wp-content/uploads/2021/11/Matar-Bahaushe-min.jpg

Matar Bahaushe

Ruqayya Manaf ƊanGambo ‘yar majalisar wakilai ce mai tausayi da ganin ta taimaki al’umma. Captain Anwar Sarari da Honorable Bamanga Jafaru, na daga cikin mazajen da ke mararin ganin sun mallake ta a matsayin matar aure. Sai dai kuma, tuni ta daɗe da yi wa mazan duniya gaba ɗaya kuɗin goro, hakan ya sa ba ta da lokacin su.


wp-content/uploads/2021/12/Kwamin-Nadama-by-Rashida-Usman.jpg

Kwamin Nadama

Baƙin kishi ya sa Ladiyo cakumar wuyar mijinta tana mai sauke masa kayan rashin mutunci tare da tabbatar mishi da cewa bai isa ya yo mata kishiya ba. Shi kuwa Kabiru, don ya gwada mata lallai ya haifu bai yi wata-wata ba ya danna mata saki biyu. Tun daga nan ta shiga tashin hankali da ruɗani, musamman da ta tuna cewa za ta bar gidan kuma zai kawo wata.


wp-content/uploads/2021/12/Ummu-Hani-by-Fadimafayau.jpg

Ummu Hani

Rayuwar Ummu Hani ta sauya cikin dare ɗaya, bayan mahaifiyarsu ta rasu ta barta da ƙanne biyar ba tare da wanda zai kula da su ba, ciki kuwa har da jariri sabon haihuwa. Sai dai ta ɗauki aniyar kulawa da ƙannen nata ko ana ha maza ana ha mata.


wp-content/uploads/2021/12/Baindiya-by-Haiman-Raees.jpg

Ba'indiya

Ba’indiya kundi ne na rubutattun waƙoƙin yabo wa jaruman fina-finan Indiya. Any shirya waɗannan waƙoƙi ne bisa hikima da basira domin samar da nishaɗi.


wp-content/uploads/2021/12/Sirrin-Boye-by-Halima-Zakariyya.jpg

Sirrin Boye

Mairo yarinya ce mai kaza-kazar, bata da son jiki ko yanƙwana. Talakawa ne su masu rufin asiri. Tana da yayye guda biyu, Amadu da Kabiru. Tana matuƙar tsoron Yaya Amadu, sannan ta shaƙu sosai da Yaya Kabiru. Babban abin da ke ɗaure wa Mairo kai shi ne irin yadda ba sa so Kulu tana raɓar inda take, ta kasa fahimtar wane irin ɓoyayyen sirri ne ke tattare da Kulu wadda tun tana ƙarama take fama da cuta mai kama da ta hauka.


wp-content/uploads/2021/12/Alkawarin-Allah-by-Khadija-B.-Ahamad.jpg

Alkawarin Allah

Alhaji Usman Ibrahim Matawalle ba ya barin kowa zuwa zance wajen ‘ya’yansa, watau Maryam da Fatima saboda mutum ne shi mai zafi sosai. Soyayyar Maryam ta kama Nuraddeen, kuma sai bibiyarta yake yi har sai da ya gano gidansu. Shin ko zai dace da samun soyayyar Maryam tare da amincewar mahaifinta?


wp-content/uploads/2021/12/Wa-Ya-Kashe-Zahrau-by-Fatima-Galadima.jpg

Wa Ya Kashe Zahra'u?

Matakin tashin hankali da ruɗanin da ya ɓarke a gidan Alhaji Aliyu Ibrahim MD ya kai maƙura, yayin da aka wayi garin ranar ɗaurin auren ‘yarsa guda ɗaya tilo a duniya aka same ta a mace. Angon nata, wato Zayyan ya suma sakamakon jin wannan mummunan labari. APC da DCP Sardauna suna ta bincike domin gano wanda ya shigo har cikin gidan ya kashe Zahara’u duk kuwa da tarin matakan tsaron da ke gidan.


wp-content/uploads/2021/12/Daurin-Huhun-Goro-by-Rashida-Usman.jpg

Daurin Huhun Goro

Halin yunwa, talauci da kuma matsatsin rayuwa da ake ciki ne suka tunzura Tabawa har ta kai ga tana bin layi da lunguna tana zagin shugabanni, ‘yan siya da kuma ‘yan kasuwa. Domin ita a ganinta, duk su ne sanadin faruwar hakan a cikin al’umma. Ta kuma ƙudiri aniyar kawo sauyi game da wannan lamari.


wp-content/uploads/2023/07/Wata-Rayuwa-Ce-by-Khadijah-Ishaq.jpg

Wata Rayuwa Ce

Alhaji Buhari hamshaƙin mai kuɗi ne na gaban kwatance, sai dai matarsa Hajiya Jamila ta hana shi saƙat saboda neman abin duniya. Wannan dalili ne ma ya sa ta sa Maza da Alamz suka sace Sadiya da ‘yarta suka jefar da ita. Ya zama dole Alhaji Buhari da amininsa Alhaji Saleh su nemo Sadiya matuƙar suna so burinsu ya cika.


wp-content/uploads/2021/12/Kudi-Ko-Rai-by-Mustapha-Abbas.jpg

Kudi Ko Rai

Alhaji Ahmad Mukhtar na ta faman kashe kuɗi wajen ganin ya samar wa ɗansa guda ɗaya tilo wato Mashkur lafiya amma abu ya ci tura. Sai dai duk da haka ya sha alwashin ƙarar da dukiyarsa gaba ɗaya wajen nema wa ɗan nasa lafiya. Abinda bai sani ba shi ne, matarsa Zinatu na da hannu dumu-dumu bisa rashin lafiyar ɗan nasa.


wp-content/uploads/2021/12/Kukan-Kurchiya-by-Halima-Zakariyya.jpg

Kukan Kurciya

Ana gobe ɗaurin auren Mujahida da masoyinta da suka yi shekaru biyar suna soyayya, wato Nura ya ce ya fasa. A gigice ta shiga gida da taimakon ƙanenta Mujtafa, sai dai shigarta cikin gidan ya yi daidai da furta kalmar saki da mahaifinta wato Habibu ya yi ga mahaifiyarta wato Bilkisu.


wp-content/uploads/2021/12/Nawa-Bangaren-by-Queen-Nasmah.jpeg

Nawa Bangaren

Gimbiya Naheela ita ce ‘ya guda ɗaya tilo a wurin sarkin aljanun Zuwatu, wato Zawatunduma. Naheela ta jarabtu da soyayyar Yarima Naheel ɗan sarkin aljanu Zimba, sai dai shi kuma baya son ta, ya tsane ta matuƙa. Wannan dalili ne ya sa ta aika Zamzila domin ya nemo mata inda Yariman ya ɓoye.


wp-content/uploads/2021/12/Mysterious-by-Haiman-Raees-Mujahid-Matashi.jpg

Mysterious Pen

A collection of mysterious poems about society, religion and more. Dive in and enjoy, as the mysteries unfold.


wp-content/uploads/2021/12/Kaddarar-Mutum-by-Mustapha-Abbas.jpg

Kaddarar Mutum

Tun bayan mutuwar mahaifinta, wato Malam Tanimu, Asma’u da mahaifiyarta Inna Hauwa suka shiga cikin tsangwama a wurin mutanen ƙauyen Somayi. Hakan ko ya samo asali ne sabo da ta ƙi amincewa da batun auren duk samarin garin, musamman Muntari da yake ɗan Maigari. Ba zato ba tsammani kuma sai wani ya yi wa Asma’u fyaɗe har ta samu ciki. Wannan dalili ne ya tursasa mata barin ƙauyen ba don tana so ba. Ko za ta samu mafita a inda ta nufa?


wp-content/uploads/2021/12/Na-Cancanta-by-Halimatu-Khalil.jpg

Na Cancanta

Sumayya Abdullah Khalil mace ce mai hakuri da tarbiyya daidai gwargwado. Talakawa ne su, wannan ya sa a dangi ake ƙyamar su, ake gudun su kuma ba a son ganin su. Domin da an gansu za a fara tunanin wani abu suka zo nema. Babban abin da ya fi ci wa Sumayya tuwo a ƙwarya shi ne irin yadda dangi ke zargin halin da suke ciki ya ta’allaƙa ne da ‘ƙashin tsiya’ irin na mahaifiyarsu.


wp-content/uploads/2021/12/Allah-Daya-Gari-Banban-by-Bukar-Mada.jpeg

Allah Daya Gari Banban

Yayin da matar Abdullahi masunci ta haihu a karo na goma a rayuwarta, sun yi farin ciki sosai. Hakan ne ma ya sa Abdullahi tafiya bakin kogi domin ya yi su ya samo abinda zai ciyar da iyalansa. Amma wani abin mamaki shi ne, sai da ya yi kwanaki arba’in yana zuwa su ba tare da ya kama ko da kwaɗo ba, ga shi yana matuƙar jin kunyar mai gurasa wanda ke binsa bashin da yake ta bashi a kullum ba tare da gajiya ba.


wp-content/uploads/2021/12/Lullubin-Biri-by-Halima-Zakariyya.jpg

Lullubin Biri

Hankalin Yusuf ya yi matuƙar tashi sakamakon halin da matar da aka kwantar a asibitin take ciki, matsananciyar damuwa ce take fama da ita wadda har ta kai ta ga fita hayyacinta. A gefe kuma, Fillo (Halimatu) da masoyinta Amir suna ci gaba da more soyayyar su, har ma maganar aure ta shiga tsakani. Kwatsam sai Turaki, wanda ke ɗauke da wani ɓoyayyen sirri ya shigo cikin rayuwar Halima. Shin ko menene wannan sirrin.


wp-content/uploads/2021/12/Kasaitar-So-by-Nana-Haleema.jpg

Kasaitar So

Zaid sangartaccen matashi ne wanda ke ji da kansa da kuma taƙama da kuɗi. Yana da yaransa ‘yan daba da ke masa aiki, su ne Gaye, Mugu da kuma Wizzy. Ƙaddarar rayuwa ta sa Gaye ya fara bibiyar Jidda, wadda ƙanwar Ibteesam ce wato Maryam, zafin rai irin na Ibteesam ya sa ta yi musu kaca-kaca, shi kuma tun daga nan ya sha alwashin sai ya lalata mata rayuwa.


wp-content/uploads/2021/12/Laifin-Wa-by-Mustapha-Abbas-RLemo.jpeg

Laifin Wa?

Ladidi matashiya ce mai ji da ƙuruciya, hakan ya sa ta faɗa harkar bin maza domin ta hucewa kanta haushin rashin ɗauke mata ɗawainiya da iyayenta suka kasa. Duk da cewa sun san irin abin da ɗiyarsu ke aikatawa, amma ba su da ta cewa. Saboda wani lokaci ma wurinta suke zuwa su yi ‘yar murya.


wp-content/uploads/2021/12/Ta-Ki-Aure-by-Fatima-Abubakar-Saje.jpg

Ta Ki Aure

Sawwama da Kawwama yaya da ƙanwa ne da suka jima basu yi aure ba. Shekarar Sawwama talatin da biyar ba ta yi aure ba, yayinda ita kuma Kawwama shekararta talatin da biyu ba ta yi aure ba. Hakan ya sa kowa a dangi ke ta faman yi musu surutu. Kwatsam sai ga Jalil ya zo neman auren Kawwama, an sha biki an gwangwaje, sai dai kuma Jalil na ɗauke da wani ɓoyayyen lamari da ba kowa ya san da shi ba.


wp-content/uploads/2021/12/Indo-A-Birni-by-Rashida-Usman.jpg

Indo A Birni

Indo ta gallabi mutanen ƙauyensu baki ɗaya. Kowa ƙorafi yake yi da ita, abu ya yi tsamari dai har da kai ta ƙara gaban Mai Gari, kullum iyayenta mutanen kirki suna zarya wajen magance matsalolin da take jawo musu amma kamar ba sa yi. Sai dai duk da wannan hauka da rashin kan gado nata, Allah ya jarrabe ta da soyayyar Muhammad Mustapha wanda ke zuwa daga birni. Anya kuwa za ta samu shiga a wurinsa? Musamman da yake akwai wata ‘yar uwar tasa ma a birni da take son shi amma ba ya ko kula ta.


wp-content/uploads/2021/12/Izina-by-Khadija-B.-Ahamad.jpg

Izina

Aisha (Ma’isha) da Abdul’aziz ‘yan’uwan juna ne, kuma dukkansu lauyoyi ne. Sai dai a karo farko za su kara da juna a gaban ƙuliya domin kare mutane biyu. Iya Aisha tana ƙoƙarin ƙwato wa wata mata da ‘yarta
‘yancinsu ne a hannun wani mugun mai kuɗi. Shi kuma Abdul’aziz yana kare shi. A wani ɓangaren kuma, yayansu jami’in ƙasa da ƙasa, Deputy Commissioner of Police Abdulmalik Ibrahim Ahmad ya zo Nijeriya domin ya gudanar da bincike na musamman akan kisan da aka yi wa wani babban jami’in tsaro, kwatsam kuma sai ƙaddara ta haɗa shi da ‘Yar Jarida Intasar Mahmood Abdullahi.


wp-content/uploads/2021/12/Na-Sake-Ta-by-Mustapha-Abbas-1.jpg

Na Sake Ta

Hamshaƙin matashin mai kuɗin da ake ji da shi, wato Usman One boy ya samu Kamal mayen kuɗi da batun wani irin kasuwanci mai ban mamaki. Usman ya yi alƙawarin ba wa Kamal kuɗi naira na gugar naira har miliyan biyar, matuƙar dai ya yarda zai saki matarsa Hajir domin ya aure ta. Ashe Kamal na gab ne da fahimtar cewa ba komai bane kuɗi ke iya yi wa mutum.


wp-content/uploads/2021/12/Waye-Zabin-Munibat-by-Husaina-B.-Abubakar.jpeg

Waye Zabin Munibat?

Munibat natsattsiyar yarinya ce, maraici ya sa ta shiga cikin uƙuba a hannun matar mahaifinta wadda a kullum take nuna mata ƙauna a fili, a ɓoye kuma tana gasa mata gyaɗa a hannu. Shin wane zaɓi Munibat take da shi? Yaya za ta yi wajen ganin ta fita daga wannan ƙangi?


wp-content/uploads/2021/12/Nisfu-Deeniy-by-Deejasmah.jpg

Nisfu Deeniy

Nadeefah Yusuf Yerwa, wacce a gidansu ake kira da Lele, kyakkyawar budurwa ce ajin farko. Allah ya jarrabe ta da son Burhan Abdallah Yerwa wanda ake kira da Islaam, son da take yi masa ya yi ƙarfin da har sai da ta fito fili ta faɗa mishi abinda ke cikin zuciyarta. Sai dai shi kuma ba ya sonta, bai ma ɗauketa da muhimmancin da zai iya ko kula ta ba, a madadin hakan, Suliem Aliyu Yerwa yake so, ita kuma bata ma san yana yi ba. Wannan soyayya ta mutane uku kuma ‘yan ahali ɗaya tana ɗauke da jimirɗa sosai. Waye zai yi nasara?


wp-content/uploads/2021/12/Su-Ne-Sila-by-Aisha-Abdullahi-Yabo.jpg

Su Ne Sila

Tsananin raɗaɗi da zogin da ciwukan jikin Zainab ke yi mata ba su kai rabin wanda zuciyarta ke yi mata ba sakamakon tsintar kanta da ta yi a gidan yari. Duk irin tsusayinta da Safiya ke ji bai sa ta saki jiki da ita ba. Daga ƙarshe ma dai yanke shawarar kashe kanta ta yi. Domin a tunaninta hakan kaɗai mafita a gareta.


wp-content/uploads/2021/12/Munafukin-Miji-by-Naima-Sulaiman-Sarauta.jpg

Munafukin Miji

Ridayya na matuƙar son mijinta Zameer. Ta mallaka mishi dukkan rayuwarta da duk wani abu da ta mallaka. Saboda shi ta rabu da iyayenta da ‘yan’uwanta. Sai dai shi kuma a nashi ɓangaren, Zameer cin amanarta yake yi, ha’intarta yake yi6, kuma amfani da ita kawai yake yi wajen cimma muradansa. Duk irin yadda Mardiyya ta so ta nuna wa Ridayya gaskiyar abinda mijinta ke yi ta kasa fahimta saboda makauniyar soyayyar da take yi mishi.


wp-content/uploads/2021/12/Mutum-Da-Kaddararsa-by-Maryam-Ibrahim-Litee.jpg

Mutum Da Kaddararsa

Bilkisu matashiyar mace ce mai ƙarancin shekaru, sai dai ƙaddarar rayuwa ta sa zaman aure ya gagare ta. Da farko ta auri Aminu wanda suka samu ɗaa guda ɗaya da shi wato Amir. Bayan sun rabu ne sai ta auri Malam inda suke zaune tare da uwargidarsa Hajja. Kisisinar amaryar Malam ne tai ta jawo musu damuwa har aurenta ya mutu a karo na biyu. Bayan ta koma gidan gwaggo Maryam ne masoya biyu suka fito neman aurenta. Hassan mai shagon siyar da kayayyaki da kuma Ɗan Majalisa Hashim Bello. Kowa na mata kwaɗayin auren Ɗan Majalisa, sai dai ita kuma tunaninta daban.


wp-content/uploads/2023/11/Abbakar-by-Fadimafayau.jpg

Abbakar

Abbakar Malami ne da ke koyarwa a jama’ar B.U.K. Allah ya jarrabe shi da matsanancin son wata ɗalibarsa mai suna Ummulkhairi, sai dai ya kasa faɗa mata. Kwatsam watarana sai ya gano cewa ashe matar aure ce, har ma tana da ciki. A gefe kuma ga ƙawarta Aisha da take matuƙar son Abbakar ɗin.


wp-content/uploads/2021/12/Tsinin-Harshe-Ya-Fi-Na-Mashi-by-Sadik-Abubakar.jpg

Tsinin Harshe Ya Fi Na Mashi

Al’amura sun dagulewa Zainab tun bayan da bakinta ya jawo mata jalli-joga sakamakon sharrin maita da ta yi wa Jummai a gidan suna. Lamarin ya kai matuƙa a fagen tsamari ne ya yin da aka aiko mata da takardar sammaci daga kotu a bisa wannan zargi, ana tsaka da wannan kuma sai mijinta Auwal ya sake ta.


wp-content/uploads/2021/12/Jini-Ya-Tsaga-by-Hajara-Ahmad-Hussain.jpg

Jini Ya Tsaga

Hafsat bazawara ce da ke zaman zawarci a gidansu. Mahaifiyarta ta rabu da mahaifinsu mai suna Kamaluddeen, amma sauran matan nasa guda uku suna zaman lafiya sosai da junansu. Hafsat ta sha alwashin kai mahaifinta ƙara ofishin ‘Yansanda bisa zargin nuna rashin adalci a tsakanin matansa. Shin ko za ta ci nasara?


wp-content/uploads/2021/12/Nima-Matarsa-Ce-by-Habiba-Abubakar-Imam.jpg

Nima Matarsa Ce

Taufiq ya shiga gagarumar damuwa sakamakon irin bita-da-ƙullin surikarsa wato Hajiya Murjanatu. Tun da ya nuna yana son ‘yarta Mujaheeda, shikenan ta shiga kawo tsirfa iri-iri duk don ta ga an fasa, domin a cewarta bai dace ya auri ɗiyarta ba. Shi kuma yana son Mujaheed, ita ma kuma tana sonsa. Anya kuwa ko da sun yi auren Hajiya Murjanatu za ta bar su su zauna lafiya?


wp-content/uploads/2021/12/Duniyar-El-Dorado-by-Abubakar-Abubakar.jpg

Duniyar El-Dorado

Bayan shuɗewar lokaci mai tsawo da rabuwarsu, Khadija Muhammad Lamiɗo, wadda aka fi sani da Deejah, ta kawo wa Abou Adem ziyarar bazata a gidan yarin Kirikiri Maximum Security Prison da ke Apapa, Lagos State, Nigeria. Wa ya faɗa mata an kama shi? Me ya kawo ta? Waɗannan na daga cikin tambayoyin da yake buƙatar sani a hanzarce.


wp-content/uploads/2021/12/Saadatu-by-Usaina-Salisu.jpg

Sa'adatu

Zarah da Ahmed masoyan juna ne, soyayyarsu har ta kai ga an saka ranar aurensu. Ana saura sati biyu bikin ne sai aka sace Zarah, ba kowa ne ya sace ta ba face Aljana Zainab da masoyinta Safwan ɗan sarkin aljanu. Sun yi hakan ne kuma domin su cimma wani mummunan ƙuduri nasu da suke da shi akan waɗannan masoya.


wp-content/uploads/2021/12/Falsafa-by-Haiman-Raees-Mujahid-Matashi.jpg

Falsafa

Waƙoƙin Falsafa waƙoƙi ne da aka tsara su akan fannoni da dama dama. Kama daga soyayya, zamantakewa da sauran al’amuran yau da kullum. An shirya waɗannan waƙoƙi ne domin su zamo ababen ɗebe kewa ga masu karatu tare da kaifafa tunani game da batutuwa masu amfani.


wp-content/uploads/2021/12/Mafarkin-Deluwa-by-Asmau-Abdallah-Ibrahim.jpeg

Mafarkin Deluwa

Malam Shitu, Malam Lawal, Malam Tsalha da Malam Zaidu ma’aikatan wata maƙabarta ce da ke ƙauyen Ɗanduƙus. Tsananin firgici ne ya ziyarce su a lokacin da suka ga wata ‘yar wada ta shigo maƙabartar da suke kula da ita tana neman taimakon su binne mata gawar. Saratu, wadda aka fi sani da Deluwa ta yanke shawarar kashe masoyinta Chibunzu, kamar yadda Alhaji Labaran ya umurta domin cika burinta na zuwa Makka.


wp-content/uploads/2021/12/Ba-Kauyanci-Ba-Ne-by-Fatima-Abubakar-Saje.jpg

Ba Kauyanci Ba Ne

Alhaji Abdulƙadir mutum ne ɗan zamani wanda kiyaye haƙƙoƙin addini bai dame shi ba, to amma ‘yarsa Salma da mahaifiyarta Hajiya Bilkisu suna da kyawawan halaye kuma suna matuƙar kiyaye dokokin shari’ar Musulunci. Alhaji Sameer da Hajiya Samira suna da ɗa guda ɗaya da suka haifa mai suna Kamal. Duk iya ƙoƙarin da Alhaji Sameer yake yi na ganin Kamal ya shiryu, ita mahaifiyarsa gani take takura ce. Kamal ya kama hannun Salma a wurin wani taro inda ta wanke shi da mari. Sai daga baya yake jin ashe mahaifiyar Salma mahaifinsa ya fara so ya aura kafin mahaifiyarsa.


wp-content/uploads/2021/12/Abinda-Babba-Ya-Hango-by-Fatima-Abubakar-Saje.jpg

Abinda Babba Ya Hango

Okasha Sani Sa’id matashi ne mai taƙama da kuɗi da kyawun halitta. Hakan ya sa yake wasa da hankulan ‘yanmata tare da ɓata musu rayuwa. Ƙaddara ce ta haɗa shi da Jameela, wadda ta bijirewa shawarar mahaifinta ta auri Okasha ba don suna so ba. Kash! Da ta san abin da zai biyo baya da ba ta yi wannan aure ba.


wp-content/uploads/2021/12/Ranar-Birthday-by-Abba-Abubakar-Yakubu.jpg

Ranar Birthday

Ruƙayya Mohammed (Rukky) ta shirya tsaf domin tunkarar ranar zagayowar haihuwarta da wani irin bazata. Ta sha alwashin kawo gyara, sauyi da kuma canji a zukatan mutane game da yadda aka ɗauki bikin zagayowar ranar haihuwa (wato Birthday Party) a cikin al’ummar Hausawa. Shin ko za ta yi nasara?


wp-content/uploads/2021/12/Zuciya-da-Hawaye-by-Aisha-Faruk.jpg

Zuciya Da Hawaye

Rumana tana cikin wani irin mummunan hali sakamakon farmakin da mahaifinta ke yawan kai mata don ganin ya cimma burinsa. Alhaji ya damu sosai bisa mafarkin da ya yi da masoyinsa Jabir, yayin da ita kuma Zully take fusace da mahaifinta sakamakon irin azabar da yake gana wa mahaifiyarta. Shin me ke faruwa ne a cikin zukatansu? Me ke hana duk wanda ya yi yunƙurin keta wa Rumana haddi damar cimma burinsa?


wp-content/uploads/2021/12/Kabari-by-Fatima-Abubakar-Saje.jpg

Kabari

Bawa ba ya sanin muhimmancin lokaci har sai ya ji shi a cikin kabari. Kabari shi ne gidan kowa. Yaro ko babba, mace ko namiji, attajiri ko talaka, jahili ko malami. Kabari na maraba da kai, ko ka shirya ko ba ka shirya ba.


wp-content/uploads/2021/12/Dare-Daya-by-Yareema-Shaheed-1.jpg

Dare Daya

Salim ya shiga cikin jarrabawa babba. Shekaru uku kenan da kammala karatunsa amma har yanzu bai samu aikin yi ba. Kwatsam! Ana cikin haka kuma sai wani mai mota ya bige mahaifiyarsa, inda har ta samu karaya bakwai a jikinta. Likita ya bayyana za a yi mata aiki, amma ana buƙatar Naira miliyan uku domin yin aikin. Ga shi Salim ba shi da kosisi.


wp-content/uploads/2021/12/Maaurata-by-Aisha-Abdullahi-Yabo.jpg

Ma'aurata

Habibu mijin Ruƙayya ne, kullum cikin yi mishi masifa take saboda in ya fita gida ba ya dawowa sai dare sosai, hakan kuwa ya faru ne saboda ƙazantarta da rashin girki da gyaran jiki, wani lokaci ma hana shi haƙƙinsa take yi ta ce sai ya biya. Fahad shi ma ba ya wani zaman gida, kuma a buge yake dawowa Fatima, wani lokaci ma ya haɗa mata da duka da zagi. Shin ko za su samu mafita?


wp-content/uploads/2021/12/Mijina-Wukar-Fidar-Cikina-by-Ahmad-S.-Muri.jpg

Mijina Wukar Fidar Cikina

Salahuddeen na kwance tare da matarsa Muhibbat sai ga kidnappers sun yi musu dirar mikiya inda suka ɗauke shi tare da yi wa matarsa dukan tsiya. Bayan kwana huɗu da faruwar hakan sai suka buƙaci da a basu miliyan ɗari. To sai dai yanayin yadda suka san bayanai game da surikar Salahuddeen ya tabbatar da cewa akwai wani makusanci da ke basu bayanai a ɓoye. To amma waye?


wp-content/uploads/2021/12/Tekun-Labarai-by-Danladi-Z.-Haruna.jpg

Tekun Labarai

Bayan Sarki Shamsuddini da matarsa sun gudu da tsakar dare domin su tsira daga harin da waziri Ashfanu da mabiyansa suka kawo musu. Dole tausa suka bar ɗansu jariri a tsakiyar dokar daji. Bayan komai ya lafa sai suka yi neman duniya amma basu ganshi ba. Sai dai ƙaddara ba ta gama jaraba su ba, domin kuwa ɗa ya dawo gidan ubansa ba tare da shi kanshi ya sani ba.


wp-content/uploads/2021/12/Tsanin-Nasara-by-Hamza-Dawaki.jpg

Tsanin Nasara

Duk da cewa amaryar ta jima a gidan mijinta har ma ta tara yara. Gwalagwalan shawarwarin da mahaifinta ya ba ta sun zamo mata tsanin hawa matakin nasara a gidan aurenta da ma rayuwarta baki ɗaya.


wp-content/uploads/2022/10/Wane-Ne-Ni-by-Umar-bin-Ally.jpeg

Wane Ne Ni?

Ba zato ba tsammani Ahmad ya farka ya ganshi a gadon asibiti ba tare da ya san yadda aka yi ya zo wurin ba. Ba ma wannan ba, ya kasa tuna hatta sunansa da kuma ko shi waye. Bayan Dr. Aminu ya yi masa wasu ‘yan gwaje-gwaje sai aka gano cewa ya kamu da cutar mantuwa ne. Kwatsam sai ga wata mai suna Hafsat ta yi wa rayuwar shi shigar ba zato, sai dai likita kuma ya ce ita ɗin ba gaskiya bace, kawai tunaninsa yake hasaso mishi hakan. Shin ko Ahmad zai yarda da wannan batun?


wp-content/uploads/2021/12/Soyayyar-Da-Na-Yi-by-Habiba-Maina.jpg

Soyayyar Da Na Yi

Mamma ta fidda rai gaba ɗaya da samun soyayyar gaskiya sakamakon rashin masoyinta Abdul da ta yi a baya. Ga kuma wani matashin saurayin na ƙoƙarin kunno kai cikin rayuwarta a wani irin yanayi mai ban mamaki.


wp-content/uploads/2022/12/Sakacina-Ko-Halin-Maza-by-Jamila-Lawal-Zango-Jamcy-.jpeg

Sakacina Ko Halin Maza?

Juwairiyya yarinya ce mai matuƙar kamun kai. Sai dai halin da suke ciki na talauci na neman yi wa mutuncin nata barazana. Ga kuma ƙanin mahaifinta Baba Sani da ya kafa mata ƙahon zuƙa ba tare da wani takamaiman dalili ba.


wp-content/uploads/2021/12/Marubuci-by-Umar-bin-Ally.jpg

Marubuci

Yayinda wani matashin marubuci ya saurari wata tattaunawa da aka yi da wani fitaccen jarumin fina-finai, hakan ya ƙara mishi ƙwarin gwiwar ci gaba da rubutu tare da zama tsanin samun nasararsa a harkar rubutu.


wp-content/uploads/2021/12/Bincike-by-Umar-bin-Ally-1.jpg

Bincike

Sipeta Sani ƙawararren Ɗan Sanda ne da bai san faɗuwa ba a aikinsa, sai dai garkuwa da ɗan minista da wasu ɓata gari suka yi na nema ya kai masa ruwa rana a bincikensa.


wp-content/uploads/2021/12/Mijin-Novel-by-Lubna-Sufyan.jpg

Mijin Novel

Bayan fafutuka da kai ruwa rana, Hindatu ta samu irin mijin da take so, wato mijin Novel. Kyakkyawa, mai ilimi, kuɗi da sauransu. Sai dai abinda ba ta sani ba shi ne, shin ko ta shirya yin sadaukarwar da ta dace domin yin rayuwar aure da Hamza?


wp-content/uploads/2021/12/Fatalwar-Sinu-by-Haiman-Raees.jpg

Fatalwar Sinu

Katoɓara da ɓarin baki suka sa Haiman bayyanawa duniya irin abubuwan da yake so a bashi a matsayin kyautar barka da sallah. Sai dai ya samu kyautar da ta fi ƙarfin shi, yayin da wata kyautar ta fito daga lahira kuma daga hannun wani gagarumin maƙiyin da bai san yana da shi ba.


wp-content/uploads/2021/12/Akan-So-by-Lubna-Sufyan-1.jpg

Akan So

Safiyya ta biyewa So da ya makantar da ita ta bi Fu’ad sun yi aure ana gab da yi mata aure da Ado. Wannan ya sa iyayenta suka tsame hannunsu daga komai nata. Shi ma Fu’ad ɗin hakan ce ta faru da shi. Sai dai tashin hankali ya fara ratsowa cikin zamantakewar tasu ne yayin da Fu’ad ya fara nuna ƙiyayyar shi da son haihuwa. Saboda hakan ne ma ya je asibiti aka kashe mishi ƙwayoyin haihuwar shi. Abin da bai sani ba shi ne, Allah Ya riga Ya ƙaddara rabo a tsakaninsu da Safiyya.


wp-content/uploads/2021/12/Ko-Ruwa-Na-Gama-Ba-Ki-by-Hadiza-Isyaku.jpg

Ko Ruwa Na Gama Ba Ki

Kwaɗayin abin duniya ya sa ‘yar gidan Malam Amadu ba wa saurayi kanta har ya yi mata cikin shege. Gashi kuma mahaifinta shi ne limamin ƙauyensu, ciki kuma har ya kai kusan wata biyar ba tare da an ankare ba. Wannan dalili ne ya sa mahaifiyarta Asabe ta ɗauki karan tsana ta ɗora mata.


wp-content/uploads/2021/12/Tun-A-Duniya-by-Nana-Aicha-Hamissou.jpg

Tun A Duniya

Alhaji Garba ya shiga wani irin mummunan hali na ban mamaki. Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci duk dukiyar da ya tara ta salwanta, sannan lafiyarsa ma kanta ta fara ƙoƙarin ƙaurace masa.


wp-content/uploads/2021/12/Canjin-Bazata-by-Maryam-Ibrahim-Litee.jpg

Canjin Bazata

Halin rashi ya yawaita, gashi bikin Yayar Shuhaina ya matso, sai dai babu kuɗin da za a yi musu kayan ɗaki. ‘Yar gonar gadon tasu da aka saka a kasuwa kuma ba a yi mata tayin daraja ba. Ga mutanen gida sai yada wa mahaifiyar su Shuhaina zance suke yi, domin su a wurinsu, duk macen da ba a yi wa gara da kayan ɗaki na kece raini ba, to ba ta cika ‘ya ba.


wp-content/uploads/2021/12/Fasaha-Haimaniyya-by-Haiman-Raees.jpg

Fasaha Haimaniyya

An gwangwaje fasaha, hikima da kuma fikira wajen shirya waƙoƙin da ke cikin wannan kundi domin su farkar, fadaƙar, nishaɗantar, su kuma nusar da duk wanda ya karanta su.


wp-content/uploads/2021/12/Jawaheer-by-Fatima-Ibrahim-Dan-Borno.jpg

Jawaheer

Mujaheed Muhammad, wanda aka fi sani da M.D ƙawararren jami’in C.I.D ne da ake ji da shi a duk faɗin Nijeriya. An turo shi garin Kaduna ne domin ya gudanar da gagarumin bincike akan Alhaji Saleh Mu’azu Mainasara. Ƙaddara sai ta haɗa su da Jawaheer, wadda ‘ya ce a wurin Alhaji Saleh Mu’azu Mainasara, wadda ta faɗa kogin son shi kamar ta yi hauka. Shi kuwa ya yi alƙawarin babu wata mace da zai iya rayuwa da ita bayan tsohuwar matarsa. Babban abinda ke ƙara dagula mishi lissafi shi ne, irin yadda Jawaheer ke yin abubuwa irin na tsohuwar matar tasa, wato Nayla.


wp-content/uploads/2021/12/Bakon-Yanayi-by-Hadiza-D.-Auta.jpg

Bakon Yanayi

Munawwa da Munara yan tagwaye ne masu kama daya. Yana da wuya ake iya bambance su, to amma wannan kamar a ido kawai ta tsaya domin kuwa halayyansu sunyi hanun riga. Wannan banbanci nasu ya jawo saurayin daya daga cikin su ya zo musu da wani Sabon Yanayi na jarraba soyayyarsu. Shin yaya zata kaya? Shin mai saurayi zata ci gaba da samun soyayyar saurayinta ko ko labarin zai canja?


wp-content/uploads/2021/12/Jini-Ba-Ya-Maganin-Kishirwa-by-Qurratul-Ayn-Salees.jpg

Jini Ba Ya Maganin Kishirwa

Kamal ya shirya tsaf domin ganin ya auri Hajiya Shema’u, duk kuwa da tazarar shekarun da ke tsakaninsu. Shi dai kawai miliyan ashirin ɗin da zai samu yake hange. Wannan dalili ne ya sa har suka fara samun matsala da babban abokinsa Zayyad da kuma ƙanwarsa Farida. Ita kuwa matarsa ta fari, Sakinah, haƙuri kawai take yi tare da maida komai ba komai ba. Shin ko zai hankalta ya sauka daga kan keken ɓeran da yake ƙoƙarin jefa kanshi?


wp-content/uploads/2021/12/Fansar-Fatalwa-by-Shamsiyya-Manga.jpg

Fansar Fatalwa

Ƙawaye sun yi wa Amrah mummunan lahani a rayuwa, wanda hakan ne ya zamo silar mutuwar ta. Hakan ya sa ta dawo a matsayin fatalwa tare da shan alwashin ɗaukar fansa a kansu. A bisa wannan dalili ne ta kawo wa Afrah farmaki ana saura kwana uku bikinta da masoyinta, wato Anwar. Shin wa kuma za ta kai wa hari na gaba?


wp-content/uploads/2021/12/Baba-Dattijo-Dan-Bursin-by-Mukhtar-Spikin.jpg

Baba Dattijo Dan Bursin

Yayin da wani ɗan jarida ya je gidan yarin Kurmawa da ke Kano ya gamu da wani dattijo mai ban mamaki da ke rayuwa a wannan gida na kaso. Shin ko ta yaya za a iya shari’ar kashe mutumin da ya riga da ya mutu tun shekaru 29 da suka gabata?


wp-content/uploads/2021/12/Ina-Matsalar-Take-by-Rahma-Sabo.jpg

Ina Matsalar Take?

Yayin da aka nemi Safwan sama ko ƙasa ba a gan shi ba har na tsawon wasu kwaki, sai mahaifiyarsa Amina ta matsa wa mahaifinsa game da nemo inda yake. Domin har ta fara fatan ina ma ace masu garkuwa da mutane ne suka sace shi, a tunaninta ko ba komai za su ji yana raye kuma su san nawa za su biya. Babban abinda ya fi tayar wa da mahaifin Safwan hankali shi ne irin yadda ya ziyarci ofisoshin ‘Yansanda har biyar amma babu inda aka yi mishi tarbar kirki, sai ma tayin kuɗi da suke masa. To ina matsalar take?


wp-content/uploads/2021/12/Hoton-Mijina-by-Aicha-Hamissou-2.png

Hoton Mijina

Muka amsawa da amin muna sakar wa juna murmushi. Tun daga ranar duk wasu makaman yaƙina na zubar da su, har mamakin kaina nake yi da tambayar kaina anya kuwa ni ce Rashida? Zaman lafiya ya samu matsuguni a tsakaninmu tamkar ba kishiyoyi ba. 


wp-content/uploads/2021/12/Zinariya-by-Queen-Nasmah.jpg

Zinariya

Tashin hankalin da ya afku a ƙauyen su Hamida ne ya sa ta rasa ‘yanuwanta gaba ɗaya kuma ta koma rayuwa a daji. A cikin wannan yanayi ne ta haifi Zinariya, kuma ba da jimawa ba ta rasu. Sarauniya Jahiyana wadda ke mulkin masarautar aljanu ta Gimatuwa ce ta tsince ta a dokar daji ta kai ta gidanta kuma har ya aiyana ta a matsayin wadda za ta gaje ta. Sai dai kuma wannan shiri bai yi wa gimbiya Juhaina daɗi ba. Shin ko yaya za ta ƙarke a tsakaninsu?


wp-content/uploads/2021/12/Rabon-A-Yi-by-Fareeda-Abdallah.jpg

Rabon A Yi

Farida, wadda aka fi sani da ‘Ferry’ ta yanke shawarar zuwa bikin babbar ƙawarta Jiddah, duk kuwa da cewa mijinta Mukhtar ya tabbatar mata da cewa baya so ta je. Hankalinta ya tashi sosai yayin da ta na gidan bikin aka ce an yi sata, ana cikin rigimar sata kuma aljanun wata suka tashi. Ga kuma Mukhtar yana kiranta a waya.


wp-content/uploads/2021/12/Aminaina-Ko-Ita-by-Rashida-Usman.jpg

Aminaina Ko Ita?

Nafisa, kyakkyawar matashiya mai tashe da ji da kanta, ta ɗana wa ɗaya daga cikin ‘ya’yan Ambasada Ahmad Ɗangiwa mai suna Haidar tarkon soyayyar ƙarya domin ta samu maƙudan kuɗaɗe a wurinsa. Abin da ba ta sani ba shi ne, rikicin da ke kewaye da ahalin su Haidar ya sha gaban tunaninta, domin kuwa akwai waɗanda suka fi ta son kuɗin da take hangen samu, kuma har kisa za su iya yi domin su cimma burinsu.


wp-content/uploads/2023/07/Barrister-by-Maryam-Ibrahim.jpg

Barrister

Burin Yazid na zama Barrister ya cika, dukkan ‘yan’uwansa kowa sai taya shi murna yake yi. Ita kuwa Nadiya, ta ƙwallafa rai akan Yazid, babu abinda take so face ganin ta aure shi, duk kuwa da cewa shi ba sonta yake yi ba. Zahra na cikin matsanancin tashin hankali sakamakon ciwon da mahaifiyarta ke yi wanda take buƙatar kuɗin kai ta asibiti. Ga kuma yayarta Zainab da kullum ba ta da aiki face musguna mata.


wp-content/uploads/2021/12/Wata-Kaddara-by-Shamsiyya-Manga.jpg

Wata Kaddara

Mubarak Yusuf Maikuɗi matashin mai kuɗi ne da ya taso da taka-tsan-tsan da kuma jajircewa akan tarbiyya. Babban abin da ya fi tsana a rayuwarshi ita ce sata. Sai dai kash… Ƙaddara ta sa ya auro ‘yar wani ƙasurgumin ɓarawo ba tare da ya sani ba.


wp-content/uploads/2021/12/Alkalamin-Kaddara-by-Lubna-Sufyan.jpg

Alkalamin Kaddara

Altaaf Tafida ya daɗe da yin aure amma har yanzu bai samu haihuwa ba, gashi kuma Allah ya jarabce shi da son yara. Kwatsam watarana sai ƙaddara ta sa ya ci karo da wasu ‘yan biyu waɗanda ko tantama babu nashi ne, sai dai karɓarsu daidai yake da neman jaki mai ƙaho. Rafiq ya kasa fahimtar dalilin da ya sa ba ya iya tuƙi, alhali kuwa yana iya tuna lokutan da yake tuƙa kansa a mota, tashin hankalinsa ya hauhawa ne ya yin da ya fahimci sabuwar amaryarsa Tasneem ta zo gidan shi ba tare da budurcinta ba. Kafin kuma ya gama ji da wannan, sai ga wani sabon asirin da ka iya rusa komai na rayuwarsa ya fara fitowa fili.


wp-content/uploads/2023/03/Warwara-by-Haiman-Raees.jpg

Warwara

Wasu al’amuran suna buƙatar warwarar zare daga cikin abawa kafin a fahimce su da kyau.


wp-content/uploads/2022/10/Hukuncin-Allah-by-Umar-bin-Ally.jpeg

Hukuncin Allah

Salim matashi ne da bai yarda da cewa abubuwa suna faruwa ba ne a bisa yadda Allah ya ƙaddara za su faru ba. Abinda ya aminta da shi kawai shi ne, duk wani mummunan abu da ka ga ya faru, to sakacin wanda abin ya faru gare shi ne ya ja mishi.


wp-content/uploads/2021/12/Yes-She-Is-by-Fatima-Abubakar-Saje-1.jpg

Yes, She Is

A mother’s love is irreplaceable, her beauty is unimaginable and her heart is beyond this world.


wp-content/uploads/2023/02/Ina-So-by-Muntasir-Shehu.jpeg

Ina So

Halima mace ce mai kamun kai da shiga ta kamala a kowane lokaci, ba ta taɓa bayyana fuskarta hatta a wurin aikinta. Kullum cikin saka niƙabi take. Rayuwarta ta canza ne sakamakon dawowar ɗan mai kamfanin da take yi wa aiki daga ƙasar waje. Shin ko izzar Ali za ta yi tasiri akan Halima?


wp-content/uploads/2022/06/Voice-of-Love-by-Haiman-Raees.jpeg

Voice of Love

Love is a living, breathing entity by itself. It is adorable to feel, but seldom to hear. These voices of love are yearning to be heard, so let’s hear them through this collection of poems.


wp-content/uploads/2021/12/Relationship-by-Fatima-Abubakar-Saje-1.jpg

Relationship

Dwell in this piece of work to find the meaning and purpose of relationship.


wp-content/uploads/2021/10/Kwaya-Tushen-Tsiya-by-Danladi-Haruna.jpeg

Kwaya Tushen Tsiya

Ƙalubalen rayuwa ya sa wani matashi yanke shawarar shan miyagun ƙwayoyi domin su taimaka mishi wajen ɗaukar fansa. Abinda bai sani ba shi ne, su ma ƙwayoyin tasu rigimar ta musamman ce.


wp-content/uploads/2023/03/Abul-Khair-by-Salmeert-Sani-Salman.jpg

Abul-Khair

‘Yan biyu masu matuƙar kama da junansu wato Abul da Khair kyawawa ne na gaban kwatance. Saboda tsabar kamanninsu ma ba kowa ke iya bambance su ba. Sai dai kuma akwai wani ɓoyayyen lamari game da su. Shin ko wane irin lamari ne?


wp-content/uploads/2022/11/Rayuwarmu-by-Lubna-Sufyan.png

Rayuwarmu

Hajiya Beeba ta asirce Auwal domin ganin ta mallake shi ko ta halin ƙaƙa. A sanadiyar wannan asiri ne har ta raba shi da matarsa ta farko, kula da su ya dawo hannun Dawud duk da ƙarancin shekarunsa. Tashin hankali ya yi wa Labeeb yawa, abubuwa sun cukurkuɗe mishi. Dukkan ‘yan gidansu sun canza mishi. Ga Dawud na fushi da shi saboda cikin da ke jikin Zulfa, ga yaro an kawo mai da bai san daga inda ya fito ba, ga matarsa na neman rabuwa da shi, babban abokin shi ba sa ko magana, kwatsam kuma sai ƙaramin ƙanin shi ya mutu.


wp-content/uploads/2023/02/Bakar-Tafiya-by-Amina-Abubakar.jpg

Bakar Tafiya

Basma, Jafar, Salma, Rabson Guy da Biba sun shirya tsaf domin yin wata doguwar tafiya, sai dai kafin su isa inda suka nufa dole sai sun bi wata shu’umar hanya wadda ta ratsa ta cikin wani baƙin daji da ake yi wa laƙabi da ‘Kai Ka Zo.’ Kowa a cikinsu tana da babban dalilin da ya sa zai yi wannan tafiya. Sai dai tun kafin a yi nisa kowannensu ya fara da na sanin yin tafiyar a lokacin da kwatsam direbansu ya mutu ba tare da sun san dalili ba.


wp-content/uploads/2023/02/Rumfar-Kasuwa-by-Murja-Naikke.jpg

Rumfar Kasuwa

Alhaji Isah mutum ne da ke ƙoƙarin sauke nauyin gidansa daidai gwargwado a koyaushe. Sai dai hakan bai sa matarsa ta gode wa Allah ba, domin kuwa tana yi wa ‘yarsa awara tana siyarwa bai sani ba. Maryam kuwa tsula tsiyarta take yi yadda ta ga dama matuƙar za ta siyar da kayan siyarwarta, duk kuwa da irin nasihar da ‘yar uwarta take yawan yi mata.


wp-content/uploads/2021/12/Siddabaru-by-Muntasir-Shehu.jpeg

Siddabaru

Ko da yake yasan ba a mutuwa a dawo, bayyanar hotunan gayyatar auren Maryam da ya gani a Facebook tare da cikakken sunanta da ya gani sun ƙara tabbatar wa da Isah cewa lallai akwai wani ɓoyayyen al’amari game da mutuwarta. Ita kuma Jalila ko ya za ta yi da irin halin ko in kula da mijinta ke nuna mata?


wp-content/uploads/2022/07/Our-Friendship-by-Fadimafayau.jpg

Our Friendship

When Zainab caught her best friend Sa’ada with her husband naked on their matrimonial bed, a ruckus ensured which ended the marriage shortly after. But is that really the solution she sought? Are things going to happen the way Sa’ada planned?


wp-content/uploads/2021/11/Martabarmu-by-Lubna-Sufyan.jpeg

Martabarmu

Ahmadi cikakken ɗan boko ne, auren soyayya suka yi shi da matarsa Maimuna wacce kuma ‘yar danginsu ne. Sai dai rikici ya ratso cikin zaman lafiyar da suke yi da juna ne daga lokacin da ya sa ɗambar auren Maryam wadda ita ma ‘yar danginsu ce.


wp-content/uploads/2022/10/Tsaka-Mai-Wuya-by-Umar-bin-Ally.jpeg

Tsaka Mai Wuya

Umar Bin Ally ba shi da aikin yi a kullum face kula ‘yanmata a shafin sada zumunta na facebook. Kusan kullum sai ya yi sabuwar budurwa, bisa tsautsayi wata rana sai ya fara soyayya da matar ministan tsaro na ƙasa ba tare da ya sani ba.


wp-content/uploads/2022/12/Tambaya-by-Haiman-Raees.jpeg

Tambaya

Kundi ne na rubutattun waƙoƙin hikima da jawo hankali waɗanda duk wanda ya karanta su zai fara sabbin tunane-tunane dangane da al’amuran yau da kullum da ma rayuwa baki ɗaya. Wane ne ni? Yaushe zan yi kaza? A ina ake kaza? Me ya sa abu kaza ke faruwa da dai makamantan waɗannan tambayoyi duk za su zowa wanda ya karanta su.


wp-content/uploads/2021/12/Malam-Jatau-by-Haiman-Raees.jpeg

Malam Jatau

Rikita-rikitar Malam Jatau da rashin kan gadonsa na nema ya fi ƙarfin shi. Ga matansa su ma sun sako shi a gaba. Ko wa ya faɗa mishi mutum na iya yin faɗa ruwan sama? Ya gwada yin hakan kuma bai ji da daɗi ba.


wp-content/uploads/2022/05/Gidan-Gado-by-Zainab-Muhammad.jpg

Gidan Gado

Kakan su Habiba ya mutu ya bar wa mahaifiyarsu wani makeken gida, sai dai ɗan uwansa Malam Umaru ya yi kane-kane akan wannan gida ya ƙi bari a raba a ba wa kowa haƙƙin shi. Duk wanda ya taso da maganar ma sai ya yi mishi barazanar ganin bayan shi. Magada dai sun sha alwashin ƙwato haƙƙinsu, shi kuma Malam Umar da matarsa Saude sun sha alwashin tauye wannan haƙƙi ta kowane hali.


wp-content/uploads/2021/12/Kaddarata-by-Umar-bin-Ally.jpeg

Kaddarata

Rayuwa takan zo wa wasu da sauƙi, wasu kuma takan zo musu da akasin haka. Rayuwar Fatima Zahra cike take da ƙalubale, kuma ga dukkan alamu ba ta gama fuskantar ƙalubalen ba.


wp-content/uploads/2021/12/Abdulkadir-by-Lubna-Sufyan-.jpg

Abdulkadir

Kowa ya sha mamakin yadda aka yi har soyayya ta ƙullu a tsakanin Abdulƙadir da Waheedah saboda bambancin da ke tsakanin halayensu tamkar na ruwa da wuta ne. Yayin da wasu kuma ke tunanin halin da za ta shiga a zamantakewar aurenta da shi. Sai dai sun ba mara ɗa kunya sosai na tsawon wani lokaci kafin babbar ƙawar Waheedah da ake kira Nuriyya ta kutso kanta jikin Abdulƙadir tare da ƙoƙarin ganin ta aure shi.