Skip to content
Part 25 of 39 in the Series Ummu Hani by Fadimafayau

Satin su biyu kawai da zuwa Zariya Ummu Hani duk ta bi ta rame ta kuma baƙi in ka kalli fuskar ta tayi fayau da ita abin tausayi baka ganin komai sai dogon hancin ta da manyan idanun ta da suka kuma girma sabida kunburin kuka da sukai dan waccan Jarumar Ummu Hani wadda bata kuka ta jima da suma dan kuwa wannan Ummu Hanin ko yaya ta ɗora idanun ta bisa mijin nata hawaye ne ke wanke mata fuska.

Zuciyar ta cike take da tausayin mijin ta in ta ganshi a kwance tamkar gawa zuciyar ta kuma tsinkewa ta ke ji take kamar mafarki ta ke fatan ta ita kam Faruk ɗin ta ya zo ya tashe ta daga wannan mugun baccin da take.

Hajiyar Faruk tana tausayin ɗan ta anma in har zata ɗora idanun ta bisa kan Ummu hani sai taji tausayin yarin yar ya cikata gata karamar yarin ya ga goyo ga kuma jinyar miji, wani zubin kawai kai zuciyar ta nesa ta ke anma in ta ga Ummun zaune gefen gadon Faruk ɗin riƙe da hannun sa sai ta ji tamkar tasa kuka sai dai bata son gwarin gwiwar da yarin yar ta ke dashi ya tafi.

Tana kula kusan tun zuwan su yarin yar bata wani cin abinci yaron da take shayarwa ma tamkar yasan halin da ake ciki ya rage tsotso da kwalafucin dole sai Ummun ce zata ɗauke shi dan yanzu yana yadda da mami din harma da Umar yakan bari ya ɗauke shi.

Furar da Abban Faruk ya kawo ce Mami ta shigo ɗakin rike da ita kanar kullum Ummu ɗin na zaune bakin ta da alamu addu’a ta ke inda hannun ke riƙe da hannun Faruk ɗin aikin ta kenan daga sallah sai wannan zaman sai in nurse ta zo goge wa Faruk jiki ta amsa ta goge masa.

Ummu ta ji Muryar mami ta kirata ɗagowa ta yi a hankula ta ce na’am Mami, ungo nan ki sha Mami ta faɗa tana miƙo mata kwaryar da ke hannun ta, girgiza kai Ummun ta yi a’a na ƙoshi ta faɗa a hankula, bawai shawara ko roƙon ki na ke ba a’a umarni ne kisha kinaji na ko Mami ta faɗa.

Amsar kwaryar tayi ta kafa baki ta hau sha ko kaɗan ta daina jin ɗan ɗano ɗaci ɗaci ma taji furar na mata sai dai ganin hajiya a tsaye yasa ta sha sosai kafin ta aje kwaryar bisa kan ƙaramin firgin da ke gefen ta.

Leƙa kwaryar hajiya ta yi ganin Ummun tasha sosai yadda ko ta yini bata ci komai ba yunwa bazata cutar da ita ba yasa mami ƙin cewa komai kawai ta ɗauki Muhammad suka bar ɗakin.

Wurin sati uku kenan jiki yaƙi daɗi dan har lokacin Faruk baima san inda ya ke ba bare ayi batun fara masa gashin da akewa masu irin lalurar sa wannan yasa Abban Faruk yanke hukuncin fita da ɗan nasa waje dan nema masa magani.

Da Ummu ya ce zasu tafi tunda ita ɗin matar Faruk ce inda ya ce Fatima ta koma gida suga mai hali zai yi sai dai ina Fatima tuburewa ta yi ita dole fa a tafi da ita da kyar Dady ya nuna mata tunda ba’a daura auren ba akwai kuma wadda auren Faruk ɗin ke kanta ita yafi can can ta a tafi da ita.

Dole badan Fatiman ta so ba ta koma gida Kano yayin da akai akai Ummu ta dawo gida ta ɗaibi kaya ta ƙi dan ita tsoron ta da tashin hankalin ta kar ta motsa Faruk ya mutu.

Duk wani shirye shirye an gama shi yau suke shirin ta shi Ummu ta so mai a maida Muhammad Kano duk da bawai har kasan ranta ta so haka ba sai dan kar ta ɗorawa Abban Faruk nauyi anma sai Allah ya dube ta Dadin da kansa ya ce da Muhammad ɗin zasu tafi duk da ranta babu daɗi anma hakan ya mata daɗi, yayin da shi Dady ɗin ya yi hakan ne dan ko hankalin yarin yar ya ɗan kwanta.

Sun sauka lafiya inda aka bawa Faruk Ɗaki kafin likitoci su fara duba shi yayin da su asibitin ba kamar na Zariya ba ne mara lafiya baya bukatar ƴan jinya dole Ummu hani take bin Hajiyar su Faruk zuwa hotel ɗin da suka sauka lokaci lokaci suke zuwa gun Faruk duk da ma yawancin lokacin ta a asibitin ya ke ko da bata ɗakin Faruk ɗin tana harabar asibitin tana kallin patient masu kai kawo.

*****

Matashin saurayin zaune yake yana duba computer ɗin sa kira ya shigo wayar sa hannu yasa ya ɗauki wayar sunan abokin da Abraham ya gani ha tawo bisa kan wayar murmushi ya yi kafin ya ɗaga “what’s up man.” ya faɗa cike da nisha.

Daga ɗayan ɓangaren wanda ya kira ya ce cikin harshen turanci na kira in baka mamaki ne, mamaki kuma Matashin ya faɗa eh yau naga yarin yar zanen da ke ɗakin ka, gyara zama matashin yayi zane na fa ka ce da gaske kake ko wasa ya faɗa shima cikin harshen turan ci.

Allah da gaske nake ɗan kashe ina zuwa minti kaɗan Abraham ya turo masa da pic ɗin da ya ɗauka a airport miƙewa Matashin yayi tabbas ita ce aljanar yarin yar da ya gani ta hanashi sukuni and gashi ya ganta a hoton kamar yarda ya ganta wancan karan a asibitin yara harma da goyon ta yauma ɗin she’s still the same, no way ya faɗa baima san ya faɗa ba.

Calm down Ayatullah ni ba don in tada ma da hankali na kira ba kawai na kira ne in faɗa ma bawai aljana kake so ba tunda naganta, waya ce ma ba aljana ba ce yanzun ma tazo nan ne ta tadamin da hankali Ayatullah ya faɗa a ɗan rikice wanda har sai da Abraham yaso yin dariya.

But she’s with her family banjin tama san da kai ni dama ban kira ka ba ya faɗa kafin ya kashe wayar.

Kasa komawa kan computer din Ayatullah ya yi inda ya miƙe zuwa ɗakin sa inda zanen yarinyar yake tabbas baiyi kuskure ba wurin zayyanawa mai zanen suffar ta ita ɗin ce a hoton da Abraham ya turo ya zama dole in nai me ta inji mai ya sa ta takurawa rayuwa ta ya faɗa kafin ya fi zari keys ɗin motar sa ya bar gidan.

Kai tsaye Hotel din kusa da airport ya nufa tunanin sa ko nan ta sauka sai dai da alamu ba nan ba ne dan akwai abokin karatun sa anan cikin sirri ya bincika masa babu wata bakar fata da suka sauka a dazu a hotel din haka ya baro da zummar gobe zai koma wani dan neman inda suka sauka.

*****

Kusan kwana uku da zuwan su jiki ya fara kyau dan har ya bude idon sa duk da duk kan san su ba wanda take nan lokacin da ya buɗe idon anma an nuna musu a video hakan ba ƙaramin daɗi yayi wa Ummu Hani ba wannan wata ɗayan da Faruk ya yi ba lafiya jin ta take tamkar shekara dubu sabida kunci da rayuwar ta mata.

Tana zaune cikin kayan da ake bata a duk lokacin da zata shiga ɗakin dan gudun karta yaɗa masa cuta kanta na bisa gefen katifar tasa taji Muryar sa tamkar daga sama ya ce Ummu na da hanzari ta ɗago ta ɗora idanun ta bisa nasa inda karaf suka haɗa idanu ya sakar mata murmushi wanda kana kallo na karfin hali ne kasa magana ta yi sai faman kallon sa da take kawai ya yunkura da zummar kamo hannun ta sai dai ina ya kasa ahankula ya ce Ummu riƙe min hannu na ina son jin ɗinmin ki.

Da hanzari ta kalli hannun ta da yake damƙe da nasa a hankali ta ɗago masa hannun nasu da ke a haɗe ya yo kasa da kwar idon sa mamaki ne ya cika shi dan kuwa ko kaɗan har yanzun baima ji motsin hannun ta ya kama nasa ko kuma ɗago hannun nasa da tayi ba, ji yake tamkar ba shi ba, a hankula ya ce wai mai ke damu ne mai likitoci suka ce.

“Ah ba komai sunce kana samun sauki ka dai na yawan magana kaji kaga baka jin daɗi ta faɗa tamkar ta yi kuka, Tom shikenan gimbiyar Faruk ni wallahi da badan wannan ba da kin matso hakan sai ya fimun daɗi ya faɗa yana kallon kirjin sa da ke sanye da wadu wayoyi, murmushi tayi indai ni ce sai ka gaji da ni bari ka samu sauki.

Karamin tsaki ya ja inafa Faruk zai gaji da Ummu wannan ko a mafarki bazai yuwu ba, murmushi kawai ta yi batason yin kuka, ada burin ta ya buɗe idanun sa anma yanzu da yayi magana sai tausayin ta ya cika shi gadai baki ya buɗe tangararas sai dai ina gashi a kwance tamkar gawa itakam batasan wannan wanne irin ciwo bane hankalin ta mai makon ya kwanta saima tashi da ya kuma yi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ummu Hani 24Ummu Hani 26 >>

2 thoughts on “Ummu Hani 25”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×