Skip to content
Part 8 of 10 in the Series Waye Zabin Munibat? by Husaina B. Abubakar

Bismllahir Rahmanir Rahim

A ranar nayi kuka tamkar numfashi na zai bar gangar jiki na, nayi baƙin ciki mara musaltuwa a daren nan sai naji dama ban faɗa ma sa baki na ba, jingina nayi a jikin bangon ɗakin mu haɗi da kifa kaina tsakankanin cinyoyi na, ina sakin wani wani marayan kuka cikin sarƙewar murya nace” yaushe zan huta ne? yaushe zanyi farin ciki? me yasa Mama ta tafi ta barni? yanzu in Kawu bai yarda dani ba ina zan kama?”

A hankali naji a turo ƙofar ɗakin, cikin sanɗa ta shigo kamar ɓarauniya, daga ɗaya gefen ta tsaya muryar ta kasa-kasa tace” baki ƙwanta ba ne Munni?” Tayi maganar kamar bata san abinda ya faru ba.

Zuciya ta sake tafasa cike da jin haushin ta nace, “Mene ne amfanin ƙwanciyar tawa, tunda ni ba ƴa bace kamar su wannan..” nayi maganar ina nuna mata yaran ta.

Dariya tayi cikin alamun farin ciki tace” kin ɗauka zan zuba miki ido ne haka kawai? Hhhhh maza ki sauya tunanin ki domin ni a tsaye nake ba a zaune ba, tun kan na fara aika ki maganar ta gama shiga jikin sa da jijiyoyin sa, karki manta Shafa’atu suna na a yanzu ina miki maraba lale, domin zaki fara fuskantar waye Kawun naki, hhhhh wai kin ɗauka zan zuba miki ido ki shiga tsakanin uba da ƴaƴan sa baki isa ba kinyi tsararo, Abban su ne su kaɗai ba da kowa ba, ana nuna miki fifiko akan nawa amma yanzu salan wasan zan sauya domin zai fifita nashi ne akan ki tunda kin zaɓi Bara, mamaulaciya kawai..” tayi maganar tana takemin ƙafa da ta ta ƙafar.

Wani irin zafi ne ya ratsa min ƙwanyata cikin zubar da ƙwalla nace” dama bata taɓa ƙin mutun, amma kin fi kowa sani waye mamaulacin amsowa kawai nake amma ban san yanda ake dasu ba, daga rana irin ta yau naga wanda zai sake aika ni yawon maula kuma naje…” har zuciya ta ban so gaya mata haka, nima maganar ce kawai ke fita ba tare dana tauna ta ba.

Dariya tayi kana tace ” ga fili ga mai doki nan to…” tana zuwa nan a zance ta fice  a ɗakin..  Ni kuma na ci gaba da sana’ata.”

Washe gari,  kamar kullum na fito na kama aiki na, tun farar safiya na shirya mata yaran ta tsaf nima na ƙimtsa jiki na, munci mun ƙoshi ‘na sake haɗe ƙwanikan da muka ɓata  na fara wankewa kenan su Anti suka fito cikin sauri ta iso inda nake take cewa” Munibbat har abada baza ji faɗa na ba ko? Nace ki ɗaina aikin nan amma kin ƙi ko? wai yaushe zaki ɗaina tashin sasafiyar nan ne? ke bakya gudun mura ta kama ki ne?” ta faɗa tana ɗago ni.

Cikin dabara na zame hannu na daga roƙon da tayi min, har yanzu fuskata bata washe ba nace” wannan ai ba shine farko ba, domin tun daga ranar dana sako ƙafata cikin gidan nan nake wannan aikin, Antin!!! na faɗa cikin wata irin murya nace” kiwa Allah kiwa an’nabi ki rabo dani da wannan bogin soyayyar taki, na gaji ‘na gaji  ki nuna asalin wacece ke a gaban kowa Anti…” ‘na faɗa ina me haɗa hannuwa ina waje guda alamar roƙo, hawaye na zuba a idanuna.”

Mamaki na ya hana Anti ko ƙwaƙwaran motsi, sai Kawu ne yace” ashe yanzu rashin kunƴar taki har ta kai haka? dama ta sha gaya min kina mata rashin ɗa’a sani ba halin ki bane yasa naƙi yarda amma yau na gani da ido na, Shafaatu!! daga ranar irin ta yau duk wani aiki na gidan nan ya koma kan ta bance ki sake hana ta ba ko da wasa umarni na ne wannan, ko mutun ɗaya kar wanda ya taya ta tunda ta ɓata wayon ta…”  duk faɗan nan da yake yaƙi kallon fuskata domin tsantsar tausayi na na hango a cikin ƙwayar idanun sa.

A hankali na furta zan kasance me biyayya Kawu, wallahi bazan taɓa saɓa makaba, alfarma ɗaya nake nema a wajen ka shine kar ka sauya min kawu domin ba san ina zanje naji dadi ba a rayuwa ta ‘in babu kai Kawu na…” ina kuka kasa-kasa cikin wani yanayi me wuyar fassara wa.

Da sauri ya fice a gidan ko abin karin bai tsaya yaci ba, Anti tayi ƙwafa ita ma ta wuce ni.

To tunda abin nan ya faru Kawu na ya ɗai na sakar min fuska, ko dariya yake da ya gani yanzu zai haɗe rai, ‘in na gaida shi da kyar yake amsawa, gaba ɗaya na dawo  wata iri dani damuwa ta taro tayi min yawa, a cikin sati biyu kawai nayi wata irin rama, na koma makaranta kamar yanda nake buƙata sai dai a yanzu inda matsalar take  tunanin yayi mun yawa har yana shafar karatuna,  a yanzu rayuwa ta abar tausayi ce domin bani da wani maceci sai Allah, Aysha da Nafeesat suna ƙoƙari sosai gani sun sani a cikin farin ciki, amma a banza zuciya ta na can wajen Baffa na, buri na ya dai na fushi dani.

Tun kan a tashe mu nake ji wata iriyar yunwa kamar zan mutu, domin yau ban ci koma ba na fita a gida, an’a tashi ko Aysha ban tsaya ba na tahu gida da sauri, da sallama a baki na na shiga ciki a gurguje na cire kaya na, kana na laiƙa daƙin Anti na mata sannu da gida, cikin biyayya nace” Anti me za’a dafa?”

Tashi tayi ta zauna cikin farin ciki tace” yunwa kike ji ko?” ta faɗa tana wani waro min ido.

A daƙile nace” Eh da yake ɗazu ina sauri ne gani na kusa makara shiyasa na wuce ban tsaya naci ba.”

“Ok yayi miki kyau abinda kika bari gashi can a tsakar gida kije ki ɗauka kici, yau baza’ayi girki a gidan nan.” 

Yunwa nake ji gaskiya da sauri na nufi gindi madafa, domin haɗa abinda zanci a buɗe naga tuƙunyar taliyar ciki ta bushe, gaba ɗaya babu abin kirki a cikin ta, a hankali na fara ambaton sunan Allah a raina ina Allah yasa ba shine abinci nawa ba.

“Anti banga abinci ba sai wata bushashiyar taliya kin ganta, baza ma ta ciyo ba..” na faɗa ina miƙa mata tukunyar.

“Ha’a!! me zanyi da ita kuma ni? a’i ke kika dafa ko to shi ne rabanki in zakici kici ‘in bazaki ci ba kuma ki zubar domin yau baza’a dafa komai ba a gidan nan.” tayi maganar tana sakar min murmushi.

Ji nayi kamar na fada ihu cikin karayar zuciya nace” Anti ‘in nayi miki wani laifi ban sani ba ‘dan Allah kiyi haƙuri, ki bani abinda zanci wallahi yunwa nake ji sosai.

“Naga alama kamar rainin yayi yawa a tsakani mu, amma tunda yanzu ƙarfin ki ya kawo zaki iya zuwa ki ƙwata ko ki turo me ƙwatar miki..” tana rufe bakin ta ‘na fashe mata da wani irin rikitacen kuka, cikin wani yanayi nace” Anti wannan tsanar da kike nuna mun tayi yawa, dan Allah ki daure ki faɗa min abinda na tsare miki a rayuwa ko nakeyi wanda bakya so wallahi azamin zan gyara, abin yayi min yawa ki rabani da me tausayi na jigon rayuwa ta, ki toshe mun hanƴar farin ciki abin har ya shafin buri na, ki tausaya mun ‘dan girman Allah.

Na faɗa ina wani irin kuka kamar zan shiɗe.

Cike da jin zafi na tace” sabida na tsane ki, wallahi tun daga ranar da ya fara nuna miki so da tatali fiyya da ƴaƴa na, tun a lokacin na tsaneki bana ƙaunar ki ko kaɗan Munibbat, ina zaune dake ne kawai ‘dan kina kula min da yara ‘na da gida na amma ba dan haka ba da tuni na jima da korarki, kiyi ƙoƙari kafin nan da wani lokaci ki bar mana gidan mu ‘dan Allah ina so mahaifin su Ya nuna musu ƙauna fiyya sa zaton ki yarinya.”  ta faɗa sa ƙarfi.

Cikin tsoro nake kallon ta  jikina na rawa hawaye na gudu a kan ƙunci ‘na, nace” zan cika miki burin ki Anti.” ina faɗar haka na wuce ɗaki da gudu.

Tsaki kawai taja abin ta.

Allah sarki rayuwa, nayi kuka kamar zan mutu har sai da hawayen ma ya daina zubowa sai shasheƙa kawai nake,  nayi bala’in taƙurewa waje guda, ina auna iyakar farin ciki ‘na tunda nazo gidan nan.

A zaune Aysha take gaban Umma cikin biyayya tace” Umma da zaki yarda dana koma wajen gwaggo na da zama tunda kinga bata ɗa ko ɗaya kuma tasha roƙarki amma kin ƙi, tunda tace zata dawo nan garin da zama ‘dan Allah ki barni naje ko ranar asabar da lahadi ne inayi ina dawo wa gida.

Murmushi tayi kana tace” Aysha ke yarinya ce  tsakani ‘na da gwaggon ki babu wata danganta me ƙarfi, haka kawai sai na ƙwasheki nace gaki TA riƙi min ƴa,  dadiɗawa su masu ƙuɗi ne sosai ba irin mu bane ni bana son kalan dangi gaskiya kowa ya ci tuwan gidan su.”

“Umma ‘dan Allah fa nace!”

“Aysha bana son naci akan abinda bai zama dole ba, ki kama kan ki kinji.”

*****

Anyi gyara bana wasa ba, babu ɓangaren da ba’a gyara ba a cikin gidan, aka sake zuba sabanin kayan ta ko ina, gaba ɗaya cikar gida babu in da ya kai ɗakin Auta kyau sa tsaruwa an kashe mata kuɗi sosai, gaskiya Auta ƴar gata ce gaba da baya hajiyace ta tsaya akan komai, inda Mommy tayi gajeruwar tafiya acewar ta bata son cikowar mutane ‘in aka gama ta dawo.

Anyi gyara an gama  masha Allah gida ya dawo sabo dal dashi, ranar laraba insha Allahu Hajiya Nusaiba zata dawo kano da rayuwar auren ta.

*****

Like, comment and share.

Mrs Abubakar ce

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Waye Zabin Munibat? 7Waye Zabin Munibat? 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×