Skip to content

Wani Gida (Gidan Gado) | Babi Na Daya

2
(2)

Bis-millahir-rahmanir-rahim

“Wallahi yau ko kana ji da masifa da bala’i sai an raba gidan nan kowa ya san matsayin.”

Na jiyo muryar matar tana ta shi daga wani ‘katon gida, ya yin da muryarta ko fita bata yi saboda tana in-ina ga kuma masifa tana yi.

Nan na jiyo muryar wani dattijo ya na cewa,

“Oho ke kuma tanan kika ‘bullu? To bari ki ji na rantse da Allah idan har ina da rai ba wan da zai gaji gidan nan.

Idan kuma mutum ya ce zai ja dani wallahi sai na kashe shi na ‘batar da shi a doran ‘kasa.”

Ai kuwa nan ita ma ta dada kara kaifin masifarta da cewa,

“To in banda abinka so nawa kana fadar irin wannan kalmar, kuma idan ka kashe ni kana ganin zaka zauna lafiya ne? To wallahi da sai ka ga sakayya gun Allah.

Kuma wallahi gidan nan sunansa rababbe, wannan gidan gidan gado ne balle ka ce za kai iko dashi, kuma uwata tana da gado a ciki.”

Sai na ga dattijon ya fara kuka yana cewa,

“Yan zu Habiba ni ki ke so ki zaga?”

“Ai ba zancen zagi bane kawai dai gaskiya ce da baka so a fada, kuma ni sai na fada ko zaka kasheni.”

Habiba ta fada ba tare data ji tausayin sa ba ko kadan.

Wata ‘yar tsohuwa na ga ta fito daga wani daki kafin ta ‘karaso inda Habiba take ta rike ta,

Tana cewa,

“Ke Habiba shige ki tafi gidan ki tun da dai wannan gidan mune kuma mi nake da gado ba ke ba.”

Hakan da ta ce ne yasa na gane cewa mahaifiyar Habiba ce.

Nan Habiba ta ce,

“Kinga Iya ki kyaleni dan koda ban karbi na ki ba ai naga Baba shiya mutu a bawa ‘ya’yan sa mana su mora.”

“Tun da dan uwanki ne ai sai ki karba ki sa su din, kuma wallahi bazan kyaleki ba.”

Dattijon ya fada yana buga sandarsa a kasa.

Wata mata naga ta fito daga dakin da dattijon ya ke wajan, kafin ta ce,

“Ke Habiba kiji tsoran Allah, wannan fa ‘kanin uwar ki ne dan da bazan magana ba amma naga rashin mutuncin na ki ya wuce hankali.”

Aikwa nan dattijon ya dada har zuka da cewa,

“Ba mara mutunci ba ce tunda itace tsagera, ki rabu da ita zata san dawa take zancen nine fa Umar ba’a ja dani a zauna lafiya.”

Habiba bata koma ta kan sa ba ta kalli matar sa saude da tai magana, kafin ta ce,

“Kinga Saude ki de na shiga abinda ba ruwan ki a ciki.”

“Na shiga ‘din tun da mijina ake ai dani ake yi.”

Wata kyakykyawar mata naga ta fito daga wani daki dake hanyar soro, wanda shekarunta ba za su huce 45 a duniya ba. Tana zuwa ta jawo Habiba tai hanyar dakinta da ita, yayin da Habiba take cewa

“Ai wallahi Maman Nufaisat da kin barni na ci uban ta.”

Koda suka shiga daki Maman Nufaisat hakuri tai ta bawa Habiba.

Ita kuma Habiba tana cewa,

“Wallahi ku kai shi kara a karba muku hakkin ku.”

Ita kuma Maman Nufaisat tana cewa,

“A’a rabu dashi nuniyar guda nawa take.”

Sallama na ji wata zazza’kar murya ta yi a dai-dai kofar dakin Maman Nufaisat, kafin kuma ta daga labule ta shiga ‘dakin.

“Wow!” Na fada a dai-dai sanda mai wannan zazza’kar muryar ta shigo, wani irin madarar kyau nagani a tare da ita wanda alkalami ba zai iya fada ba amma dai nai karatu ka kissima irin kyau da take da shi.

Komai na baiwa da ubangiji ya ke wa dan adam ya yi mata, domin duk da namijin daya kyallah ido a kanta sai ya ji wani abu, hatta ga ‘yar uwarta mace ma haka kake ji idan tai arba da ita.

Nufaisat kenan, matashiya mai kimanin shekaru 16, Allah yai mata baiwa iri-iri domin tun tana shekara 8 ta sauke alqur’ani mai girma.

Wannan kenan!!!

Ganin Habiba da mamanta a zaune, kuma Habiban da alamar ranta a ‘ba ce yasa, ta dubi maman ta da cewa,

“Mama me ya faru naga kamar Anty Habiba ranta a ‘ba ce ya ke?”

‘Dagowa Mama ta yi ta kalli Nufaisat, nan da nan na ga ta shige daki sumi-sumi, hakan ya tabbatar min da cewa kallo ma idan maman ta yi masu sun san me take nufi.

Nan dai Mama tai ta bawa Anty Habiba hakuri kafin ta tashi ta tafi gidanta.

A can kuwa bangaran Saude da mijinta, ganin Fateema(Maman Nufaisat )ta janye Habiba sunyi dakinta, yasa ta shiga fada masa sukaita zagin Fateema suna ce mata ai ita ce munafukar.

Bude baki dattijo yai da cewa,

“Duk ki rabu dasu za su san ba dani ake wannan ba.”

Cike da zuga Saude ta ci gaba da tunzura mijinta, aikwa ya tunzuru sosai domin ya yiwa kansa alƙawarin ba zai kyale su ba.

Ɓangaran su Nufaisat bayan Anty Habiba ta tafi, nan Maman Nufaisat ta zauna tana tunanin irin halin da ta tsinci ganta ita da ƴaƴanta a gidan.

Nufaisat da ke tsaye akan Mama tana tai mata magana, amma gani da tai Mama ba ta san ma tana yi ba yasa ta ɗan bubbuga ƙafar maman.

A ɗan zabure maman ta juyo saitin inda Nufaisat ta ke, ita kuwa Nufaisat ta zubawa maman ido ganin fuskarta ta chanza alamar damuwa.

“Mama lafiya? Wai me ya faru yau a gidan?”

Nufaisat ta jehowa maman tambayoyin.

Shiru kawai Mama ta yi tana kallonta, cikin muryar tausayi ta ce,

“Mama dan Allah ki faɗan me ya faru?”

A jiyar zuciya Mama ta sauke, kafin ta ce, “hmmm!

Nufaisat kenan, mene ne ma ba zai faruba in dai a gidan gado ne?”

Cikin kalar tausayi Nufaisat ta ce,

“Mama wani abun baba Umar ya yi miki?”

Girgiza kai Mama ta yi da cewa,

“Ba dani akai ba da Habiba Iya akai”

“To Mama mai tai masa?”

Nufaisat ta sake tambayar Mama.

Mama ta sake cewa,

“Tazo ne akan a raba gado a bata na mahaifiyar su, shi ne yai mata cin mutunci ita dani.”

“To Mama ke mene na ki a ciki tunda ba ke ki ka ce a baki gadonba?”

Nufaisat ta sake tambayar mama rai ɓace,domin ita ta tsani ace wani ya ciwa mahaifiyarta mutunci ko waye shi kuwa.

Mama tai murmushi ganin har ran Nufaisat ya ɓaci, kuma dama itan haka take a duk lokacin da taji wani yaci ma mamanta mutunci take ranta zai ɓaci.

Dan haka sai Mama ta ce,

“To in banda abinki Nufaisat kin fa san halin baban na ki.”

Da sauri Nufaisat ta ce,

“Allah ya kiyaye, ni ba babana ba ne, babana ya riga ya rasu.”

“Kul na ƙara jin irin wannan daga bakinki, kina da wanda ya fishi ne?”

Mama ta faɗa tana harararta.

Miƙewa Nufaisat ta yi ya shige daki tana ƙunƙuni.

Koda ta shiga ɗaki kan gado ta faɗa, a ranta tana mai ɗaukar alwashi saita kawo ƙarshen wannan yayan baban nata, saita yi maganin zaluncinsa.

Da wannan alwashin ne bacci yai awan gaba da ita.

Ba ita ta farka ba sai ƙarfe 4:06pm sannan ma Mama ce ta tasheta ta yi sallah, dake ranar juma’a ne ba islamiyya.

Bayan ta idar ne ta share gidan tsaf, kafin taje ta tambayi Mama me za su ci da daddare?

Nan Mama ta bata ragowar 500 ta ce taje ta siyo musu taliya leda ɗaya su dafa.

Karɓa tayi ta sa hijab ta fice, a hanyar dawowarta ne ta haɗu da ‘yar wajan baba Umar (sai suna Saddiqa).

Zagi sai Saddiqa ta shiga surfawa Nufaisat, amma abu ɗaya da bata sani ba Nufaisat bata kula duk wanda ya takaleta faɗa in dai a wajane ba gida ba.

Saida wani mutum ya zo hucewa ya ga ana ta cewa Saddiqa ta bari amma taƙi, dan haka sai kawai ya wanke ta da mari.

Yana cewa,

“Ke saboda rashin mutunci ana cewa ki bari kinƙi, alhalin ma ita bata kulaki ba.”

Aikwa sai saddiqa ta danna wani uban iwu tai gida da gudu.

Tana shiga tunkan ta ƙarasa Suade mahaifiyarta ta fara tambayarta, “lafiya? Waya taɓa ta?”

Saboda tsabar rashin tsoran Allah sai cewa ta yi,

“Ba kawai na zo wucewa bane waccan tsinan niyar Nufaisat ɗin ta kamani da faɗa wai iyayena tsinannu ne, babana wai yaƙi basu gadonsu, shine wani mutum ya mareni.”

Ai kuwa kafin Suade ta ce wani abu Malam Umar da ke ɗaki ya dako tsalle, yana cewa,

“Rabu da mutsiyata zanyi maganinsu, waccan matsiyaciyar uwar tata taji tana faɗa.”

Ita kuwa Mama ba ta san ma wainar da ake toyawa ba saboda tana bene wajan abokiyar zamanta, da ke bazaka taɓa cewa kishiyoyi ba ne saboda suna zaune tamkar ‘yan uwa.

Hayaniya da suka jiyone yasa suka leko ta barandar benan, ganin Malam Umar da matarsa sauna ta faɗa ga Nufaisat a tsaye yasa suka sakko danjin ba’asi.

Nan Amina wato abokiyar zaman Maman Nufaisat, ta tambaya ko lafiya?”

“Wannan ƴar iskar yarinyar nan Nufaisat ce ta ga Saddiqa a waje shine ta shiga zagin mu saboda lalacewa da hali irin na uwarta.”

Umma (sunan da suke kiran abokiyar zaman mamansu da shi.)

Ta ce,

“A’a Saude ki dena faɗar irin waɗannan maganganu akan ƙaramar yarinya, alhalin kin san faɗa ne ya haɗa, kuma da zaki bibiya Saddiqan ita ta takaleta domin Nufaisat bata faɗa saida dalili?”

“Kinga dallah Amina rufama mutane baki, dama kema ai munafukarce, kuma wallahi bari kiji ma na faɗa miki tun farko nifa ba kaunarki nake ba.”

Duk yaran su Mama da Umma sai da sukai gigir saboda kalmar da sukaji a bakin Saude, domin sun san dama ba kaunar tata take ba, amma data bar abinta a ranta da yafi.

Murmushi Umma ta yi duk da bataji daɗin kalmar Suade a kantaba, amma sai ta ce, “Hmmm! To in banda abinki Saude dan ba kya kaunata sai me? Dubun dubatar mutane suna kaunata.”

Daga haka bata bari Saude ko Malam wani ya sake cewa komai ba ta ce subar gun har ƴaƴansu.

Bayan umma ta koma benantane Nufaisat ta shiga, kwance ta samu Umma akan gadonta da wayarta a hannunta.

Tsutsuguggunawa Nufaisat ta yi kafin ta ce,

“Umma dan Allah kiyi haƙuri a kaina an faɗa miki kalmar ƙiyayya, kuma wallahi Umma bani na takaleta ba ita ce.”

Murmushi Umman ta yi, kafin ta ce,

“Ai Nufaisat ba wai saboda ke bane Saude ta ce bata kaunata ba, a’a damacan akwai hakan a raanta damar faɗane kawai bata samuba sai yau.

Kuma Nufaisat nasan wallahi ba ke ce ki ka tsokaneta ba ita ce, amma dake jinin sharrice ai gashi ta tsara abinta.”

Nufaisat ta ce

“To wai Umma me yasa shi Malam ba zai raba gadon nan yaba duk wani magaji ba?”

Kafin Umma ta ce wani abu Nawwara ƴar Umma mai sa’ar Nufaisat, ta ce”to in ban da abinki Nufaisat ba a gabanki magadan gidan suke cewa a basu ba, amma ƙarshansu cin mutunci da tozarci yana cewa zai nakasa mutum.”

Kallon Nawwara dukansu su kai, tabbas abin da ta faɗa haka ya ke.

Nufaisat ta ce,

“Ai wallahi Umma ɗazu baki ga abin da ya yiwa Anty Habiban Iya ba, kawai daga tace ya raba gado yaba kowa.”

Umma ta ce, “Ai dazu Mama take faɗamin yadda a kai”

Nufaisat ta sake ce wa, “Umma na chanja burina.”

“burinki name kuma Nufaisat?”

Umma ta tambayeta.

Nufaisat ta ce,

“Umma akan karatuna na chanza ra’ayi ada ina son na zama doctor ne, amma yanzu na fasa zan zama barister kodan na kawo ƙarshen Malam wallahi.”

Mirmushi Umma ta yi mai cike da farin ciki.

Mama data shigo ɗakin yanzu, ta ce,

“U’um Nufaisat karfa ki cika zurfafawa abu”

“Wallahi Mama bana kaunar zalunci da kuma mai yin zalincin.”

Nufaisat ta faɗa cikin ɓacin rai.

“wahalalliya”

Nawwara ta faɗawa Nufaisat, saboda sun saba cin kai kamar me, amma da sun gama da sun shirya.

Nufaisat ta ce,

“Mtssss kaji shashasha wane yasa dake?”

Harara Nawwara tai mata da cewa,

“Ni kin ganni wallahi ina yin aure bani ba Baba Malam.”

Nufaisat ta ce, “A’a ni bazan gaba dashi ba amma zan maganinsa da zarar na zama cikakkiyar barrister.”

Nawwara ta ce, “Ni wallahi jina nake kamar kafin muyi candy zan aure.”

“Lahhh! Nawwara wai yaushe ki ka zama mara kunya ne?”

Umma ta faɗa tana kallon nawwara.

Take kunya ta lulluɓe nawwara, sim-sim ta fice daga ɗakin.

Dariya Mama ta yi da cewa, “A a da gaskiyarta dan tafi Nufaisat”

Umma ta ce, “A’a fa Mama Nawwara batafi Nufaisat ba, domin Nufaisat tana son yin karatu dan tai taimako, domin ba babana kaɗai za tai magani ba hatta sauran azzaumai masu tauye gadon ƴan uwansu za tai maganinsu.”

Miƙewa Nufaisat ta yi tana cewa,

“Amma Umma kalmar ƙarshe ba dai-dai bane.”

Murmushi Umma ta yi da cewa, “Au wai dan nace babanki? To ƙarya nai?”

“A’a Umma ban ce ba, amma ai ni babana ya daɗe da rasuwa”

Nawwara ta faɗa ya yin da idanunta ya cicciko da hawaye, wai kawai saboda ance babanta.

Dariya sosai su Umma su kai mata, ya yin da ita kuma haushi yasa ta fice ta bar musu ɗakin.

Nan sukaci gaba da hirarsu ta duniya.

*****

“Sannu da dawowa Heesham, ya ake ciki ne yau?”

Wata yar dattijuwar mata ta faɗa, wadda daka ganta kasan tsabar wahalace ta fito mata da tsufa.

Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya halicci Annabi Muhammad da alayansa da sahabbansa da duk wata wata halitta daya halitta.

Saida na gigice ‘ni Zainab’ saboda tsabar tsagwaran tsantsar madarar kyau dana gani a tattare da wannan saurayi mai suna Heesham, Allah ya yi halitta bata wasa ba a tare dashi,  domin duk inda haɗaɗɗan namiji yake to Heesham ya huce hakan ma, ya huce zaton mai zato.

Duk da yana cikin halin rayuwa da matsi da talauci, amma hakan baisa kyansa ya ɓuya ba.

Cikin halin damuwa Heesham, ya ce, “Wallahi Ammi yadda na fita haka na dawo saima wahala dana sha.”

Ya ƙarasa faɗa idansa na ƙoƙarin kawo hawaye.

Ammi ta ce, “Subhanallahi tsarki ya tabbata ga Ubangijin daya haliccemu ya bamu ciki da hanji da nakin da zamu ci, Heesham Allah daya haliccemu yana sane damu yana kuma kallonmu a wannan yanayi.

Amma Heesham abin da nake so da kai kada ka taɓa cire tsammani a tare da kai, Heesham ka dinga tunawa da Allah shi ne mai bayarwa kowane lokaci kuma mai hanawa a kowane lokaci.

Dan haka Heesham kada ka taɓa cirewa kanka rabo daga ubangijinka, domin shi Ubangiji da kowanne irin abu yai maka to jarrabawace yai maka.

Idan Ubangiji ya baka jin daɗi da kwanciyar hankali da lafiya da da duk wani abu na more rayuwa, to wallahi ka sani jarrabawace yai maka ya gani zaka cinye ko baza ka cinye ba.

Haka kuma idan ubangiji ya yika talaka mara lafiya da kwanciyar hankali da kayan more rayuwa,to shimafa jarrabaka ya yi kada ka taɓa cewa wai ai allah ya yiwa wane kai bai maba,a’a kar kace haka a koda yaushe kasance mai yawaita faɗin alhamdulillahi ga ubangijinka.

Amma duk waɗannan abubuwa idan har ka kasan zuciyarka tanada tsarkin imani da yarda da ƙaddarar Allah a duk sanda ya jarrabeka, to wallahi ka dace kuma ka samu babban rabo duniya da lahira”

Tunda Ammi ta fara magana Heesham ya zuba mata ido, duk abin da ammi ta faɗa ya yadda ubangiji ke ƙaddarasu, dan haka.

Ya ce, “insha Allah Ammi koda bayan ranki baza ki taɓa samuna da saɓawa Ubangiji ba, kuma Ammi na yadda da ƙaddara mai kyau ko akasin haka.”

Murmushi kwance akan fuskar Ammi, ya yin da zuciyarta kuma godiya take ga Allah daya bata ɗaya mai tsarkakarkiyar zuciya.

Wannan kenan.

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

2 thoughts on “Wani Gida (Gidan Gado) | Babi Na Daya”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×