Skip to content
Part 29 of 35 in the Series Yini Sittin Da Daya by Hamza Dawaki

Yini Na Talatin Da Takwas

Kamar sauran labarai, labarin jawaban Kunkuru na jiya da kuma yadda suka kayatar da Sarkin da alama sun karade dajin. Don haka yau fadar ta cika da ‘yan Jari hujja-irin su Babba Da Jaka, da ‘yan sa ido, irin su Kururu, da ‘yan guntsi-fesar, irin su Shaya da Carki, da ‘yan barbada irin su Yanyawa, da dai sauran rukunan dabbobi da tsintsayen da a baya ba su ma damu da zuwa fadar ba. Kuma ba sa yi mata biyayya irin ta sau-da-kafa. Wadanda kuma ganin su a fadar ya tabbatarwa da da dama cikin mazauna fadar cewa tsegumi ne kawai da sauran bukatu na karan-kai suka kawo su.

A haka aka yi jira har lokacin da Sarkin ya fito, ya zauna, kuma dukkanin dabbobi suka yi gaisuwa gare shi. Daga baya, bayan kowa ya gama shehin malamin ya yi tasa cikin kasaita. Kuma Basaraken ya kara ce masa “Akaramakallahu.” Kalmar da bai ambata ba yayin da yake kaibar gaisuwar Malam Kahuhu.

Korafi daya kawai ya saurara, na wata Magen Juda ta wani katon Siyaki ya cinye mata ‘ya’ya har guda biyar. Bayan ta aminta da shi, ta kuma  ba shi amanar  ‘ya’yan kafin ta dawo daga wani balaguro. Dayake wata maganar tana cin sa a rai, bai tsawaita bin diddigin yadda abin ya faru ba. Sai kawai ya yi umarni da a kai Sayakin magarkama a ajiye. Sannan ya kafa wani kwamati mai dabbobi biyar karkashin Gwanki, ya umarce su da bin diddigin hakikanin yadda abin ya faru.

Gamawarsa wannan shari’ar ke da wuya kuma ya dubi Kunkurun ya ce, “Wai Alaramma kai kuwa a in aka yi karatu?”

Kunkuru ya yi murmushi irin na kasaita, sannan ya ce. “A wurare da yawa:” Ya dan gisganya ya sauya salon zamansa, sannan ya ci gaba, “Tun ina da makonni  uku a duniya, watarana mun fita kiwo da gyatumata muka ci karo da wata katuwar Kura maras imani. Ta kama ta ta take mata baya, ta rika kwakular hannaye da kafafunta tana ci. Ita kuwa ba abin da take yi sai faman ce min in gudu in buya. Da na lura ba abin da zan iya yi fiye da hakan, sai na bi umarnin nata. Ina cikin wannan firgicin na hadu da wani Gwaggon Biri. Sai ya dauke ni ya kai gidansa ya ajiye. Haka muka tashi tare da yaransa mu yi wasa mu ci mu sha tare. Bayan shekara guda kuma sai wasu Kurayen suka addabi wannan mazauna tamu. Don haka wannan uba namu ya tarkata mu da sauran iyalansa ya nufi sabon matsuguni. Wanda a cikin wannan hijira da yawan iyalan suka gamu da ajalinsu, ciki har da shi. Sakamakon manyan garkunan dabbobi masu farauta da muka rika arba da su.

A sabon matsuguni da muka zauna, ba mu sani ba ashe kusa da wani babban titi ne da ya hada kasa da kasa. Watarana sai kawai wasu  Bil’adama suka zo suka daka mana wawa. Sa’ar da muka ci, su ba kashe dabbobi suke yi ba, wai sha’awarsu suke kawai. Don haka sai su dauki dabba su sa a mota su yi tafiyar kwana da kwanaki da ita. Inda suka yi zango don cin abinci, ita ma su kawo mata wanda suka san tana ci. A wurin wadannan direbobi na yi ashirin shekaru bakwai, suna yawo da ni daga gari zuwa wani. A nan na koyi yaruka da al’adun bil’adama da bambance-bambancensu da dama.

Daga baya da ubangidana ya tsufa, sai ya kawo ni gidansa ya ajiye a cikin iyali. Na zauna na zama tamkar dan gida, ina iya shiga kowane daki a duk sa’ad da na so a gidan. Bayan rasuwarsa ma aka sha rigima a kan wane ne zai gaje ni, daga baya dai suka hakura suka bar wa wata ‘yar’autarsu. Ita ma ta tafi da ni har gidan aurenta. Ban gushe ba ina tare da ita har ta gama haife-haifenta ta rasu. A tsakanin wadannan gidaje biyu masu mutane da dimbun yawa, na fahimci yadda duk bil’adama suke zamantakewarsu. Na saurari gulmace-gulmace da makirce-makircensu da cin amana da tsabar rashin adalcinsu.

Daga baya da sabuwar uwargijiyata kuma ‘yar’autar ubangidana na farko ta rasu, sai ita ma daya daga cikin ‘ya’yanta ya gaje ni. Shi kuma rikakken Malamin Tsubbu ne. Wanda masu neman sarauta da sauran madafun iko da ‘yan kasuwa da mata suke yi wa tururuwa. Kowa da irin bukatun da yake kawo shi, kuma kowa da irin karyar da Malamin nan yake yi masa. A nan na koyi hada magunguna da dama, na kuma ga yadda ake sakin layi a yaudari masu zuwa neman taimako, musamman mata. A saka su su yi abubuwan da ba shikenan ba, bukatunsu kuwa ko su biya ko kar su biya, shi dai Malam nasa sun biya.

Da wannan Malamin ya mutu, sai na koma wurin kanensa, wanda shi kuma malami ne mai koyar da karatu. Manyan mutane ne suke zuwa su zagaye shi suna daukar karatu. Ni ma duk lokacin da ya fita makaranta sai in je in zauna, in saurari karatu. A nan na samu sama da rabin ilimin addini da zamantakewa. Watarana muka yi wata tafiya da shi Malam da iyalansa, don zuwa wata ziyara. Sai wasu mau garkuwa da mutane suka kama mu a daji. Suka tsare mu, sai da danginsa suka biya fansa, aka sake su, ni kuwa suka rike ni.

Ban gushe ba a wannan dajin, ina zama da su a kan dole, har tsawon shekaru uku. Ban kubuta daga wurin wadannan azzalumai ba, sai da wataran wasu jami’an tsaro suka yo musu wani sumame na ba-zata. Suka tarwatsa su, suka kashe na kashewa, suka kama na kamawa. Daga nan ni ma na samu na sulale na nitsatso cikin daji.”

Tsawon lokacin da ya yi yawa wannan bayani, idanun Zakin suna kansa, yana kuma gyada kai cikin alamun kayatuwa lokaci bayan lokaci. Da ya kawo wannan gabar sai ya ce masa, “Lallai Alaramma an sha gwagwarmaya!”

Kunkurun ya kara fasa kai: “Shekaru dari biyu da yini sittin da daya na kwashe a cikin bil’adama! Shi ya sa kuma babu wani abu da za a gaya min game da su.”

  Zakin ya ce, “Na yarda.”

Tsawon lokacin da ya dauka yana wannan bayani kuma babu wanda ya tanka masa tsakanin Dila da Kahuhu, har ya kama sukuwa da zamiyarsa. A can gefe kuwa cikin sauran dabbobi da ke fadar, su ma kaso mai tsoka babu wani alamun kayatuwa da bayanan da suka yi. Sai dai tare da haka a wannan karon ya samu tsirari da suka nuna matuwar burge su da Malamin ya yi yayin da ya zo kammala jawabin.

A haka fadar da gama zamanta na wannan lokaci ba tare da furta ko uhm daga wadancan tofaffin masanan na fadar ba, in ka dauke gaisuwa da suka yi yayin shigowa Basaraken fadar da kuma yayin fitarsa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Yini Sittin Da Daya 28Yini Sittin Da Daya 30 >>

1 thought on “Yini Sittin Da Daya 29”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×