aura? Ta je daki ta kwanta a dandaryar kasa ta yi ta kuka. Ta tabbata ta rabu da mahaifiyarta kenan har abada! To amma kauna da kulawa irin wanda Al’ameen ke nuna mata, wani abu ne dake rage bakin ciki da takaicin da zuciyar ta ke ciki.

Ta kan tambayi kan ta yaushe ne wannan daukin da Najib ya kwadaitar da ita zai zo ne? Ko ko Al’ameen ne? Shi yasa ya dage su yi aure? Allah Sarki! Tana matukar tausaya masa, bata taba ganin mai son ta bayan Faisal, irin Al’ameen ba, ai ko ita shegiya ce ya kyautu ta aure shi hakan nan. To amma a matsayin da take kai a yanzu wa zai mata auren?

*****

12 Jumada Akhir (Hijriyya)

Rana Mai Dimbin Tarihi A Gare Ta

Faisal Bello Makarfi ne ke saukowa daga jirgin MEA International, ranar sha biyu ga watan Jumada-Akhir. Gaba daya Engineer Faisal B. ya canza tamkar ba shi ba, yana sanye cikin bakaken suit ya kuma daura thick coat saboda matsanancin sanyin da ake tsugawa, bakin takalmi sau ciki ne a kafarsa kirar Italy, hannun shi na hagu daure da agogon Rado yayin da na daman ke rataye da matsakaiciyar jaka irin wadda matafiya kan zuba passort da sauran kayan amfani na gaggawa.

Bai fara tozali da kowa ba sai Ya Ameenu da rabonsa da shi shekaru goma sha biyar. Ya karasa da gudu suka rungume juna suna juyi kafin su soma hawaye. Abubuwa da dama sun faru, na farin ciki da na bakin ciki, na bakin cikin shi ya fi yawa.

Bai taba zaton zai kara ganin Al’ameen ba a rayuwar shi, har suka iso gida kuka suke wiwi. Ya rasa mai yasa bai kullaci Aminu ba? Amsar shi ne don yana son shi, ko a cikin ‘yan uwansa Aminu daban ne. Kuma tunda har Daddy ya yafe masa shi a kan me ba zai yafe masa ba?

Bai fara tambayar kowa ba sai Inteesar dinsa, Aminu ya ce, “An ce tana makaranta amma daman kwanan nan za mu kai mata ziyara tunda ga ka ma ka dawo shi kenan.”

Ya yi shiru cikin tunani, shekarun da suka gabata suna da yawa, ya ci a ce yanzu ta yi nisa a jami’a in har lissafin da yake daidai ne. To ko a jami’ar take? Ya so kwarai ya tambayi Al’ameen sai ya share, ko da can Al’ameen na shiri da Intisar ne balle yanzun? Ya sauke shi a kofar gidansu ya juya ya tafi gidansa don yana da abin da zai yi da yawa.

Haka kuma a ranar ne motar Daddy ta sauke Aunty Saratu, Zarah, Goggo Jumami da aminiyar ta Jami a harabar gidan, sabanin da su kai da motar Al’ameen na mintuna uku ne kacal, Aunty Saratu again a matsayin matar Daddy Makarfi.

Ta kara kiba, ta kuma yi haske sosai na samun hutu da kwanciyar hankali. Baben ta Zarah na kwance a kafadun Jami tana barci suka shiga sabon sashin Aunty Saratun wanda da farko sun dauka ba a Nigeria suke ba, babu abin da Daddy bai zuba mata ba na jin dadin rayuwar duniya irin abin nan dai da ake kira Aljannar Duniya.

Dakin Inteesar kadai abin kallo ne don a naira miliyan biyu cif Daddy ya sa kamfanin edcel interior decoration suka yi wa Intisar da yake tsammanin tana makarantarsu a Riyadh.

Tun kafin ta zauna ta ke kwalawa Intisar kira tun karfin ta, sai Khalil ya shigo yana toshe kunnensa haka su Goggo suna

“Kar ki lahanta mana dodon kunne.”

Khalil ya ce, ‘Anty ki yi hakuri, ba jiyo ki za ta yi ba, don tana can sassan ‘yan aiki, bari in je in dauko miki ita kawai aka, don in na ce ta zo ko kallo na ba za ta yi ba.”

Hawaye suka fitowa Saratu sharr! Wai Saratun ta ce a sassan ‘yan aiki? Ta daura hannuwa aka ta fasa kururuwa ta ce,

“Amma Allah ya isa tsakanina da ke Haj. Nafi.”

Da haka ta kwasa da gudu babu ko dankwali tuni ya yi nasa waje, ta bi hanyar da zai sada ta da sashin ‘yan aikin. Khalil na bin ta yana kira shi ma kukan yake, a daidai lokacin da Faisal shi ma ya fito daga cikin gidan bangaren Hajiyarsu ko jakar hannunsa bai aje ba saboda kururuwar da ya ji ta gigita shi na muryar da ya tabbatar Antinsu ne, ganin Antin tana gudu babu ko mayafi bai san san da ya yar da jakar hannunsa ba ya rufa mata baya, yana

“Aunty Saratu ki tsaya!” Ta ce,

‘In tsaya, uwarku ta karasa kashe min ‘yar? Ban san me Saratu ta tsarewa Hajiyarku ba haka Faisal, wannan karon ba zan taba amincewa ba!”

Bata kuma tsaya da gudun da take ba, hakan nan hawayen ta ba su bar ambaliya ba.

Tana tsaye tana farke buhun semovita don zubawa cikin ruwan zafi tafasashshe, Aunty Saratu ta rungumeta ta baya, yayin da hawayen ta da ke ta kwarara suka dinga sauka a kirjin Inteesar! A fusace ta juyo, a zaton ta Al’ameen ne ta ce,

‘What a nuisance, Aminu?”

To amma sai ta ga mamarta, da ko a mafarki ba ta zaci sake gani nan kusa ba. Idanuwanta suka bubbude gaba daya tamkar sa fado. Ta kai hannu ta shiga tattaba ta a gigice ta dai tabbatar ita din ce hanci, ido, baki fuska, babu abinda ya canza a jikinta. Ta bude baki kamar mai son yin magana amma sautin ya kakare ya ki fitowa sai dai labban ta da ke motsi yanayin motsin na nufin, “Mamana?”

Aunty Saratu ta janyo ta ta rungume tsan-tsan a kirjin ta cikin yanayin fita hayyaci ta soma cewa.

‘Saratu? Haka Nafi ta maida ke? Allah ya isa tsakanina da Hajiya Nafi, ba zan taba yafe mata ba haka duk jinin ta, in Allah ya yarda sai ya ga tozarci a rayuwa…”

Faisal ya yi saurin toshe kunnensa yayin da gaba daya suka rikice da kuka. Yana ji yana gani ana bin su da mugun al’kaba’i, a kan laifin da ba nasu ba, a kan abin da bai shafe su ba, a kan abin da in da yana nan… ba zai taba faruwa ba!

Yasa hannu ya matso kwallar da ta tarar masa a kwarmin ido, kafin ya ankara tuni sun fice daga kicin din, ya mara masu baya tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki. zuciyarsa cike fal da nadamar zuwa Najeriya.

Shin me ya yi zafi haka? Me Hajiyarsa ta yi wa Intisar din sa haka da zafi? Ya san Aunty Saratu mace ce mai dumbin hakuri, tabbas yau an kure ta an kuma kawo ta bango, tunda har ta kai ga furta wannan kalami.

A babban falon Anty Saratu kuka diyar ta Saratu ma kuka, maimakon farin ciki. Tun suna ba Goggo Jummai tausayi har suka koma ba ta haushi ta mike ta na gyara daurin zanin ta tace,

“Jami, na fasa kwanan gidan nan, tunda Saratu da Saratu ba su san yarda da hukuncin Allah ba.”

Jami ma ta ce, “Kya fada dai Hajiya Jummai, kuma tunda komai ma ya zama tarihi, ni ban ga amfanin zubda hawayen ba. Dubi irin wannan duniya da Bello ya shirya masu amma duk ba su gode Allah.”

Intisar ta rike hannun Goggonta ta ce,

“Ki yi hakuri Goggo don Allah, daga yau ba za mu sake kukan nan ba, ban taba zaton Mama za ta dawo ba ne, ko a mafarki.” Ta share hawayenta.

Goggo Jummai ta shafi kanta suka koma suka zauna tana kara yi masu nasiha kan muhimmancin yarda da kaddara mai dadi ce ko mara dadi.

A yau kam Antin da diyar ta kwanan bakin ciki da farin ciki suka yi a zaune, in suka ce idanun su sun runtsa ko na sakan daya to sun yi karya, kowanne na bai wa dan uwan shi labarin bayan rabo. Intisar rungume take da kanwar ta Zarah da ba ta san an haifa ba, tamkar ta tsaga kirjin ta ta sanya ta don so da kauna.

Amma sam yarinyar nan ba ta gayawa mahaifiyar ta irin azabobin da Hajiya ta rika gana mata ba ta dai ce ita ke yin girkin gidan kawai, wannan ya dan sanyaya ran Antin.

Daddy ya je meeting Lagos sai a washe gari zai dawo, duk da haka ya yi wa Antin waya ya ji yadda suka iso ta ce sun iso lafiya cikin alkhairi, ya ce idan ya iso a goben sati mai zuwa za su tafi Riyadh su dubo Saratu karama.

Ta ce, “Wace Saratun kuma ban da wannan da muke a kwance tare?’

Daddy ya yi shiru cikin dogon tunani, can ya ce, ‘Aminu ya ce da ni Saratu na Riyadh?”

Ta kara tabbatar da abinda Mal. Sidi ya ce da ita, na cewa Daddyn baya cikin hayyacinsa a duk tsayin lokacin sai ta ce,

‘Shi Aminu ba bako ba ne? Yaushe har ya yi zaman da zai san me ke faruwa cikin gidan?”

Ya ce shi kenan tunda ga Al’ameen a gida, ya kamata a sake mata glasses a kirawo masa ita.

Ita dai a tsorace ta gaishe shi, amma wai sai yake ce da ita wato tun tuni ta zo hutun ‘yar boye take yi mai a gidan ko? To ta yi asarar tsarabar da ya yi niyyar kawo mata…” ta jingina da bango, hawaye na karshe na zubar mata ta ce,

“Ni dama na san wancan mutumin is not my real Dad (Ba shi ne babana na hakika ba), ban kuma taba kullatar Daddy na ba, even once (ko da sau daya).

A kullum ina yi masa uzri, gare ni duk yadda rayuwa ta zo… a karbeta…, ayi mata uzuri da abubuwa guda biyu; Faisal da Daddy Makarfi.”

Aunty Saratu na share mata hawayen da hannunta ta ce,

‘Kin ga Faisal ya dawo?”

Ji ta yi tamkar an kwara mata ruwan kankara, ta zaro ido ta ce,

“Haba don Allah! Allah Sarki Brother!! Wallahi ban gan shi ba sam.’

Antin ta ce,

“Ni dazu da na kusa haukacewa saboda bakin cikin uwar su ko kulasa ma na yi?”

Ta ce, “Ayya Mamar mu! Ina laifin Hajiya zai taba shafar Ya Faisal, ina!”

Sai wasu hawayen sharrr!

Ta ce (cikin rarraunar murya),

“Ni don farin cikin dawowarku ma ke da Ya Faisal, domin Faisal, na yafewa Hajiya har cikin raina.”

Sai Antin ta bi ta da kallo, zuciyar ta cike da mamakin sanyin zuciya irin na yarinyar, bata daukan al’amuran duniya da zafi, ba ta da daukar kunci ko kadan, yanzu ne za a yi mata abu yanzun ne za ta manta tun tana mitsitsiyar ta. Amma ba ta manta alkhairin da mutum ya yi mata ko yaya yake. Saidai ta manta batancinsa gareta.

Tana mamakin irin kaunar da take musu, tana mamakin irin kaunar da take wa Daddyn ta da ‘yan uwanta maza… ina ma a ce wannan shi ne bakin cikin yarinyar na karshe a rayuwa?

Wannan tunanin ya kara mata kauna da tausayin yarinyar, ya kuma dugunzumar da zuciyar ta duk a lokaci daya, ta yadda duk wani farin ciki da ta zo da shi sai ya dushe zuciyarta ta koma bakikkirin. Ta roki Allah kada ya nuna mata ranar da Saratu-Intisar za ta fahimci…

Me za ta fahimta?

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.8 / 5. Rating: 16

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siradin Rayuwa 7Siradin Rayuwa 9 >>

5 thoughts on “Siradin Rayuwa 8”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×