Skip to content
Part 9 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Tahir wanda ke kwance bisa gadonsa, idonsa yana kallon sama ya tada kai da hannayensa, a zahiri za kayi tunanin kyakykyawan rufin dakin nasa yake kallo, amma a baɗini tunani me zurfi ya faɗa. Matan da ya tara, kowacce da irin matsalarta, saboda rashin dace da samun me aikin da ta iya girki, yasa shi saka dokar kin amincewa da ƴan aiki su girka abincin da zai ci.

To matan nasa ma, Basma da Latifa sai godiya, abincin suka kwabo maka shi, sai dai ka ci kar ka mutu, Ummulkhairi da Halima ne kaɗai ya dace ta wannan fannin. Halima tunda ya auro Basma ta ga ta zo da me aiki, a rashin dabara irin nata sai ta watsar, ta bar yi ita ma. Idan ya nemi ta yi masa wanda zai ci sai ta ƙi, idan ya nemi hukuntata sai ta ce dan ita ba diyar masu kudi ba ce shi yasa. Dan da za a kawo Basma ta taho da me yi mata aiki, yawan gutsiri tsoma daga Halima yasa dole ya tattara me aikin Basma ya sallame ta, yasa a ka kawo ta gida duka, Halima mace me matuƙar tsafta da gyara, shi ma zuwan Basma kasantuwar ta mace me dan banzan ganin kyashi ta watsar da ko kauda tsinke a cikin gidan.

Cikinsa da ke kuka ya dawo da shi hayyacin sa, ba shi da zaɓi, dole miƙewa ya yi, dan ko abincin rana bai ci ba. Makaranta ya shiga da ya tashi ya tafi duba harkokinsa, flaks din da ake zuba mishi black tea ya ɗauko ya tsiyaya. Cake din da Ummulkhairi ta kawo masa ya dauko ya hada yana sha, ya kusa kammalawa Latifa ta fado dakin, kallo ɗaya ya yi mata ya maida kansa ya cigaba da abin da yake, duk da uban kishin da ta ji, ganin yana cin cake din nan, haka nan ta jure, tana ta mishi kwarkwasa har ya gama duk abin da zai yi suka kwanta. Bayan me aukuwa ta auku, Latifa har ta shiga barci, sai minsharinta ke tashi a dakin, dubanta kawai ya yi ya ja tsaki, jin sabon al’amarin da ya bakunce shi yasa shi miƙewa, wanka ya yo ya dawo ya kwanta, sai dai ina, al’amarin da ɗa gaba yake, duka ya ɗaɗa mata wadda ta yi ɗaiɗai kamar wadda za a yanka, zafin dukan yasa ta farkawa duk da nauyin barcin ta. “Sweety lafiya? ta fada tana mutsutstsuke ido, ƙara tamke fuskarsa ya yi, “Me kika sa a gabanki? ya haddasa min ƙaiƙayin gaba da zafi”. Faduwar gaba ta ji, tare da saurin watstsakewa “Ni kam me zan sa? Ni ban sa komai ba” Shiru ya mata yana jin al’amarin na ci gaba, sun kai wani lokaci tana rantse rantsen ita bata saka komai ba. Gajiya ya yi ya bata wuri, alwala ya dauro ya shiga sallah, tun tana sa ran zai gama har barci ya sace ta, cushion ya koma ya kwanta.

Yana dawowa sallar asuba Dr Muhammad ya kira, ya shaida mishi abin da ya same shi, ya ce ya same shi gida. Har ya gama shirin sa ya fita Latifa na barcin ta, haushin ta kuma da yake ji ya hana shi tashin ta, sai da ya zagaye ɗakin matan nasa kafin ya fice, yana tashin motar wayar mahaifin Basma ta shigo, wanda tun jiya yake neman wayar bai samu ba dan a rufe take, bai kula da gaisuwar da Tahir yake masa ba cikin izza ya soma fadin “Wane irin riƙo kake wa ƴata har gwoggonta za ta zo zama da ita a bar ta da yunwa, to ba zan lamunta ba, har Basman zan turo direba ya ɗauko min su.

Dole sai mun yi zama na musamman, na gindaya sharadi kan zamanta.” Shiru Tahir ya masa har ya ƙare maganganunsa ya kashe wayar, ɓacin ransa ne ya nunku kan wanda yake ciki. Ɗora kansa ya yi bisa sitiyari, ya jima kafin ya ba zuciyarsa magana, Ya tashi motar, sai ya bar gidan. Latifa bata tashi ba sai bakwai, rashin ganin Tahir yasa ta shiga neman sa, gane ya bar gidan yasa ta saukowa zuwa ɗakinta, sai da ta kintsa ta shiga kitchen da taimakon Indo ta hada abin karin, suna yi tana bugun cikin Indon dan ta ji yanda Ummulkhairi take haɗa abincinta, da kalolin maggin da take amfani da su, sai dai duk yadda ta kai da bugun cikin ta kasa fahimtar komai, gane ba za ta gane komai ba yasa tilas ta hakura, tana kara ɗaura mummunar manufarta kan Ummulkhairi.

Mun fito mun karya, ni dai na ci abincin ne kawai dan tsoron saba umarnin megidan, wanda na san su ma haka ne. Shigowar kosassun matan su biyu ya samu zuba ido muna kallon su,ba su yi ma kowa magana ba, sai Basma da ta miƙe ta nufe su tana fadin “Anty kune da safiyar nan? Wadda ke gaba ta taɓe baki, sai a sannan kuma na gane ta, matar babanta ce da na taɓa gani a asibiti, “Ba dole mu yi zuwan safiya ba, daga gidan naku an koma zama da yunwa.” gaba dayan mu zuba mata ido muka yi jin zancenta, suka wuce ciki zuwa dakin Basma, sun samu Gwoggon na shan tea, dan daidai da kwan da Latifa ta soya ta ce bata ci, sama sama suka gaisa matar baban ta dubi dakin, “Ya baku haɗa kaya ba? Cikin rashin fahimta Basma ta ce “Wane kaya za ta haɗa ban da na cikin Jakarta?” Fuskantar Basman ta yi “Babanki hada ke ya ce min in zo mishi, dan ba zai lamunci zama da yunwa ba.” “Yunwa kuma? Basma ta tambaya cikin haɗa rai ƙawar Auntyn ta kama haɓa “Ga gida dai har gida, kai ba za ka taba tunanin na ciki zai san wani abu yunwa ba.”

A fakaice Basma ta harare ta, “Ni gidana ba yunwa, duk wanda ya ce ma akwai yunwa karya yake.” Gwaggon ta dauki salati ni ke miki karya Basma sai ta fara fyace hanci “Ni ban ce ba abinci ba, amma matan gidan ba su iya ba, ni kuma ba zan iya ci ba.” ta nufi wurin jakarta ta ɗauka, “Ku mu kama hanya Hajiya Usaina” Antyn ta ce “Basma ki shirya mu wuce dan hada ke mahaifinki ya ce min.” tura baki tayi “Ni ba inda za ni, haka kawai mijina bai min komai ba a ce sai na tafi.” Nan fa suka kada suka raya amma Basma ta kafe, wayarta ta ciro ta kira mahaifin Basma dan shaida mishi abin da kenan, ya nemi a bata wayar, sai ta ruga da gudu ta hau gado tana kuka, tilas ya ce su rabu da ita.

Dan ɓacin rai Tahir bai dawo gidan ba sai yamma likis, ya sha mamakin ganin Basma dan shigowar sa ya yi daidai da fitowar ta kitchen ta dauko ruwa, sun kalli juna kafin ya wuce ta zuwa ɗakinta, sai ga ta “Me kika zauna yi a nan? ba ki bi umarnin mahaifinki ba?” Bata yi magana ba, baƙaƙen maganganu ya gaigaya mata tana ta kuka, a zatan sa ita ta kai karar sa gidansa ana zama da yunwa, har ya karaci maganganun sa ya fita kuka take tayi. Kiran matan nasa ya yi gaba ɗaya, faɗa ya yi da sa musu doka kan kula da girkin gidan da kuma wajabcin ayi me daɗi.

Su fa dama masu kudi dole ana musu alfarma” maganar Halima kenan take fadi ƙasa ƙasa “Me kike cewa? Tahir ya tambaye ta, “A’a cewa nayi daga masu kudi sun zo gidan nan suna yada maganar gidan nan ana zama da yunwa, ka ga ai baka ga laifin ƴar su da ta ɓata ka ba, sai mu da aka raina aka sanya mu riƙa wa ƴar gwal abinci me daɗi.” Glass din idonsa ya zare, “Ni Halima ni kike faɗa wa magana haka kai tsaye irin wadda tayi miki daɗi? Baki ta murguda “Yo ƙarya na yi.” Nan suka shiga sa in sa abin ba ko tsari a gaban mu, Basma da Latifa babu wadda ta tamka sai ni na bada hakuri, wani ashar ta lailayo ta danna idan na kara sa mata baki.

Dan haka tsam na miƙe nayi ɗakina, ganin missed call a wayata yasa na duba Asiya ce, baki na rufe dan na ji kunya, kira nayi tana ɗauka na soma bata hakuri ta ce ba komai, ni da na damu da ke ba ga shi na kira ba, na dafe kai “Dan Allah ki dubi girman sa ki yi min uzuri, kina raina ina ta son kiranki Allah ne yasa sai an yi hakan” ta ce “Shi kenan, ya gidan ya na bar ku? Na ce lafiya lau” mun shiga fira har muna dariya ta ce “Yaushe za ki zo min yini? Na ce sai na tambayi ogan ina za ta gan ni” ta ce “Meye sirrin humrar da kika bani” na ce “Sirrin kenan abin da kika gani” muka yi dariya ta ce “Na yarda ta sirrin ce, ina so a min hanya zan saya” Na ce “Kuma idan kika ga Aunty Kulu za ki dara” ta ce “Kwarai kam dan na ga alamun hakan” muka yi dariya, mun sha fira kafin muka yi sallama, jin hayaniya har lokacin yasa ni bude kofa, Halima ce ke kuka, Tahir yana tsaye yana fadin wallahi yau sai ta bar masa gida, dan wallahi ya gaji da zama da matar da bata ganin girman sa.

Haj Hajara ita ma iyakar karfinta take ba shi hakuri, ganin abin ya ci tura yasa ta kira Kawu Attahiru a waya, shi kuma ya ce ta ba Tahir wayar, dan baya Kaduna ya koma Lagos. Ta waya ya yi mishi magana, tsallake su ya yi ya haura sama, Haj Hajara ta kama ta zuwa ɗakinta, tana kara gaya mata girman miji. Washegari maigidan na fita Halima da Latifa suka take masa baya, sai dai kowacce da inda ta nufa, Latifa unguwar su makeran kakuri gidan su kawarta Fadila tayi wa tsinke.

“Za su haukata ni! Za su haukata ni! Za su haukata ni Fadila” Kalmomin da take ta maimaitawa kenan yayin da ta daga labulan ƙofar ɗakin kawar ta ta, Fadila da ke kwance kan luntsumemiyar katifar da ke yashe tsakar ɗakin nata ta tashi zaune. “Lafiya ƙawata? “Ina fa lafiya, na rasa inda zan tara waɗannan ƴan iskan kishiyoyin ko ogan kansa, ban shiga da niyyar barin kowacce shegiya ba. Amma yi nake kamar ba nayi”. Ta ƙarashe zancan tana fashewa da kuka. “Ki zauna ƙawata mu yi magana, me ya faru? Zaman tayi tana lissafa mata irin matsalolin da take fuskanta. Na rasa yanda zan yi in yi girki ya gamsar da me gidan, in yi a ce ba daɗi, dan sheri har gwoggon waccan shashashar Basman wai ta kasa zama dan ana yin abinci ba ta iya ci, shi kuma ogan ya zo yana mana bala’i. Ke kuma maganin da kika amsar min uban kuɗaɗe, mun kwanta da shi, ya tsare ni sai na faɗa mishi abin da nasa ya haifar mishi da ƙaiƙayin gaba da zafi” Fadila ta zaro ido “Ni ba ta garin nan ba yaƙi ya ci kwartuwa, to ni dai wallahi salin alin duk wanda nasa mawa sai san barka.” Ta ja mummunan tsaki, “Ai duk ke kika ja, muna zaman zaman mu, muna murza rayuwa kika haukace kan gayen nan ke sai kin aure shi.” Latifa ta share idonta ni dai ki bar wannan maganar, mu nemi mafita” Fadila ta gyara zama “Yawwa za mu shiga kasuwa, duk wani littafin girki ki tabbatar kin mallake shi, haka nan daga kin ji kin gani dole ki zage dantse, sannan akwai wani sabon malami a sabon kawo za mu kai mishi ziyara.

Maganin mata kuma ai ba dainawa za ki yi ba” Saurin girgiza kai Latifa tayi “A’a ba yanzu ba tukuna, mutumin nan shu’umi ne, ganewa zai yi” sun jima suna kullawa da kwancewa kafin Latifa ta dubi agogo, “Wucewa zan yi Fadila, sai dai gobe, yau zan yi girkin rana.” Taɓe baki Fadila tayi “Girki dai girki dai! haka kawai ki takura rayuwarki, ban iya zama namiji guda na juya ni.” Miƙewa Latifa ta yi tana daukar gyalenta “Shekaru sun fara ja Fadila, gwara ka yi wa kanka faɗa kayi auren, tun ba a kare yayin ka a bariki ba.”

Wani uban tsalle Fadila ta daka “Wa! wallahi yanzu na fara bariki, ko tatata ban fara ba a bariki rarrafe nake” Latifa ta gyaɗa kai “Shi kenan, muje ki rakani suka fito, sai sannan Latifa ta ga mahaifiyar Fadila sun gaisa suka yi waje. Wani yaro da bai wuce shekaru bakwai ba ya ce “La! Aunty Latifa” diban su suka kai inda yake “Taye ina za ka? maimakon ya maida mata da hausa sai ya amsa mata da yarensu. Sun wuce shima ya ruga cikin gidan su dan fadin ya ga Latifa, dan ƙanwarta ne da ke zaune gidan su tana zawarci, “Ba za ki shiga gidan ku ba? Fadila ta tambayi Latifa, “Sauri nake ba zan shiga ba” Nafef suka tare Latifa ta shiga ita kuma ta juya. Ban samu zuwa karbo dinkunana ba sai da aka kwana takwas, dan na roƙi Tahir zuwa gidan Asiya, da direba muka fita sai da ya fara kai ni na karbo dinkunan wadanda suka yi matuƙar kyau, sai muka karasa gidan Asiyar. Kyakykyawar tarba na samu daga gare ta, sai fira muke kafin daga bisani muka shiga kitchen, girke girke masu kayatarwa muka yi. Da rana da Muhammad zai dawo sai ga su shi da Tahir, sun jima har bayan la’asar da za su fita ya ce in zo mu wuce gida, amma sai Asiya ta shiga rokon sa ya bar ni zuwa dare akwai girkin da za muyi kan dole ya bar ni.

Sai da nayi sallar isha’i ya zo muka taho, bayan Asiya ta faɗa mishi akwai friend ɗinta da ta haihu za ta zo muje suna tare. Tahir ya ce “Za dai ki buɗe wa matata ido ta san gari” dariya tayi ta ce “Ni dai zan zo” ya ce “Sai kin zo.” Yana gaba ina biye da shi muka shiga falon, duka matan suna zaune da alama zaman ganin shigowarmu suke ina riƙe da ƙatuwar ledar dinkunana.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wa Gari Ya Waya? 8Wa Gari Ya Waya? 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×