Skip to content
Part 14 of 58 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Ledoji ne manya guda biyu ta shigo dasu, yanayin yanda take rike dasu zaka san kayan ciki ba ‘yan kadan bane ba, kallonta Abida takeyi tana karajin tsanar tashin da sukayi. Duka a cikin Bachirawa ne, sai dai nan din wani yanki ne da bata takowa ba duk shekarun data shafe a cikin a unguwar kuwa, sun sha kuka ita da makota da aka saba dasu, har nan din da yawa suka rakato, wanda basu samu yin rakiyar ba duk sunzo daga baya, suna kara jaddada mata tazarar da aka samu ba zata taba yanke zumuncin daya kullu shekara da shekaru ba. Gidane madaidaici mai dakuna uku, dan karamin kicin sai bayi. Dakin da yake gefe jere da kicin shi Abdallah da Fa’iza suka dauka. Gado ne kawai a ciki sai kuma sif din kaya, ita tace su dauki daki biyu lokacin da Abdallah yazo mata da maganar an samu gidan da zasu iya kamawa, ya dauketa sukaje suka gani. Da yaje mata da maganar sai tace masa

“Daki daya ya isheni, abarwa Amma daya, sai su Sa’adatu su dauki dayan, in ba dai kai kake bukatar dakuna biyun ba…”

Ba haka Abida taso ba, tayi shiru ne, inda zabin ranta za’abi, kuma akwai halin, me zaisa su zama gida daya da suruka? Su dukansu a takure, shisa da Furaira tace a saka wata biyu lokacin bikin, dan suma su dan shirya. Abida tayi na’am da maganar, su suka fara tarewa a gidan, ko bakomai a ganinta sun samu akalla satika wajen hudu, kafin su koma gidan. To Furaira din ta dauki Asma’u sun wuce Lagos, daga ita sai Jidda da Sa’adatu suka. Sadiya tun rasuwar Asabe tana gidan Nana, wannan idanuwa Abida ta dauka ta saka musu, ta dai fada musu har abada Sadiya na da wajen zama a tare da ita idan taso hakan. Kawai yanzun matsalarta shine sana’a. Duk da tabi shawarar Fa’iza, data shiga makota dan a gaisa, tace musu suna yin awarar siyarwa da kuma wainar filawa, harda ma taliya da wake da manja da safe.

To taliyar kamar ta dan fara samun karbuwa fiye da sauran abubuwan, tunda yar murji ce ta hausa. Sai dai duk da haka kudin ba wasu masu yawa bane ba, inda Allah ya taimaketa, su Amira da suka harhada kudade, suka ajiye mata kayan abinci, har kuka tayi randa Nabila tazo gidan, taga an shigo da buhun shinkafa, taliya da macaroni, sai kuma su Maggi, mai, manja da sauran kananun abinda ba’a rasa ba

“Amma meye amfaninmu idan bamu taimaka miki ba? Wallahi duka bamajin dadin wannan kikiniyar da kikeyi, musamman yanzun daya kamata ace kina hutawa, idan mun samu yanda muke so, ba zaki dinga siyar da komai ba”

Share hawayenta tayi

“Nabila ai ba’a zama haka a wannan rayuwar, kinga ga kudin haya, kafin kice meye sai kiga shekarar harta zagayo, ga kuma hidimar yau da kullum, ga dan abinda kake ajiyewa ko da lalura zata taso maka…”

To kuma tana zaune ma Nana tazo ta kawo mata dubu dubu biyar, dan kuka tayiwa Amira a waya sosai, sai da taita fama lallashi, akan sun wareta, sun hada kudi sun siyawa Abidar kayan abinci ita ba’a tuntubeta ba

“Nana gani nayi duka yaushe kikayi auren…bawai wareki mukayi ba”

Kukan taci gaba dayi

“Ai da naga unguwar mutane ce, ga yara, sai nayi masa magana na fara yin su alawar madara da kwakumeti kinga yanzun inayin ciniki sosai, kusan duk kwana biyu sai nayi, dan Allah ni dai Yaa Amira karku kara wareni”

Abida ta rikesu duk da basu zame mata dole ba, bata taba bambanta su da yaran data haifa ba, balle yanzun da babu Asabe, ji takeyi duniya basu da kamar Abida, ita kadaice Nana ke da yakinin in sun shiga lalura zata tsaya musu karfin jiki dana aljihu. Idan basu kyautata mata bama ai batajin zasu ga haske a lamurransu. Shisa ma damuwar rashin shigowar kudi ta fannin sana’ar yayi ma Abida sauki. Ga kuma Sa’adatu da take ganin ta sake ta koma hidimarta kamar wani abu bai taba rayuwarta ba. Hakan da farko yayiwa Abida dadi, sai ta fara kula, a kalaman Sa’adatu kamar halayenta na da suka dawo sai suke neman ninkuwa. Daman Islamiyya, Jidda kawai Abdallah ya samowa anan layin da suka dawo, baima yiwa Sa’adatu maganar ko tana son komawa ba, saboda ganin walwalarta kamar ya danne komai a wajen shi.

Akwatunan lefenta daman ko gidanta ma basu gani ba, duk da ba yanda batayi da Abdallah ya dauki akwatunan ko da guda biyune a ciki dan ya sakawa Fa’iza kayanta a ciki yaki, ta dibi wasu a cikin atamfofin da lesunan, kayan kwalliya dangin su man shafawa, hoda da turaruka tace nata gudummuwar kenan, harda jakunkuna sai da ta hada masa, daga shi har Fa’iza a wajenta sunfi karfin wannan kayan, takalma ma wata irin karamar kaface da Fa’iza shisa bata daukar mata ba. An dinka mata da yawa daga cikin lefen da nufin ta dauka a cikinsu tayi fitar biki, saima bikin yazo musu a haggunce. Yanzun ne take jin dadin kayan, sosai take dandansa gayu ta kafa dauri idan zataje ma Abida aike, musamman idan kasuwa ne. Ita Sa’adatu wannan tashin da sukayi dadi yayi mata sosai.

Ashe a Bachirawa akwai layi me kyau irin wannan? Ba hayaniya, babu tarin kwatoci, ko kwatance zatayi yanzun ba zatace sai an ketare kwatoci biyar kafin a karaso gidansu ba, ko masu adaidaita sahu inta hadu da marassa kirki lokacin da suke can layin ana karyo kwana suke cewa ba zasu karasa da ita su bata tayar dan sahunsu ba

“Ai wallahi da kince mun layin Sahalu mai almajirai nema ba zan daukoki ba, dazun nan aka wanke mun babur din nan haka kawai in bata tayata”

Wani ya taba ce mata, kawai lokacin ta hango wasu Samari ne tsaye bakin wata zukekiyar bakar mota, shisa ta sauka salin alin, da ta tsaya ta biye masa sun dan taba rashin mutuncin daya nuna mata. Amman yanzun da karsashi zatayiwa kowa kwatancen layin nasu, idan akayi kwana ma gidaje ne masu matukar kyau daga haggun su, irin gidajen nan masu manyan gate. Ga motoci na alfarma suna yawan wucewa. Hakan kawai wani karin karsashin yin kwalliya ne a wajen Sa’adatu, watakila wannan ce damar da take da ita na cika tsohon mafarkinta. Natsuwa take arowa tana kara sakawa a duk wani takunta, a cikin irin wannan tafiyar ne da wani yammaci, wata dankareriyar Jeep ta tsaya a gabanta. Motar ruwan toka ce mai duhu, da bakaken gilasan dana ciki zai iya hangoka, amman na waje ba zai iya ganin komai ba.

Tsallen da zuciyarta tayi bai hanata bugawa a lokaci daya ba, saboda yawancin irin motocin nan a zahiri ba’a littafi ko fim ba, in dai zasu tsaya gaban budurwa irinta, a unguwa irin tasu, tabbas da wata manufa ne, manufar da idan ka tace ta a cikin kashi dari, to da wahala a samu biyar na kirki. Bata matsa daga inda take tsaye ba, saima kanta da ta kauda gefe, aka danna hon sau wajen hudu cikin son aja hankalinta ta gane tsayuwar dominta ne. Yanda duk taso ta juyo sai ta daure

“Yan mata…”

Taji an kira, sai sannan ta juya, taga matashin daya zuro kai ta gefen direba inda ya zuge gilas din bangaren yana washe mata baki, duk da bashi da wata makusa, amman kallo daya zakayi masa kagane cewa direba ne, wayewar shi bata kai a dangantashi da mallakar mota mai wannan girman ba, ganin bata da niyyar cewa komai yasa shi fadin

“Ki zagayo Alhaji na son magana dake”

Wani sashi da take tunanin shine mahangar hankali a tare da kwakwalwarta ne ya shiga gargadinta da karasawar. Idan ta shiga akayi gaba da ita fa? Idan masu garkuwa da mutanene dai asarar lokacinsu zasuyi, dan in kasheta zasuyi sai dai su kasheta, danginta kaf duk wanda aka daga aka zazzage dubu goma ma zai wahala ta fito, sai dai idan yan yankar kaine, wannan zatayi musu amfani, ga siyasa ma data matso, masu dogon buri a ciki da zasu iya komai dan ganin cikar burinsu na iya amfani da wannan damar. Sai dai kafin ma ta karasa jin gargadin kafafuwanta sun fara takawa zuwa motar, babu wani dogon tunani ta kama murfin baya ta bude tana shiga da sallama dauke a muryarta, tana mamakin kamshin daya gauraye motar, wani kamshi irin na masu kudi. Data dan juya ta kalli mutumin da yake gefenta yana mata murmushi sai taji zuciyarta ta tsinke.

Tabbas ta kawo kanta mahallaka, ba dattijo bane wannan, idan akace Dattijo a lissafinta dan shekara sittin zuwa saba’in. Wannan tsoho ne, tsoho da idan zai bude bakinshi ace za’abi kowanne hakori a girgiza tabbas ba za’a rasa mai girgidi ba, idan wani ma bai kai da faduwa ba

“Yan mata ke ba kalar da ya kamata ace kina tsaye a bakin titi da irin wannan kwalliyar kananan yara da basu san darajarki ba suna kallo, harma a samu wani mai tsaurin idon yace zai taya”

Wani abu Sa’adatu ta hadiye daya tsaya mata a wuya. Cikinta kuwa sai ya kulle ta gefe daya lokacin daya saka hannu a aljihu taga ya ciro da bandir din yan dari biyar, sababbi dasu, sai kuma wani kati yana mika mata

“Ina sauri yanzun. Ga wannan dan Allah ki dauki shatar ko taxi ce ta kaiki inda zakije, ki sake dauka ta mayar dake gida saboda kananan yaran nan, in kin natsu saiki kirani muyi magana…sunana Alhaji Danladi Maitaya…meye sunan?”

Ya karashe yana mata murmushi, bakinta takeji ya bushe har makoshi.

“Sa’adatu…”

Tace dakyar

“Sa’adatu matar manya, ki killace mun kanki dan Allah, kinji ko?”

Kai kawai ta iya daga masa tana daukar kudin da katin da taji sunyi mata nauyi, ta bude motar ta fito, mamaki takeyi ta shaki wata iska daban data motar, basu gudu da ita ba, kuma da alama ba wani boka bane ya bashi sa’a yace ya nemo bazawarar da bata cika shekara ashirin ba. Ai ba tama iya karasawa inda zatace ba ta juya tayi gida

“Sai ya dauki har dubu hamsin ya baki? Daga ganinki? Dubu hamsin kuma kika saka hannu kika karba Sa’adatu? Saboda ke baki da hankali baki da tsoro…ya za’ayi mutum ya dauki wannan makudan kudaden ya baki daga ganinki? Ki ma dauke su daga gabana, ki kuma dauki katin ki kirashi yazo ko ya aiko a karbar masa kudin shi kafin ranki yayi mummunan baci…”

Abida ta rufeta da fada bayan ta koma gida ta nuna mata kudin ta fada mata abinda ya faru. Data tashi ma taje ta jawo Fa’iza zuwa dakinsu ta bata labari tana nuna mata kudin da suketa daukar ido na sabunta, a tsorace take kallonta

“Idan kudin tsafine fa? Anya Sa’adatu?”

Sai taji hankalinta kuma ya fara tashi. Ta samu tsohuwar jakar islamiyyarta ta saka kudin a ciki ta rataye a sama, ta kira lambar jikin katin yafi sau goma ba’a daga ba. Sai ta tura masa takaitaccen sako kawai, ta kwanta zuciyarta nata bugawa, bugun ya kara tsananta da Abdallah ya dawo ya kirata, duk da akwai bacin rai a kasan zuciyar tata na yanda Abida take zabar ta dinga hadata dashi a duk wani karamin abu da zai faru. Tace ta mayar masa da kudin shi, kuma har gaya mata tayi tana ta kira bai daga ba, daya daga zata fada masa. Ta dauka shikenan magana ta kare

“Kanwata…”

Kafin yace wani abu ta kalleshi da idanuwanta da suke cike da kwalla

“Yayaa zan mayar masa da kudin shi, na fadawa Amma fa, daya daga wayar…dan Allah karkayi mun fada”

Murmushi yayi

“Ki dinga kula da kanki kinji ko? Kar wani ya cutar mun dake”

Kai ta daga masa tana saka hannu ta goge hawayenta, ko saida safe batayi masa ba ta koma daki ta kwanta kusa da Jidda da taketa bacci. Dan ita tana idar da sallar isha’i take kwanciya bata cika hirar dare ba. Sai dai wajen karfe goma da kusan rabi sai ga kiran Alhaji Danladi, bayan sun gaisa ta bude baki da nufin yi masa maganar ya aiko a karbar masa kudin shi ya katseta da fadin

“Kinganni dai Sa’adatu, shekaruna sun wuce mu tsaya muna dogon zance, naganki, kin kwanta mun a rai, matana hudu, uwargidana bata jima da rasuwa ba yanzun sauran su uku, in dai baki da wata matsala kiyi mun kwatancen gidanku, zanzo ku kara fahimtar juna, dan ni aurenki nake sonyi, bana kuma bukatar aja lokaci”

Nan taji tsohon dan majalisa ne, kuma har yanzun ana damawa dasu a siyasa, musamman da gwamnatin jam’iyyarsu ce akan mulki. Duk wani abu da yake tunanin mai muhimmanci ne kuma ya kamata ta sani saida ya fada mata. Itama kuma anan ta fada masa ta taba aure, kaddara ta rabata da mijin, bai nuna ya damu ba, ya daiyi mamakin jin ta taba aure. Data sukayi sallama sai ta dinga juye-juye tana saka da warwara a ranta. Tabbas tsoho ne, amman ko bai fada ba duk wata alama ta nuna yana da kudi, kuma yanzun ko a Facebook ai tanata ganin irin auren nan ‘yan mata suke yayi, auren wuf. Ka samu wani tsoho mai kudi da zai baka duk wani jin dadi na rayuwa kayi zamanka. Idan ma Allah ya taimakeka haihuwa daya ko biyu, sai ya mutu, kai da yara ku bude sabon shafin rayuwa da dukiyar da zaku gada.

Data tashi da safe ma sai taji zuciyarta ta kara natsuwa, bata damu da Abida da take binta da harara ba duk inda zatayi

“Kin fada masa yazo ya karbi kudin shi ko kuwa?”

Abidar ta tambaya da taga har yamma Sa’adatu batace mata komai ba

“Yace zaizo”

Ta amsa a takaice tana shigewa daki, da aka sake kwana ma, duk fadan da Abida ta dinga yi shiru ta zabi tayi mata

“Kin kirashi kuwa Sa’adatu?”

Fa’iza ma ta tambayeta jin fadan Abida yayi yawa, tasan ranta ya baci

“Na kira”

Ta amsa Fa’iza a takaice. Abdallah kuwa bai sake mata magana ba, kwanaki biyar aka dauka kafin Alhaji Danladi yazo kwatancen da Abida tayi masa, ya kuma zo mata da siyayyar kayayyaki masu yawa, daga dogayen riguna, turaruka da tun daga kwalayen zaka gane masu bala’in tsada ne sai kayan ciye-ciye. Da daddare yazo bayan Isha’i, direba ya kawo shi, kuma baifi minti sha biyar ba yace zai tafi saboda yana da inda zai biya daga nan. Suna sallama ta fito daga motar mashin na sauke Abdallah, ko canji bai karba ba ya karaso inda suke da saurin shi ganin irin motar kuma Sa’adatu ce ta fito daga ciki. Yana tsoron yaran masu kudin nan da yawanci tsoron Allah yayi musu karanci, yana kuma tsoron Sa’adatu da son rayuwar jin dadi, kar su mika mata hannu ta kama su ja masa ita mahalaka.

Sai dai duk wani tunanin shi sai yayi daukewar wucin gadi da yaga Alhaji Danladi, Sa’adatu tana gabatar dashi a matsayin wanta. Mamaki sai ya lullube shi jin Alhaji Danladi

“Babban Yayaa Ina wuni”

Ya bude bakin shi ya rufe ya sake budewa yafi a kirga amman kalma daya ta gagara fitowa saboda mamaki

“Yanzun ina sauri, akwai uzurin daya taso mun…dan Allah a kara kulawa da ita Babban Yayaa, kasan kanwar taka ba kalar yara bace ba. Ke Sa’adatu ga wannan saiki bashi ya saka kati”

Ya karasa yana lalubawa gefenshi ya dibo kudi da zasu kai dubu ashirin yana bama Sa’adatu, tana masa murmushi ta karba hadi da yin godiya. Suka kara yin sallama kafin ta rufe masa murfin motar, direba yaja shi suka wuce. Har lokacin Abdallah na tsaye mamaki ya daskarar dashi

“Yayaa muje…”

Sa’adatu ta fadi tana tattara ledojinta tayi cikin gida. Sai dai shi ya kusan shafe wasu mintina biyar din a tsaye kafin ya iya shiga cikin gidan, inda ya samu Sa’adatu tsaye a tsakar gida tana jiran shi

“Amma!”

Ya kira saboda bayajin shi kadai zai iya daukar abinda ya gani

“Wannan tsohon ne ya baki kudi rannan?”

Kai ta daga masa a hankali tana dorawa da

“Aurena yace zaiyi, zai turo manyan shi ayi magana…”

Sa’adatu ta fadi tana turo baki, lokacin ne kuma Abida ta fito daga daki

“Manyan shi? Wanne manya kuma Sa’adatu? Ai ko neman aure za’aje shi yayi tsufan ma da za’ace a tausaya masa ya zauna gida ya wakilta wasu…Amma kinga tsohon da yazo wajen Sa’adatu? Wallahi zai wahala bai haura tamanin ba…tsoho ne Amma”

Sake tura baki gaba Sa’adatu tayi

“Ni ina son shi…babu ruwana da tsufan shi, na gaya masa na taba aure kuma banga yace babu komai…”

Baki bude Abdallah yake kallonta, idan lissafi bai bace masa ba, sau daya hannunshi ya taba sauka akan Sa’adatu da sunan duka, duk kuwa girman laifin da zatayi a gabanshi, yau kuma yana gab da sake saka mata hannu a karo na biyu ko zata dawo hayyacinta.

“Amma…”

Ya kira yana kallon Abida cike da son ta kawo masa dauki kafin ya mari Sa’adatu

“Bana auri yaron ba? Me na tsinta a auren nashi banda tukwicin saki har uku kwana daya da auren…Yayaa wa kake tunanin zai aure ni in ba tsohon ba? Waye zai yadda haka kawai babu laifin da nayi Yaa Tahir yayi mun sakin da yayi mun kwana daya da auren mu? Ko nemo shi akayi don bincike aka tambaye shi kana tunanin za’a yadda?”

Ta karsa maganar hawaye na zubo mata, daga Abdallah har Abida jikinsu yayi wani irin sanyi da maganganunta.

“Zai wahala in samu wanda ba zai duba tabon da Yaa Tahir ya barmun ba ya aureni, kaima ka sani Yayaa…Amma ma ta sani…”

Wannan karin data karasa maganar saita shige daki ta barsu anan tsaye. Dama can soyayya ce ta rufe mata ido, saboda soyayyar ne ta hakura da komai, Tahir ne ya danne duk wani mafarkinta, yasa ta daina ganin komai banda shi, yanzun kuma idanuwanta sun kara budewa, shi ya waska mata mari da takardar saki uku yana farkar da ita daga magagin soyayyar da ta fada. Auren soyayya dai, ko labari akazo anayi tana da na bayarwa, ba zataji kewar komai ba, ta gwada soyayyar, bata da sa’a a cikinta sam. Zuciyarta da kanta da taji wahala na gashi yanzun ta dawo hayyacinta ba? Tana so subi wata hanyar daban, su taru suyi abinda take so, auren hutu, auren kudi, ba ita kadai ba, su kansu su Abidar wahalarsu zata yanke da dukkan alamu.

Kunnenta zata toshe

Idanuwanta zata rufe

Duk wata shawara da zasu bata zata shiga ta kunnen dama ne ta fita ta haggu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.7 / 5. Rating: 6

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tsakaninmu 13Tsakaninmu 15 >>

2 thoughts on “Tsakaninmu 14”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×