wp-content/uploads/2024/02/Matakan-Nasarar-Iyali-by-Hamza-Dawaki-1.jpg

Matakan Nasarar Iyali

A irin wannan yanayi da muke ciki da matsalolin iyali da yadda za a tafiyar da su suka yi wa al’ummarmu É—aurin dema, haziÆ™i kuma fashihin marubuci Hamza Dawaki ya zo da wannan sabon littafi mai cike da ilimi mai tarin yawan da misalta shi ma ba Æ™aramin aiki bane. Karanta wannan littafi zai canja rayuwar mutane da dama tare da hasko musu lungunan da ba su taÉ“a tsammanin sun wanzu ba a rayuwarsu tare da ba su damar kakkaÉ“e duk wata Æ™ura da ke cikinsu.

wp-content/uploads/2024/11/Kirkira-by-Bala-Anas-Babinlata.jpg

Kirkira

A cikin wannan littafi mai suna ‘ƘirÆ™ira’, shahararren marubuci Bala Anas Babinlata ya zayyane dukkan wani abu da mutum ke buÆ™ata ya sani game da Æ™irÆ™ira. Ya kuma bayyana hanyoyin da mutum zai bi domin gano irin tasa baiwar ta Æ™irÆ™ira da kuma yadda zai iya sarrafata har ta kai ga yi masa amfani ta kuma amfanar da sauran al’umma.

wp-content/uploads/2026/02/BintO-1.jpg

Binto

Zuciya ba ta da kashi, kuma ba ta shawara kafin ta zabi wanda take so. Amma me zai faru idan kaddara ta tazo miki da son mutumin da duniya ke miki kallon bai dace da ke ba? Wani lokaci, zuciyar dan Adam takan zama abin al’ajabi; tana iya guje wa abin da ke kusa da ita, wanda ke nuna mata tsantsar kauna ba tare da fuskantar wata fargaba ba kamar yadda zuciyar Binto ta kasa kallon Dan uwanta Isma’il da ke tsananin sonta.

Duk da bambancin da ke tsakanin su tamkar sama da ƙasa ne Binta ta zabi rayuwa da burin zuciyata, ta zabi komawa kauyen su Tsalha, sai dai kash tunanin ta ba ɗaya yake da rayuwar da ta gani ta zahiri a ƙauyen ba, rayuwa ce cike da kunci da fargaba, azaton Binta rayuwar kauye cike take da kwanciyar hankali, ashe kallon kitse takewa rogo duda kasancewar mijin ta ya zame mata Mijin marainiya rayuwar ta a garin tasanya ta fahinci rayuwar aure bawai kai da mijin bane kawai…

Shin soyayyar Tsalha za ta wadatar da Binto a lokacin da gata ya juye zuwa wahala? Ko kuwa za ta yi nadamar Zaɓar so kan gata da dukiya?.