Skip to content
Part 15 of 30 in the Series Fasaha Haimaniyya by Haiman Raees

YA RABBANA

Da sunanka Rabbana ni zan fara

A taskarka Rabbana nake ta bara

Baiwar da ka min nai godiya babu gadara

Ka ninka min Rabbana tai ta kwarara

Roƙon da nake yi Rabbana ka kiyashe mu.

*****

Amin!

*****

Tsira da amincin Allah mara adadi

Ka yi wa Manzon Allah ba adadi

Da sahabbansa masu sonsa da tauhidi

Ahlul baiti na saka su da tauhidi

Da duk mai sonsa tajiri ko maigadi

Roƙon da nake yi Rabbana ka kiyashe mu.

*****

Amin!

*****

A yau zamani ya riga dai ya canza

Al’ummar mu dukka kowa ya canza

Komai na gidanku in ka duba ya canza

Wasu na ƙaunar mangyaɗa wasu ko manja

Wasu na sulhu wasu ko na ja-in-ja

Roƙon da nake yi Rabbana ka kiyashe mu.

*****

Amin!

*****

A yau mun ɗau gulma tamkar sa kaya

Ba ma tsoron cin amana ko ƙarya

Munafunci da sa ido su muka kama

Mun ɗau bidi’a sai ka ce wasu ‘yan kama

Ga son banza ba mu son aikin wahala

Mun bar ilimi dukka mun ɗauki jihala…

*****

Wayyo!

*****

Yau zalunci ake ta yi babu hidaya

Ga cin hanci ba batun wani jin kunya

Karɓar rashawa ta zamo mana halayya

Shan ƙwayoyi ke wargaza mana tarbiyya

Masifu ga su nan sun fi ƙidaya

Roƙon da nake yi Rabbana ka kiyashe mu.

*****

Amin!

*****

Talakawa mu ba so a yi zalunci

Mu burinmu shugaba ya yi adalci

Amma kullum mu muna yin ha’inci

A junanmu muke yi wa zalunci

Mun ɗau shagala da ɗabi’ar shashanci

Roƙon da nake yi Rabbana ka kiyashe mu.

*****

Amin!

*****

‘Yan matan mu ya kamata su bar talla

Domin yinta ya tabbata kwai illa

Iyayenmu ya kamata ku bar mita

Illar talla ya kamata ku hankalta

Domin talla tana fa jawo lalata

Gara su yo aure, gidan maza su zamo mata.

*****

Ya fi!

*****

Jagororin mu ya kamata ku yo duba

Rayuwar talaka ya kamata a ɗan duba

Haƙƙi nasa ya kamata ku sa a gaba

Domin ku ne kuka zam masa alƙibla

Kuma dai ku ne ya ɗaga kai sama zai kalla

Haƙƙinsa fa lallai ku sani yana kanku.

Sosai!

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 8

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fasaha Haimaniyya 14Fasaha Haimaniyya 16 >>

4 thoughts on “Fasaha Haimaniyya 15”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×