Skip to content

Waye Zabin Munibat? | Babi Na Biyar

5
(1)

<< Previous

Bismllahir Rahmanir Rahim

Alhaji Abdulazizi nera, shine inkiyar sa kaf garin kano babu wanda bai san da shi ba, mutum ne mai kuɗin gaske, ya kasance mutumin kirki da son jama’a kekkyawa dattijon asali, domin shi kuɗin sa basu rufe masa ido ba, kowa na shine baya kyamar talaka ko kaɗan,  shi ɗan asalin garin  kano ne a wani ƙauye da ake kira  rangaza, a nan kakaninsa suke da zama, yana da mata biyu.

Babbar matarsa ita ce Hajiya Ameena, tana da yara huɗu maza uku mace ɗaya, Hajiya Ameena macece me tsanani da nuna isa da iko, a duniyar ta ta tsani talaka ya raɓe ta ko ƴaƴanta, shi yasa duk wanda take hulɗa dashi to fa sai ya taka matsayi me girma a cikin masu kud’in ma, ita yar asalin rangaza ce, zamu iya cewa auren zumuci ne tsakanin ta da  mijinta, suna da rufin asirin su daidai gwargwado, ta auri Alhaji tun bai dashi har Allah ya hore mai ya zama  wani a duniya.

Alhaji ko kaɗan baya ƙaunar wannan halin Ameena na tsanar talaka da take yi, sau tari ya sha zaunar da ita yayi mata nasiha, amma da ya bar wajen shikenan ta manta da abin da ya ce mata, kaf cikin yaranta babu wanda ya ɗauki muguwar ɗabi’arta, sai dai ɗanta na biyu mai suna AN’NUWAR ya bi sahun nata yaƙi jinin talaka sosai a rayuwarsa, shi har yaso ya fi  Hajiayar tasu ma, bashi da abokai talakawa abokansa duk ƴaƴan masu ƙuɗi ne, gashi mayen mata, amma duk ƙaunar sa ga mace in ba ƴar masu ƙuɗi bace to shi kallon namiji yake mata, bai taɓa aikata Zina ba, domin a kullum Mommy tana mai huɗuban hatsari zina ga rayuwar ɗan adam sosai, ya yi karatun addini da boko sosai inda ya karanci fannin kimiya da fasaha wato computer science, tun kammala karatunsa yaƙi aikin gwamnati acewar sa tunda Daddy ya tara musu dukiya ba sai ya nema aiki ba.

Babban ɗan Alhaji shine Aliyu haidar, sunan babban yayan Alhaji ne wanda Allah yayi masa rasuwa kafin haihuwarsa, bayan yasamu ɗansa na farko sai ya mayar da sunan  kan Haidar wanda suke kira da BIG man, gaba d’aya Aliyu halin shi irin na mahaifinsa ne, babu inda ya baro shi, kyakykyawa ne na bugawa a jarida, duk abin da ake nema a wajen namiji Haidar  ya haɗa shi, ƴan mata kam da kan su suke kawo kan su gare shi, shi wani irin mutum ne  wanda mata sam basa gaban shi, bashi da burin da ya wuce yayi karatu me tsayi. Alhamdulillahi burin sa ya ciki ya samu duk wani matsayi da kuka sani na fanni ilimi yayi isilamiya yayi boko,tashin farko baiyi shawara da kowa ya nemi aikin  koyarwa, shima ba a ko ina ba sai a government school, lokacin da hajiyarsa taji labari ba ƙaramin hauka tayi masa a kan bai isa ba, dole ne ya ajiye wannan aikin shima ya zauna kamar yanda d’an uwan sa yayi, magana tayi girma in da har sai da aka je gaban Hajiya Nafeesa uwa ga Alhaji kenan, a nan ne ita ma ta nuna ikon ta akan jikan nata da ɗanta, dole Mommy taja bakin ta d’inke, domin Hajiya ta fita bala’i, dalilin haka ne ya sa Hajiya dawowa gidan da zama, a cewar ta Amina zata lalata mata jikoki, Daddy kuma ya goya mata baya…

Abu na farko da Hajiya ta fara a gidan shi ne, gaba d’aya gidan zasu hallara a babban falon ta, cikin Isa da  ƙasaitacciyar hajiya tayi gyaran murya ta ce “to Alhamdulillahi naji daɗi sosai yan da naga kun samu nutsuwa daga zuwa na, abin da nake so da kai Abdulazizi ranar Monday in Allah ya kai mu da rai da lafiya, ina son takorata a mayar da ita government skul, shi kuma Bashir dake ƙasar waje ina so ya dawo gida najeriya ya ci gaba da karatun na sa a nan, ina fatan ka fahimceni ni?..” ta fad’a tana mai wani irin kallo na ka kiyaye ni.

Cikin biyayya ya ce ” insha Allah Hajiya yan da kika ce haka za’ayi, muddin hakan zai saki farin ciki..” ya fad’a cikin girmamawa.

Hajiya ta saki murmushin k’asaita tana aikawa da Mommy banzan kallo, murya can k’asan mak’oshi tace” Amina ko kina da abin cewa?”

Tamkar jira take tace” niko nake da abin cewa , gaskiya Hajiyar mu nayi hak’uri a kan  Big man, amma a kan Auta da Bashir , ba najin zan iya zuba ido, a juyani yara baza su tab’ayin government sochol ba, gaskiya karma na sake jin wannan maganar, Big Man dama na kune to na bar muku shi, nima a bar min nawa, kiyi hak’uri fa Hajiya ni zaɓin  raina na fad’a.” Ta fad’a cikin isar ta   da nuna ita watace…

Hajiya ta mayar da kallon ta ga Abdulazizi taji me zaice, kamar ya san me take nufi kuwa yace” har abada ba’ayi macen da zan aura uwata ta bada umarni ita kuma tace baza’ayi ba, ko da wasa Hajiya ta sake magana akan ƴaƴana ki kace  ba haka ba, to ko zan saɓa miki!, Auta kamar tayi government sochool ta gama, Bashir kuma shima ranar Monday war  haka yana tare damu a cikin gidan nan…” shima ya fad’a cikin dattaku da iya sarrafa magana, duk masifar yawon yaro bazai gane da fad’a yayi mata maganar ba sai ita da Hajiya ne kawai suka gane haka,  shiru tayi bata sake magana ba zuciyar ta nayi mata zafi.

Big man, ya matso kusa da mahaifin na shi cikin girmamawa yace” Daddy me zai hana a saka su a makarantar da nake aiki, sabida akwai karatu sosai, kuma zan kula da Auta da kyau Daddy…” ya fad’a yana wani karya wuya cike da shagwab’a.

Hajiya ta amshe zancen da cewa” Allah yayi maka albarka yaro na, na ma damk’a maka amanar tak’ora a hannu ka, kaje kayi duk yanda za’ayi ranar Monday ta fara zuwa, kuma bana san nuna fifiko in kuje can.”

ta fad’a ta sakin murmushi.

“Yauwa sai maganar masu aikin gidan nan, na gaji da gani masu jajayan k’unnuwan nan, ina so duk a sallame su a kawo mana wanda suke jin yaren mu, yan gargajiya suma na bada nan da sati naga sauyi, in ba haka ba kuma ni zan koma gida na..” ta fad’a cike da neman rigima.”

Mommy ji tayi kamar ta k’walla ihu dan tsananin b’acin rai, wallahi ba dan Hajiya y’ay’ar maman ta bace, da ba abinda zai hana ta karta mata rashin mutunci, amma sai ta d’aure gani ta ko ina Hajiya ta haura tunani ta, sai ta zuba ta gumi tana kallon mijin nata irin kaji tausayi na.

“Hajiya inda wannan ne baki da matsala, kafin ranar za’a kawo wasu wa’inan kuma za’a sallame su, haka yayi miki?”

“Eh sai maganar masallacin da nace ka gina a rangaza banji komai a akan shi ba.”

“Hajiya wannan ko sati ba’ayi ba da gama aikin sa, so nake dama in Bashir yazo ganin gida sai muje can gaba d’aya, kiga wuri daga nan kuma muyi zumuci.”

Allah yayi maka albarka d’ana shi yasa nake alfahari da ka, Allah yasa wan can busha-shan yaron ya dawo yabi halin ka.” ta fad’a tana nuna AN’NUWAR dake cika yana batsewa, tunda yaji an ambaci ‘kauye.

Ameen suka ce, Mommy da haushi yake neman kashe ta, ta mik’e da sauri ta shige ciki abin ta.

*****

Kamar yanda Hajiya ta fad’a ranar Monday NAFEESAT ta fara zuwa government sochool, zuciyar ta cike da farin ciki, tashin farko aka had’a su ajiya d’aya da su AYSHA da MUNIBBAT benchi su d’aya, ba laifi NAFEESAT na da k’ok’ari, haka yasa suma suka saki jiki da ita, bata da wulak’anci ko kad’ai a matsayin ta na y’ar masu kud’i, tana da saukin kai, gashi in kayi abu bata gane ba, ka tsaye take tambayar su MUNIBBAT ko AYSHA.

Wannan Kenan

Aliyu haidar malami ne a cikin makarantar tasu, duk yanda ka kai ga sa idon ka bazaka tab’a gane yana da Y’ar uwa a cikin makarantar ba, yana kula da ita amma a boye ta yanda ko ita kan ta sabata sani ba, tana karatun yanda ya kamata, sun sha’ku da su AYSHA sosai kullum ta koma gida sai  ta bawa Daddah labarin su Aysha da irin k’ok’arin su, haka ya sa Daddah jin yaran sun kwanta mata a ran ta.

An samo yan aiki, hausawa irin mu, sai dai irin tsangwamar da ake musu a gidan yasa, ko sati basayi suke guduwa, wannan abu yana damu Daddah sosai, kuma har yanzu tak’i janye dokar.

Wannan shi ne cikaken labarin su AN’NUWAR da Had’ari.

Rayuwa ta a gidan Anty rayuwa ce da zan iya kiran ta da rayuwar k’uncin, domin yanzu abin yakai ya kawo har duka na take wani lokaci ta hanin abinci, tun abin bai shige ni ba har na saba, sa’a ta d’aya yaran ta suna sona, suna kuma bani girma na musamma bishira, a cikin su dama dole za’afi da gwani marar kunyar cikin su ita ce fiddusi, amma in tayi min bana raga mata, domin bazan jure cin k’ashi a wajen ta ba, dan Allah yayi min san girman tsiya musamma in na san na girmemaka dole ka bani girmana.

Yau da wuri na tashi nayi komai, na gama na zauna ina karatu domin exam zamu fara a cikin satin nan, dan muna ta shirin zamu h’aure muje S.S 1, shi yasa na nutsu akan karatuna, banyi aune ba naji saukar mari a  k’uncin na, cikin gigita da firgici na d’ago idanun da suka ciciko da k’walla na zuba su akan ta, tana tsaye tana aiko min mugun kallo.

Littafin dake hannu na duba da sauri na boye shi a baya na, dan sai yanzu na tuna laifi na.

tana matsowa ina matsawa a haka har muka kai bango, tsayawa nayi cak jikina yana rawa cikin d’acin rai tace” wato dan ubanki ni ban isa dake ba ko? bana ce kar na sake ganiki da littafi a hannu ba muddin kina cikin gida nan?  ko dan kin mai dani sakarai ne..?” ta fad’a tana sake d’ib’eni da mari.

Ba shiri na yarda littafin gefe guda na d’afe k’unci na duka biyun, ina raba ido  cikin murya k’asa-k’asa nace” kiyiwa ma’aikin Allah kiyi hak’uri Anty wallahi na manta ne, kuma naga kin fita amma ba dan haka ba bazan d’auko ba.”

“Ok wato idan bana cikin gidan nan iskacin ki kike son ranki, to d’aga yau bari kiji kullum sai kin fita, kamar yanda nake fita kuma wallahi ki tabbatar kin samo kud’i kafin ki dawo gidan nan ko nawa ne, in ba haka sai na yanka ki shegiya me fuskar aljanu.”

Tayi maganar tana tura ni gefe, ra’kub’ewa nayi a gefe ina ta kuka k’asa mak’oshi gudun kar ta k’ara min, take tunanin iyaye na suka fad’o min.

Kamar yanda ta fad’a tun d’aga ranar kullum tare zamu fito da ita, maganar gaskiya ban san ina Anty take zuwa ba, gashi nima tace sai na nemo mata kud’i babu tallan komai na kud’i bare na siyar na kawo, haka nai keta bin layi ina shawagi, har inda ban tab’a zuwa ba a rayuwa ta ranar sai da naje sa a cikin uguwar nan, amma ban samo ko biyar ba, wani gidan ma idan na shiga da gudu ake biyo ni, duba da kayan dake jiki na masu kyau ga takalmi ga hijabi na sha, kamar zani isilamiya duba d’aya zakayi min ka sheda babu abinda narasa, kawai tsabar maula ce, ranar haka na wuni Allah yaso ni ma ba makaranta, wallahi ban samu komai ba haka dawo gida a gajiye.

Gaskiya ranar na sha wahala a hannu Anty har sai da wata mak’ociyar ta, ta zago ta amshi ni da k’yar, ga mamaki na lokacin da matar tace” lafiyar ki kuwa Shafa? irin wannan duka da kike mata ai sai kiji mata rauni.”

Kawai sai Anty ta fashe da kuka cikin kuka tace” kin san ance rok’on maraya sai hak’uri, yarinyar nan so take ta k’ashe min aure, ashe kullum na fita ita ma sa k’afa take ta fice yawon maula, dan Allah dubi yarinyar nan dame na rage ta dashi a gidan nan?”

Matar ta saki sallati tana tafa hannuwa, cikin rik’e baki tace” ke Shafa kiji tsoran Allah? yarinya da kullum nazo d’iban ruwa nake samun ta a cikin gida nan a zaune tana miki gadin gida da yara, shi ne zaki d’aura mata sharri? kaf cikar layin nan an sanki da shegan yawo, kawai dai kin so zalintar marainiyar Allah ne, kika rufe ta duka…””  ta fad’a cikin kumfar baki domin babu wanda bai san Suwaiba a layin mu, gata ta iya gulma sosai yawan ci mata a gidan ta suke taruwa,  ta saba zuwa gidan mu d’iban ruwa da yake rijiya gare mu.

Anty tayi mik’i-mik’i da ido da yake makirace sai cewa tayi” inda har sharri nayiwa yarinyar nan Suwaiba kar na motsa a nan wajen, ke ko ba maula kika je?..” ta fad’a tana zarre min ido.

Cikin kuka nace, “Eh nan naje.”

Suwaiba ta saki murmushi tace” MUNIBBAT kwantar da hankalin ki akwai Allah wallahi, duk wanda ya cutar da d’an wani ai ya san bashi yaci, kuma zai biya a lokacin da bai  dashi…” tana zuwa nan a zance ta fice a gida cike da jimamin.

To Sawaiba fa aka samu nayi, lokacin da majalisar ta had’u ta shiga bada labari, irin wahalar da Anty take bani har da karya, a hankali labari ya fara zaga unguwar mu, har ya kai k’unnen  Maman su AYSHA,   ta kirani ta zauner dani  dajin gaskiyar batu, ban boye mata  ba na shiga yi mata bayani, duk irin halin da nake ciki, sosai ta tausaya min.

*****

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, wata rana farin ciki wata rana bakin ciki marar yankewa, sosai nake shan wahala gashi yanzu kawu ya rage zuwa a wata sau d’aya yake zuwa kuma baya jimawa yake komawa, wallahi in kuka ga yanda Anty take lalab’a ni a gaba kawu na da jama’ar gari babu yanda za’ayi ku yarda da batu na, a da-dafi na samu har muka shiga S.s2 in da a yanzu babu wanda yake sani farin ciki kamar su AYSHA da NAFEESAT.

Maganar maula tunda ta fara jin ana zagin ta a gari sai ta d’aga min k’afa, ta hanin zuwa ko ina d’aga makaranta sai gida, wannan abun yayi min dadi sosai, take jiki na ya fara dawowa nayi kyau abu na tunda bamu rasa ciba bamu rasa sha ba, haka nake raba dare ina karatu na, zuciya ta cike da nishadi.

Kawu mu ya dawo, lokacin da ya ga na sauya ba k’aramin dadi yaji ba, a gaba na yace “Gaskiya SHAFA’ATU kinyi k’ok’ari sosai wajen kula min da Mama na kuma naji dadi, dan haka ga tuk’ici..” ya kar’kace ya zaro kud’i aljihun sa, ya bata har dubu biyar a matsayin kyauta, da nuna jin dadin sa, bakin ta har k’unne ta amshe kud’i tana wani kashe murya take cewa” tsakanin da kai ai babu gode Baban mama, zan kula maka da ita tamkar d’iyar cikina muddin haka zan saka farin ciki, matsala d’aya da nake fuskan ta da ita shine har yanzu, tak’i sakin jikin ta dani, yanzu duba fa ka gani tunda ka dawo tana mane da kai kamar cimgom..” ta fad’a tana ruzo hannu ta matse min k’umatu, a matsayi wasa.

Jina yi a lokacin kamar nace karya take, amma bani da halin bare huja, dole haka naji baki na nayi shiru ban sake magana ba, ban da rad’ad’i zuciya da nake.

*****

Kawu bai koma ba sai da yayi wata guda damu, inda ya nuna min kula sosai wace ta sake firgita Anty, domin tana bak’in ciki da kulawa da yake nuna min fiyya da y’ay’an cikin ta, lokacin da zai wuce an bamu rasiti din biyan kud’in makaranta, to bai samu zuwa ba sai ya bawa Anty nawa akan taje ranar Monday ta biya min, da fara’ar ta amshe kud’i tana ta zuba mai godeya, har ya fice d’aga gidan.

Ranar Monday na shirya na tsaya a bakin kofa ina jiran Anty ta fito mu wuce, shiru shiru lokaci na ta tafiya, a hankali na tab’a k’ofar ina cewa, “Anty zan wuce,” nan ma shiru.

*****

Like, comment and share.

Mrs Abubakar ce

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×