Jikin Husna ya dauki kyarma bakinta na karkarwa ta kasa cewa komai.
Ina zata Kai Daddy da sunan miji? Bata taba kawo hakan a Ran ta ba sai yanzu ta gano abinda Anty Amal take nuna Mata. Da kyar ta samu ta kwato maganar da Bakin ta yayi gardamar furtawa.
"Wallahi ban San hakan ba sai da Kika Ankara Dani . Ni da kaina yaci ace na gano hakan Amma da Yake Rai na da hankali na suna Kan Yaya muhsin sai ban kawo hakan ba.
"Ta Yaya Anty Amal zanyi Haka? Baban Yaya muhsin? Ko duk Duniya maza zasu Kare. . .