Skip to content
Part 1 of 2 in the Series Wane Ne Ni? by Umar bin Ally

Rayuwata ta fara ne a wata safiya mai cike da abin alajabi, rana ce da bazan taba mantawa da ita ba. Na bude idanuwa na ne kawai na ganni a wani daki a kwance kan wani gado na karfe. Firgigit na mike cikin tsoro, a zuciyata ina fadin, “Ina ne kuma nan?”

Zuwa wani dan lokaci sai ga wata mata ta shigo dakin dauke da wani dan faranti da wasu yan karafuna kanana a kai ganina da tayi a zaune yasa ta ajiye farantin ta juya da gudu tana fadin yafarka nikuwa tuni tsoro ya kara lullubeni nakoma daga can kuryar dakin na rakabe na rufe fuskata cikin tsananin tsoro

Jim kadan sai ga wannan matar ta dawo tare da wasu mutanen guda biyu namiji guda daya da ita wacce ta shigo daga farko saikuma wata budurwa ina ganinsu nakara tsorata nafara jada baya ina basu hakuri karsu cutar dani namijin ne ya matso gareni a hankali yana cewa karka damu ba cutar da kai zamuyi ba nan din asibiti ne kuma nidin likita ne. Suna na Dr Aminu wadannan kuma malaman asibiti ne.

Sai a lokacin naji hankalina ya fara kwanciya dasu sannan ya ce na tashi na zauna. Na zauna akan gadon dakin ya zauna akan wata kujera ya fuskanceni ya fara da cewa yau akalla kayi kusan wata guda a wannan asibitin kana cikin halin doguwar suma sakamakon hatsarin mota da kasamu amma abun mamaki tsahon wannan lokacin babu wani dan uwanka ko aboki koma wani da yanuna yasanka amma Alhamdulillah tunda yanzu kafarka sai muji komai daga bakinka.

Da farko ina so ka fada mana sunanka dan shigarwa a cikin file dinka da aka bude yafada adaidai lokacinda ya daura alkalamin rubutunsa akan takarda yana jiran nafada masa kawai ya rubuta nikuma adaidai lokacin hankalina yakara tashi mamaki da tsoro suka nunku azuciya ta bakomai ne yasa hakan ba sai jina da nayi nakasa tuna sunana zuwa wasu yan dakiku sai yadago kai yakara tambayata yaya sunanka bude baki nayi nace dashi bansani ba.

Baiwami nuna alamun mamakiba sosai yasake tambayata awane gari kake nanma dai bantuna ba yaringa yimin tambayoyi dai akan kaina amma duk bansani ba kwakwalwata tadawo tamkar farar takarda da babu rubutun komai akanta nakasa tuna koda kaina ko iyayena ballantana kuma gari ko abokai da likitan ya fuskanci halinda nashiga ya mike tsaye yana fadin karka damu ka kwantar da hankalinka ka kara nutsuwa ka hutawa zuwa gobe zamu karasa.

Kashe gari da safe akazo aka daukeni akasaka ni acikin wani irin inji saiga hoton kwakwalwata yafito ajikin wani screen nantake likitan yayi dube dubensa zuwa wani lokaci aka cironi aka mayar dani dakin da nake sai bayan kusan awa biyu sannan litan nan naga yashigo hannunsa rike da wasu takardu dakuma wani bakin abu shima maikama da takarda da wani irin hoto ajikinsa bayan likitan ya karaso gareni sai yazauna dab dani muka fuskanci juna sannan yace dani.

Karka damu da abinda zan fada maka awannan lokacin domin kuwa komai zai koma daidai bawata matsala bace domin ansamu irin wadannan matsalolin harma wadanda sukafi wannan kuma an samu sauki sai ya miko min wannan bakar takardar yace dani wannan hoton kanka ne sakamakon hatsarinda kasamu kabugu akanka sanadin haka ka kamu da wata cuta da ake kira (dementia) a hausa kuma ana kiranta da cutar mantau shine dalilin da yasaka baka tunawa da komai…..

Kafin yagama maganar nayi saurin tarar numfashinsa nace saiyaushe zasu dawo kenan likita kodai shikenan bazan tuna ba likita kodai na haukace ne dan Allah likita ka taimaka min nan take Dr Aminu ya rike hannayena cikin yanayin rarrashi yace dani azahiri tunaninka bawai gogewa sukayi ba gaba sunanan acikin kwakwalwarka amma suna wani bangaren da ba anan yakamata ace sun kasance ba bari nayi maka wani misali.

Sai yadauko na’urar laptop da take agefen sa ya kunna saiga wasu folders kowacce da sunanta wata an rubuta video wata images wata music dadai sauransu yace dani kadauka cewa wannan na,urar shine kwakwalwarka wadanan foldojin kuma sune guraren ajiya dake cikin kwakwalwa wannan folder ta video kadauka itace ma,ajiyar yare sukuma videos din ciki sune yarenka kaga meyasa baka manta da yaren hausa ba saboda yarenka yana cikin folder ma,ajiyar yare saiya bide folder video ya nunamin videos din ciki.

Sannan yashiga folder music ya kwashe wakokin ciki yazuba su acikin folder images sai yace dani wannan folder ta music itace ma,ajiyar tunaninka na baya wakokin ciki kuma sune tunanin naka saimuka daukesu muka sakasu a folder images kaga idan muka shiga zamuga babu komai amma kuma akwaisu meyasa bamu gansu ba saboda basa inda yakamata ace sunanan to kaima kamar haka ne tunaninka yananan awani bangaren na kwakwalwarka.

To yanzu likita akwai yadda za,ayi adawo dasu inda zan iya tunawa dasu sai naga yafito daga cikin foldojin ya danna wani guri da aka ributa search sai ya rubuta sunan waka saigashi tafito sai yace dani ta wannan hanyar za,a doraka akan magunguna wanda sune zasu zama kamar wannan search engine din zasu taimakawa kwakwalwarka wajen searching din tunaninka da ganin sundawo cikin asalin folder da yakamata ace suna ciki haka dai muka gama aka dorani akan magani.

Haka nashafe sati guda amma haryau ban tuna da komai ba to daganan ne sai likitan ya yanke hukuncin mika cigiyata aka dauki hotona aka rarraba gidajen jaridu gidajen TV harma da shafukan sada zumunta aikuwa cikin sa,a kwana biyu dayin hakan nafito bakin asibitin ina dan zazzagawa saiga wata budurwa tanufo gareni cikin tsananin farin ciki.

Tana karasowa batayi wata wata ba kawai sai gani nayi na rungumeni tana kuka bance da ita komai ba na kame kikam tamkar wani sakago zuwa wani lokaci tajanye jikinta daga nawa muka fuskanci juna sannan tace ashe dama kana raye ashe zansake ganinka meyasa baka nemeni ba cikin rawar murya nabude baki nace da ita wacece ke?

Cikin tsananin mamaki ta dubeni sannan tace dani meya sameka haka nima wai baka iya tunawa dani na gyada mata kai alamun eh sannan nakara da cewa koda kaina ma bana tunawa bansan waye ni ba taya zan iya tunawa da wani bata kara cewa komaiba ta saka hannunta acikin jakarda ke rataye a kafadarta tadauko waya tabude nafara nunamin hotuna na tare da ita nantake kuwa farinciki yakama zuciyata kobakomai ansamu wanda yasan waye ni.

Tafara da cewa nidai sunana hafsat kaikuma sunanka ahmad munhadu dakai amakarantar kimiyya da fasaha dake garin nan na sokoto kuna nidin ma yar garin nan ce amma kai daga garin yobe kazo munkasance muna kaunar junanmu dakai harmuka gama makaranta bayan mungama makaranta katafi da alkawarin dawowa amma bansake koda jin labarinka ba nakira number ka sau ba adadi nayi kuka har nagaji amma kullum inata zuba ido akan ganin dawowarka inaji ajikina tabbas watarana zaka dawo gareni.

Sai yau kawai naganka ana tura hotonka a Facebook shine nataho gareka yanzu kazo mutafi gidanmu nasan acikin abokanka na makaranta za,a samu wanda yasan gidanku bantsaya wani tunani ba kawai natashi nabita mukabar harabar asibitin muna fita titi ta tsare dan motar taxi ta fada masa sunan wata unguwa da bazan iya tunawa ba nantake kuwa aka kaimu muna sauka kuwa muka je ga jerin wasu gidaje iri daya sunkai guda ashirin tabude daya daga cikinsu muka shiga tace dani iyayenta basanan nazauna najirasu.

Zama na keda wuya bacci ya daukeni ina tashi kuma naga batanan sannan gidan ba kowa saini kadai naduba ko ina banganta ba nafito kofar gidan na naga wani maishago dake fuakantar gidan namatsa kusa na tambayeshi ko yaga fitar wata daga gidannan cikin mamaki yace dani ai gidajen nan gaba daya ba mutane aciki kuma yaga shigata gidan nikadai nashiga kuma tunda nashiga bawanda yakara shiga ko ya fita.

Nandanan mamaki gami da tsoro suka kama zuciyata jiri naji ya kamani ban ankara ba sai kawai ji nayi nazube kasa sumamme farkawa nayi kawai naga Dr Aminu atsaye gefena nayunkura natashi na zauna dakyar ya dubeni sannan yake tambayata meyasa nafita nabar asibitin batare da sanin kowa ba nakwashe duk labarin abinda yafaru tsakanina da hafsat nafada masa.

Ina magana kawai ya tsira min ido yana kallona bayan nagama yadanyi jim bayan yadanyi dogon nazari akaina sai yacemin wannan matsalar ana kiranta da suna (hallucination) shine zaka ringa ganin abinda azahiri babu shi harma ka iya tabashi ko kajishi dole ne sai ka kwantar da hankalinka kadaina yawan wahalarda kwakwalwarka domin haryanzu kai majinyaci ne kwakwalwarka haryanzu bata gama dawowa daidaiba.

Tun daga ranar nan nasake birkicewa kusan kullum sainaga bakin mutane sunzomin saidaga baya nagane cewa ba gaskiya bane musammam ma hafsat duk da cewa nasan ba gaskiya bace amma nasaki jiki da ita muna zama tare muyi hira har na saba da ita.

Wata rana kawai sainaji ni amatsayin likita duk wani abu na likitanci sai na ji na sani wata rana inji ni ina yaruka kala-kala kamar faransanci wani lokaci har indiyanci da chinan ci sainaji na iya wani lokacin na ji ni nazama engineer komai na lantarki nasani kuma ina iya gyarawa tun abun yana bawa likitoci mamaki har yafara tsoratar dasu wasuma suna ganin kamar ba dan adam ne ni ba nikaina wasu lokutan ina tsoron kaina abubuwanda mutane suke daukar shekaru suna koya ko karanta ni kawai sainaga rana tsaka na iya su batare da ko yadda akeyi nataba gani ba

Wata rana kamar yadda aka saba saiga hafsat tazo gareni mukadauki lokaci mai tsayi muna hira dukda nasan ba azahiri take ba nasaki jiki da ita inata bata labarin abinda ke faruwa dani tadanyimin kalamai na kwantar da hankali bayan mungama haka na rakata har kofar asibitin nadawo nazo zanshiga asibitin kenan sai ga wata malamar asibiti maisuma farida takecewa dani wacece waccan da naganku atare nace mata itace hafsat da nake baku labari tayi dariya tawuce nima nawuce dakina

Bayan nashiga daki nazauna kawai saina tuna da yadda mukayi da farida araina nace kenan hafsat azahiri take tunda har farida taganta cikin cikin sauri nafito da gudu ina nemanta nazagaye ko ina banganta ba ina kokarin dawowa kawai muka hadu muryata tana rawa na tambayeta shin dazu kinga wacce muka fita da ita tace eh me yafaru nace idan dai kinganta to tabbas ba wani maganar hallucination hafsat azahiri take tana wasane kawai da hankalina cikin sauri natafi neman Dr Aminu domin na fada masa.

Koda naje na fada masa basu yadda da abinda na fada musu ba kallona sukeyi tamkar na haukace. Dr Aminu ya yi iya bakin kokarinsa dan ya nuna min cewa wata magani daban kawai tunanina yanunamin Hafsat ce amma fa sam awannan karon na kasa yadda da maganarsa. Na nuna musu kamar na yadda amma a zuciya na gama yanke hukuncin tafiya nemanta dukkanin abubuwanda suka faru na yadda tunanina ne ba zahiri ba amma Hafsat ba makawa gaskiya ce kuma ita ce kadai damata ta gane WANE NE NI.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Wane Ne Ni? 2 >>

4 thoughts on “Wane Ne Ni? 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×