Cikin Baure by Hadiza Isyaku

Auren Asma’u da Abbas ya kusa, sai dai ko kaɗan ba ta son shi. Hankalinta na kan wani matashin mai kuɗi da ake kira Alhaji Nas, alhali kuwa shi bai san ma tana yi ba. A haka dai aka ɗaura auren ba don tana so ba. Kwaɗayin dukiyar Alhaji Nas da fafutukar ganin ta shiga rayuwar daula suka sa soyayya ta makantar da ita har sai da ta kashe aurenta ta fito domin ta auri Alhaji Nas. Burinta ya cika ta aure shi, sai dai irin halin da ta tsinci kanta a rayuwar zaman gidan ko a mafarki ba ta hango wa kanta hakan ba.


Hakabiyya by Asma'u Abdallah Ibrahim

Yayin da fafutukar nemawa mijinta magani ya kai Zawwa zuwa ga tone kabarin wata budurwa mai ciki, hakan ya zamo matakin farko na cukurkuɗewar rayuwar Haƙabiyya tun kafin ta fito duniya. Hameedu, wanda ya canza sunan shi zuwa Huzaif yana ɗauke shi ma da wani ɓoyayyen sirri wanda ka iya fayyace komai ko ruguza komsi. Makirci ya haɗu da makirci, tsafi ya haɗu da mugunta, sirri ya ci karo da sirri, shin ko gaskiya ita kuma za ta yi halinta daga ƙarshe?