Skip to content
Part 9 of 30 in the Series Tambaya by Haiman Raees

Wane Irin Malami Ne Ni?

01.

An san malami da tsoron Allah,

An san malami akwai son Allah,

An san malami akwai bin Allah,

Amma ni ko sai na kama shagala.

02.

Tun ina ɗan ƙarami ina tatata, 

Aka kai ni ga Allo don in fafata, 

A can na san ma duka rayuwata, 

Allahu ya sani har na rabauta. 

03.

Na yi karatu tuni har na sauka,

Na yi rubutu kamar na yi hauka,

Na bi malamai kuma nai bauta,

Yanzu na isa dole ne fa na huta.

04.

Ina da ɗalibai ɗari biyu reras, 

A ƙauyen Garun Gabas cankas, 

Na riga nai ƙarfi ba mai ce min as, 

Don haka in na nishaɗu nai linkis. 

05.

Mata guda huɗu ba wai ne ba, 

Ga masallaci gare ni ku duba, 

Gonaki na takwas ku yi duba, 

Kowacce filoti goma ne ɗan baba. 

06.

Bayan nan kuma ina dabbobi ma, 

Shanu da awaki kusan dubu goma, 

Cikinsu har da su kaji ɗan nama, 

Kullum gidana lallai a samu nama.

07.

Kuɗi ko a wajena ka ce attajiri ne, 

Kayan alfarma sai ka ce sarki ne, 

Ƙasaita da taƙama duk ni ne, 

Na ɗauka Ilahu baya sane da ni ne. 

08.

Tsafi dai an ce malami baya yi, 

Amma ni ko kun ga ina yi, 

Tsibbu ko wannan ai kowa na yi, 

Bugun ƙasa gare ni tsohon yayi. 

09.

In mace ta taho biɗar magani, 

In na ga alama mai maiƙo ce, 

To kuwa za na bita sai na lasa, 

In samu in ɗebi rabona Yasin. 

10.

In kuma na ganta mai kyawu ce, 

Sai in bita duk in kalamance, 

In ce zata bani kanta sai a dace, 

In kuma taƙi suciyarta in asirce. 

11.

Ni dai ba boka ba ba malam ba, 

Ba na son raini ko kuma zamba, 

Kuma ni gashi ba wani alheri ba, 

Daɗin duniya ɗai nake ta sharɓa. 

12.

Gashi yau jama’a duk na tsiyace,

Dabbobi gare ni duka sun lalace,

Matana guda huɗu duk sun fece,

Gonakina duka gashi sun ɓalɓance.

13.

Ɗalibai na kuwa ku sani duk basu,

Masu zuwa wurina yau duk basu,

‘ya’yana guda shida duk basu, 

Na bani na shiga uku na ga tasku. 

14.

Ga cuta gare ni ta kama ni, 

Wai aka ce Korona ta kama ni, 

Shi yasa kowa ya guje ni, 

Cikin gida ni kaɗai aka rufe ni. 

15.

Wayyo ni wayyo ni na tuba,

Na rantse da Rabbi ba zan sake ba,

Tsula tsiya aradu ba zan ƙara ba,

Rabbana ka yafe ni don na tuba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tambaya 8Tambaya 10 >>

2 thoughts on “Tambaya 9”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×