Skip to content
Part 1 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Sai da ƙarfe ɗaya muka shiga Kaduna, kayan kwalliyata na ciro na kuma gyara fuskata. Na goggoga turaruka a jikina. Ina nuna ma direba hanya muka isa har gidan, horn direba ya yi, ina niyyar sanar ma shi ba maigadi ya saurara, aka wangale get ɗin, wani wanda ban taɓa gani ba sai a yau, shi ya buɗe, ya kuma iso wurin yana tambayar wurin wa muka zo. Ni na yi mishi bayani, haƙuri ya shiga bani kafin ya soma gaishe ni.

Motar ta kunna kai cikin gidan, Maigadin ya biyo mu da sauri, na fito ina kallon yanda aka ƙara gyara gidan, taɓe baki na yi ƙila sanda zai yi amarya ya yi gyaran. Direba ya shiga fito min da kayana, maigadi ya kira Garba me wanki wanda shi na bari kafin tafiyata Lagos. Kuɗi na ciro babansu Laila ya bani da na je yi mishi sallama, ya ce ba lallai ina da kudin nan ba, in riƙe za su yi min amfani. Nayi ma direba alheri na sallame shi, Maigadi da Garba suka biyo ni da kayana, Knocking nayi a ƙofar main falon, daga ciki aka bada izinin shigowa, Takun ƙwas ƙwas da takalmina ke yi yasa mazauna falon maido hankalinsu inda nake.

Zaune suke a kujerin da suka yi wa falon ƙawanya dukkansu har maigidan. Maigadi da ke bayana ya tambayi inda za a ajiye min kayan, Ƙofar ɗakina na nuna masa, Zama ayi ɗaya daga cikin kujerun, kowace da irin kallon da take min, kafin suka soma min sannu da zuwa, na yi mamakin canzawar su, mun gaisa na gaida maigidan, suka bi ni da kallon ita ɗin ce koko wata aka canzo bayan na miƙe zuwa ɗakina.

Key na fiddo cikin handbag ɗina, na buɗe dakin ina cusa kai mamaki ya rufe ni dan ko ina a gyare yake tsaf yana tashin ƙamshi. Ba alamar an daɗe ba a yi amfani da shi ba. Jakata na ajiye na cire takalmi, na koma kofar daki na shigo da jakunkuna na. Basma ce ta shigo abinci ta miƙo min, na ƙarba tare da godiya cikin wani bala’in mamaki da ya kara rufe ni game da matan na Tahir, Na dai ajiye na yi alwala nayi sallah, da na idar na ji cikina yana bukatar abinci, amma zuciyata bata nutsu in ci wanda aka kawo min ba dan ni dai ina ta mamakin canjin na su.

Wani dambun nama da laila ta sanyo min cikin kayana na ci sai na sha ruwa, canza rigar jikina nayi zuwa wasu riga da wando masu santsi na koma bisa kujera na miƙe ina latsa wayata. Tahir ya shigo, Zaune na tashi ina ƙara gaishe shi ban samu amsawar shi ba illa faɗan da ya lullube ni da shi, Mutum shi da iyalin sa an nuna masa iyakar shi, ana ma shi iko da matarsa.

Shiru na yi ina sauraren shi, zuciya na kawo min wuya, kamar in ba shi amsa sai na kasa, har ya ƙare wai kuma sai yana faɗa min ni zan yi girki yau, komawa na yi na kwanta. Na ce “Gaskiya a gajiye nake ka bar mai girki ta kare girkinta in ya zagayo kaina sai in yi.”

Wani kallon mamaki ya kafe ni da shi, “Saboda me? “Saboda ba yau zan tare da kai ba” ba tare da na dube shi ba na ba shi amsar wata iska ya furzar me bayyanar da takaici sai ya mike ya nufi hanyar fita. “Ki tabbatar kin shiga ɗakina kin gyara girkin ba dole bane, zan zo da takeaway.” Daga haka ya fice.

Ban ko bi shi da kallo ba dan wani ƙullutun bakin ciki da ya tokare ni, wannan ita ce marabar da ta dace in samu a wurin mijina, bayan shafe tsawon watanni biyu bana nan. Na miƙe zan shiga bed room kiran Aunty Kulu ya shigo amaryar kawun Tahir ce wanda ya riƙe shi, na ɗauka da murmushin karfin hali a fuskata, ta ce “Mutanen accan kasar, tun jiya nake neman layin yaki shiga.”

Na ce “Ban canza sim ɗin ba Aunty.” na soma gaisheta, ta yi min fatan Allah yasa an yi karbabbiya. Na ce “Aunty na ga akwatunana, an kuma gyara min ɗakina, ƙamshin da naji yana yi na tabbatar da hannunki a gyaran.” ƴar dariya ta yi.

“Na zo Kaduna, ganin Sodangi yana kadunan saboda karatun shi yasa na taho maki da kayanki, gyara kuma ni na ce idan akwai key ya bayar a gyara maki ɗakin, sai na sa masu aikin gidan malam na nan suka taya ni muka yi gyaran. “Na kuwa gode Aunty, Allah ya ƙara girma.” Ta ce “Da zan tafi bamu haɗu da Sodangi ba, sai idan Malam zai zo zan ba shi key ya zo maki da shi.” Na ce “To Aunty.”

Mun jima muna fira hakan ya mantar da ni damuwar da na shiga daga dawowata. Ina ɗakina ban fito ba, sai bayan an yi sallar isha’i sai ga shi ya shigo. Wai ba zan fito in ci abinci ba? Na ce “Zan fito” Kowace da ledar ta a gabanta, soyayyar taliya ce da kaza, gamawata sai na miƙe, da niyyar in koma ɗaki, dakatar da ni ya yi ya ce “In zauna a yi fira.”

Suna firarsu ina nazarin maganganunsu, ina kuma ta tambayar kaina ko bayan yin amaryar matan suka samu hadin kai haka, ban dai yarda na sanya masu baki ba.

Goma dai dai nayi masu sai da safe na wuce abuna, key na sanya ma ƙofata, na yi shirin kwanciya na kwanta.

Tunda ta bar wurin hankalinsa ya koma kanta, sai dai ganin idon sauran matan na shi yasa ya ci gaba da zama yana aikin shi a system ɗinshi, duk da ba wani gane aikin yake ba, dan kacokan hankalin sa ya koma kanta. Basma ta soma tashi, Halima ce ƙarshe, ganin shigewar su shima ya miƙe, har ya ƙare shirin kwanciya ba Ummulkhairi ba alamar ta, wayarshi ya dauko ya lalubi lambarta a rufe ya ji ta, ya yi wurgi da wayar bisa gado, ya kwanta dafe da goshinsa yana tunanin mafita, dan zuciyarsa na ba shi shawarar ya share ta kawai ya shiga barcinsa. Sai dai wata kuma na zuga shi da kwaɗaita masa matar tasa da kewarta da ya yi.

Ya daɗe yana juyi amma barci ya kasa nasarar sace shi zuciyar shi ke azalzalar a samo mata abinda take muradi. Ganin ba shi da zabi yasa ya mike, silifas ya zura sai ya sauko ƙasa inda ɗakunan matanshi suke, a hankali yake takawa dan gani yake kamar cikin matan nashi wata za ta fito ta gan shi, sanin ba wacce yake bi sai dai ki kawo kanki, amman kuma ya makara dan Basma da Halima mutanen da kishin kwanan da zai yi da Ummulkhairi ya hana su barci, musamman ganin yanda ta canza ta waye ta goge kamar wacce ta shekara ƙasar Turai.

A hankali yake ranƙwashin ƙofarta, gaba dayansu kowace ta leƙo Halima da ke da window ta inda za ta riƙa hango shi ta ɗaga labulan, Basma kuma ƙofarta ta buɗe kaɗan ta fito. Tun yana yi a hankali har ya zage yana bugawa, amma ba alamun za a bude, cikin matuƙar bacin rai ya juya dan komawa wurinshi, A sittin Basma ta faɗa dakinta ta rufo, sai Halima da ta sha gabansa, duk da rashin wadataccen haske bai hana shi gane ta ba, Sun aika ma juna wani bahagon kallo, dan yasan tsayuwarta nan baya nufin alheri, yayinda ita kuma wani bakin kishi ya tokare mata kirji.

Zai ratse ta ya wuce ta sha gabansa ta ce “Lallai wasu matan rako wasu suka yi, ta yamutsa baki. “Adalci kenan? wace macen ka taba bi dakinta, koko sai ita da yake nata abin na gwal ne” Murmushin takaici ya yi “Duk a maganganunki babu karya, wata ko da kanta ta kawo maka sai dai kayi kan dole.”

Daga haka ya ture ta daga bake baken da ta yi masa a hanya ya wuce. Wani uban ihu haɗe da kuka ta fasa, duk wanda ke wurin ya ji sai dai me nauyin barci, Basma da ke lekensu ta saki labulen tana tsaki, da itama ta yi gigin tunkararsa tare zai gasa masu maganar da za ta hana ta runtsawa, gara ma Halimar ita kaɗai yake daure wa tsiyar ta.

In ita ce bata san iya abinda zai mata ba. wata shegiyar kwafa ta yi ta sulale bisa gadonta. Tahir yana wuce Halima saman shi ya hau ya rufe ƙofar, dan yasan wannan bakar maganar da ya yaɓa wa mata bata barinta, zama kawai ya yi ya rasa wane ma irin tunani zai yi.

Ina kwance naji fasa kukan Halima, nasan labarin gizo bai wuce ƙoƙi, sanin zafin kishinta. Maida kaina kawai nayi na kwantar, na rufe idona da ƙarfi a fatan da nake barci ya ɗauke ni.

Ina idar da Sallar asuba duk da gajiyar da nake ciki kitchen na shiga, gudun ƙara wa kaina laifi, dan abinda na wa Tahir a daren jiya ban san hukuncin da zai yanke min ba, ina cikin aikin me masu aiki ta shigo ba Ade ba ce wata baƙuwar fuska ce a gare ni. Ita ta kama min bayan ta gaishe ni da girmamawa, sai da na shirya komai kan dinning, kafin na wuce ɗakina, wanka nayi me kyau na zauna na gyara jikina,

turaruka na musamman da mahaifiyar su Laila ta saya mana na yi amfani da su wanda na san Tahir na shaƙa sai ya sukurkuce.

Saƙon ƙamshin da na aika masu yasa su juyowa, zaune suke matan biyu kan dinning,

sai dai ban san me ya hana su fara ci ba, kowaccensu kamar dole ta amsa gaisuwar da na haɗesu na yi masu, kamar yadda na yi hasashen zaman na su ma kamar dolen ce ta sasu yin shi, Basma na latsa wayarta, Halima ta yi tagumi kawai fuskarta kamar hadari.

Takun saukowar maigidan yasa kowaccen mu gyara zamanta, kallo ɗaya na yi masa na maida kaina ƙasa na sunkuyar, dan yadda na ga ya haɗa fuska kamar gobara.

Maimakon ya zauna wurin karyawar, hanyar fita ya nufa ban san na shagala

wurin bin bayan shi da kallo ba cike da alhinin wannan cin fuska da ya yi min a gaban kishiyoyi, sai da naji tashin shewar matan biyu, wa’anda abinda aka yi min ya yi matukar kayatar da su.

A fakaice na dube su kafin na maida idona kan kayan abincin zubawa nayi na soma ci kamar bani da wata mas’ala, alhali ji nake kamar zuciyata za ta fashe, Basma ta zuba itama ta fara ci, kammalawa ta sai na miƙe zuwa ɗaki inda nayi ta zubar da hawaye tare da ƙudiri kala kala na yanda zan rama abinda Tahir ya yi min.

Cikin kunci na wuni wanda na lura su kuma ɗanyan ganye suke abinda ban san basma da shi ba dan girman kanta ba ya barinta sakin jiki da kowa. Maigidan dai bai kuma shigowa ba har sai da aka yi sallar isha’i, Ina ji matan nashi na tambayar inda ya shiga, ni kam kokowa nake tayi da zuciyata me cewa in share shi saboda wulaƙancin da ya yi min, sai kuma mai rarrashina da cewa auren kenan cike yake da ƙalubale,

hakuri shi ne kawai. Da haka na samu ta rinjayi me min zugar in share shi.

Na fito na karɓi jakar da ya shigo da ita, na ratsa saman shi na ajiye ma shi, sai da na haɗa ma shi ruwan wanka sai na sauko, ban tsaya inda suke ba ɗakina na wuce kamar inyi wanka sai dai na miƙe bisa sopa dan wata kasala da naji ta rufe ni. Hannuna na sa na dafe goshina idanuwana suna lumshe, Muryar Halima na ji a kaina tana shaida min in fito in basu abinci, da to na amsa mata na tashi zaune ina bin bayanta da kallo, tare da jinjina girman tseguminta, miƙewa na yi bakina ɗauke da addu’a, dan faɗuwar gaban da ta sanyo ni gaba dan nayi imani ba tsakani da Allah Halima ta shigo ɗakina tana neman in zo in basu abinci sai dan sha’awar ganin wane irin tozarci Tahir zai min yanzu kuma.

Na fito jikina a mace. Sun hallara sai maigidan ne babu, wanda kafin in kai ga zama ya soma takowa step ɗin benen, cikin jallabiya yake me guntun hannu ƙamshin turarenshi ya cika wurin, ya zauna na zuba ma shi sosai ya ci ya dora da jus ɗin da na haɗa masa wanda na san sosai yake san shi.

Gaban system ɗinshi ya koma ya umurce ni in ɗauko masa phone ɗin sa a daki, ko da na kawo zama kawai na yi ina danna wayata, gyaran murya ya yi wanda yasa kowaccen mu ƙara shiga nutsuwarta. “Idan Allah ya kaimu gobe amaryata za ta tare.” Ko da ban sani ba a tare gabanmu ya faɗi, dan kallon da kowaccen mu ta yi saurin aika masa. Ba kuma wacce ta furta komai illa Halima da ta yi saurin miƙewa ta wuce zuwa ɗakinta.

Basma ma bata ɓata lokaci ba ta bi bayanta ni na yi saura a wurin, goma na bugawa kamar jiya na miƙe sai na nufi ɗakina. Yana ganin ɓacewarta ya janyo wayarshi, Amarya Latifa ya kira, Bugu guda tayi picking tare da fara masa salo da gwalangwaso, sai da ya gama saurarenta, ya ce “Idan Allah ya kaimu gobe za ki tare.”

Farin ciki tare da faɗuwar gaba suka ziyarce ta a lokaci guda, ga koshi ga kwanan yunwa, jin shirunta ya yawaita ya ce “Ba ki ji na in kashe wayata? Ta yi saurin daidaita kanta, Ina ji Darling, na gode sai dai… Sai dai me sarkin complain?

“Kayan ɗakina ban gama biyan me kayan ba.” “To yanzu ya kike so ayi? “Ka taimaka min darling.” dan guntun tsaki ya ja “Ba abinda zan baki, duk kuɗaɗen da nake baki me kike da su? idan kuma ba za ki tare ba Allah ya bamu alheri.”

Kit ya kashe wayar ta cire ta a kunnenta, jikinta sai tsiyayar gumi yake ta kira shi ya ki ɗagawa ta san ba zai daga ba. Sai ta yi mashi text ta ba shi hakuri da cewa za ta taren.

Miƙewa tayi ta yayumi mayafi sai ta bar gidan makota ta shiga wurin kawarta, sai dai maman kawar ta shaida mata bata nan ta tambayi yaushe za ta dawo ta ce bata sani ba.

Ta yi mata sallama ta koma gida. ɗakinta ta shiga ta rarumo wayarta ƙawar tata ta kira sai dai har ta katse ba a ɗaga ba, sai da ta yi kira shida aka daga cikin masifa ta ce, “Dan ubanki ina ta kira kin ki ɗagawa dan baƙin wulaƙanci.” Cikin wata irin murya ta ce “Da kika ga ban ɗaga ba da kin ƙyaleni ƙawata.”

Mugun tsaki ta ja “Wallahi dan b…” Daga can ta katse ta “Ko za ki bari sai gobe,

idan na dawo sai muyi maganar? Cikin ƙaraji Latifa ta ce “Wai kin san cikin masifar da nake?”

“To wallahi ko da wane ƙato kike, ya saurara maki ki saurari matsalata, yanzu Tahir ya kira ni, ya ce “Gobe in tare kin san shi kuma kaifi ɗaya ne, ni kuma ban da komai, abinda zan karya da shi da safe ma bani da shi.” Daga can ɓangaren ƙawar ta ce,

“To da kika rasa komai buƙata bata biya ba, ga shi yau da bakinsa ya ce ki tare, ai komai ya zo da sauƙi ki bari in dawo da safe.”

Tsaki Latifa ta ja “Wai wane jarababben kike tare da shi, da ba za ki dawo yanzu ba?” Dan murmushi me sauti tayi “Ki dai yi hakuri zuwa safiya ƙawata.” Kan dole suka ajiye waya ba dan latifa ta so ba.

Haka ta kwana kai kawo ta kai gwauro ta kai mari, tana tunanin inda za ta samu kuɗin kayan ɗaki. Gari na wayewa ta dosa kiran wayar kawarta Fadila, sai goma ta diro, shima daga inda ta kwana ko gidansu bata shiga ba a ɗakinta ta same ta sun aika ma juna kallo, Latifa duk ta yi wani iri dan zullumi da fargaba da ta kwana ciki, Fadila kuma cikin kwalliya take ta wani dakakken less sai tashin ƙamshi take.

Bakin katifar dake yashe tsakar ɗakin ta zauna “Wai meye haka kika bi duk kika tashi hankalinki. ki zauna muyi shawara” Latifa ta dofana ta zauna “Ya ba zan tashi  ankalina ba, cikin kishiyoyi fa zan shiga bani da ko katifar da zan jefar a ƙasa.”

Akwai zaɓi guda biyu Latifa.”

Fadila ta faɗi tana taunar cingam, “Faɗi muji” Alh Yahya har yanzu bai haƙura da ke ba,  jiya da abokinsa muke tare, na faɗa mishi matsalarki ya ce ki same shi yanzu zuwa azahar kun gama abinda za ku yi, ki je ki zaɓi kayan gadon da suka yi maki” wani kallo Latifa ta yi mata “Mu je zaɓi na biyu.” rafar dubu daya ta ciro cikin jakarta

“Ko in ba ki waɗannan sune gudummuwata muje ki sayi katifa da zannuwan gado,

kayan abinci gidan Tahir ba matsala bane shi ke sayen komai, kinga ba ƙatuwar da za ta ɗaga maki hanci.” Latifa ta sosa ƙeyarta da ke mata ƙaiƙayi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.4 / 5. Rating: 15

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Wa Gari Ya Waya? 2 >>

4 thoughts on “Wa Gari Ya Waya? 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×