Skip to content

Waye Zabin Munibat? | Babi Na Tara

5
(1)

<< Previous

Bismillahi Rahmani Rahim

Bayan kwana biyu abubuwa dama sun faru ciki har da ƙarin sauyawar Kawu na, ina ƙoƙari sosai wajen gani ya fahimce ni, naje wajen sa sau babu adadi akan ya yaffe mun amma ko kallon arziki ban ishe shi ba.

Laraba

Yau ne na tashi da wani irin ciwon kai mai tsananin, har bana gane wanda ke gaba na, sosai ciwo ke nuƙur-ƙusata cikin wahaltuwa na rarafo na fito tsakar gidan, cikin marainiyar murya nace, “Anty!! Anty! Zan mutu! Ki taimake ni Anty, kai na!” Na ƙarke maganar ina zubewa a bakin ƙofar ta, shiru tun ina sa ran fitowar ta har na cire, na jima  a wajen sosai gani babu me taimako na sai Allah sai na rarafa zuwa bakin ƙofar gida, ina zuwa wajen numfashi na na ɗaukewa na faɗi a nan ban sake sani inda kai na yake ba, sai farkawa nayi na gani a ɗakin mu a ƙwance Kawu na nayi min firfita.

Cikin dashashiyar murya nace, “Kawu na! kai na!” Da sauri ya yunƙuro yana cewa” sannu Mama na! Allah ya baki lafiya, ina ne yake miki ciwo yanzu?”  ya faɗa a ruɗe gaba ɗaya tausayi na ya gama cika mai zuciya.

Cikin rauni nace, “Kai na ke ciwo sosai Kawu! Bana jin dadin jiki na ma!”  “Sannu kinji Allah ya baki lafiya, tashi ki sha maganin nan.” Ya fada yana d’ago ni, amsa nayi na sha sannan na koma na ƙwanta, har ya miƙe zai wuce nayi saurin roƙo hannun shi, cikin wani irin kallo me kashe jiki da zuciya, murya ta na fitar da wani sauti me wuyar fassrawa nace” Kawu na!! dan Allah ka yafe min? bazan iya jure fushin ka ba Kawu na! kar ka manta ni marainiya ce! bani da kowa sai kai bana gani kowa naji dadi sai kai Kawu na!, A yanzu kai ne farin ciki na Kawu me yasa baza kayi bincike ba? Kafi kowa sani wace ce MUNIBBAT, bazan taɓa aika abinda nan gaba za kayi kuka dani ba, tabbas naje bara amma dole akayi min bani da yanda zanyi ne, ni biyayya nake yi Kawu! ka gafarce ni dan girma Allah kai daina fushi dani, ina cikin matsananciyar damuwa Kawu na!, Fushin ka yana mutuƙar damun rayuwa ta, kayi haƙuri kaji sanyin idaniya ta!!” Na ƙarke maganar cikin wani salo da roƙon me girma.

Tsananin tausayi na ya hana shi motsawa ɗaga inda yake, cikin wani yanayi ya waigo face dinsa yana kallo na, a hankali ya dawo kusa dani ya zauna har yanzu hannu na cikin nashi, cikin dabara ya riƙe min hannu da hannun dana riƙe shi, yana kallon yanda nake fitar da ƙwalla jefi-jefi murmushi yayi min me cike da nuna ƙauna, a hankali ya girgiza min kai alamar na daina kuka cikin taushin murya yace”  ni na san Mama na  yarinya ce me biyayya, ina so ki ɗore a yanda na sanki ko da wasa karki sauya, ina alfahari dake sosai bana son wannan Barar da kike, me kike nema kika rasa Mama na? menene bana miki a cikin gidan nan? kina tunani zanji dadin halin da kika saka kanki ne?  bakiji yanda zuciya ta tayi baki ba lokacin da Antyn ki ta sheda min kina zuwa bara kullum dashi nake ƙwana nake tashi, Mama na har kuka nayi sabida baƙin ciki da damuwa, nayi mamaki sosai lokacin da ta bani kuɗin da kike samowa, sai nake ganin kin Raina abinda nake miki kenan, ina tausayin ki sosai Mama na dan Allah kar ki sake fita yawan maula, har yanzu ina nan akan baka ta muddin nasake samun labarin zuwanki to ɗaga ranar zaki bar min gida na!”  Ya ƙarke maganar da ƙura min ido, cikin nutsuwa nace” insha Allah bazan sake ba Kawu ka yafe min?”

“Na yafe miki yata Allah ya baki lafiya, ni zan wuce yau inga sai nan da satin biyu zan dawo..”

“Allah ya tsare hanƴa Kawu, Allah ya bada sa’a ya taimaka yasa ka tafi a sa’a.  Ameen mama na ki kasance me jin magana kinji, karki aikata komai marar kyau, sai na dawo.”

Haka muka rabu da Kawu cike da kewar juna, da nuna soyayya a gare mu.

Bayan sallar la’asar Anty ta fito cikin ɗaure fuska, a tsaya na ganta a kai na tana cika tana batsewa tace.” Ke tashi kije ki nemo min abinda kika saba.”

Dam gaba na ya faɗi cikin rauni nace” Anty a gaban ki fa Kawu yace muddin na sake zuwa yawan maula, kar na dawo mai cikin gida, yanzu idan kika turani ya zanyi kenan? kuma ma fa bani da lafiya tun safe.” na faɗa wasu hawayen tausayin kai na na zubo min.

“Me ya dame ni da korar ki da yayi? Ciwo kuma ko zaki mutu a yau sai kin fita bara yarinyar, in ba haka kuma yanzu zanyi miki dukan da zai sake ƙwantar dake munafika…” ta fad’a cikin tsiwa.

Cikin kuka nace” Anty kiyi haƙuri dan Allah wallahi bazan iya fita ko ina ba a yanzu.”  Cikin kuka nayi maganar.

“Shikenan naga me baki abinci a cikin gidan nan, dan wallahi kamar yanda bakici na safe ba haka zaki wuni da yunwa.”

Tana gama maganar ta wuceni abin ta.

Kuka naci sosai ina ɗaga ƙwance, haka na wuni da yunwa ga ciwo, gani dare ya fara shigowa yasa na tashi dan nemawa kai na abinda zanci, a hankali ba fice a gidan.

Like, comment and share.

Mrs Abubakar ce

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×