Skip to content

Waye Zabin Munibat? | Babi Na Bakwai

5
(1)

<< Previous

Bismllahir Rahmanir Rahim

“Bana jin zan cigaba da jure abunda ake min a cikin gidan nan, karka manta nima fa ina da haki akan ka, kamar yanda Hajiya take dashi me yasa a koda yaushe burin ta shine ta ƙuntata min, na gaji gaskiya muddin ka matsa akan sai Nusaiba ta dawo cikin gidan nan to nima zan tatara ne na bar maka gidan ka.”

Mommy ta faɗa cikin fushi.

Daddy dake zaune a gefen bed, ya jingina da fuskar bed din yana duban ta cikin mamaki, zuwa can yace” amina zo nan…?” ya faɗa yana nuna mata kusa dashi alamar tazo ta zauna.

Cikin turo baki ta zauna tana kallan gefe, murmushi yayi cikin nazarin halin da take ciki a yanzu, ya tausasa muryar sa ta yanda zata fahimce sa yace” Uwargidan sarautar mata, menene na ɗaga hankalin ki akan wanan ƴar maganar eyy, sanin kan ki ne hajiya ita kaɗai ta rage min a rayuwa ta, a matsayin ki na babba me hankali da nutsuwa wace shawara zaki bani game da ita, karki manta i uwata ce har abada bazan samu tamkar ba, kinga kuwa biyayya ya zama dole a gareni, ina so ke ma ki mata biyayya da dukani ƙarfin ki, wallahi ‘in kikayi haka darajar ki ƙimar ki matsayin ki martabar ki har abada ba zasu taɓa gogewa a idanuna ba, ke mafa uwa ce a gare ki ko kin manta da matsayin ta ne…?”   gaba ɗaya jikin tana yana cikin nashi sai a’ukin shafa ta yake cikin dabara.

Tayi limo a jikin sa, zuciyar ta wani iri tace” zan baka shawara mafi amfani a rayuwar ka, ni har abada bazan manta da matsayin hajiya a gareni ba, kawai ni abinda take min ne bana so dear.”

“to kiyi haƙuri kinji komai zai zamo tarihi, kema ki rage wannan halin naki ko zaku samu jituwa, gobe za’a gyara bangaren ta, ‘dan Allah aminta ki riƙa girmanki kinji, bana so ace yau ga wani abu marar kyau ya fito kuma kece sila, ki gyara halaiyar ki ko dan yaran ki karfa ki manta ƙwana nan zaki fa tara surukai, bazan so su sameki a haka ba gaskiya dole ki sauya halin ki kinji tawaje na…!”  Ya faɗa cikin rarashi..

“Shikenan ya wuce, Allah ya kawo ta lafiya amma fa da sharaɗi, kar tazo kuma ta saka min ido a cikin lamari na bazan lazumci wannan ba.”

“baki daya matsala sarauniya ta, nusaiba ai babu ruwan ta ita, zakiji daɗin zama da ita sosai.”

“Umm a gaba na kake yaban matar ka ba komai na gode.” Ta faɗa tana tura baki gaba, ita a lallai kishi.

Dariya yayi cikin manya ce yace, “ke kullum ba kya girma ko? to bari ki gani.”

*****

Shiru nayi a ɗaki ina ta saƙe-saƙe ni kaɗai a gaskiya na gaji da wanan yawon da take sakani, mafita kawai nake nema a yanzu tsafa na gama shirya abinda zanyi da murna na miƙe waje na fito aiko nayi sa’a yana zaune bai tashi ba, a gaban sa na tsuguna cikin mutuƙar biyayya nace, “kawu na! dama ina san magana da kai ne?”

Sai yanzu kuma na fahimci nayi wauta, amma wani ɓangaren na zuciya ta yana kara ingiza ni, ya ɗago cikin kulawa yace, “baki da matsala in da nine zauna nan ki faɗa min menene damuwar ki.”

“Kawu in ba damuwa ina so ka mayar dani garin mu tunda gidan mu har yanzu yana nan kuma babu kowa a cikin sa, nayi maka alƙawari zan kula da kai na da kyau, kuma zanyi karatu a nutse ni ɗai dan Allah Kawu wallahi bana jin daɗin zaman nan din kullum wuya nake ci bana san yawan da ake tura ni, ina tatalin rayuwa ta sosai ba fata nake ma kai na ba amma na san a irin haka wata rana in tsutsayi   ya afka min tsaf zan rasa martaba ta Kawu ina so na koma zama ni kaɗai Kawu dan girma Allah…” Na fad’a cikin  matsanancin kuka domin na kasa jurewa, gara na faɗa mai duk abinda za’ayi ayi kawai.

Da wani mugun sauri ya tashi zaune cikin kaɗuwa da tsantsar mamaki yace” Munibbat kan ki ɗaya kuwa? na barki ki koma zama ke kadai  kika ce? tamkar baki da gata ko ce miki akayi bama san ki, tun wuri ki sauya tunanin baki da kowa a duniyar nan face ni baki da wanda zai kula dake face ni, Idan na sake jin irin wannan furici a bakin ki sai nayi mumman saba miki, a nan din waye yake ta kura miki? WAYE yake saka ki yawon da kike tunanin martabar ki zata zube maza faɗa min ina jinki..?” ya fad’a cikin mugun ɓacin Rai.

Cikin kuka na ɗago raunanu idanuna ina kallon cikin idan sa nace” wallahi tallahi na rantsi maka da Allah da manzan sa, gaskiya nake fad’a maka kullum ƙwanan duniya sai anty ta korani bara, ga duka da take min kamar zata kashe ni ko shekaran jiya sai da matar gidanan tashigo ta amshe ni, gashi ta hanin zuwa makaranta ta in kuma har karya nake mata kaje ka tambaya a makarantar domin taki biya min kudin suklpic, ina da sheda kawu in dai baka yarda da batuna ba.” Na faɗa cikin wani mugun yanayi domin na karaya da irin kallon da yake min.

Tsananin mamaki na da alajaɓi na ne ya hana shi motsawa, cikin jimami da ɗaurewar kai yayi gyaran murya yace” wato dama abinda Shafa take gaya min gama dake gaskiya ne ko? sabida tsabar taurin ido irin naki shine kika sakani a gaba da banzan zanceki, ko ki ɗauka ban san kina zuwa yawan bara ba? ta Jima da faɗa min akan na taka miki birki tausayin ki da ƙaunar ki da yarda da nayi miki ya hanni aikata komai akan ki, bakin cikin da damuwar halin da kika saka kan ki na ƙasƙanci yasa na rage zuwa na gida, ba dan komai ba sai dan Ke!! amma dan kin ɗauke ni ƙaramin yaro shine kike gaya min ita take sakaki? MUNIBBAT da me na rage ki a cikin GIDANAN menene bana miki, wace irin kulawa kike nema a duniya wace bana miki, na fifitaki akan ƴaƴan cikina duk dan na saki farin ciki amma ki rasa da abinda zaki saka min sai da yawon BARA ni zaki tozarta MUNIBBAT ni zaki wulaƙanta a idon duniya? so kike ana yawo dani ana cewa iyayen ki sun mutu na kasa riƙe ko? wace irin daɓi’a kika ɗauko MUNIBBAT ba tambayar ki nake ba me na rage ki dashi?”  Yana daka min wata irin tsawa wace tunda uwata ta kawo ni duniya babu wanda ya taɓa min irin ta.

Tsananin tsoro da mamakin kalaman sa ya hanni magana, wato Anty ɗai duk ta tsallake tunanin na, cikin kuka da rauni fuska ta tayi jajir hanci na yayi ja idanuna sunyi tulu-tulu, na kasa magana sai kuka nake da jimamin irin yanda Anty ta ɗaure ni a wajen kawu.

Maganar ta naji a kai na cikin kukan kirsa take cewa” dama na faɗa maka, yarinyar nan babu abinda baza ta iya ba duk lokacin da na kawo maka ƙarar ta sai ka gwaleni to yau gashi nan ta nuna maka halin ta a fili, yanzu MUNIIBAH duk yanda nake kula dake fiyya da ƴaƴan cikina ki rasa da wa zaki haɗani sai miji na sakayyar da zaki min kenan?”

“ka yarda dani Kawu wallahi ba karya nake maka ba, aje makarantar ma a tambaya kuma ko gidan su Aysha akaje zasu shedani!! ka yarda dani gaskiya nake faɗa maka bazan cutar da kai ba Kawu, bare kuma kai na ka fahimci zance na ko.”

Tasss ya tsike ni da mari, cikin ƙunar zuciya yace” wallahi kika sake magana a nan sai jikin ya gaya miki, wawuya wacce bata san me yake mata ciwo ba, sharaɗi na ƙarshe sa zan kafa miki duk ranar da kika sake fita a cikin gidan nan da sunan Bara to karki sake tako mun cikin gida na, na cire hannu akan ki munibbat tunda baki da kirki.

Mik’ewa nayi tsaye hawaye na bin ƙuncin na cikin gigita da jin kaman sa nace” ni na san iyaka gaskiya ta na faɗa maka Kawu amma tunda baka yarda dani ba shikenan, komai yana buƙatar bincike amma tunda ka yanke huƙunci naji na amasa, domin Mamana tace na kasance me biyayya a gare ku, Anty na karki manta Mama na ba’a san ranta ta tafi ta barni ba maraici bai wuce kan kowa ba, na gode da roƙon da kika min.” Ina zuwa nan a zance na wuce da mugun gudu zuciya ta na ingizani akan abinda nake hari.

Jikin ta yayi masifar yin sanyi ta kasa cewa komai sai ido da take bini dashi, Kawu na kam ya riga da yayi fushi sosai baya jin ko tausayi na a yanzu, domin ta jima tana kawo mai sukata bai yarda ba sai yau, kuma tun jiya da ya dawo ta bashi kuɗin makaranta ta da cewa wai  nace ko an biya ma ba zani ba, domin bara  tafiye min karatun acewar ta kenan, ya amshi kuɗin zuciyar sa cike da raɗaɗi amma bai nuna mata ya yarda ba kawai ta saka shi a gaba tana karanto mai karya da gaskiya akai na kamar yanda ta saba duk zuwan sa.

*****

Like, comment and share.

Sannan ku biyo ni a babi na takwas don ci gaban labarin.

Mrs Abubakar ce

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×