Wallafa Littafi

Idan kuna da wani littafi da ku ka rubuta (ko ku ke son rubutawa) kuma ku ke bukatar ku wallafa shi don yadawa ko sayarwa ga al’umma sai ku tuntube mu.

Za mu iya buga muku littafin sannan mu taimaka muku wajen sanyawa a kasuwarmu don ku samu masu saye.

Ana iya sayen littafi a kasuwarmu ta hanyar biyan kudi kai tsaye sannan a sauke littafin kai tsaye a waya ko kuwa komfuta.

Kudin da mutum zai biya don wallafa littafi ya danganci yawan rubutun littafin da irin gyare-gyare da mawallafin ke bukata. Don samun cikakken bayani sai ku tuntube mu ta hanyar cikewa da kuma aiko da wannan fam dake kasa.

Ku yi cikakken bayani game da abinda ku ke bukata.

Za mu aiko muku da amsa cikin dan kankanin lokaci. Kuma in Allah Ya yarda bada bata lokaci ba za mu wallafa muku littafinku.

Sai mun ji daga gare ku.