Skip to content
Part 18 of 35 in the Series Yini Sittin Da Daya by Hamza Dawaki

Yini Na Sha Takwas

Bayan turo rinduna ta biyu, kusan babu wani babban aiki a fadar Zaki, don haka a wannin yinin da ya fito, ya taras fadar a cike makil. Sai ya dubi Dila ya ce. “Ina ganin ai ma iya ci gaba da sauraren labaranmu ko?”

Dila ya dan gyada kai cikin rashin kuzari, tare da cewa. “Haka ne Rankayadade.”

Sarkin ya dube shi cikin shakku ya ce. “Amma da alama akwai wani hanzari ko?”

Dila ya ce. “To idan ma dai da shi bai fi jan kunne wa dukkan masu bayar da labarin cewa kowa ya takaita labarin a iya rukuninsu ba: Kar babba ya bayar da labarin karami, balle kuma kramin ya bayar da kabarin babban.”

Sai a lokacin ne kuma Zakin ya tuna ashe fa sun hada zaman fadar wuri guda, tun a lokacin da suke zaben ayarin dakaru na biyu da za su bi bayan na farkon.ya dan  yi murmushi bayan fahimtar inda maganar Dilan ta dosa, sannan y ace. “Kwarai da gaske, wannan abu ne mai kyau.”

Dabbobi da dama suka daga hannu, da burin a ba su damar bayar da nasu labarum. Sai Dilan ya nuna Hazbiya ya ce. “Fatan dai kin ji ka’idar da aka gindaya ko?”

Ta ce. “Ina ji kuwa.”

Ya ce. “To ya ya sunan labarin naki.”

Ta ce. “Kunshin Cakwaikwaiwa.”

Ya yi murmushi. “To bisimillah.”

Hazbiya ta gyara zama ta ce. “Wani lokaci can zamanin Kurciya da Cakwaikwaiwa dukkansu suna ‘yanmata. Suka kulla kawance mai karfi, kullum suna tare fara ka raba. Duk wadanda suka san su, sun san idan ka ga rabuwarsu kawai lokacin bacci ne ya yi. Sai dai babban abin da yake damun Cakwaikwaiwa a kullum shi ne, duk inda samari suka tare su, sai su ce Kurciy suke so. Cakwaikwaiwa ta rasa me yake yi mata dadi, samari har suka  fada suka rika yi a kan Kurciya. Amma ita Cakwaikwai ba labari. Har dai ta gaji ta karya billenta da kanta ta ce wa wani saurayin Kabarai tana son sa. Shi ma ya bula mata kasa a ido, ya ce “Da dai kurciya ce.” 

Daga baya sai ta tsaya tsai, ta fara nazarin wai me ma ya sa ake son Kurciyar nan? Me kuma take da shi wanda ita ba ta da shi?  Har dai ta gamsu daga baya cewa bambancinsu kawai wannan rangadeden kunshin da ke kafar Kurciyar. Don haka sai ta fara tunanin yadda za   a yi ita ma ta yi wannan kunshi, ta magance wannan bakin jinin nata.

Ta rika yawo gari-gari tana neman mai kunshi, amma ba ta samu ba. Har garin nema wataran wasu suka yi mata kwatancen gidan Shaho. Ta sha da kyar, ta dawo gida. Ta samu Kurciya ta yi mata magiya cewa ta raka ta, ko ta fada mata inda aka yi mata wannan kunshi, ita ma ta je a yi mata. Kurciya ta yi dariya, sannan ta ce mata: “Kawata kenan, dama shiru na yi miki in ga iyakar gudun ruwanki. Na ji an ce kina ta yawon neman inda aka yi min kunshi, ke ma a yi miki. Amma fa maganar gaskiya bambancinmu da ke ba batun kunshi ba ne. Wasu abubuwan ne can da ba ki zata ba.”

Cakwaikwaiwa ta ce. “Wadannan kuwa wadanne bambance-bambance ne kawata?”

Kurciya ta ce mata: “To ina fatan dai in na fada miki za ki yarda, kuma ki gyara inda ya kamata ki gyara.”

Ta ce. “Ni kuwa mai zai hana ni yarda, alhali ina so in fita daga kangin bakin jinni, ni ma a yarda mace ce, kamar ke?”

Ta ce. “Madallah, da farko yana da kyau ki sani cewa mafi yawan maza ba kyau suka fi damuwa da shi ba, kamar dabi’a.”

Ta ce. “To fah.”

Kurciya ta ce. “Don haka abu na farko shi ne ki kama kanki: Ki dena wannan sakin bakin da kike yi, ki yi ta zuba  a ko ina kamar wata kanya.”

Ta ce. “Au yanzu managar ma laifi ce? Na ga in macen ba tai magana ba, su ma cewa suke yi ba ta waye ba.”

Kurciya ta yi dariya: “Kar ki damu da rudin maganganun maza, sau da yawa abin da suke so daban, abin da suke ambata daban.”

Ta ce. “Ban gane ba.”

Ta ce mata. “Za su zuga ki, ki yi ballagazanci, za su zagi wata saboda ta yi ki yi, amma daga karshe, bayan sun gama yi miki tafi, sun yabe ki, sai su koma su ce waccan wadda suke zagin suke so.”

Cakwaikwaiwa ta ce. “Ka ji tsi………”

Kurciya ta yi sauri ta toshe mata baki. “Kar ki yi haka mana kawata.”

Ta ce. “To ai abin nasu ne na ji har da ingiza mai kantu ruwa.”

Kurciya ta ce. “Ai ina fada miki ne don ki kiyaye daga yau kuma ba sai sun ga mai kantun ba, balle su angiza ta?”

Dukkanu suka yi dariya. Cakwaikwaiwar ta ce. “Hake ne kuwa.” Kurciyar ta dora:

“Bayan wannan, ki kame, kar ki nuna kina da araha, ko saukin samu, ta hanyar bude musu hanyoyin magana da ke cikin sauki. Kawai ki dake, ki yi kamar ba kya bukatar kowa ma ya kula ki. Tsakaninki da su gaisuwa, in har ba su suka kara magana bayan nan ba, to ki ja bakinki ki yi shiru. Maza ba irin mata ba ne, sam ba sa son abu mai saukin samu, sun fi son abin da suka sha wuya kafin su same shi.”

Cakwaikwaiwa ta dauki lokaci tana gayada kai a hankali, alamar ta tuno wani abu da ya faru.

Kurciya ta dauki lokaci tana yi wa Cakwaikwaiwa bayanan halin maza da abubuwan da suke sawa su so mace da kuma irin wadanda suke gudu tsaf. Bayan ta gama sai ta ce mata. “To duk na gamsu, zan gyara, amma ni ma a yi min kunshin nan tukun.”

Kurciya ta ce. “Wannan kunshi fa ba yi min aka yi ba, a haka aka haife ni.”

Ashe Cakwaikwaiwarka ba ta yarda ba, da ta fita sai ta tafi ta ci gaba da neman wurin kunshinta.  Tana cikin wannan hali ta hadu da Baini. Ta tambaye ta inda ake yin kunshi, ashe dama can Bainu tana jin haushin ta, ta taba zuga ta ta shiga tarko. Don haka sai ta ce ta shirya da daddare za ta nuna mata inda Kurciya ta yo nata kunshin. Tun kafin dare ya yi Cakwaikwaiwa ta zo ta sa Baini a gaba, har sai da ta gama dukkan shirye-shiryenta, suka rankaya.

Suka kama hanya ba su zame ko in aba, sai majema. A ka kuwa yi sa’a a lokacin masu jimar sun tashi kenan. Ta dubi wata tukunya  wanda aka gama hada dukkan kayan jima, aka cika ta da fatu, tana ta fama tiriri. Ta ce wa Cakwaikwaiwa.

“Waccan tukunyar za ki yi tsalle ki tsunduma kafarki, sai ki fito. Za ki gan ta radar da kunshinta.”

Har Cakwaikwaiwar ta yunkura, sai ta kara ce mata: “Amma fa kar ki manta; kamar sauran kunshi, dadewar kafarki a ciki, shi ne abin da zai sa kunshinki ya kama rau. Idan kuma kika tsoma dan dangwala kika fito, to za ki yi birji-birji kenan.”

Cakwaikwaiwa ta ce. “Ke dai tsaya ki sha kallo ‘yar albarka.”

Ta kuwa daka tsalle ta tsunduma kafafuwanta cikin tukunyar jima. Ai da zafi ya yi zafi sai kawai ta rikice, maimakon fitowa ta saki jiki, sai da ta nitse dukkanta a cikin ruwan zafin nan, sannan ta kara yin tsalle a gigice, ta ci sa’a ta fado waje sumammiya! Wannan kuma shi ne ainishin kasancewarta bakikkirin har yanzu.”    

Fada ta cika da dariya. Aka yi mamakin labarin, musammam ma irin ketar Baini, wadda ake ganin ta tamkar wata mai kirki. Kodayake ita Cakwaikwaiwa da ke zaun a wurin fuskarta a turbu ne take, tamkar wadda aka aiko wa jakadan mutuwa.

Malam Kahuhu ya ce. “Lamari dai bai yi kyau ba, amma kamar kowace matsala, wannan ma akwai darasi da ita Cakwaikwaiwa da ma sauran mata za su iya dauka a cikin lamarin.”

Ta ce. “Sai dai wasu su dauka ai, amma ni mai zan dauka a ciki, bayan abin da zai faru ya riga ya faru?”

Da yawa daga dabbobin suka ci gaba da dariya. Sannan daga bisani mai bayar da labari na biyu, Zalbe ya ci gaba.

A wannan yinin ma sai da fadar ta saurari sama da labaru biyar, sannan Basaraken ya tashi ya koma gida. Sauran dabbobi suka kama nasu hanyoyin zuwa nasu gidajen.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Yini Sittin Da Daya 17Yini Sittin Da Daya 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×