Skip to content
Part 3 of 5 in the Series Ta Ki Aure by Ummu Adam

Kawwama ta yi ta ƙoƙarin faɗawa alwalin Jalil abunda ke faruwa amma sai ta kasa saboda nauyin maganar, haka ta yi ta haƙuri tana ta addu’a kamar yadda Sawwama ta shawarce ta.

Kamar wasa shekarar Kawwama biyu a gidan aure amma sai dai taji ana labarin yanda aure yake, bata san me ake kira soyayya ba tsakanin miji da mata, babu shaƙuwa, babu biyan buƙata, babu komai da ya shafi rayuwar aure sai fama da zuciyarta da ta keyi wajen bijiro mata da hanyoyin saɓon Allah amma haka ta daure ta kau da kai kuma ta nisanci Amir dan gudun ruɗin shaiɗan.

Kawwama kan kai ziyara duk sati ta gaida Hajiya mahaifiyar Jalil musamman ranar juma’a, yau ma dai ta shirya dan zuwa gidan, ta yiwa Hajiyar girki na musamman da kunun gyada mai daɗin gaske. Tana shiga ta jiyo hayaniyar Siddiqa da Hidaya, a ranta ta ce “Sun dawo kenan.”

“Salamu alaikum.”

Hajiya ta amsa, “Wa’alaikum salama, barka da zuwa Kawwama!”

Da gudu suka fito, “Oyoyo Anty Kawwama, yanzu muke shirin yi miki surprise visit.”

“Allah sarki yaushe kuka dawo ban sani ba?”

“Jiya da yamma muka dawo kuma munce wa yaya karya faɗa miki.”

Hajiya ta ce, “To ai kwa bari ta zauna dai ko?”

Bayan ta zauna suka gaisa da Hajiya da sauran mutan gidan. Yini ta yi a gidan har bayan sallar magriba amma ji take kamar karta koma gidanta saboda gidan babu daɗi. Kamar Siddiqa taga zuciyarta ta ce,

“Anty tare zamu tafi da ke muyi sati ɗaya.”

Kawwama tace, “Wata ɗaya zaku yi dan sati yayi kaɗan.”

‘Hmm Kawwama yaran nan zasu dame ki da hayaniya kinsansu da surutu.”

“Haba hajiya ba komai ai nima kinga na samu ‘yan hira.”

Hajiya ta ce, “To shikkenan kuje amma kar su wuce sati biyu”

“Hajiya a taimaka a bamu wata ɗayan nayi kewarsu sosai.”

“To shikkenan Allah ya bada zaman lafiya. Amma a kula kar naji abunda bai kamata ba ke Hidaya ki kula da Siddiqa kinsanta da rawan kai.”

“To Mama, sai mun dawo.”
Bayan fitansu ƙanwar Hajiya da ke gefe ta ce,

“Na rasa meye abun so ajikin Kawwama matar da ta doshi shekara uku amma ko ɓatan wata bata yi ba, dama da ganinta ba san haihuwa zatayi ba, irin sune matan nan da basa san ciki dan kar halittan jikinsu ya canza.”

“Karima na sha faɗamiki bana san jin wannan maganar, daga yau kada ki sake.” Inji hajiya.

“Ai dama nasan haka za ki ce sam bakya ganin laifinta ai shikkenan.”

Zamansu Hidaya alkhairi ne ga Kawwama dan ta samu masu ɗebe mata kewa kuma ta samu lafiya dan sati ɗaya da zuwansu hawan jininta ya fara sauka. Ta na zaune a ɗaki bayan ta idar da sallan walaha sai Hidaya ta yi sallama ta shigo ta zauna gefenta, ta ce,

“Anty yau satinmu biyu amma banga Yaya Jalil ba ko dai tafiya ya yi?”

Ƙawwama ta ce, “Ba tafiya ya yi ba kawai dai ya san kuna nan ne zaku tayani hira shiyasa bai damu da yazo ba.”

Hidaya tayi mamakin jin haka amma sai ta taƙaita tambaya, ta ce,

“To shikkenan barin je na ɗaura mana girki dan yau duty na ne.”

“To ba komai na gode fa Hidaya na ji daɗin zuwanku.”

Bayan wata guda hajiya da kanta ta zo dan ɗaukansu Siddiqa dan gani take sun takurawa Kawwama, bayan komawarsu gida sai Hidaya ta samu Hajiya ta yi mata bayanin yadda zamansu Kawwama da Yaya Jalil ya ke, tabbas Hajiya ta yi mamakin jin haka sai ta ɗau waya ta kira shi kuma ta kira Kawwama suka haɗu a parlour ta. Hajiya ta nemi suyi mata bayanin abunda ke faruwa tsakaninsu amma sai Jalil ya nuna babu komai suna zaune lafiya, ganin yadda yake magana babu tsoron Allah ba kunya abun ya bata mamaki, ganin haka yasa ta kwashe labari kaf ta faɗawa Hajiya.

Banda salati Hajiya ta kasa cewa komai cikin gaggawa ta kira general meeting tsakanin family ɗin guda biyu, cikin sa’a ɗaya da rabi kowa ya haɗu guri guda nan take Hajiya ta bayyanawa kowa halinda ake ciki kuma Sawwama ta jaddada gaskiyar abunda Kawwama ta faɗa.

“Haba Kawwama yanzu ashe ba zaman daɗi ki ke yi a gidan ɗana ba amma baki taɓa faɗamun ba nima fa kamar uwa nake a gurinki ina ƙaunar ki kamar yadda nake san yarana, haba malam yanzu harda kai za’a haɗa baki a yi shiru akan maganar nan.”

Malam ya ce, “Nima bansan abunda ke faruwa ba sai yanzu amma duk yanda akai ta hana yaran ne su faɗamun dan haka sai ki faɗi dalilinki na yin shiru duk da kinsan abunda ke faruwa.”

Maman su Kawwama ta ce, “Ni fa gani nayi bai kamata ace yarinya ta jima ba aure kuma daga auren ace har an fara ƙorafi ba sannan idan maganar ya shiga dangi zamu ji kunya.”

Hajiya ta ce “Hmm, kinyi tinanin kuwa amma banda ‘yarki baki kyauta ba sam Mama ko kinsan wannan matsalar da Kawwama ta shiga yana jefa matan aure cikin damuwa wanda sanadin haka wasu ke afkawa zuwa ga zina, maɗigo, da masturbation (yin amfani da yatsa ko wani abun wajen biyan buƙata) musamman irin matan da mazajensu keyin tafiya tsawon lokaci amma ki ka bar ‘yarki saboda gudun abun kunya kin manta yaran nan amana ne a hannunmu dole ne muna bibiyar al’amuransu na rayuwa ko da ace sunyi aure.”

“Kuskure kam nayi dan Allah kuyi haƙuri Malam ka yafe mun kema Kawwama ki yi haƙuri na zalunceki ‘ya ta!”

“Kawwama tana kuka tace ba komai Mama na fahimceki.”

Hajiya ta ce, “saura kai babban ja’irin ka wani sunkuyar da kai kamar mai ciwon wuya zaka mun bayani dalilin da yasa ka wulaƙanta amanar da aka baka ko sai kaga ɓacin rai na?”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ta ki Aure 2Ta Ki Aure 4 >>

1 thought on “Ta Ki Aure 3”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×