Skip to content
Part 14 of 30 in the Series Fasaha Haimaniyya by Haiman Raees

WAKAR GARGADI

Assalamu Alaikum

Ya ku ‘yan uwana

Na taho gare ku

Ɗauke da saƙo

*****

Ku ɗan ba ni kunne

Ko kun gane

Rayuwa da daɗi

Abin hakane

*****

Rayuwa bata da tabbas

Za ka samu cikas

In ka yi haƙuri

Za ka wataya

*****

Ka bita a sannu

Arziƙi ka samu

In ka yo garaje

Za ka sha wuya

*****

Idan ka so masoyinka

Baka babu kuka

In ka je ga maƙiyinka

Za ka sha wuya

*****

In ba ki da gashi na wance

Ko cikin kwatance

In kika nace

Kya sha wuya

*****

Abinda ba ruwanka

Kar ka saka kanka

In ka jefa kanka

Ka sha wuya

*****

Aikin da babu lada

Ko kuma al’ada

Kai ma da jinsa

Ai a sha wuya

*****

In ka zamo mai amana

Ko gidan kunama

Ina tabbatar maka

Baka shan wuya

*****

In ka samo mai ha’inci

Ko cin hanci

Ka zam mamugunci

Kuma za ka sha wuya

*****

Ɗan uwa rage buri

Yana toshe nuri

In ka rage buri

Ka fice wuya

*****

Ka zamo me alheri

Ko an maka sharri

In ka yi haƙuri

Ba ka ba wuya

*****

Ni ne dai Jamilu

Ƙanin su Rabilu

Yaya wajen Kabiru

Me son gaskiya

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 8

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fasaha Haimaniyya 13Fasaha Haimaniyya 15 >>

3 thoughts on “Fasaha Haimaniyya 14”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×