Skip to content
Part 32 of 39 in the Series Ummu Hani by Fadimafayau

Daurewar da marar tata ta mata ne ya ɗan saki da kyar ta yunkura cike da juriya ta miƙe gami da karasa cikin soron kuma gaida mutanen ta yi sannan ta ce “dan Allah bawan Allah ku taimaka ku kara mana lokaci wata guda bai isa mu samu wani gidan da zamu koma ba koda wata uku ne ku taimaka mudin bamu da gata bamu da inda zamu in lokacin ya cika in har bamu samu wani gun ba maimakon azo ku kuna korar mu, mu kuma muna ganin baku mana adalci ba da zaifi kyau ku sa mana lokacin da ko an samu akasi sai da aka koremun zamuji kwarin gwiwar barin gun gami da cikakken tunanin ai kun bamu lokaci.”

Shiru dattijan su kai kafin dayan ya ce “eh gaskiya ne to matsakar mu dillalai ne bamu da iko da gunnan sai dai adalci guda da zamu muku mu haɗa ku da wanda ya siyan din in yaga zai iya kara muku sai ya kara.” Godiya sosai su Ummu din su kai har ta kulla musu kosai kafin su tafi.

Rayuwa kam ta ma Ummu zafi sosai cikin ta kullum cikin damun ta yake da motsi tunanin kannen ta ya cika ta tsoron ta biyu ne a kullum ta wayi gari yanzu in ta mutu fa wurin haihuwa kamar Umman su ya su Aisha zasuyi in kuma tana raye wanne irin bayani zata yiwa jama’a game da hallacin abinda ta haifa tasani Allah ya sani abin cikin ta na halak ne sai dai anma ai mutane basu san gaibu ba.

Yawan yadda maganar cikin ta ke yawo agari da yadda in ta fita kai markade ko sayen wani abu ake yada mata da magana ya kuma tada mata da hankali tsoro ya kuma cikata wanda shine dalilin da yasa ta fara rama silar haka cikin yadan fara nuna kansa fiye da ada daya bi jikin ta yanzu kam bata da kwanciyar hankali mutuwar Faruk ta jefa ta cikin tashin hankalin da bata taɓa tunanin zata shiga ba.

Tana zaune a dakin su tana tunanin yau wata guda ya rage mai gidan yazo ya tashe su tunda sun samu ya kara musu wata biyu sun gaza samun gun komawa ita ayanzu ma tafi subar unguwar dan abin ya fara yawa ko yan biyu yara sun dena wasa da su da sun fita zaka ji ana ihun Umman su tayi cikin shege.

A’isha ce ta leƙo ɗakin yaya an gama abincin za’a fiddashi mai kikeson a zuba miki girgiza kai tayi a’a na koshi kawai ta ce, Aishah bata ce komai ba ta fi ce Kausar ce ta shigo riƙe da abinci ta zauna kusa da yayar tata kafin ta ce Yaya dan Allah ki daure ki ci abincin kinji kodan abinda ke cikin ki, kuma ko dan kiji kwarin jikin ki kar haihuwa tazo miki alhalin kina cikin yunwa zaki galabaita.

Tsoro ne ya cika Ummu sosai gabanta ke faduwa wato kannen ta sun san tana da ciki kenan wato sunma yadda, tsoro ne ya kuma kamata kardai suma kallon mazinaciya suke mata innalillahi wa’inna ilaihirraji’un ta hau faɗe aranta.

Kausar kamar tasan abin da Ummu din ke tunani ta ce “Kusan tun dawowar ki bayan mutuwarsa nasan kina da ciki maganar da mutane ke ta yadawa ta kuma tabbatar mun sa zargina Su Aisha har yanzu basu yadda ba sun dauki abun kawai sharri ne ake miki dan anga mu marayu ne muna rayuwar mu cikin rufin asiri duda cewar ni nasan ba sharri bane sai dai ban taɓa yadda cewar cikin bana halak bane ki daina damuwa dan Allah yaya Allah yana tare da ke kinji.” ajiyar zuciya Ummu ta yi kawai ba tare da ta ce komai ba ta fara cin abincin.

Fitar Kursum keda wuya ummu ta kai abinci bakin ta tunanin ya fado mata da hanzari ta mike ta fi ce Hajiya na zaune tana gyara wake Ummu ta ce Hajiya ina takardun gadon nan nawa suna daki inji Hajiya yawwa dauko muga Hajiya bata tambayi mai zatayi da su ba ta mike ta dauko.

Dubawa Ummu ta yi kafin ta mikawa hajiya daya ciki ta ce ‘Wannan shine na gidan man da aka bai gama ginawa ba ko ina ganin mu sai da shi kawai mu sayi gurin zama” Inji Ummu.

Amma ayi haka Ummu inji Umman su Salma dake wanki eh Umma gwanda a siyar da mutumin nan ya zo ya tashe mu, kadara bata da anfani in har zamu wulakanta, tom shikenan yanzu ya za’ai wurin siyarwa din da sayen gidan Hajiya ta tambaya.

Eh to da tunani na muje mu samu Kawu Musa ya wuce mana gaba tunda komai da namiji yafi sannan kuma inma ya cucemu akallah bazai cinye duk kudin ba nasan zamu tsira da ko gidan ne sabanin in wani ne cikin dillalan, eh hakan ma shawara ce Allah ya wuce gaba suka ce amin.

Washe gari Ummu ta shirya tsaf dan su tafi gidan kawu sai dai bata jin dadi kwata kwata dole ta haɗa Salma da Kursun suka tafi dan tasan Aisha zata iya masa rashin kunya in ya kawo musu wargi, Su salma sun same shi ba wani ja’inja ya amince zai wuce gaba.

Kasancewar gun a bakin titi basu sha wuya ba ya siyu cikin kudi mai tsoka shi kansa kawu yayi mamakin darajar gurin ya kuma kara yadda yarinyar ta kudance tunda gashi guri daya kawai an siya makudai asatin aka fara meman gida nesa dasu Ummu ta ce a samo dan kam ita bata shirya ci gaba da kwasar bakin ciki ba duda tasan halin mutun wasu sai sun bita ko ina ta koma sub ɓata mata suna.

Gida ne normal na masu rufin asiri daki hudu da bandaki da madafa sai gareshi da karamin tsakar gida da shago cikin sauran kuɗin ta sa aka hade shagon da garejin aka dan shigo da tsakat gida ya tada katon waje aka gyare shi aka zuba kujeru da tebura ya dai zama kamar wani restaurant inda aka sa masa suna Hani’s glee gun ya yi kyau sosai hana gidan ma dai dai misali kowa zai rayu cikin sa musanman wanda baida dogon buri.

Sati guda da siyan gidan suka koma washe garin komawar su suka fara sana’ar su ta girki yanzu kam ba zaman kofar gida sai na gurin nasu kasancewar gidan a bakin titi yake kan kace me sun yi suna suna ciniki sosai dan abincin nasu da dadi ga arha kowa kan iya siya.

Sauran kudin gun da aka siyar miliyan biyar ta rabawa yan uwanta da su hajiya miliyan biyu ta bawa su kawu miliyan hudu su raba aikam sunji dadi sosai haka kuma sunji kunya sosai.

Kamar kullum tana zaune su Aisha na raba abinci ga customers da ke zaune taji marar ta ta kulle ita dai a lissafin ta cikin wata takwas da wasu kwanaki inma yakai tara kadan ne dan haka kullum tunanin ta haihuwa sai wani watan jin da tayi abin da gaske ne yasa ta mike dakyar ta iya shiga gida ta shige can uwar daka ta cige  baki tayi sa’a ba kowa a tsakar gidan Hajiya ce dama kawai take nan Umman su Salma ta fita.

Tun tana daurewa har ta fara kuka kasa kasa ta rike bakin ta sosai dan karma a jiyo kukan ya sa’ar ra guda ba kowa din agidan kuma dakin ta ne na karshe a gidan, azaba kam tasha ta dan har ta fara tsanmanin mutuwa zatai cikin ikon Allah wannan karan azabar hade da abinda ke cikin nata ta tawo sai kuma me kamar an zare mats taji sakayau yayin da ta bi abinda ta haifa da kallo namiji ne kwance cikin jini dan ƙanƙani ne sosai ko motsi bayai hakan bai tsorata ta dan batayi tsanmanin wani abu ta yanke cibiya har lokacin bai ko yi kuka ba tana kokarin daukan sa ciwo ya dawo sabo tsoro ya kamata kodai mutuwa zan nima.

Cikin ikon Allah ta kuma haifo wani mamaki ne ya cika ta dan ita kam bata taɓa zaton biyu bane kodan bata taba zuwa awo ba oho shima din karami ne kamar wancan yadda wancan din bai koka ba haka wannan sai alokacin ta tuna Muhammad yana ta kuka lokacin da Umman su ta haifeshi kuka tasa kodai nawa basu da rai.

Shi kuwa Ayatullah damuwarsa kullum karuwa take duk yabi ya fada abu guda ya hanashi tawowa shine yasan in tawo baisan inda zai ganta ba haka kuma sai ya maimata shekara guda abinda baya fata kwata kwata.

Yadda ya tsara shi ne yana gama exam shi bazai tsaya bikin graduation ba tafiyar sa zaiyi sai dai yau yan uwansa zuwan bazatan da suka masa ya bata masa shiri dole yanaji yana gani ya zauna akai komai dashi kafin su dingumo su dawo Nigeria.

Washegari da sassafe ya shirya ya wuce asibitin yara nan ya fara ganin ta zaton sa zai ganta sai dai me bata nan, yafi sati kwata kwata bai taɓa sa’ar gainin ta ba anma ya kasa gajiyawa kusan yakan aje motar ya shiga unguwannin da ke kusa da abitin ya fara da gwangwazo sai dai hakan ma bai masa ba dan ko mai kama da ita ko wanda yasan sunan ta bai samu ba.

Yau yaje yawon sa ya dawo Alhajin su ya kirawo shi bayan sun gaisa yake tambayar sa a ina zaiyi sanin makamar aikin sa ya ce eh to shi koma ina ne Alhajin ya ce tom shikenan da dai na ce Aminu kano anma da aka ban shawara ance san ka kuma kwarewa sosai Murtala zaifi da exam din ta fito sai kaje ka samu Director din nasu munyi magana da shi

Godiya Ayatullah ya yi ganjn zai mike Alhajin ya ce yawwa sai maga ta biyu wato aure da na ce sai ka kammala komai ka fara aiki to tun dawowar ka  Usman wato kanin Alhajin ke damuna yana son a hadaku aure da Aisha ganin yadda ya takura yasa na amince dan banason yaga dan cikin mu shi kaɗai ne baida arziki shi yasa naki yadda.

Tsoro ne ya kama Ayatullah hankalin sa ya tashi yayin da gaban sa ya hau faduwa aure kuma da Aisha innalillahi wa’inna ilaihirraji’un Umnun fa shikam ita kadai ce tsarin sa haka kuma shi a yanzu ko type din nasa ce ita zuciyar sa ta riga ta ginu da son Ummu gaban sa ne ya kuma faduwa matar wani ce fa Ya Allah ya dafe kai.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ummu Hani 31Ummu Hani 33 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×