Skip to content
Part 10 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Sama ya wuce Halima ta bi shi a baya dan ta samu ya sauko ya daina fushin da yake da ita, ita ke da shi kuma a yau take son tambayar sa kuɗaɗen da za ta yi amfani da su kan tafiyarta gida.

Shiyasa ta danne bala’in da ke cin zuciyarta na fitar da ya yi da Ummulkhairi suka kuma kai dare. Tayi mishi iya abin da za ta yi masa sai ta sauko inda ta samu Basma da Latifa, zama ta yi suna yar firar su da Latifa, “Wai ina labarin kudaden da abokin Sweety ya bamu ranar da suka zo da matarsa?” Latifa ce ke tambayar Halima, wani duba Halima ta mata. “Wane abokin Sweety kuma?”

Dan murmushin kin raina min hankali Latifa ta yi, kuɗaɗen da ya ajiye da za su wuce kin san ko kowa bai gani ba ni na gani kuma ba yarda zan yi ba sai an bani hakkina.”
Cikin hasala Halima ta taso “To ba za a bayar ba.” Nan fa suka kaure ka ce na ce, na fito zan shiga kitchen na wuce su suna tayi, ba su san da zuwan ogan ba sai tsawar da ya daka musu ita ta sa kowaccen su shiga cikin nutsuwarta, ya kuma ce duk wadda ta kuma magana yau sai dai ta kwana gidan su.

Halima ta fara wucewa ɗakinta kafin Latifa ta bi bayanta. Latifa na shiga ɗakinta ta buga tsalle ta faɗa kan katifa, “Ko dai ban samu kuɗin ba na bata mata daren.” ta fadi cikin farin ciki.

Nima na fito na wuce ɗakina ina tunanin wannan rashin zaman lafiya na wannan gida, kamar nan aka fara zaman kishi.
Na daɗe zaune barci bai ɗauke ni ba tunanin farkon haɗuwa ta da Tahir da rayuwata ta baya na gilma min a cikin ido.

Zawarci bai yi ba! Ita ce kalmar da ta subuce a fatar bakina, yayin da na zauna dabas kan wata tabarma da na samu a shimfide a barandar gidan mu. Hannuna na kai kan goshina na share zufar da ta tsatstsafo min, Mahaifiyata da ke fitowa daga kitchen ta dube ni cikin kulawa, “Har kin dawo Ummulkhairi?

“E Amma” na bata amsa ba tare da nayi fara’ar da kowa ya san ni ya san ni ma’abociyar ta ce, “Hala ba ki samo kuɗaɗen naki ba? Ƙara bata rai nayi ina turo baki “Ina fa Amma sai bakar tafiyar da na sha da uwar ranar da na kwaso, Allah daga yau na haƙura da sai da ƙwan.”

Wani kallon mamaki ta bi ni da shi, sai dai kafin ta kai ga magana gwoggo Rabi abokiyar zamanta ta fito daga ɗakinta, “Anya Ummulkhairi, me zai sa ki daina? kina dan samun abun biyan bukatunki na yau da kullum.
Gwoggon ce ta yi maganar na ce “Allah Gwoggo Balarabe me shayin ne dan rainin hankali, sai ya yi ta wahalar da ni. Yasa ni in ta jerangiya bisa hanya. Sun ci gaba da maida zancen, wanda duk lallashi na suke da nuna min alfanun sana’a komai kankantarta. bani da niyyar yarda da cigaba da saida kwan, dan haka miƙewa kawai nayi na wuce daki hijab din da na shigo da shi na sauya zuwa na makaranta, na fito nayi wa su Ummanmu sallama.

“Ba za ki tsaya ki ci abinci ba Ummulkhairi an kusa saukewa? na ɗan yamutsa fuska, “Na yi latti Umma idan na dawo na ci.” Da damuwa a fuskarta ta ce “Shi kenan sai kin dawo.” Na sa kai na bar gidan.

Ƙarfe ɗaya da minti biyar aka tashe mu, sanawiyya nake ina shekarar ƙarshe, maimakon in wuce gida sai na shiga wurin ƙawata Hafsat mijinta shi ke da makarantar, na samu tana sallah dan haka wucewa nayi na dauro alwala na kabbara tawa sallar kusa da ita.

Tana idarwa miƙewa ta yi ta shiga kitchen ɗinta ta fito daidai ina kammala addu’o’ina, ɗauke take da wani tray me faɗi ta dire shi gabana, gaisawa muka yi kafin ta kafe ni da ido, na san me take nufi dan haka sai na shiga buɗe kwanonin ina cewa “Ƙawata Sarkin girki me aka girka mana?

ƴar harara ta bani “Sai ka ce ci take” siririyar dariya na saki”Ina ci mana.” Waina ce shar shar da tayi matukar bada sha’awa a ido, sai kwanon miyar miyar taushe ce da ta ji wadataccen tantaƙwashi, na karshen farfesun yan ciki ne sai kunun aya shi na tsiyaya na sha kafin na zuba waina biyu ta ce ban isa ba sai na kara na kara biyu farfesun ma kadan na zuba da na kammala ci na kara kunun ayan sai na rufe komai na koma kan kujera na miƙe, ba tare da na damu da kallon da Hafsa ke min ba. Ta gaji ta ce “Ƴar rainin wayau ki rasa wa za ki yi wa fulatanci sai ni, komai na kawo maki ki ci sai ki ƙi ci.”

Yar dariya n ayi “Iyakar cikina kenan, wa zan yi wa fillancin ke?” Ta ce “Yawwa Baban Ramlah na neman ki, tun jiya ya bar min sallahu, ya ce in kin shigo in shaida miki.” Ido na buɗe na tashi zaune “Lafiya dai ko? Malam ke nemana, me ya faru? kafadarta ta noƙe “Bai faɗa min ba, amma na san yana hanyar shigowa.”

Sallamar sa muka ji littafin da ke a riƙe a hannunsa yasa na gane daga makaranta shi ma yake, kujera ya samu ya zauna, cikin nutsuwa na gaishe shi, kamar yanda shi ma yake a nutsen. Cikakken ustaz ne wanda jama’a suka shaida tsantseninsa da gudun duniyar sa, a takaice malami ne me matuƙar tsoron Allah an shaide shi kan rashin hulda da mata, ko ni da yake yarda mu zauna har muyi fira saboda na kasance ƙawar Hafsa da bata da wata kawa sama da ita, tun muna yara har girmanmu, shi ɗin malaminmu ne ya koyar da mu muna yammata, lokacin ya dawo karatu daga Misra.

Yin aurensu ba daɗewa ya sayi tafkeken fili ya gina gida hada masallaci da islamiya, a hankali makarantar ke bunƙasa, har ta zama tana daga cikin makarantun da ake ji da su a garin namu Dutsinma, saboda koyarwarta. Gama gaisawar mu ya ce “Hafsa ta fada miki sakona? Kai na daga mishi tare da cewa “E”

Ya ce “Yawwa dama muna neman malami ne, da zai riƙe mana aji biyu na ɗaliban safe, shi ne na ce bari in tuntube ki ko za ki yi.” Wani farin ciki na ji ya lullube ni, ƙara nutsuwa na yi “Zan yi malam” ya ce “Yawwa daga yau muna Laraba idan Allah ya kaimu Asabar sai ki fara.”

Na ce “Allah ya kaimu malam na gode.” Tashi ya yi ya wuce dakinsa, Hafsat ta bi bayan sa, zuwa can sai gata ta same ni tsaye cikin shirin tafiya “Har za ki yi me?
Ta tambaye ni “Wucewa zan yi Hafsa, ke ko ai na daɗe Umma tana can tana zuba ido ta ga ta inda zan ɓullo.” Muka yi murmushi ta rako ni nan nake bata labarin shawarar da na yanke ta daina saida ƙwai, na kara da cewa, “Kina jin mu da malam?
ta ce “Na ji kin zama Malama, Allah yasa daina saidawar shi ya fi alheri.” Na ce “Amin.”

Na nufi gida, inda na shaida ma su Ummata koyarwar da na samu, su ma murnar suka ta ya ni dan hukumar Saudiyya ta san da zaman makarantar, dan haka akwai albashi me kauri ga malaman makarantar.

Washegari babu makaranta dan haka sharar tsakar gida nayi kamar yanda na saba, sai na zubo koko na matsa Ummata ta zuba min suga na zauna na sha, gamawata kayan wankin mu ni da Ummata na haɗo na wanke su tas, sannan nayi wanka kwalliya nayi sama sama sai nasa atamfata, farin hijab na saka sai na ɗauki pos ɗi ta, na gaya wa Umma zan karbo kuɗaɗena wurin Balarabe.

Inda na saba tsayawa nan na tsaya na aika yaro ya min magana da shi, sai ga shi da saurin shi, sai kallona yake na tambaye shi kuɗina, ya buɗe baki zai soma gaya min in yi hakuri in dawo na tsaida shi ta hanyar daga mishi hannu, “Ya isa Balarabe, wannan shi ne zuwana wurinka na ƙarshe, matuƙar baka bani yau ba to ka riƙe na haƙura, ba za ka sake ganina da niyyar zuwa karɓar kuɗi ba.”

Ƙara zuba min ido ya yi, “Na ji amma me zai hana ki bani dama in zo ƙofar gidan ku? kin fi kowa sanin irin son da nake miki, haba wai so ya taɓa zama laifi? Ya ƙarashe maganar yana wani marairaicewa. Taɓe baki nayi “Son ne yasa kake wahalar da ni?
Idan aka kawo maka kwai sai in yi sati kana wahalar da ni, ina famar gantali a hanya.

Ƙara kwantar da murya ya yi “To ya kike so in yi idan na zo gidan ku wannan yayan naki ya hanani ganin ki, in ba hakan nayi ba ta yaya kike gani zan samu in gan ki?
Miyau na haɗiya “Indai wannan ne damuwarka ya kusa tafiya karatu, sai ka zo abin ka.”

Farin ciki ne ya mamaye fuskarsa, “Ki ce Allah? Wani busashshen murmushi na sakar masa “Zan maka karya ne? Hannu yasa a aljihu ya ciro kudade ya kirga sai ya miƙo min, na ga karin dubu biyu kan kuɗina, na dube shi murmushi ya sakar min “Ki sayi hoda” na ce “Na gode.”

Muka rabu ni da shi kowa cike da farin ciki, shi na jin yayana Mustapha zai tafi karatu ya samu ya rika zuwa wurina zance kamar yanda na tsara shi. Ni kuma ina murnar zare zaren da nayi na karbi kuɗaɗena, me kama da ni ma ba sake gani zai ba.
Fara saida ƙwai na ya samo Asali ne bayan mutuwar aurena, akwai yayata sana’ar ta kenan, sai mijinta ya yi sabon gida suka tashi, shi ne ta shawarce ni ko zan cigaba da kai wa costomominta, shi ne fa shi yana ƙyalla ido akaina sai ya ɗafe min shi dole so na yake yi.

Ranar da ya fara zuwa ƙofar gidan mu da sunan ya zo tadi yayana Mustapha ya kore shi, ni kuma ya kwakwkwara min zagi wai ni wawuya ce da ban san kaina ba, kowane tarkace sai ya kwaso jiki ya ce ya zo zance wajena karshen lalacewa hada wani me shayi.

Ban shiga gida ba sai da na biya wani shago na sayi yadikan hijabai kala uku dan su nake fatara, sai takalma su ma kala uku masu sauƙin sakawa, ban shiga gida ba sai da na shiga gidan su Hafsa wurin mahaifiyarta, muka yi fira. Fara koyarwata ya rage min wahalhalu idan aka bani albashi na kan sayi yan kayan bukatuna na mata.

Wata ranar Asabar da ba zai yiwu in mance ta ba cikin tarihin rayuwata, na nufi makaranta cikin sauri dan makarar da na zabga, tun daga get na ɗaga likab dan ajin yammata nake, kuma doka ce ta makarantar su daga likab, saboda kama wani da aka yi cikin matan ya sanya hijab da likab.

Ganin akwai malami ajin mu yasa jikina sanyi kar ya hana ni shiga, cikin sanyin nayi sallama, juyowa ya yi yana dubana baƙon malami ne wanda ban taɓa gani a makarantar ba sai yau, idanuwansa suka yi min kwarjini sai na sunkuyar da kaina.

Daga ina haka sai yanzu ake zuwa makaranta? Muryarsa ta ƙara jefa ni cikin wani yanayi, sai da ya ƙara tambayata na yi ƙarfin halin ba shi amsa da cewa “Daga gida nake”
“Amma kin san kin yi latti ko? Ban yi magana ba sai ma kara sunkuyar da kaina da nayi, “A’a ɗagowa za ki yi ki dubi agogo”
Dole na dubi agogon, “Na yi latti a yi haƙuri” a raunane na faɗa dan yadda duk na bi na muzanta da zuba min ido da ƴan ajin suka yi.
“Shi kenan zan haƙura amma bisa sharaɗi, ni sabon malami ne da zan riƙa ɗaukar ku darasin matanin risala asabar da Lahadi, kun yi girman da ba sai an an riƙa dukan ku ba, dan haka duk wanda ya yi laifi zan mishi tambaya ne kan karatun da a kayi.
Dan haka yanzu kun tsaya wane babi ne?

Na ce “Mun gama babin zakatul fiɗr mun soma babun fil hajji wal umra.
“Da kyau” ya faɗi yana gyaɗa kai, “A yanzu za ki gaya min inda mutanen kasar Sham da Misra da magrib, da juhaifa, da mutanen Iraqi da Yaman suke ɗaura niyyar su?
Ban ko yi gargada ba na jero mishi su, ya sallame ni ya ce in je in zauna.

Sabon malamin nan ya cigaba da ɗaukar mu darasi a ranakun Asabar da Lahadi, sai dai zuwan sa ajin namu sai ya dauki wani sabon salo game da yammatan ajin, basu da wani zance sai na shi, idan ya shigo ajin ya kan rasa nutsuwarsu, surutun da suke barkewa da shi ya kan sa shi fita ya bar musu ajin, wanda su kuma ba haka suke so ba suna yi ne dan ya san da su, dan wai ai ranar da ya fara shigowa lattin da nayi yasa ya yi min tambayoyi kuma tun daga ranar da ya shigo ajin ni ce dai yake wa magana.

Ranar wata Laraba na tashi dalibaina na fito, malam Mas’ud mijin Hafsa na gani zaune da bakon malamin nan, wanda har sai da na ji mamaki dan tunda ya soma koyar da mu, bai taɓa zuwa in ba ranakun Asabar da Lahadi ba.
Na shige su zuwa cikin gidan, shanya na samu tana yi ta tsame hannunta tana min murmushi, “Har kun tashi?
Na daga mata kai sai na shige ɗakinta, mug na gani saman fridge ɗinta dauka nayi na ce “Zobo akayi kenan? saurin cire shi a bakina nayi ina yamutsa fuska, “Ashe ma tsimi ne”.
Karɓa tayi ta shanye “To ya ba ki sha ba? wani kallo na mata “Dalili da me kuwa zan sha, ni ba miji ba ba kwakwkwaran farka ba.”

Dariya muka yi ta ce “Kina tsaye ba ki zauna ba duk satin nan ma sai cigiyar ki nake ba ki shigo ba.

Na ce “Da an tashi gida nake wucewa, yanzu ma sauri nake wanki gare ni, kin san ranar Asabar za mu tafi suna Katsina na Aunty Rahma.” Baki ta rike”An ko yi haka, amma ya kamata ki fitar da miji mu kuma sai mu sha biki zaman ya isa haka.” Na ce “Sai ki taya ni addu’a, dan duk masu zuwan ban gane kansu ba.”

Yar dariya ta yi “Dama mazan kawuna ne da su?” Muka yi dariya.

Jin gyaran muryar malam ya sa mu shiga nutsuwarmu, sallama ya yi sai ya shigo na gaishe shi ya ce “Sai sauri nake in shigo kar ki fito, son ki ake Ummulkhairi, shi ne aka biyo ta hannuna.” Shiru na yi ina sauraren sa. Ya cigaba “Aikin hajji muka yi ni da shi mun shaku matuka, a Kaduna yake zaune duk da yake haifaffen ƙanƙara ne, zai zo ku daidaita, ya damu in nema mishi izni a gidan ku.”

Ba tare da na ɗago ba na ce “Allah ya kawo shi” Ya ce “Amin mutumin kirki ne abokin nawa, matansa biyu sai dai bai taba haihuwa ba.” Saurin haɗa ido muka yi da Hafsa, “Mata biyu kuma Hafsa ta fadi cikin damuwa. Ni kuma na ce “Tsoho ne kenan abokin naka malam? Dan murmushi ya yi “Wa ya ce miki tsoho ne? idan ya zo za ki gan shi.”

Ya fadi yana ficewa daga dakin. Dariya muka yi tayi ni da Hafsa dan shiririta muka ɗauki abin, wace ila ni kam ta kai ni auren me mata biyu? Hafsa ma haka ta ce.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 10

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wa Gari Ya Waya? 9Wa Gari Ya Waya 11 >>

1 thought on “Wa Gari Ya Waya? 10”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×