Skip to content
Part 2 of 2 in the Series Wane Ne Ni? by Umar bin Ally

Washe garin ranar tun da sassafe kafin ma’aikatan asibitin su fara zuwa na tattara yan kayayyakina da niyyar sulalewa na gudu amma sai nayi tunanin idan na bar nan ina zanje sai kawai nayanke shawarar zama amma zanci gaba da bincikena a sirrince.

Haka naci gaba da zama ina bincikena a hankali na kuma cigaba da bin duk wata hanya da zanbi na tabbatarwa Dr Aminu cewa Hafsat fa gaskiya ce da wannan tunanin nawa kuwa watarana bayan mun hadu da ita na faki idonta na dauke wani USB cable a cikin jakkarta dan na nuna musu nabbatar musu amma cikin rashin sa’a saina manta dashi a aljihuna ba tare da natuna ba ballantana na nuna musu.

Wata rana cikin dabara na tambayi Farida malamar asibiti nace mata ya sunan wannan unguwar da aka tsinceni lokacin da na fara ganin Hafsat batare da wata wata ba kuwa ta fada min ina tashi ban zame ko ina ba sai unguwar.

Ina zuwa sai na nufi wannan shagon mutumin da na tambaya yace min nikadai nazo unguwar amma bisa ga mamaki sai na nemi shagon sama ko kasa na rasa hakan ya kara tabbatar min da cewa komai shiryashi akayi saboda ayi wasa da tunanina.

Sai na maida ganina zuwa ga jerin gidajen nan amma nakasa gane wanne ne wanda muka shiga a ranar natsaya kawai ina kallon gidajen tareda yin dogon tunanin akan zuwanmu saina lura da wani abu guda daya gaba daya gidajen akulle suke da kwado iri daya kana gani kasan andade ba,a koda bude gidajen ba amma kuma ga gida daya nan babu kwado ajikin kofar sa sannan kana ganin gidan kasan tabbas ana rayuwa acikinsa domin kuwa babu kura da yana kamar yadda sauran suke.

Hakan ya tabbatar min cewa tabbas wannan shine gidan da nake nema ba tare da fargabar komai ba kuwa na nufi gidan gadan gadan ina zuwa na bude nashi ga ina shiga kuwa na hau dube dube da bincike bincike amma banga kowa ba ban kuma samu komai ba.

Nan take kuwa na juya da niyyar ficewa daga gidan amma sai naji kamar motsi a cikin dakin amma na duba ko ina banga kowaba nasake juyawa zanfita sai na sake jin wannan motsin juyowar da zanyi kuwa kawai sainaga an turo wata yar karamar kofa ta kasa daga tsakiyar dakin kawai sainaga mutum yafito ta wajen ashe dakin karkashin kasa ne a cikin dakin yana gama fitowa kuwa sainaga ashe wannan mutumin ne da nake nema.

Aikuwa muna hada ido dashi kafin na ankara yakoma ciki yakuma kulle taciki nayi iya bakin kokarin dan naga na bude amma nakasa daganan kawai sai nayi tunanin na nemi hanyar kulleshi aciki aikuwa bantsaya wata wata ba naringa janyo kujeru da abubuwa masu nauyi ina dorawa a daidai kofar daga nan kuma sai nayi tafiyata nabar gurin na tafi nabarshi aciki.

Tunda natafi kuwa ban dawo ba sai bayan kwana biyu inda natabbata koda ban nemi ya bude ba zaibude da kansa aikuwa ina zuwa nafara janye abubuwanda nasaka abakin kofar ina kama kofar kuwa najita abude batareda fargabar komai ba kuwa na zura jiki nashige dakin.

Dakine tamkar wani dakin iko na yan sanda ko ina kaduba jerin wayoyi ne dakuma tarin na’urorin computer a zuciyata nace tabbas wadannan sune ake kira da masu kutsen yanar gizo wato (hackers) shikuwa gogan naka yana nan zaune magashiyan yunwa da kishirwa duk sun galabaitar dashi.

Nantake kuwa na dauko biscuit da ruwa da nataho dashi na tura masa gabansa nantake yadauka yabude yafara ci tamkar wani yunwataccen zaki da yayi Karo da karamar dabba bayan yagama ci ne nadauko wannan USB cable din da nadauka a jakar Hafsat na daure hannunsa ta baya sannan na fara masa tambaya da cewa wanene ni?

Cikin mamaki ya dago kai ya kalleni yace bansanka ba kuma nagaji da zama anan ka tambayeni akan abinda nasani na fada maka kabarni natafi nasake tambayarsa ina Hafsat take yace dani shima tun daga wannan ranar bai sake ganinta ba nace dashi a ina zan sameta.
Cikin damuwa yace dani ai kafini sani idan ma gwadani kakeyi ka kyaleni ni bansan komaiba.

Nace dashi me kake nifi da nafika sanin inda take ya bude baki da kyar yace dani ai nasani kungiyarku daya da ita wannan cable din da ka daure hannuna dashi duk duniya mutum uku ne kadai sukeda shi agurinta akwai daya ga daya ahannunka shikuma dayan yana gurinsa.

Nasake shiga rudani na matsa kusa dashi cikin alamum rikicewa nace dashi nifa bana iya tunawa da komai inaso kaimin bayanin abinda kake nufi wannan cable din ba nawa bane shine dai na wajen Hafsat ina bukatar karin bayani sai yasake kallona yace to tabbas akanka aka gwada kuma da alama anyi nasara.

Sai ya fara da da bani labari cewa akwai wani programmer da ba wanda yasan wanene shi kokuma yasan sunansa sunan da aka sanshi dashi kawai shine Red dragon wanda ya shahara a duniyar dark web dandaline haramtacce da ake saida kayan laifi yana kirkirar software da ake amfani dasu wajen hacking sannan ya sayar dasu a dark web ya shahara awannan bangaren wata rana yayi tallan sabuwar software dinsa wacce da zarar anyi amfani da ita ga dan adam to za,a iya connecting kwakwalwarsa da computer kwakwalwarsa zata zama tamkar hard drive na computer ta yadda za’a iya goge komai nacikinta sannan za’a iya saka masa duk wani tunanin da ba nasaba ko wani ilimi ko bayanai kuma yadauka amatsayin nasa kuma agogesu alokacinda akeso tamkar wani hard drive.

Wannan software da yayi tallanta yayi matukar jan hankalin mutanen duniya da suke amfani da wannan haramtaccen shafi na dark web da yawa sun nuna bukatar su ga wannan software inda suka zuba manyan kudade akan asayar musu wasu kuma suka fara tunanin mallakarta ta karfin tsiya.

Wanda hakan yasa shi ya kara tsananta buyansa ta yada mutum biyu ne kawai sukasan inda yake sune amintattun yaransa wannan cable din da ka daureni dashi shine ya hadashu da hannunsa gaba daya guda uku ne a duniya ya rike guda daya sai kuma wadannan amintattun yaran nasa guda biyu ya basu daddaya.

Hafsat tana daga cikin mutum biyun zata iya yuwuwa kaine mutum na biyun kuma anyi gwajin software ne akanka Domin kuwa ranar da aka kaika asibiti yayi daidai da ranar da ya kaddamar da gwajin wannan software din.

Tazo ta sameni akan cewa zata hadani dashi amma zanyi mata wani aiki shine dalilinda yasa wancen ranar nayi maka bayanin karya kancewa kai kadaine kazo aranar kuma bayan ta tafi bansake ganinta ba kuna tun daga ranar gaba dayansu aka daina jin labaribsu koda kuwa a dark web din.

Nikuwa kaina ya kasa daukar bayanan da yakeyi hakan yasa nabarshi adaure nayi saurin tahowa asibiti dan nayiwa Dr aminu bayani domin shikadaine zai fahimceni yakuma yimin bayanin da nima zan fahimta.

Ina zuwa kuwa offishinsa nawuce kaitsaye ina mai kwalla masa kira tun daga bakin kofa amma abinda na gani yasa nakame kam ko kyakyawan motsi nakasa bakomai nagani ba face irin wannan cable din da akace guda uku ne kawai a duniya a rataye a wuyansa.

Nan take kuwa na fara tunanin kenan Dr Aminu da Hafsat sunsan juna bakinsu daya shiyasa yaki ya tsaya ya saurareni akan maganarta to shine mutum na biyu da aka bawa cable din komadai shine red dragon din?

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wane Ne Ni? 1

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.