Skip to content
Part 31 of 35 in the Series Yini Sittin Da Daya by Hamza Dawaki

Yini Na Arba’in

A yini na arba’in sai Kahuhu ya ki fitowa fada, shi kuma Dila da ya fito ya zauna kyam, bayan gaisuwa da ya yi yayin da Zakin ya fito bai kara cewa kowa ci kanka ba. Abin da ya fi wannan bayar da mamaki kuma shi ne yadda Zakin bai ko tambayi me ya sa Dilan ba ya magana ba, balle ya tambayi Kahuhun da ba ya nan!

Kai tsaye ya ci gaba da saurararon masu korare-korafe daban daban, yana sulhu tsakani.

Sabanin yadda yake yi a baya, in ya ji wani sha’ani mai sarkakkiya ya juya ya tambayi Dilan ko Kahuhu, yanzu da aka kawo karar wata Cilakowa da ake zargin ta da kwaso cuta ta barbada wa makwaftanta, sai ya juya ya ce wa Kunkurun. “Wai dama Alaramma wannan abin yana iya faruwa, ko ko dai camfi ne irin na dabbobinmu?”

Kunkuru ya ce, “Yuwuwa kai Yallabbai. Ai lokacin da na zauna a cikin kogin Cile ni na yi wa kifayen Salmona shara’a a kan irin wannan matsala.”

Zaki ya ce, “Me ya faru da su?”

Ya ce masa, “Watarana wani matashin Kifin Salmona mai kyakkyawan jiki da kwarjina da yake tashen jin karfinsa, ya bazama yawo cikin teku. Ya shiga nan ya fita can, yana ganin halittun ruwa iri-iri. Ya yabi wannan ya tsokani wancan, ya kori wannan wancan ya kore shi, har sai da ya isa can kasan kogi. Ya yi yawo son ransa, sannan ya juyo ya nufo sashen da danginsa suke. Sai dai bai sani ba, ashe a cikin wannan yawon da yake yi ashe ya debo wata irin nau’in kwarkwatar teku.

Dawowarsa cikin dangi sai ya zame musu annoba, a hankali in wancan ya zo jikinsa sai ya kwasa, shi ma in ya je jikin wancan ya goga masa. Cikin dan kankanen lokaci sai kwarkwatar nan ta mamayi kaso mai tsoka na kifayen nan. Har dai ta kai sun fara gudun juna, wani ba ya son zuwa kusa da wani.  Watarana wani kato daga cikin kifayen nan ya zuciya sai ya hadiye wancan matashi da ya fara kawo cutar.

Da dangin wancan matashi suka kawo min kara, sai na fada musu gaskiya cewa, hakan shi ne abin da ya fi kamata dama. Kuma idan har so ake cutar ta kare baki daya, to sai dai su kashe dukkan mai dauke da ciwon. A hankali sai duk sauran kifayen ma suka tattauna suka kuma yarda kan cewa hanyar kawai da za a bi a dakile ta kenan. Daga nan sai suka shiga hadiye duk wanda suka gani da cutar, sannu a hankali sai da suka karar da su kaf. Wannan kuma shi ya kawo karhen cutar a cikinsu.”

Zaki ya gyada kai a sannu, ya ce masa. “Ashe dai Akarami kun dade kuna taimakon al’umma.”

Ya ce. “Yo mu kuma Yallabai ba sai dai abin da labari ya biyo ta kansa in muka ambace shi a ji ba. Amma ai mun yi gwagwarmaya!”

Sannan Zakin ya juya ga wadancan masu kara, ya ce. “Ku koma ku ci gaba da neman magani, ita kuma za mu ajiye ta a magarkama mu gwada mata wasu magungunan, har sai mun ga yadda yanayin ciwon zai kasance.”

Ya juyo da Kahuhun ya ce. “Wato sha’anin wannan kifaye ya kayatar da ni matuka. Anya kuwa akwai wadanda suka fi su tsari wurin kiwon lafiya?”

Ya ce, “Ai ba ma za a samu ba.”

Da jin haka sai Tururuwa ta daga hannu. Basaraken ya ce mata. “Kina da magana ne?”

Ta ce, “Eh Yallabai.”

Ya ce. “To ina ji.”

Ta ce, “Muna da tsarin da ya fi wannan mu.”

Ya ce, “Ya kuke yi?”

Ta ce, “Idan daya daga cikinmu ya kamu da wani ciwo ko ya mutu, sai mu ware shi gefe guda, ko mun san ciwon da ya dame shi ko ba mu sani ba. Ka ga kenan, idan ma ciwon wanda ake dauka ne to mun riga mun dakile yaduwarsa.”  Ta dan dakata, sannan ta ce, “Bambancinmu da wadancan kifaye shi ne, mu dama can wannan al’adarmu ce, ba wai sai wani ya ba mu shawara ba.”

Kafin Zakin ya yi magana Kunkurun ya ce. “To kin san wa ya taba ba wa kakanninki shawarar ne tun can farko?”

Ta yi dariya, snnan ta ce, “Malamai manyan duniya!”

 Sauran dabbobi da ke wurin suka ci gaba da dariya. Har zuwa lokacin da Zakin ya  kara bude baki. “Lallai ku ma kan tsarin naku yana da kyau matuka.”

Tare da haka a wannan karon ma da zai tashi sai da ya kara tuna masa cewa. “Yau ma ina jiran ka.” Sannan ya yi sallama ya shiga gida. Fadar ta tashi, kamar yadda suka saba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Yini Sittin Da Daya 30Yini Sittin Da Daya 32 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×