Skip to content

About

Hikaya taska ce da aka kirkira don masu sha’awar rubuce-rubuce da karance-karancen littattafan labari da adabi.

Kowa na iya karanta littattafai daga shahararrun marubuta daban-daban. Akwai free littattafai da dama, sannan akwai littattafan da sai an biya kudi ta hanyar subscription za a iya karanta su.

A latsa nan don ganin wasu daga cikin litattafan da muke da su. Ga masu son yin subscribing, sai a latsa nan.

Hanyoyin sanya littattafai

Marubuta na iya dora littattafansu a Hikaya ta hanyoyi guda biyu kamar haka:

  1. Ta hanyar dora littafin nasu babi-babi (series) don masu karatu kyauta. Ga masu sha’awar yin hakan, da farko sai a yi rajista, a yi login, sannan sai a je main menu a latsa publish. Ba za a iya ganin ‘publish’ ba idan har ba a yi login ba.
  2. Ta hanyar sayar da kammalallen littafi ga Hikaya don itama ta dora ta sayar wa makaranta ta hanyar subscription. A latsa nan don karanta sharuddan sayar da kammalallen littafi da kuma yadda za a aiko da littafin.

Don sauran tambayoyi da suka shafi amfani da taskar sai a je FAQ page namu ko kuma a tuntube mu kaitsaye ta contact page.

Har ila yau, don sannin ka’idojin amfani da taskar sai a ziyarci terms and conditions ko kuma privacy policy.

Mun gode.

The Hikaya Team