Skip to content
Part 1 of 9 in the Series Soyayyar Da Na Yi by Habiba Maina

Ina cikin tafiya gefe na kuwa kwalta ce amma hankali na gida domin na gaji ina sauri in isa gida in huta. Ina cikin tafiya sai naga mai kayan marmari a sa’inda idanuna suka sauka akan ayaba. Kaf cikin kayan marmari ba wacce na fi so kamar ta, haka yasa naji ina sha’awar ta ai kuwa ban ɓata lokaci ba sai na isa wajen mai kayan marmarin nayi mishi sallama ya amsa nace ina son ayaba na tambayi kudinsa ya faɗa min. Jin kuɗin ayabannan ya bani mamaki domin ba yarda na saba saya bane gashi kuɗin da ke ja’kata bata kai ba nayi tayi iya kuɗi na amma sai yaki sayar min na haƙiƙance harda magiya amma mai kayan marmarin nan haka ya rufe idanunsa.

Raina ya matukar ɓaci cikin fushi na so in firta masa mara daɗi amma sai zuciya ta ta dakatar da ni tace da ni ‘In banda rigimarki ki sayi wani abun mana koh kin’manta iya kuɗin da ke jakar ki kenan toh idan kika saya da mai zaki hau motar zuwa gida?” Ina cikin wannan tunanin sai naji horn karar Mota a Baya na amma ƙarar bata sa na juya ba Ni dai hankali na na kan siyan ayaba ban ankara ba sai na ji tashin turare mai kamshi da ya bigi hanci na amma kamshin turarennan bai sa na juya ba na tsaya nayi jugum kamar gunki sai Muryar mai kayan marmari naji kamar a mafarki na sauka cikin kunnuwa na yana cewa, “Malama koh ciki neh da ke bazan siyar miki haka ba don Allah ki matsa min gaban kayan sana’a.” Jin haka yasa na sake tunzura zan tanka “Sai na ji ance Malam ka saka mata na dubu biyu amma kafinnan ka bata hakurin wulakanta ta da ka yi.”

Na mintuna biyar cikin sauri na juya sai wani sankaɗeɗen saurayi na gani mai matsakaicin jiki da idanuwa dara-dara muryarsa mai ratsa zuciya nayi mamakin ganin saurayinnan domin da macece shi muna kama sai nace a zuciya ta wannan saurayin kamar ɗan uwa na, na jini amma duk da haka bai sa na tanka masa ba ganin ni budurwa ce da na datse soyayya a tsakiyar rayuwa ta, Sai na ce da shi “waye kai? Kuma mai yasa ka saya min abunda ban roƙe ka ba?”

Sai ya ce da “Ni tun akan gada na hango ki sai zuciya ta ta umurce ni da in biki haka yasa na biyo ki. Amma sai ki ka ɓace min da gani cikin ikon Allah kuwa sai zuciya ta ta zaɓa min hanyar shigar da na bi kuwa sai na hango ki tun a nesa naga yarda kukayi. Shiyasa na matso na kawo karshen tsiwar.” Sai nace masa “Na gode amma ka riƙe kayan ka duk son da nake wa ayaba amma yanzu ta fita a raina.”

Jin haka daga gare ni ya bashi mamaki har ya manta cewa yau ne ranar da muka fara ganin juna sai ya tambaye Ni cikin mamaki ke ma’abociyar cin ayaba ce? Sai nace o’ho! Cikin fushi sai na yi gaba ina cikin tafiya sai na iso wata unguwa mai girma kuma mai tarun gidajen yan siyasa an ƙawata gidajen nan tamkar a turai kai kace bada Yashin garinnan aka yi ba kallo ɗaya nayi Wa gidajennan na sunkuyar da kai na Ni dai buri na in isa tashar mota ina cikin tafiya na shanyo wata layi sai nayi ciɓis da saurayinnan. Na firgita na so na ruɗe amma sai na jure na basar kar tsoratar da nayi ta bayyana shi kuma ya rainani sai na ci gaba da tafiya ta sai saurayinnan ya sauko a bayan motar sa ya tare ni yace da ni,

“Mai yasa ɗan adam akoda yaushe idan ya hau sallaya sai ya ɗaga hannu ya roki Allah ya buɗa mishi, ya ɗaukaka shi sannan kuma ya bashi abokin rayuwa na gari amma idan Allah ya bashi sai ya ki shin kina ganin za’a sake bashi kenan?”

Maganar sa ta ratsa ni amma sai dai ba yau na fara jin romon bakan samari ba mai sirkin guba saima na sake tunzurowa na kalle shi har cikin idanun shi nace a’a baza a sake bashi ba amma idan na kasance daga ciki, zanzo ka roka min sai a bani sai naga yayi dariya a wayence mai salon murmushi sai yace gaskiya naji dadi koh haka ya nuna min cewa zamu sake haduwa budan baki na sai nace Allah ya sawake in sake haduwa da kai?, A mai kenan? Hmm ciwon kai! Na yunkura zan tafi sai ya sake tare Ni yace ga mota ta muje in kaiki karki Sha wahala sai na juya cikin kallon sanarwa nace “Da kai ka kawo ni nan koh kai ka fito da ni a gida? Da ka magance min wahalar farko sai ka magance min wannan amma indai ba haka ba, ka riƙe kayar ka.”

Na yi gaba cikin sauri don na hango mai taxi da babu fasinja Amma ina kiransa baya ji na. kan in ankara ma yayi nisa rai na ya matukar ɓaci ina faɗin ba’ga irinta ba duk yunkurin da nayi na kauce masa sai da yasa nayi asarar motar hawa sai kace abun arziki zai bani na dakata da faɗin haka sai nace kai yaufa nayi jarumta a zuciya ta “wai nice nake haɗa idanu da saurayi na kai minti biyar ina magana a zuciya ta tare dabin hanyar da taxinnan yabi da idanu nace nmm gwara dai kiyi gaba kar ɗan anacinnan ya sake biyo ki sai na kara gaba ban wuce minti biyar ba sai gani a dap matsayar motar unguwar sai nayi ajiyar zuciya tare da godewa Allah Alhamdulillah tare sai na hango wani mai taxi sai na isa gare shi sai nace da shi sannu yace yauwa sannu sai na ce Abuja zaka sai yace a’a ba nan zai je ba sai na matsa wurin wani magidanci nace sannu baba yace yauwa sannu ya’ta nace Abuja zaka je shima yace ba nan zai je ba haka na kara gaba na tarar da wani saurayi na cewa Abuja zaije sai mai taxinnan ya dauke shi amma da naje kusa nace Abuja zanje sai mai taxinnan yace ba nan zai je ba duk sai suka ƙi ɗauka na kowa sai kallo na yake a tashar nan. a wannan, yanayin kuwa.sai nashiga ruɗani toh maiyasa kowa baya so ya ɗauke ni shin ko dai akwai wani abu a jiki nane? anya kuwa babu wata aljana da take canza min kama? kai a’a ai toh da dariya jama’a zasu ke min haka nayi ta faɗa a zuciya ta ina ta waige-waige haka na fice a tashar na hau kan hanya ina tafiya banyi nisa ba sai naji horn din Mota da ya tsoratar da ni matuka ganin ya shige gabana kamar zan haɗu da shi na ci briki kamar mota kara ganin Wannan saurayin yasa nakasa cewa komai a bayyane a zuciya ta kuwa nace innalillahi wa inna’illaihirraju’un wai mai zanyi wa gayennan ne mai gayennan yake nema a guri na? Sai ya sauko a motar sa yace nasan ranki ya ɓaci koh? Toh ina neman afuwa banyi miki haka don tozarta wa ba wallahi ina da burin taimakonki ne wannan karon ganin kin rasa motar hawa yasa na biyo ki in sake yi miki tayi koh zaki dubi hakan da idanun basira da jin maganar sa sai zacyata yace min ki amince kawai ya kai ki ki huta amma sai ɗayar zuciyar tace min a’a ta yaya zanyi saurin karaya da hukuncin da na yankewa kai na yanzu saboda ya jajirce ne zanyi saurin yarda da shi nawa ma sukayi irin muna fircin sa.

Wai nan kai mutumin kirki ne? Kana kokarinda ba zai taimke ba ni ban gaji ba balle in huta aha kai kaje ka huta kuma gargaɗi na karshe karka sake min magana,kar ka sake tinƙarata da magana ina fatan ka jini da kyau wallahi sai wani mutum ya dakatar da rantsuwa ta wanda ban san ko wa nene ba sannan banga ta inda ya taso ba haka kuwa shigar sa ta tsoratar da ni yana sanye da farar riga wacce ban taɓa ganin farin ta ba yana da suma matuka ita ma sumar fara sol kamar rigar sa sannan Muryar sa mai kakkarwa yace da Ni

Idan kika boye abunda ke ranki toh ki sani Allah yana gani, idan kika hana zuciyar ki abunda take so toh ki sani za ayi miki hisabi da zuciyar ki idan kika yanke wa kanki hukumcin da Allah bai yanke miki ba toh ki sani kin cuci kanki kuma hakan bazai biya miki bukata ba cikin tsoro zan tambayi tsohonnan waye shi sai muka ji ƙara tamkar ƙararrawa da ake samu a gidan tarihi na zamanin da irin ta larabawa bama ta Africa ba muka juya da sauri domin ganin mai nene sai muka ga ashe bakanake ne ya ɗebo kayan gyaran sa suka zube masa amma duk da haka bai sa zuciyata ta yarda da karannan mai karfi ta kayan bakanaken ba ne domin Wannan karar ta ƙararrawa ce ta zamanin baya. Juyawar mu ke da wuya bayan tunawa da nayi da tsohonnan da ke kusa da mu sai muka taradda babu wannan tsohon cikin mamaki nace ha’ah ina wannan tsohon sai saurayinnan yace da Ni kin san a neh?sai nace a’a sai yace toh tayu wannan saƙon ki ne sai kiyi wa kanki hisabi amma hakan bai shafe Ni ba komai na zuciyar ki sai abunda kika yanke. A nawa ɓangaren kuwa har yanzu ina kan baka na kizo muje in kaiki gida nan take na sake saka idanu na a idanun sa nace a zuciya ta a’a sai na tuna da maganar tsohonnan kar in kauce wa maganar sa in Shiga da na sani toh amma idan bakin su ɗaya ne fa? Toh idan bakinsa ba ɗaya bane mai yakawo tsohonnan cikin al’amarin amma kuma cewa yayi taimako na zaiyi ba sona yake ba kuma a wannan zamanin da taimako ake cutar mutane. Anya wa’ƴannan ba masu satan’mutane bane kuwa? Ina kallon sa acikin idanun sa ina faɗin haka a zuciya ta. Na ƙasa cewa eh na ƙasa cewa a’a.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Soyayyar Da Na Yi 2 >>

2 thoughts on “Soyayyar Da Na Yi 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.