Skip to content

Waye Zabin Munibat? | Babi Na Goma

0
(0)

<< Previous

Bismillahi Rahmani Rahim

Bayanin halin da nake ciki nayi mata, cikin tausayawa ta ce, “Allah sarki Munibbah, gani nan da kike min yanzu haka wajen me shago zanje naciyo bashin garin ƙwaki domin tun safe da Baba ya fita bai dawo ba haka ma Yaya na, shine Mama tace naje ‘na amso in yaso da ya shigo sai akai mai kuɗin, amma karki damu za’a san yanda za’ayi yanzu zo muje ki rakani…”

Cikin rauni na ce, “a’a Aysha karki damu dani, na gode da kulawar ki, zanje gida sabida har yanzu bana jin dadin jiki na, ki gaida min da Mama..” ina gama fad’in haka na wuce zuwa gida jikina na rawa domin yunwa takai yunwa…

Cike da tausayi na Aysha take bin bayana da kallo, a haka har na ɓace ma ganin ta…

Bayan Sallar isha’i, ina zaune ina juyin yunwa su Anty suna gefe na suna cin abinci cikin ƙwanciyar hankali da salama, ƙamshi sai tashi yake a tsakar gidan, yawuna sai  tsinkewa yake cikin murya ƙasa-ƙasa nace” ANTY dan Allah ki taimake ni da ko tauma ɗaya ce wallahi ciki na sai kullewa yake..”

Banza tayi dani ban sake jin ko motsin ta ba bare na sa ran zata saurareni, na nisa cikin wahala nace” Anty nayi miki Alk’awari gobe da wurin zanje, kuma zan samo miki fiyya da yanda na saba kawowa, dan Allah yanzu ki bani abincin…?”

” Ai dama baki wahalar da kan ki a banza ba, abinci ne bazaki ci shi ba, gobe kuma ko zaki mutu sai kin fita kinji na gaya miki…”   ” Anty kin fa san bana iya jure yunwa, kirji na ya fara zafi da yaji…”

“Ko mutuwa kike kike dawowa bazaki ciba tunda ba tsohun ki bane ya nemo..”  shiru nayi ban sake magana ba, domin bana so ana cima iyaye na mutunci…

A hankali Bushira ta miƙe tsaye hannun ta ɗauke da ƙwanon abincin ta, kai tsaye waje na ta nufo dashi fuskar ta cike da tausayi na tace” Anty Munni zo muci nawa kinji! ki daina kuka zaki samu lafiya..” tayi maganar tana share min ƙwalla…

Ranta ne ya sake baci, tace” Ke dan ubanki zo nan! ubawa yace ki bata naki? zaki ɗauko abincin ki kawo min ko sai na tashi tsaye akan ki..”

Tana maganar tana zare mata ido.

Cikin turo baki gaba ta ce, “A’a mama Anty Munni tana jin yunwa, kuma bata da lafiya gashi har kuka take ni ki bari na bata nawa tunda ke kin hana ta…” 

“Bishira!!!  Ba kya jin magana ko?” Tayi maganar cikin tsawa.

“Anty cinye duka na bar miki ni na ƙoshi, kuma in Abba ya dawo sai na faɗa mai Mama tana hanaki abinci.”

“A’a kyakykyawa ta karki sake naji wannan maganar a bakin kowa, lefi nayi ma Anty shi yasa take hukutani, ɗauki abincin ki na gode…” Nayi maganar ina ɗaura mata kwanon a hannu, rau-rau tayi da idanun ta tana shirinyi min kuka, cikin tura baki gaba tace” da safe Abba ya ɗauko ki a waje yace mana baki da lafiya, kuma da zai tafi yace in kin tashi a baki abinci, gashi har yanzu bakici komai ba tunda har kuka kikeyi ni ki ciye wannan i’n ba haka bazan ciba nima…” 

Wallahi tausayi ta bani cikin dabara nayi tauma ɗaya nace” kin gani ko naci kema ɗauki ki ci…

Tau ta tsikeni da wani gigitacen mari me shiga jika, cikin firgici na dafe ƙunci na ina kallon ta nace” dan Allah kiyi haƙuri nayi haka ne dan ta samu taci…

Bata saurara min ba har sai da taga bana motsi, nan hankalin ta ya tashi cikin firgici ta shiga girgiza ni game da raɗamin kira amma a banza domin na jima da summa tun naushin farko…

Ba san ya tayi ba ni ɗai na farka na gani a d’aki ga abinci a gefen kai na, da yake yunwa taci ƙarfi na dakyar na iya miƙa hannu na ɗauko shi, banyi wata-wata ba na fara ci hannu baka hanu ƙwarya, ina gamawa  ciwan ciki ya kunno min kai, gaskiya na sha bak’ar wuya a ranar ji nayi kamar bazan sake ƙwana a duniya ba, nayi ta kuka ina murƙususu, gashi tunda Kawu ya tafi Anty ta ƙwashe yaran ta, ni ɗaya nake ƙwana a ɗakin,  babu wanda ya laiko ni bare na sa ran za’a taimaka min a haka har gari ya waye, murya ta ta dashe idanuna sun ƙanƙance ga ƙumbura da su kayi, haka na fito tsakar gida ina zaman jiran ta …

 Kamar ta sani sai gata ta fito cikin sanɗa muna haɗa ido da ita ta sakar min harara, ban sani ko taji nace” ina ƙwana Anty ? ya su Fiddusi, Anty ciki na ciwo yake ko barci ban iya ba…”

Ga mamaki na sai naji tace” sannu Allah ya sauwake, bari na gama sai muje kyamisi din Shauwilu, jeki ɗaki ki jirani. Sororo na tsaya ina kallon ta cikin matsanancin mamanki ta, bani da baki tambaya dole na tashi na koma ciki, kamar jira na Bishira take sai ga ta shigo da gudu, fuskar ta cike da an’nuri tace” Anty Munni kin tashi lafiya? ya jikin nake…?” “Da sauki ya rashin ji?”

Dariya tayi tace” me yasa jiya kikayi barci lokacin da Mama take dukan ki? Abba ya shigo Ashe ba tafiya yayi ba zan dawo yana shigowa Mama na ta fara kuka wai kinyi irin faɗuwar safe, shima har kuka yayi sannan ya dawo dake ɗaki, ni kuma nace mai abinci aka hanaki  shine kike kuka Mama na ta dakeki, shine kikayi barci ko?..” ta ƙarke maganar da ƙura min ido alamar na bata amsa…

Daure fuska nayi cikin jin haushin ta nace” ke matsa mun a jiki, bana hanaki irin wannan surutun ba? da kika faɗa me yace..?”

Kama haɓarta tayi alamar tunanin can tace” na tuno…

Lokacin da Anty take ƙururuwa na tashi, a lokacin Abba ya dawo gida, cikin tsananin tashin hankali yace” lafiya Shafa’atu me ya faru da ita? wani abu kika mata?”

Ganin tayi shiru babu amsa ranshi ya ƙara ɓaci cikin fusata ya ce,

“wallahi muddin yarinya mutane ta mutu wallahi a bakin auren ki, yanzu dama abinda take faɗa gaskiya ne da kika hana ta abinci ina za taje ta samu taci?? ba dole ma tayi bara ba ashe horon yunwa kike mata, makira kawai to ki buɗe ƙunneki da kyau kiji, bazan fasa tafiya ba gata nan na bar miki in kinga dama ki tashe ta in baki gani ba ki kashe ta, amma ki sani abakin aurenki muddin wani abu mara kyau ya same ta kuma ta sanadin ki, domin ita amanace a gareni bata da kowa sai Allah sai ni, amma shine kike cutar da ita, na tafi kuma bazan dawo ba kiyi yanda kika ga dama da ita Allah yana kallo ki amma karki manta maraici yana kan kowa…”

Yana gama faɗar haka ya wuce abin sa, bayan ya gama ƙashe mata yoni.

Wannan dalilin ne yasa naga sauyi a wajen ta ba komai ba, bayan tafiyar sa ta kama Bishira tayi mata dukan tsiya….

Kamar yanda tace ta kai ni kyamisi aka dubani, sai da tayi ta duba da Darin biyu kuɗin magani, da mun haɗa ido da ita take auna min harara, ko da muka dawo gida babu um babu umum tsakani na da ita, ranar yau ko aiki banyi ba….

To a zahiri Anty ta barni na huta ne ta ɗaura a inda ta tsaya, ba wai tausayi na ko tsoron Kawu yasa ta rabu dani ba, kimanin sati guda kenan nayi ina hutawa ko aiki banyi, lokacin makaranta nayi zan wuce abu na hankali na ya ƙwanta sosai,  ina karatu na ɗai-ɗai gwargwaɗo, gaskiya Alhamdulillahi babu abinda yafi ƙwanciyar  hankali dadi a rayuwa….

Cikin dabara Anty ta fara dawo min da asalin halin ta, amma ta sauya salo duk abinda zatayi min bata taɓa barin Bishira ta gani ko ƙannen ta, ɗaga ni sai ita sai Allah,

kamar yanda nake aiki na tun farko na dawo ina abuna…

A yanzu bana sa rai da abinci Rana a gida mu, za’a bani na safe dana dare amma banda na rana, duk inda take da zarar arahar tayi to zan gata a gida, sai tayi girkin ta gama take sake ficewa, gaskiya Anty na halin ta sai ita,  ciki na nake bawa haƙuri na zauna har lokacin na dare yayi na dafa naci…

Yau Monday  nayi shirin makaranta tsaf na fito, Anty tazo ta tsaye min ..

Kuyi haƙuri da wannan…

Mrs Abubakar ce

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×