Skip to content
Part 19 of 35 in the Series Yini Sittin Da Daya by Hamza Dawaki

Yini Na Sha Tara

A can kuwa kololuwar daji, bayan waccan runduna ta biyu ta wuce dukkan wani bigire da take tsammanin kara haduwa da wata dabba. Ba su yi aunai ba suka hangi irin wancan duhu da rindina ta farko ta hanga. Hankalinsu ya tashi kwarai, suka dauka yanzu tabbas sun gamu da abokan gaba. Sai aka fara shirin gagaga, ba kama hannun yaro. Sai bayan kowa ya kammala daura damararsan ne aka fara tunanin yadda za a afka wa rindunar. A nan sai aka samu rabuwar kai; yayin da tsageru irin su Dan Mitsu da Beguwa suke ganin kamata ta yi a yi kururuwa, waccan rindunar ta jiyo, sannan a yi musu bushara cewa yau ce ranar mutuwarsu. Su kuma su Karkanda da Gwanki suna ganin kamata ta yi a afka musu ba tare ma da wata sanarwa ba, a gama da su cikin kankanen lokaci. Akwai kuma su Mujiya da Tsagagi da suke ganin ya kamata dai a lallaba a gano su wane ne, kuma ta yaya ya fi dacewa a tunkare su.

An dauki sama da sa’a’o’i biyu babu abin  da suke yi sai faman hujjatayya cikin daga sauti. Har dai wadancan dabbobi suka fara jiyo tashin sautukansu, suka turo nasu ‘yan leken, don su gane musu su wane, kuma me yake faruwa da su. Mikiya da Tururuwa suka cika da murna bayan sun taras ashe wannan ayari wasu ‘yan’uwansu ne da suka biyo bayansu. Bayan sun gaisa, sai suka hau tambayar juna abubuwan da suka faru bayan saduwa.

Da farko ransu ya yi matukar baci da suka ji ashe tsawon lokaci rindunar suna nan sun yi zaman dirshen a makarantar Kunkuru, alhali can Sarki yana can yana jiran su kammala ayyukansu su dawo gare shi. Amma sai wadannan jakadu (Mikiya da Tururuwa) suka lallaba su cewa, su zo su ma su saurare shi ko da sa’a guda ne, daga baya sai su yi abin da ya dace.  Da suka amince, sai jakadun suka koma suka sanar da Malam Kunkuru cewa wani ayari ne na ‘yan’uwansu suke tafe. Kuma suna so a yi musu izini su ma su zo su saurari karatu, ko da na yini guda ne. Ba kuma tare da bata lokaci ba Malam Kunkuru ya amince da wannan bukata. Sannan suka kara komawa suka taho da su.

Lokacin da wannan ayari na biyu suka karaso, suka samu wuri suka zauna, suna ta muzurai. Malam Kunkuru kuwa bai nuna ma ya san sun karaso wurin ba, ya ci gaba da bayanansa:

“Ai kowa zai iya zama azzalumi ko mai adalci. Domin daga lokacin da ka dauki nama ka ba wa Gwanki ka dau Ciyawa ka ba wa Dila, to ka yi zalunci. Adalci shi ne ka ba wa Gwanki ciyawa, ka ba wa Dila nama. Shi ya sa kuma duk da adalci abu ne mai kyau, to amma ya fi kyau a wurin shugaba fiye da kowa.”

Aka ce. “Na’am.”

Shi kuma ya ci gaba: “Haka nan, kankan da kai duk da abu ne mai kyau, ya fi kyau ga masana. Shi kuwa hakuri duk kyansa, ya fi dacewa ga takala.”

Tun da ya kawo kan wannan gabar, ya fara lura da yadda wadancan tsagerun dabbobi suka fara nutsuwa da mayar da hankali sosai wurin saurarensa. Sai kuma ya kara cewa. “Saura wace tambaya ce ban amsa ba kuma?”

Rakumin Dawa ya ce. “Saura tawa.”

Malamin ya ce. “Wacce kenan?”

Ya ce. “Shin dabbobi ma suna shan kayan maye, kamar bil’adama?”

Malam Kunkuru ya ce. “Kwarai kuwa, a kasar Afurka ta kudu akwai wata bishiya da ake ce mata Marula, tana yin wasu ‘ya’ya masu tsami. To duk lokacin da manyan dabbobi musamman irin su Giwa suka so su bugu, sai su je su yi ta cin wannan ‘ya’yan itaciya. Sai sun ci sun sun ji sun yi tatul kuma, sai ka ga jim kadan sun fara tambele, tamkar yadda bil’adama suke yi idan sun bugu.”

Karkanda, wanda a dazu yake ta faman murtuke fuska, ya daga hannu yana cewa. “Tabbas ni ma shaida ne, na g a wannan da idanuna.”

Ganin haka  tuni sai kafatanin dabbobin da ke cikin wannan runduna ta biyu ma suka saki jiki, suka  fahimci zaman za a yi ashe.

Kunkurun ya kara cewa. “Haka Maciji yana iya zuwa duk inda ya san mutane suna ajiye kayan maye, musamman irin na ganyayyaki,  ko inda ake turara su, ya kwanta ya shaki kamshin sosai. Sai ya ji ya bugu, sannan ya tafi. Sannan akwai abokan bil’adama irin su Biri, wanda shi zai iya ma karbar  abin da suke sha su yi mayen kai tsaye, shi ma ya sha.”

“Su ma dama sukan ce wai ‘Biri ya yi kama da Mutum.’” In ji Zomo.

Sauran dabbobi suka fashe da dariya.  

Daga nan sai Mugun Dawa ya ce. “To kuma su ma dabbobi suna iya kasha kansu suna sani, kamar yadda bil’adaman kan yi?”

Malam Kunkuru ya ce. “Kwarai kuwa, domin da idona na ga wani katon Doki da ya fita a guje ya afka wani rami mai tsananin zurfi, ya mutu, bayan ya fahimci ashe Godiyar da ya haikewa jiya cikin duhun magariba mahaifiyarsa ce!”

Da yawa daga dabbobin suka hada baki, suka ce. “Assha!”

Ya kara cewa. “Kuma na ga wata Mijiya a kasar Hindu, wadda ta yi sabo da Maigidanta sosai, har tana iya fahimtar zancensa. Katsam wata rana mutuwa ta yi musu yankan kauna. Yayin da aka gama hada wuta aka fara kone wannan Ubangida nata, sai kawai ita ma ta yi alkafura ta afka cikin wutar!”

Rakumin Dawa ya ce. “Sabo tirken wawa.”

Kura ta ce. “Ka ji halasci irin na dabba, amma da bil’adaman ne ba zai taba iya yi mata wannan kara ba.”

Zomo ya ce. “Ban da abin Kura dama su ina ruwansu da wata kara ma, wadanda za su gama kiwata dabba, sai sun shaku matukar shakuwa, ana ganinsu tamkar ‘ya’ya da iyaye. Rana a tsaka sai su dauki wuka da kansu su daba maka!”

Ta ce. “Iye?”

Zomo ya ce. “Eh.”

Dabbobi suka yi dariya. Daga nan kuma sai aka bude fejin bil’adama aka yi ta surfar su ana dariya, har yamma ta yi. Da lokacin komawar Malamin na al’ada ya yi, sai ya yi sallama da su, ya nufi gida. Su ma suka ci gaba da tafiya sannu-sannu. Wuri ya fashe tsaf, aka bar wadancan rundunoni na farko da na biyu suna tattaunawa. Inda a mataki na farko dai, runduna ta biyun ta gamsu cewa makarantar Malam Kunkurun makaranta ce da ta cancanci a zauna ko da sama da yini goma ne, a nemi ilimin yaki da na zamantakewa. Don haka su ma nan yini nan kwana, in ya so duk wani shiri ma da za su yi, say i shi a hankali bayan kammala karatu.   

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Yini Sittin Da Daya 18Yini Sittin Da Daya 20  >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×