Skip to content
Part 1 of 5 in the Series Ta Ki Aure by Ummu Adam

Bismillahir Rahmanir Rahim

Ina mai miƙa godiya ga Allah subahanahu wata’ala mai kowa mai komai wanda ya bani ikon yin wannan rubutu mai albarka in sha Allahu. Salati marar adadi ga annabi Muhammad SAW da alayansa da sahabbansa da matansa baki ɗaya.

*****

Mahaifiyar Sawwama da Kawwama na zaune a ɗaki ta zuba tagumi kai kace saƙon mutuwa aka faɗa mata, malam iro ya yi ta sallama amma ko gizau bata yi ba hakan ya tabbatar masa ta yi nisa cikin tinani. Wai haryanzu bazaki cire damuwa a ranki ba gameda auren yarannan sai kace kice uwa ta farko da yaranta suka kasa auruwa?

Dogon numfashi mama ta ja tareda sauƙe hannunta ƙasa tace malam kenan ai “ruwan da ya dakeka shine ruwa” ko da ace bani kaɗai bace amma nawa na sani, wannan shekaran Sawwama zata cika shekara talatin da biyar ita kuma Kwawwama zata cika shekara talatin da biyu amma ace haryanzu suna gida basu yi aure ba! Duk inda na shiga sai an nuna mun yatsa ana gata can yaranta sunƙi aure. Malam ya kaɗa kai yace wannan gaskiya ne dan ko ni sai kinga irin kallon da ake mun a waje wai har cemun suke ko ni zan auri yaran oho.

Haka iyayen Sawwama da Kawwama suka ci gaba da tattaunawa akan babbar matsalar da take damunsu na rashin auran yaransu da wuri.

A gefe guda kuma Sawwama da Kawwama na zaune a ɗaki suma suna tattaunawa akan al’amarin da iyayensu ke magana akanta inda Kawwama ke cewa abunda ake mata na tsangwama a cikin dangi da ƙawaye yana damunta “yaya Sawwama har kunyan shiga taron biki ko suna na keyi saboda sai kiga yara ƙanana suna mun kallon raini dan kawai sunyi aure wasu ma sun haihu ko hira ake na haihuwa da na sa baki sai kiji suna cemun inbar wanda suka sani suyi magana, cikin sanyin murya Sawwama tace bai kamata ki ɗaga hankalin ki ba my sister ai kowa ya san aure da arziki lokaci ne idan Allah ya kawo lokacin ba mai hanawa dan haka ki kwantar da hankalinki muyi ta addu’a Allah ubangiji ya bamu mazaje na nagari ƙawwama tace amin amma dai ni kawai so nake ace nayi auran nan kowa ya huta, Sawwama tace a’a ki dai yi aure dan ki huta ba dan kowa ya huta ba, Kawwama tace hmn big sis bazaki gane ba na matsu nayi aure Allah dai ya kawo wanda za’ayi da shi.

Bayan kamar wata ɗaya sai Kawwama ta samu miji mai suna jalil wanda ake kira da matashi da kuɗi abokin tafiyar manya. Cikin mako uku akai maganar aure kuma aka ɗaura aka kai amarya gidanta. Sawwama bata so auren ya kasance cikin gaggawa haka ba saboda ba a yi bincike ba bare a san halaye da ɗabi’un shi amma ba yanda ta iya kasancewar Kawwama tana san shi kuma iyaye da dangi duk sunyi na’am da al’amarin musamman ma dayake abun naima ne ya samu. Anyi biki na gani na faɗa mako guda ana shagalin bikin kamar baza’a gama ba sai dai duk events ɗin da akai Sawwama bataje ba tace kar mala’iku su sa sunanta a cikin list ɗin masu zuwa party, abunda tayi ya ƙara jawo mata baƙin jini a gurin mutane harma ake ta faɗan cewa hassada ce take yiwa ƙanwarta.

A kwana a tashi ba wuya ƙawwama tayi watanni biyar a ɗakin mijinta, jalil ya kasance mutum ne mai hidima da yin alkairi ga iyayen matarsa hasalima kowa na musu murnar samun siriki kamarsa sannan kirkinsa da fara’arsa yasa kowa a dangi na ganin girmansa to amma shin hakan ya ke a gidansa kuwa?

Da sanyin safiya Sawwama ta jiyo kishiyar mamanta na habaici tana cewa taƙi aure ta zaɓi zaman gida sa’anninta na can gidan miji ana kiransu mama da inna.” Ko damuwa bata yi ba dan ta saba jin irin wannan kalaman.

Lokaci bayan lokaci Sawwama takan kai ziyara gurin ƙanwata Kawwama dan sada zumunci, wata rana ta je sai ta sameta tana kuka tana waƙe mai nuna tsananin damuwa da baƙin ciki “subahanallahi my dear mai ya faru, rasuwa akai ne? Sawwama ta faɗa cikin damuwa” Kawwama tanajin muryar yayatta ta miƙe da sauri ta rungumeta tana kuka tana faɗin na shiga uku yaya na yiwa kaina mugun zaɓe kaicona na ƙi jin maganarki na gujewa bincike kafin aure yanzu gashi ina cikin matsala.

Sawwama ta riƙe ƙanwarta suka zauna bakin gado tace faɗamun mai ya faru kike faɗan munanan kalamai haka? da ƙyar ta numfasa sannan tace tinda mukai aure da jalil bamu taɓa kwana tare ba yau tsawon wata takwas kenan amma kowa rayuwarsa ya ke yi ko hira bama zama muyi wata rana sai muyi kwana biyu bamu haɗu ba saboda ina bacci zai fita kuma ina bacci zai dawo sannan duk abunda nace ina da buƙata sai yace na faɗawa amir zaman kaɗaici na neman ya kasheni a gidannan. Sannan kuma kwanaki na faɗawa mama amma tace karma na bari aji maganar kar mutuncinsa ya zube tinda ban rasa komaiba kawai nayi haƙuri haka nayi shiru amma yanzu wata sabuwar matsala ce ke neman faruwa da ni wacce tafi wanda nake ciki na rasa ya zanyi ji nake kamar ina rayuwa a wata duniyar da babau kowa sai ni!

Sawwama tace na fahimceki Kawwama haƙiƙa kina cikin jarrabawan da ban taɓa zato ba to amma mene sabon abunda ke fatuwa da ke? Ƙawwama tace na kamu da soyayyar amir…. A tsorace sawwama tace “meyeee!

A garin yaya my dear ya akai ki kai wannan gangnancin kamuwa da soyayyar ƙanin mijinki???

Nimafa mutum ce yaya kuma zuciyar dake jikina irin ta mutane ce. me ki ke tsammanin zai faru da ni alhalilin ina cikin wannan halin, amir shi yake tayani hira, shi yake kai ni duk in da zanje, shi yake koya mun karatun computer a gida bansan ya akai ba naji na kamu da sansa…

Sawwama tace inna lillahi wa inna ilaihi raji’un tabbas kinyi kuskure ƙanwata amir ba muharraminki bane sannan kuma bai halatta ki samu kusanci da shi har haka ba musamman ma da yake kina cikin irin wannan matsalan to amma abunda ya kamata shine zanje na faɗawa kawu abunda ke faruwa tsakaninki da mijinki dan a kirashi yazo ya faɗi dalilin shi na gujema hakkinki.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.3 / 5. Rating: 7

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Ta ki Aure 2 >>

2 thoughts on “Ta Ki Aure 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×