Skip to content
Part 9 of 12 in the Series Tekun Labarai by Danladi Haruna

Rana Ta Takwas

Tun cikin dare Wazirai ke ta tattaunawa a tsakaninsu game da al’amarin wannan yaro. Babbansu ya ce, “kun ga dai wannan yaron na son ya faskare mu a wajen Sarki da surutunsa. To kuwa muddin muka yi sakaci ya samu kansa to mu kashinmu ya bushe. Don haka ku tashi mu tafi gaba ɗaya mu yi wa Sarki magana da murya ɗaya domin ya kawo ƙarshensa mu huta.”

Da gari ya waye gaba ɗaya Wazirai  suka faɗi gaban Sarki suka ce, “Allah ya ja zamaninka, ka tuna cewa ka ɗauke mu aiki ne domin ba ka shawara da duba maka game da al’amarin da zai sa ka samu nasara a mulkinka. Mun duba sha’anin wannan yaron babu alheri ko kaɗan tare da shi, muddin ba ka kashe shi ba. Wannan ya tabbata abin kunya na ƙarshe, Sarki ya kama mutum kwance kan gadonsa amma ya ƙyale shi saboda kaifin bakinsa. Mun tabbata da wata niyyar fasiƙanci ya je wurin. Ya Sarkinmu, idan ba za ka iya kashe shi ba saboda tsoronsa da kake ji, to muna baka shawarar ka kore shi daga ƙasar da kake mulki, kuma ka hana kowa ya raɓe shi.”

Sarki na jin haka ya tunzura ya fusata iya wuya, ya daka tsawa ya ce “a kawo yaro gabana!” Aka shigo da shi a ɗaɗɗaure. Wazirai suka kalle shi gaba ɗayansu suka ce da shi, “tir da halin maci amana irinka!” Sarki ya ce a yi maza a kirawo hauni saboda yau ya makara zuwa fada. Wazirai suka hau kokawa tsakaninsu, kowa na cewa a ba shi takobi shi zai fille wa yaro kai. Yaro ya dube su ya ce, “don me kuke gaggawa domin sharri, alhali ba ku da hujja a kan da’awarku? Ko dai hassada da makirci ke damun ku?” Sarki ya ce masa, “dube su ka gani mana, Wazirai na ne su goma, gaba ɗayansu sun haɗu a kan ka aikata laifi, babu ɗayansu da ya goyi bayanka.” Yaro ya yi murmushi ya ce, “ya Sarkin zamani, ka rabu da sabgar waziran nan naka, domin babu abin da ke damun su sai hassada da ha’inci da makirci. Muddin kuwa ka yarda da zancensu irin wannan da ba su da masaniyar komai a kai, to babu shakka wata rana za su sanya ka kuka da idanunka. Haka nan kuma za su iya jefa ka cikin nadama a lokacin da bata da amfani. Ni ina jiye maka tsoron yin nadama irin ta Aylanu Shahu, saboda makirci da sharrin waziransa.” Sarki ya ce, “mene ne labarinsa?” Yaro ya ce, “bari ka ji.”

Sharri Jakada Ne

An yi wani attajiri da ke da dukiya mai yawan gaske, ana kiransa Abu Tammamu. Saboda yawan dukiyarsa, bai san iyakacin abin da ya mallaka na daga gidaje da gonaki da dabbobi da bayi da sauran kadarori ba. Baya ga tarin dukiya, yana da ɗumbin ilmi da fasahar harshe, sannan ya san yadda zai zauna da kowa lafiya.  To amma ƙasar da ya ke zaune ta Sarki Shamzanu, ba ya sakewa yadda ya kamata, saboda Sarkin ya kasance azzalumi mai yawan mugunta. Da abin ya tsananta, sai ya kwashe dukan dukiyarsa ya bar ƙasar, ya yi gudun hijira zuwa ƙasar Sarki Shahu Aylanu. Bayan ya ƙare jigilar dukiyarsa duka, abin da bai iya tahowa da shi ba kuma ya sayar, sai Sarki Aylanu ya ji labarin zuwansa. Shi kuwa ya kasance mai kyautayi da adalci a mulkinsa. Ya aika aka kirawo shi ya zo ya fada.

Ya tafi gaban Sarki ya faɗi ya kwashi gaisuwa. Sarki ya amsa da fara’a, ya ce masa, “mun samu labarin irin alherinka da mutuncinka. Saboda haka muke maka marhabin a wannan birni namu. Kuma muna gayyatar ka zuwa wannan fada tamu.” Attajiri ya sake rusunawa ya ce, “Allah ya taimaki Sarki, na amince zan yi wa Sarki hidima da dukiyata da jikina da dukan abin da na mallaka, amma ina neman uzuri ga Sarki kan a bar ni, ba sai na dawo fada da zama ba, saboda ina tsoron makircin maƙiya, masu iya ƙulla gaba tsakanin aminan juna.”  Ya fito da dukiya mai yawa ya ba wa Sarki a matsayin kyauta. Ya kasance a kan kari ya kan aika wa Sarki manyan tufafin alfarma da dukiyoyi masu daraja. Sannu a hankali Sarki ya ji ba shi da wani wanda ya fi Abu Tammamu, saboda haka ya matsa masa akan tilas ya dawo fada. Kuma ya sakar masa komai. Hatta shawara a keɓe da shi ake shiryawa. Ya zamana duk abin da ya faɗa baya tashi. Masu neman alfarma wajen Sarki da masu neman afuwa duk a wajensa suke kamun ƙafa.

Ya kasance Sarki Aylanu na da Wazirai  guda uku, waɗanda tun dawowar Abu Tammamu fada, sai dukan aikinsu ya koma ƙarƙashinsa. Su dai suka zamanto tamkar hoto a fadar, domin ba su da ikon sawa ballantana hanawa. Ko da shawara suka bayar Sarki ba ya ɗauka, sai abin da Abu Tammamu ya faɗa.  Wannan ya sa suka ƙulla gaba matsananciya gare shi. Duk da ba su da ikon su cutar da shi a zahiri amma sai suka riƙa shirya masa makirci iri dabam – dabam. Shi kuwa bai ma san suna yi ba, domin a zahiri shi da su sai fara’a da juna, suna nuna masa ƙauna kamar yadda Sarki ke nuna masa. Da dai suka ga lamarin ba mai ƙarewa ba ne, sai suka haɗu a gidan babbansu suka tattauna a kan yadda za su yi maganin sa domin ya halaka kowa ma ya huta.

Waziri na biyu ya ce, “akwai Sarkin Turkawa yana da wata ‘ya kyakkyawa, wadda babu kamar ta a wannan lokacin. Sarakuna da yawa sun aika neman auren ta, amma duk wanda aka aika sai ubanta ya kashe shi. Yadda za mu yi shi ne, mu kai zancenta gaban Sarkinmu, idan ya ji irin kyawunta zai aika amintaccensa neman auren ta, wanda shi ne Abu Tammamu. Idan ya tafi sai a kashe shi a can mu huta.” Ragowar duka suka amince da wannan shawara. Suka tafi fada suka zauna. Abu Tammamu na daga daman Sarki ana shawara yadda aka saba, su kuma Wazirai  dukansu na hagun Sarki suna zazzare idanu. Can sai babban Waziri ya kawo zancen ‘yar Sarkin Turkawa, ya ce, “a nan duniya kaf an yi ittifakin a yanzu babu kamar ta a fagen kyawu da siffa da kamala da cikar halitta. Ga ilmi, ga lafazi mai taushi ga dukiya da ubanta ya mallaka mata.” Waziri na biyu ya ce, “irin wannan tauraruwa ba ta dace da kowa ba sai Sarkinmu.” Waziri na uku ya ce, “to idan haka ne sai Sarki ya aika amintaccensa watau Abu Tammamu neman auren ta wajen mahaifinta.” Sarki ya gyara amawali ya ce, “haka za a yi.” Ya dubi Abu Tammamu ya ce, ‘je ka shirya ka kai mana saƙonmu wajen Sarkin Turkawa.”

Abu Tammamu ya shirya ya tafi ɗauke da takardar da Sarki ya rubuta da hannunsa, gami da kyautuka masu yawa, har ya isa Birnin Turkistanu lafiya. Sarkin garin ya ji labarin zuwansa, ya aika aka tarbo shi aka kai shi masaukin alfarma. Sannan bayan ya huta suka gaisa da Sarki, ya miƙa masa takarda gami da kyautukan da aka aiko shi da su. Sarki ya karɓa sannan ya ce, “na ga saƙon da aka aiko ka, amma mu ba haka muke yi ba. Idan kana neman samun nasarar abin da aka aiko ka da shi, to ya zama wajibi ka je ka ga ‘yata ita ma ta gan ka. Ta yi maka zance kai ma ka yi mata.” Abu Tammamu ya ce, “ai ba ni ne mai neman auren ba, ubangidana ne.” Sarkin Turkawa ya ce, “Mu haka muke yi, ba makawa kuma kai ma ka yi haka.” Aka kai shi wani babba ɗaki inda ake saukar da baƙi ‘ya’yan Sarki, ya ga an gyara shi sosai, an shimfiɗa dardumai da kilisai, an shafe shi da ruwan zinariya, sannan an sa wasu fitilu masu haske, ga ƙamshi mai daɗi na tashi.

Da ya ga haka sai ya ce a zuciyarsa, “wanda duk ya iya sarrafa ganinsa, ba zai ga abin aibu ba. Wanda kuwa ya iya sarrafa harshensa, zai samu kuɓuta daga dukan gaɓɓansa. Shi kuwa wanda ya iya sarrafa hannunsa, to zai zama mai wadata ba zai taɓa rashi ba.” Ya shiga ya zauna a kan kujerar zinariya da aka tanada domin sa. Zuwa jimawa ‘yar Sarki ta shigo, tana sanye da tufafin alfarma. Ta caɓa ado na ban mamaki, kyawunta ya sake fitowa fiye da yadda aka wassafa ta. Duk da ƙamshin ɗakin sai turaren jikinta ya buce shi, hasken kayan adon jikinta suka ƙara haskake ɗakin, tamkar wata da taurari. Ta zauna a kujerar da aka tanadar mata ta ce, “ɗaga idonka ya Abu Tammamu ka dube ni ka yi min zance.” Ya yi shiru bai ce da ita uffan ba. Ya rufe idanunsa. Ta ce, “buɗe idanunka mana ka kalle ni da kyau.” Ya yi kamar bai ji ba. Ta ce, “to ungo waɗannan lu’ulu’u guda uku ka je ka sayar ka samu wani abu.” Ya ƙi motsawa daga inda yake. Da ta ga haka sai ta fusata ta ce, “wannan wane irin manzo ne haka? Don me za a aiko min kurma, bebe, makaho. Ku fita da shi!” Aka fita da shi.

Ta aika a shaida wa mahaifinta yadda suka yi da shi. Sarki da kansa ya je wajensa ya ce masa, “kai ka zo ne domin ka ga ‘yata, don me ba ka ɗaga kai ka dube ta ba?” Ya ce, “ni na ga komai da nake buƙata. Wancan ganin kuma ba da ni ya dace ba.”

“To ta yi maka kyauta, amma ba ka miƙa hannu ka karɓa ba. Me yasa haka?”

Ya ce, “saboda hannayena na hane su da karɓar abin da bai zama mallakina ba.” Da Sarki ya ji haka sai ya sa aka yi masa kyauta mai yawa, ya girmama shi, ya kuma sake amince masa. Bayan an natsa sai ya kama hannunsa zuwa wata tsohuwar rijiya, aka buɗe, sai ga kawunan mutane da yawa a ciki. Ya ce da shi, “waɗannan duk kawunan wakilan sarakuna ne, waɗanda aka aiko neman auren ɗiyata. Duk waɗanda muka jarraba sai mu gane cewa ba su da amana, don haka sai mu kashe su. Kai kuwa jarrabawar da muka yi maka, mun tabbatar kai mutum ne mai amana, mai kiyaye ta. Yanzu ina mai tabbatar maka cewa babu wanda zan ba wa ‘yata sai ubangidanka.” Ya aike shi zuwa ga Sarki Aylanu da takardar amincewa bisa buƙatarsa. Sannan ya buƙaci a sa lokacin da za a yi wannan bikin. Ya ƙara da cewa, “na yi maka haka saboda karamcinka da kuma amanar ɗan aikenka.”

Yayin da Abu Tammamu ya koma gida cike da busharar samun nasara, Sarki Aylanu ya tarbe shi da farin ciki. Ya ba shi kyauta mai yawa sannan darajarsa a fada ta ƙaru. Bayan wasu ‘yan kwanaki aka shirya ƙasaitaccen biki tsakanin Sarki Aylanu da gimbiya. Aka kawo amarya, Sarki ya shiga wurinta ya tare da ita, ya same ta tamkar rufaffen lu’ulu’u. Wannan ya sa darajar Abu Tammamu ta ƙara yawaita a idon Sarki, ya sake miƙa masa al’amuransa gaba ɗaya. Ya zamana hatta gidan Sarki ma sai abin da ya ce za a yi.

Wazirai suka cika da baƙin ciki ganin makircin da suka shirya bai yi nasara ba, suka rasa inda za su sa kansu. Ga shi kullum abu sai gaba yake sake yi, kullum baya suke sake komawa a fadar. Don haka suka sake haɗuwa domin ƙulla wani makircin.  Ya kasance Sarki na da wasu ‘yan babanni da ya amince wa, ba ya barci sai ya ga ɗayansu ya tsaya a kansa yana masa firfita, ɗayan kuma ya tsaya a ƙafafunsa yana yi masa tausa. Wazirai suka samu yaran nan, suka basu dinari dubu kowanensu. Suka ce musu muna son ku yi mana wani aiki. Yara suka ce, “ku faɗi ko mene ne za mu aikata.”

Suka ce musu, “Idan Sarki ya kwanta kuna yi masa firfita da tausa, sai ɗayanku ya ce da ɗaya, ‘kai wane ba ka san cewa Sarki ya fi amincewa da babban maci amanarsa ba?’ Sai ɗayan ya ce, “wa kenan?” Sai na farkon ya ce, “Abu Tammamu mana.” Sai ɗayan ya ce, “me ya sa ka ce haka?” Sai na farkon ya ce, “ai yana ta yaɗawa a gari cewa matar Sarki ‘yar Sarkin Turkawa da ya aika ya nemo masa auren ta, shi take so ba Sarki ba. Wai ashe duk wanda aka aika neman auren ta sai ubanta ya kashe shi. To shi saboda tana son sa ta sa aka bar shi, ta yarda za ta zo nan za su riƙa saduwa.” Sai ɗayan ya ce, “kai wane, ta yaya ka san wannan zancen?” Sai na farkon ya ce, “wallahi ka ji na rantse, ai zancen yanzu haka ya yaɗu a gari, kowa ya sani, Sarki ne kawai bai sani ba saboda ana tsoron fushinsa. Yanzu haka ma an ce jira yake Sarki ya fita rangadi ko farauta, ya samu ya shiga wajenta su sadu.” Sai ɗayan ya ce, “lallai Abu Tammamu ya cika maci amana, babu abin da ya fi sai Sarki ya kashe shi, ya jefa cikin rijiya a manta da shi.”

Yara suka ce, “wannan mai sauƙi ne, tabbas za mu faɗi haka.” Da dare kuwa Sarki ya zo kwanciya, yaran nan suka zo bisa aikinsu, suka aikata kamar yadda Wazirai  suka shirya musu. Sarki na jin su bai ce komai ba, amma abin ya taɓa zuciyarsa. Ya ce a ransa, ‘waɗannan yaran ba su mallaki hankalin kansu ba, tabbas ba za su iya kitsa wannan zancen ba, face sun ji daga wani waje. Da ma an ce munafukinka tabarmarka. Watau ashe shi ya sa kullum yake tambaya ta lafiyar amarya? Zan kuwa yi maganin sa.”

Wayewar gari a fusace ya tashi, ya zamana bai iya fita fada ba saboda fushi. Ya aika aka kirawo Abu Tammamu suka keɓe kamar za su yi wata shawara yadda suka saba. Sarki ya ce masa, “Wanda ya keta mutuncin ubangidansa me ya dace da shi?”

“Ya dace ubangidan shi ma ya keta mutuncinsa.”

“Wanda ya shiga hurumin iyalin mutum ya ci amanarsa, me ya dace da shi?”

“Wannan bai dace a bar shi da ransa ba. Ya tabbata maci amana.” Sarki ya harzuƙa sosai, ya dubi Abu Tammamu a fusace ya ce, “to kai kuwa ka aikata duk waɗannan laifuffuka. Na kama ka da laifin cin mutuncina a bayan idanuna da kuma yunƙurin shiga hurumin iyalina.” Tun kafin Abu Tammamu ya buɗe baki ya yi magana Sarki ya soka masa wata wuƙa mai dafi wadda ya riƙe a hannunsa. Nan take ya faɗi a wurin matacce. Da kansa Sarki ya ja shi zuwa wata tsohuwar rijiya da ke bayan ginin fadar ya jefa shi ciki ya rufe. Ya hana kowa ya yi masa zancen Abu Tammamu, fada ta zamanto tamkar ba a taɓa yin mai wannan sunan ba da ɗai.

 Da yake sharri jakada ne, idan ya tafi sai ya dawo, sai ya kasance Sarki kullum ba ya cikin walwala a fadar nan. Ya zamana kowa na shakkar yi masa magana, hatta waziran nan sun kasa gane samansa ballantana ƙasansa. Shi kuwa a ƙarƙashin zuciyarsa nadama yake yi ta yadda bai yi wani bincike ba ya hallaka babban amininsa. Ga abin na cin sa a rai amma ya kasa faɗa wa kowa damuwarsa. Matarsa na yawan tambayar sa game da abokinsa, amma ya kasa faɗa mata. Wazirai kuma suna ta zuba ido ko zai karkato gare su ganin babban ɗan adawarsu ba ya nan, amma shiru kamar an shuka dusa.

Sarki sai ya zamana a kullum ya kalli yaran nan sai ya ji damuwa, musamman idan ya tuna lokacin da yake sauraron hirar su. Sai ya riƙa bibiyar lamuransu a hankali, musamman yayin da suke zaune kafin lokacin aikinsu. Ran nan suna ɗakinsu Sarki na laɓe yana kallonsu, sai ɗaya ya ce wa ɗaya. “Ka ga dai kuɗin nan da Wazirai  suka ba mu ba wani amfani da za su yi mana, tun da ba mu da ikon mu sayi wani abu na kanmu.” Sai ɗayan ya ce, “kawai fito da su mu riƙa wasan dara da su, mun samu abin ɗebe kewa.” Ɗayan ya ce, “gaskiya ba mu kyauta ba. Da mun san abin da muka faɗa zai sa a kashe Abu Tammamu da ba mu aikata ba.” Ɗayan ya ce, “alhaki dai ba a kanmu yake ba, yana wuyan waziran da suka sa muka aikata haka.” Daga nan suka fito da kuɗi suka shiga dara. Sarki ya ga tarin kuɗi gabansu suna wasa da su. Sarki ya hasala ya shiga wajen su. Ya kama su da hannunsa ya ce, “ina kuka samu kuɗin nan haka? Watau kun fara yi mini sata ko?” Yara suka razana suka soma kuka suna cewa, “wallahi ba sata muka yi ba, Wazirai  ne suka ba mu.”

“Garin yaya suka ba ku kuɗi masu yawa haka? Ku faɗi gaskiya ko na sa a yanka ku yanzun nan!” Cikin rawar murya da rawar jiki suka faɗawa Sarki duk yadda aka yi daga farko har ƙarshe. Suka ƙara da cewa, “duk abin da muka faɗa a kan Abu Tammamu wallahi waziranka ne suka tsara mana, amma ba mu ji daga wajen wani ba face su.” Sarki da ya ji haka sai  ya yi kururuwa mai cike da nadama. Ya kama gemunsa yana fisga da ƙarfi, tamkar ya cisge shi daga matsirarsa. Ya aika dogarai suka cakumo wuyan Wazirai  suka zo da su gabansa. Ya umarci yara su faɗi abin da suka sa su aikata. Yara suka mayar da zance yadda yake. Sarki ya dube su a fusace, dukansu sun yi tsuru – tsuru ya ce, “ku maƙiya Allah, maha’inta, to yau Allah ya toni asirinku. Sharrin da kuka aika ya dawo kanku. Saboda haka za ku ɗanɗani azaba tun daga nan duniya kafin ku samu wadda ta fi ta nan a ranar lahira.” Ya sa aka aza su bisa jakuna aka juyar da fuskarsu ta baya sannan aka zagaya da su lungu da saƙo na birnin kowa yana la’antar su, ana yi musu ature. Bayan haka Sarki ya umarci hauni ya fille kawunansu. Aka ɗau gawarsu aka jefar a daji, ungulaye da sauran namun daji suka samu na kalaci.

Da amaryar Sarki ta matsa masa da tambaya game da Abu Tammamu, ƙarshe dai ya fito fili ya faɗa mata abin da ya faru. Ta yi ta kuka tana marin fuskarta. Bayan ta gama kukan ta faɗa wa Sarki duk yadda aka yi yayin da ya je neman masa auren ta. Ta ƙara da cewa, “wallahi kaf a mutanenka ba za a samu mai fasaha, mai amana, mai mutunci kamar Abu Tammamu ba, amma ga shi saboda sharri da rashin bincike irin naka, ya jawo maka asarar da ba za ka taɓa mayar da kamar ta ba.” Sarki ya sake fashewa da kuka. Ya sa aka shiga tsohuwar rijiyar da ya jefa gawar Abu Tammamu aka fito da ita. Ya gina babbar ƙubba aka binne shi a ciki. Kullum da safe sai Sarki ya shiga ya yi masa addu’a.”

Da yaro ya kawo nan sai ya dubi Sarki, wanda da dukan alamu labarin ya shige shi sosai ya ce, “Allah ya ba ka nasara ka ji yadda Allah ya mayar da sharrin waɗancan Wazirai  a kansu. Sun samu nasarar kawar da wanda suke ganin shi ne cikas gare su, amma a ƙarshe ba su samu nasarar abin da suke nema ba, sharrin da suka aika ya dawo musu. Ni dai na dogara ga Allah wanda zai ba ni iko a kan dukan masu shirya min hassada da makirci da sharri da ƙazafi da ƙage. Ni ban damu da duk hukuncin da za ka zartar akaina ba, amma ina jiye maka tsoron yin nadama a lokacin da ba za ta yi tasiri ba.” Sarki da ya ji haka sai ya yi ajiyar zuciya ya ce, “a tafi da shi sai gobe za mu yanke masa hukunci.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tekun Labarai 8Tekun Labarai 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×