Skip to content
Part 7 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Yana son dubata, amma tsegumin da hakan zai janyo yasa ya wuce sama, ruwa ya watsa ya yi alwala sai ya wuce zuwa masallaci sallar la’asar. Sai da ya dawo sallar magrib ya shigo, dakin Latifa ya fara shiga sannan ɗakina. Ina zaune inda na idar da Sallah ina azkar, gabana ya tsuguna, ya kafe ni da mayatattun idanunsa da ke cikin glass ɗinsa na rai da rai, sau daya na dube shi, sai na maida kaina ƙasa gaba ɗaya ya dabuta ni, sannu da zuwa na yi mishi ya yi min ya gida da tambayar ba wata damuwa, har yana ce min “Me yasa ba ki son fita ana fira da ke?

Murmushi kawai na yi mishi, ledar da ya shigo da ita ya miƙo min, “Tashi to ki ci”
Mikewar na yi, na karbi ledar “Ki ci yanzu tunda zafi.” Ban ƙi ta tashi ba, budewa na yi gasashshen naman rago ne me zafi.

Na sa hannu na soma ci, dagowa nayi na dube shi na ga ni yake kallo, maida kai na yi na ce, “Dan Allah ina son zuwa dalilin.” Ban yi tunanin zai yi saurin amincewa ba, sai na ji ya ce “Ki shirya gobe, sai in fita da ke.” Na ce “Na gode daga nan ina son miƙa ɗinkin da ka kawo mana.”

Ya ce, “0k.” Ya miƙe tare da ce min sai da safe, dan na ce ba zan fita ba barci nake ji, dan ni dai na tsani wannan zaman da ake yi na tsurku da faɗa wa juna magana a fakaice. Yana fita ledar da ya kawo mana na dauko, ɓacin ran da na shiga yasa ko tunanin dauko ta ban yi ba, Atamfofi ne super guda biyu, sai shadda daya less daya.
Zura musu ido nayi ina tuna kuɗaɗen da aka yi wa ta’adi kafin a mallake su.

A dakin Halima da ya shiga daru suka kwasa, dan sun shirya ita da Latifa duk wadda ya shiga ɗakinta ta zage ta nuna mishi ɓacin ranta, kan yasa doka kan girki, ga shi Basma ta taka dokar ta ƙi yi, kuma bai yi komai a kai ba.

Latifar dai da ya shiga nata dakin, bata yi maganar ba, sai ma kwarkwasa da ta yi ta mishi, dan ɗaukar hankalinsa. Halima dai ta kira shi mara adalci, kuma kalmar ta taɓa shi, sun yi baran baran ya ajiye mata nata naman ya fita.

Ya kai ma Basma hada na gwaggonta, itam ma fushi take da shi, dan yasa ta ta shiga kitchen, dole tayi musu abinci wanda ta cika ma yaji, saboda yunwa dole gwaggonta ta ci, tana kwance kirji ya dame ta,
Basma ta ci naman ta koshi ta ɗora fresh yogurt, Gwoggonta dai fresh yougourt din kawai ta iya sha, ta koma ta kwanta, tana kallon Basma na shirin zuwa turaka, ta ja mata ƙofar ta wuce. Latifa ce kaɗai a falo wai kallo take, tana ganin Basma ta haura sama, ita ma ta kashe komai ta wuce ɗakinta, cike da kishi.

Wanka ta samu Ogan nayi, dan haka wuri ta nema ta kwanta, ya fito yana share ruwa a kansa, har ya gama shirin kwanciyarsa tana kallonsa, ya zo ya raba ta ya kwanta.
Ganin ba shi da alamar kulata yasa ta mirgina ta haɗa jikinta da na shi, kamar jira sai wayarta da ke gefe ta dau ƙara, yi tayi kamar bata ji ba, dan takaicin me kiranta a wannan lokaci da ya kamata.

“Ba ki ji ne?” Ta ji maganarsa, kan tilas ta raba jikinta da nasa ta dauko wayar, Gwoggonta ce tana ɗauka ta ji tana cewa, “Basma ki zo ki kaini asibiti, ƙirjina Basma.”
Sauka ta yi kan gadon, yana tambayarta abin da ya faru, tayi mishi bayani
cikin hanzari ya mike ya saka jallabiyarsa.
Yana tafe tana biye da shi har ɗakinta, inda suka samu Gwoggonta ba yanda take dan ulser da ta taso mata. Da ƙyar ta tashi suka yi mota da ita, sai asibiti.

Cikin gaugawa suka ga likita, ya dubata aka basu magunguna, sai ɗaya da rabi na dare suka dawo gida, Tahir ya ce Basma ta zauna wurinta ta kula da ita.
Da safe ta tashi da sauki, da kansa Tahir ya sanya Indo wacce ashe jiya kwance ta wuni sakamakon zazzaɓi da ya rufe ta. Ta yi ma Gwoggon abin karyawa, ta dan ci ba laifi, ta sha magungunanta sai ta kwanta.

Ya shigo wurina mun gaisa, yake ce min in shirya da wuri, dan haka karfe goma saura na fito cikin kyakykyawar shiga, Indo kawai na yi wa sallama, dakin Halima a rufe yake haka ma na Latifa, Basma na shiga na gaishe da Gwoggonta na shaida mata zan fita.

Wata dalleliyar motarsa muka fita cikinta, muna tafiya ina kallonsa ta gefen ido, dan sosai ya mini kyau cikin wata tsadaddar shaddar da ta kwanta lub a jikinsa, ga hularsa da ke ta sheƙi ya ajiye ta a sha tara. Ƙamshi me daɗi ke fita cikin motar.

Muna tafe shiru kowa da abin da yake sakawa a ransa, har muka isa wani wuri, can cikin rabah road, daga irin galla gallan motocin da ke fake wurin za ka san wurin zuwan masu hannu da shuni ne. Ya faka muka fito, cikin girmamawa da haba haba ma’aikatan wurin suka tarbe mu.

Sai da na zauna ya ce “Idan an kare min, in kira shi.” Gyaran jiki aka yi min, kafin na zauna zaman kunshi da kitso wanda aka yarfa min, ni kaina sai kallon kaina nake.
Tahir ma jin shiru ya kira ni, wai me ake min har yanzu, ba a gama ba?
Na ce “Gyara” tsaki ya ja, “Wane irin gyara ne har la’asar ta kusa?

Na ce “Ka taho an kammala, dama ina shirin kiranka sai ga naka kiran ya shigo”
Yana isowa kudinsu ya biya su, sai muka fito, jikin wurin muka shiga na bayar da dinkunana, sun bada sati guda a zo a karba.

Mun shiga mota, Fadila ƙawar Latifa da ta zo gyaran kai, ta kuma duban motar, Tabbas! mijin Latifa ne. Lallai gayen nan naira na faɗa mishi ƙarya, bayan mata huɗu reras da ya ajiye ina kuma zai kai wannan?

Wayarta ta ciro ta soma kiran Latifa, wadda shigowarta kenan, tun fitar Tahir ta sa kai ta bar gidan, tana ɗauka ta ce, “Wai ke mijinki mata basa isarsa a……
Katseta tayi “Wannan wane irin wulaƙanci ne, ki kira ni kina zagin mijina?

“Maida wuƙar ƙawata, yanzu na gan shi da wata santaleliyar baby, wallahi in ba ku yi da gaske ba, duk sai ta karɓe muku shi, Dan tayi ba karya. “Ki saurara min dan Allah Fadila.” Ta katse ta cikin hasala dan kirjinta har wani ɗagawa yake, dan azabar kishi.

“A ina kika gan shi? Kwantar da murya Fadila tayi ta yi mata kwatance, da gaya mata har yanzu bai tashi motar ba. “Ki ɗaukar min pic din motar Please.” Wata yar shashshekar dariya tayi “Kina ganin kamar zan miki karya? Ina zuwa”
Ɗauka tayi daidai yana ribas sai ta tura mata ta WhatsApp.

Kin tada motar ya yi tsayawa ya yi yana min wani kallo, me ɗauke da ma’anoni ƙwayar idonsa ta canza kala. Hannuna ya kama yana murzawa, kafin ya janyo ni na fada kansa, dankwalina ya zame yana shafa hadadden kitson da aka zauna aka yarfa min.

Mun dade a haka kafin ya cire ni a jikinsa, ya tashi motar muka harba titi.

Daga gate ya ce in sauka zai ga wani abokinsa a layin gaban mu. Ina shiga a harabar gidan na hango Latifa tsaye kamar tana jiran wani, na wuce ta bayan nayi mata sannu, sallar la’asar na fara gabatarwa sai na sauya kayan jikina da doguwar riga mara nauyi, kafin na isa kitchen.

Tuwon shinkafa na fara daurawa, sannan na shiga haɗa miyar gyada, Indo ta shigo tana taya ni, farfesun naman kai na ɗaura karshe, kiran sallar magrib mun kammala, muka shirya komai a dinning Indon na ba ta kai wa gwaggon Basma da megadi.

Daga nan na wuce dakina, nayi sallah ina idarwa sama na wuce, falon Ogan ba laifi, dan bai yi wani datti ba, amma dakin barcin sai a hankali, komai da ya yi amfani da shi yana nan inda ya bari. Na kwashe komai na kintsa wurin na wanki nasa cikin Landry kayan sawar shi masu datti na hada su wuri ɗaya, na cire zanen gadon na canza wani, kafin na share ko’ina na goge na fesa air freshener.

Toilet ne ƙarshe na wanko shi tas. Tunda na dawo na lura matan yanzu sun sa kyashin gyaran dakin megidan, kowacce na kyashin ta gyara wata ta shiga, ni kuma ban ga dalilin da zai sa in ji kyashi ba, daga ba dan wata zan yi ba, zan yi dan mijina ne.
Sanda na fito ana ta sallar isha’i, wanka me kyau na shiga nayi, na zuba turarukan da Aunty Kulu ta bani.

Ina gaban mirror, nima har mamakin yanda na koma nake, rashin zaman lafiya da ake a gidan bai hanani yin kyau kamar ka sure ni ka gudu. Ina bukatar mijina, dan haka bani da bukatar doguwar firar da ake a falo, turarukan da Aunty Kulu ta faɗa min sai za ni turaka zan yi amfani da su, dan muddin namiji ya shaƙe su, ba zai kara zama lafiya ba, gaba ɗaya zai sukurkuce.

Na dauko na goggoga na sanya wasu riga da wando masu masifar kyau da muka saya a Saudiyya, sun kama ni daidai jikina, na yane kaina da gyalensu,
takalmi na zura na fito falon.

Duk kan su sun fito har Basma, sun bi ni da kallon kishi, an hau dinning da alama Ogan ake jira, jin taku daga sama yasa ni kai idona, shi din ne shirt yasa da gajeren wando, idanuwanmu suka shiga na juna, nayi saurin janye nawa.

Yau tsakanin Latifa da mutumniyarta Halima yar harara ce, Halima take banka ma Latifa, dan ta gane shigo shigo tayi mata. Ita kuma Latifa ba nan tunaninta yake ba, hankalinta tashe yake kuma ya rabu biyu, shin wadda Fadila ta ce ta gani da Tahir tana zargin Ummulkhairi ce, koko wata daban?

Shiyasa ta kasa zama tayo waje dan ta ga shigowarsu, amma sai Ummulkhairi ta gani ita kadai ta shigo, idan kuma wata daban Tahir ke nema wace ce ita?
Kafin ta shigo gidan Basma take hange za ta zame mata matsala, sai da ta shigo ta gane bambancin ta da babu a gidan ba shi da yawa.

Halima kuma amfani take da ita, duk abin da ya kamata tayi sai ta ingiza ta ita tayi.
Wannan yarinyar kuma nema take ta zame mata dan hakin da ka raina, kashe kuɗi take dan ta mallaki mutumin nan amma kamar bata yi.

Nasara ɗaya ta samu, ita ce auren Tahir Sodangi, tun kafin ta shigo tayi iya yinta dan nakasa rayuwar yarinyar, wadda tana dab da samun cikar burinta, na mallakar Tahir ya subuce mata ya auro yarinyar. Sai dai ita ta shigo a ta karshe.

Da suna shiri da Halima ita za ta bari da aikin, dan Halima na jin labarin fitar za ta firgice. Tashi nayi na matsa sosai kusa da Ogan na zuba mishi abincin, ya shaki daddaɗan ƙamshin da ke fitowa jikina sai ya lumshe ido.

Ya soma cin abincin, wanda ya yi matuƙar yi mishi daɗi. Matan duka ba wadda v
dadin girkin bai ratsata ba, amma wani kishi ya zo ya tsaya musu a wuya. Basma ce kadai ta ci ta yi nak.

Na miƙe zuwa kitchen ya saci kallona, idon matan biyu na kanshi wani kishi ke taso musu, har na dawo ɗauke da jug, wannan karon ya shafa’a shi da suwaye zagewa ya yi yana aika min kallon tsananin bukatuwar sa a kaina. Isowata ya ankarar da shi inda yake, ya yi saurin saita kansa, sai ya sha mur, ya maida idonsa kan farfesun da yake sha.

Na tsiyaya mishi zobon da na yi sai na ga ya mike, “Gobe idan Allah ya kaimu babban abokina, da muka yi secondary tare, zai kawo mana ziyara shi da matarsa. Tunda muka kare secondary ɗinmu ya tafi turai karatu, tun kuma tafiyarsa bai zo ba dan bayan kare karatunsa aiki suka ba shi a can, dan likita ne. Shekaru biyu da yin aurensa, wanda shi ma anan aka daura sai dai aka tura mishi matar. Cikin satin nan ya dawo, ina so ayi musu tarba ta musamman, abin da duk babu na cefane a duba sai ayi min list.”

Kowaccen mu gyada kai tayi, dubana ya yi “Ki kawo min abin nan sama, zan kwanta mura ke damuna.” Ya ture kujera ya wuce, matan suka bi shi da kallo galala, yaushe ya fara barci karfe tara? Lallai yarinyar nan ta zo da sabon salo. Ɗaukar jug din nayi na bi bayansa, ina murɗa ƙofar na ji an janyo ni, zan fasa ƙara ya haɗe bakina da na shi, ajiyar zuciya me ƙarfi na sauke. Ya jani zuwa kujera, sai mutsu mutsu nake na ce “Ka bari in zuba maka.”

Wani malalacin murmushi ya saki, “Yarinya kenan, ni na ce miki na taɓa shan wannan abin.” Ya daɗe yana jagwalgwala ni, ina maƙale da shi, amma ina mishi korafin ban yi isha’i ba. Da ƙyar na samu ya sake ni, zan fita ya ce dawo ki yi anan. da mamaki nake dubansa, amma dai ban yi magana ba, na shiga na dauro alwala, ina fitowa zane da hijab na samu a bakin gado. Bata fuska nayi, ko ya gane ba zan ɗauka ba ya ce “Ba na kowa bane, imma tunaninki kenan, ke ce ta farko da za ki yi amfani da su.” ɗauka nayi ina jin wani dan kishi kishi na taso min.”

Inda sallayar ke shimfide na isa na kabbara, da na idar da sallar addu’a nayi sai na miƙe, zan zare hijab ɗin na dubi inda yake kwance, ya yi daidai a gadon daga shi sai guntun farin wando. Na dubi kirjinsa da gashi ya kwanta sai na ji tsigar jikina na tashi, sunkuyar da kaina na yi.

“Zan je ɗaki in sa rigar barci.” Oya malama jan ran ya isa kya sanya tawa.” marairaicewa nayi na ce,”Ban rufe ƙofata ba.” Ya ce dan tsaki ya ja “Minti biyu na ba ki.”

A gurguje na sauko rigar da na tanada dan daren na zura, sai wani magani a wata yar roba, cikin wadanda maman Aunty Laila ta saya mana a Saudiyya na dauko na shanye, na rufe ƙofata. Mun raya wannan dare cike da zunzurutun kauna me tsayawa a rai.

Da safe da wuri na fito, na samar da abin karyawa ga jama’ar gidan, sai na shiga aikin taran bakin Indo na tsaye gefena tana taya ni. Main falo ma tare da ita muka gyara shi na bade shi da ƙamshi me sanyaya rai. Babu wacce ta leƙo taya mu kamar yanda Ogan ya nemi ayi.

Cincin na fara yi wanda zamu tari baƙin da shi. Sai na yi dambun shinkafa, wanda ya ji kayan ciki da kayan lambu. Cake nayi karshe wanda nayi nufin ba bakin idan sun tashi tafiya. 

Ina haɗa coconut milk pudding, Ogan ya leƙo kitchen din. Sosai ya min kyau cikin wani yadi ɗinkin South South.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.7 / 5. Rating: 7

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wa Gari Ya Waya? 6Wa Gari Ya Waya? 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×