Rumfar Kara
Malam Iliyasu shahararren malamin addinin Musulunci ne da ke da kima da daraja a idon jama’a. Sai da sai dai ɗansa Sidi bai biyo halinsa ba. Hakan ya ƙara fitowa ne bayan ya yi wa tsohuwar budurwarsa Hanan ciki, ita kuma ta je ta sanarwa mahaifinsa. A gefe kuma ga Halima, wadda ta biyewa su Gwaska da Hayat wajen neman abin duniya ta gurɓata rayuwarta.
Mijina Wukar Fidar Cikina
Salahuddeen na kwance tare da matarsa Muhibbat sai ga kidnappers sun yi musu dirar mikiya inda suka ɗauke shi tare da yi wa matarsa dukan tsiya. Bayan kwana huɗu da faruwar hakan sai suka buƙaci da a basu miliyan ɗari. To sai dai yanayin yadda suka san bayanai game da surikar Salahuddeen ya tabbatar da cewa akwai wani makusanci da ke basu bayanai a ɓoye. To amma waye?
Tekun Labarai
Bayan Sarki Shamsuddini da matarsa sun gudu da tsakar dare domin su tsira daga harin da waziri Ashfanu da mabiyansa suka kawo musu. Dole tausa suka bar ɗansu jariri a tsakiyar dokar daji. Bayan komai ya lafa sai suka yi neman duniya amma basu ganshi ba. Sai dai ƙaddara ba ta gama jaraba su ba, domin kuwa ɗa ya dawo gidan ubansa ba tare da shi kanshi ya sani ba.
Tsanin Nasara
Duk da cewa amaryar ta jima a gidan mijinta har ma ta tara yara. Gwalagwalan shawarwarin da mahaifinta ya ba ta sun zamo mata tsanin hawa matakin nasara a gidan aurenta da ma rayuwarta baki ɗaya.
Wane Ne Ni?
Ba zato ba tsammani Ahmad ya farka ya ganshi a gadon asibiti ba tare da ya san yadda aka yi ya zo wurin ba. Ba ma wannan ba, ya kasa tuna hatta sunansa da kuma ko shi waye. Bayan Dr. Aminu ya yi masa wasu ‘yan gwaje-gwaje sai aka gano cewa ya kamu da cutar mantuwa ne. Kwatsam sai ga wata mai suna Hafsat ta yi wa rayuwar shi shigar ba zato, sai dai likita kuma ya ce ita ɗin ba gaskiya bace, kawai tunaninsa yake hasaso mishi hakan. Shin ko Ahmad zai yarda da wannan batun?
Soyayyar Da Na Yi
Mamma ta fidda rai gaba ɗaya da samun soyayyar gaskiya sakamakon rashin masoyinta Abdul da ta yi a baya. Ga kuma wani matashin saurayin na ƙoƙarin kunno kai cikin rayuwarta a wani irin yanayi mai ban mamaki.
Sakacina Ko Halin Maza?
Juwairiyya yarinya ce mai matuƙar kamun kai. Sai dai halin da suke ciki na talauci na neman yi wa mutuncin nata barazana. Ga kuma ƙanin mahaifinta Baba Sani da ya kafa mata ƙahon zuƙa ba tare da wani takamaiman dalili ba.
Marubuci
Yayinda wani matashin marubuci ya saurari wata tattaunawa da aka yi da wani fitaccen jarumin fina-finai, hakan ya ƙara mishi ƙwarin gwiwar ci gaba da rubutu tare da zama tsanin samun nasararsa a harkar rubutu.
Bincike
Sipeta Sani ƙawararren Ɗan Sanda ne da bai san faɗuwa ba a aikinsa, sai dai garkuwa da ɗan minista da wasu ɓata gari suka yi na nema ya kai masa ruwa rana a bincikensa.
Mijin Novel
Bayan fafutuka da kai ruwa rana, Hindatu ta samu irin mijin da take so, wato mijin Novel. Kyakkyawa, mai ilimi, kuɗi da sauransu. Sai dai abinda ba ta sani ba shi ne, shin ko ta shirya yin sadaukarwar da ta dace domin yin rayuwar aure da Hamza?
Fatalwar Sinu
Katoɓara da ɓarin baki suka sa Haiman bayyanawa duniya irin abubuwan da yake so a bashi a matsayin kyautar barka da sallah. Sai dai ya samu kyautar da ta fi ƙarfin shi, yayin da wata kyautar ta fito daga lahira kuma daga hannun wani gagarumin maƙiyin da bai san yana da shi ba.
Bakar Kaddara
Wasu lokutan ba sai ka aikata mummunan aiki ba kafin baƙar ƙaddara ta afko maka. A wasu lokutan kuma, halayen mutane ne ke kaisu ga faɗawa cikin bala’i.
Asabe Reza
Hankalin fitacciyar Karuwa Asabe Reza ya tashi sakamakon cin amanar da ƙawarta Fakriyya ta yi mata na aure mata hamshaƙin masoyinta Hamoudi. Wannan ya sa ta sha alwashin tarwatsa musu farincikin da suke fatar samu.
Sakacin Waye?
Ummatin Mambila ta yi matuƙar ƙoƙarin gaske wajen ganin ta raini ‘ya’yanta maza uku a bisa nagarta da kamala. Ta kuma ci nasarar yin hakan har zuwa lokacin da manyan guda biyu suka yi aure. Sai dai rayuwa ta zo mata da bazata, inda mutuwa ta ɗauke matayen ‘ya’yan nata ta bar abin da suka haifa mace da namiji. Bayan zama na tsawon lokaci ba tare da aure ba, Giɗaɗo ya Auro Jaru, abinda bai sani ba shi ne, ita kuma a zuciyarta babu wanda take so sama da ƙaninsa Muhamman.
Kishiyar Katsina
Tataburza ta fara wakana a gidan Khamis tun bayan da matarsa ta farko, Aisha ta ji cewa zai mata kishiya, kuma ‘yar Katsina ce. Wannan dalili ne ya sa ta ɗau aniyar ajiye kyawawan halayenta da aka sani tare da ɗaukar sabbi bisa shawarar ƙawarta Zuzee domin tabbatar da cewa Maryam, wato amarya ba ta samu sararin yin numfashin kirki gidan ba. Duk wannan saboda dalili ɗaya: ‘Wai an ce mata ‘yan Katsina suna da asiri.
Duniyata
Irfaan da mahaifinsa jami’an ‘Yan sanda ne. Ƙaddarar rayuwa ta kai su Saulawa inda ya haɗu da Ihsan, wadda ta tsaya mishi a rai ba tare da wani dalili ba. Rashin yin soyayya balle ma batun aure ya sa iyayen Irfaan ke tunanin ko Aljana ce ta aure shi.
Marigayiya
Bayan tarin wahalhalu da kuma ƙalubalen da suka fuskanta kafin su yi aure, Rumy ta yanke shawarar yin amfani da kayan amfanin yau da kullum ɗin mijinta domin ita ma ta kamu da irin cutar da ke damun shi, wato cuta mai karya garkuwar jiki.
Fitsarin Fako
A daren tarewar auren Lantana ne ‘yan ta’adda suka je ƙauyen da aka kai ta suka watsa jama’a tare da yi mata fyaɗe kuma suka kashe mijinta. Yayanta Kamalu, shi ma sun yanke masa hannu ɗaya a wani hari da suka kawo daga baya a ƙauyen Namu-Ya-Samu bayan sun kashe mahaifin Lantana. Sai dai kuma mutuwar Lantana ta bar baya da ƙura, musamman da wasu hujjoji suka fara nuna wa Kamala ɗan yatsa.
Akan So
Safiyya ta biyewa So da ya makantar da ita ta bi Fu’ad sun yi aure ana gab da yi mata aure da Ado. Wannan ya sa iyayenta suka tsame hannunsu daga komai nata. Shi ma Fu’ad ɗin hakan ce ta faru da shi. Sai dai tashin hankali ya fara ratsowa cikin zamantakewar tasu ne yayin da Fu’ad ya fara nuna ƙiyayyar shi da son haihuwa. Saboda hakan ne ma ya je asibiti aka kashe mishi ƙwayoyin haihuwar shi. Abin da bai sani ba shi ne, Allah Ya riga Ya ƙaddara rabo a tsakaninsu da Safiyya.
Ko Ruwa Na Gama Ba Ki
Kwaɗayin abin duniya ya sa ‘yar gidan Malam Amadu ba wa saurayi kanta har ya yi mata cikin shege. Gashi kuma mahaifinta shi ne limamin ƙauyensu, ciki kuma har ya kai kusan wata biyar ba tare da an ankare ba. Wannan dalili ne ya sa mahaifiyarta Asabe ta ɗauki karan tsana ta ɗora mata.
Yini Sittin Da Daya
A fadar sarkin namun dawa, wato Zaki. Dabbobin dawa, manya da ƙanana kan zo masa da labarai iri-iri domin tattaunawa da samo mafita a cikin al’amuran yau da kullum irin nasu na dabbobi wanda yake kamanceceniya da namu na mutane.
Kuskuren Wasu
Khadija ta yi kuskure mai girma a rayuwarta, ciki kuwa har da na rabuwa da ‘yarta. Maryam ita ma ta yi kuskure mai girma, musamman na auren mijin da bai san daraja da kimarta ba. Fatima kuwa da-na-sani ne ya kamata yayin da mijinta Kabir ya fara nuna mata asalin halinsa. Alawiyya na matuƙar son mijinta, sai dai kuma wata ƙawarta na neman jefa ta cikin bala’i.
A Daren Farko
Duk da cewa Dr. Jidda Abubakar Aliyu ƙwararriyar likita ce a fannin cututtukan mata da yara, hakan baya nufin ita ma ba ta da damuwar da ke damunta. Musamman wani mafarki da ya nace mata, wanda kuma duk in ta yi shi sai ta ji ta a sususce. Shi kuwa Dr. Sani, soyayya ce ta rabo shi da Kaduna ta kawo shi Katsina neman Jidda ba tare da ya taɓa ganin ta balle ya san inda zai same ta.
Kauthar
Kauthar na cikin wani hali na ruɗani, domin kuwa mahaifinta ya yanke shawarar aurar da ita ga Abdulmalik Kwangila bayan sati biyu da kammala jarabawarta. Inda tashin hankalin yake shi ne, Abdulmalik mijin babbar ƙawarta ne, ƙawar da suke ƙaunar junansu tamkar ciki ɗaya suka fito. Yaya Faheemah wadda aka fi sani da Anty Ummi za ta ɗauki wannan labari na auren babbar ƙawarta da mijinta?
Rikon Sakaina
Ammi na so ta karɓi shawarar juma na tura Zubaida bara, sai dai tana tunanin yadda za su ƙare da Maqsood domin kuwa ya sha nuna mata rashin amincewarsa game da hakan. Ita kuwa Zubaida sai murnar lashe jarabawar da suka yi take yi ba tare da ta san abinda ake kitsawa ba.
Rabon A Yi
Farida, wadda aka fi sani da ‘Ferry’ ta yanke shawarar zuwa bikin babbar ƙawarta Jiddah, duk kuwa da cewa mijinta Mukhtar ya tabbatar mata da cewa baya so ta je. Hankalinta ya tashi sosai yayin da ta na gidan bikin aka ce an yi sata, ana cikin rigimar sata kuma aljanun wata suka tashi. Ga kuma Mukhtar yana kiranta a waya.
Tun A Duniya
Alhaji Garba ya shiga wani irin mummunan hali na ban mamaki. Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci duk dukiyar da ya tara ta salwanta, sannan lafiyarsa ma kanta ta fara ƙoƙarin ƙaurace masa.
Canjin Bazata
Halin rashi ya yawaita, gashi bikin Yayar Shuhaina ya matso, sai dai babu kuɗin da za a yi musu kayan ɗaki. ‘Yar gonar gadon tasu da aka saka a kasuwa kuma ba a yi mata tayin daraja ba. Ga mutanen gida sai yada wa mahaifiyar su Shuhaina zance suke yi, domin su a wurinsu, duk macen da ba a yi wa gara da kayan ɗaki na kece raini ba, to ba ta cika ‘ya ba.
Jawaheer
Mujaheed Muhammad, wanda aka fi sani da M.D ƙawararren jami’in C.I.D ne da ake ji da shi a duk faɗin Nijeriya. An turo shi garin Kaduna ne domin ya gudanar da gagarumin bincike akan Alhaji Saleh Mu’azu Mainasara. Ƙaddara sai ta haɗa su da Jawaheer, wadda ‘ya ce a wurin Alhaji Saleh Mu’azu Mainasara, wadda ta faɗa kogin son shi kamar ta yi hauka. Shi kuwa ya yi alƙawarin babu wata mace da zai iya rayuwa da ita bayan tsohuwar matarsa. Babban abinda ke ƙara dagula mishi lissafi shi ne, irin yadda Jawaheer ke yin abubuwa irin na tsohuwar matar tasa, wato Nayla.
Jini Ba Ya Maganin Kishirwa
Kamal ya shirya tsaf domin ganin ya auri Hajiya Shema’u, duk kuwa da tazarar shekarun da ke tsakaninsu. Shi dai kawai miliyan ashirin ɗin da zai samu yake hange. Wannan dalili ne ya sa har suka fara samun matsala da babban abokinsa Zayyad da kuma ƙanwarsa Farida. Ita kuwa matarsa ta fari, Sakinah, haƙuri kawai take yi tare da maida komai ba komai ba. Shin ko zai hankalta ya sauka daga kan keken ɓeran da yake ƙoƙarin jefa kanshi?
Launin So
Umma Maryam da yaranta uku, Samir, Abba da Samira suna cikin wani irin mawuyacin hali mai ban tausayi sakamakon talaucin da suke ciki wanda ya jawo musu ƙunci a cikin rayuwarsu. Sai sun yi bara ma suke samun abin da za su ci kuma a bola sukan zauna a mafi yawancin lokaci. Duk da cewa Alhaji Mas’ud ya basu wurin zama a cikin gidansa, shi da matarsa Hajiya Kilishi da babu irin karar tsanar da ba su ɗora musu ba. A cikin wannan yanayi ne kuma kwatsam sai Samir ya kamu da tsananin son Zuhra, shalelen Alhaji Mas’ud. Shin ko za ta karɓi soyayyar tashi?
Fansar Fatalwa
Ƙawaye sun yi wa Amrah mummunan lahani a rayuwa, wanda hakan ne ya zamo silar mutuwar ta. Hakan ya sa ta dawo a matsayin fatalwa tare da shan alwashin ɗaukar fansa a kansu. A bisa wannan dalili ne ta kawo wa Afrah farmaki ana saura kwana uku bikinta da masoyinta, wato Anwar. Shin wa kuma za ta kai wa hari na gaba?
Baba Dattijo Dan Bursin
Yayin da wani ɗan jarida ya je gidan yarin Kurmawa da ke Kano ya gamu da wani dattijo mai ban mamaki da ke rayuwa a wannan gida na kaso. Shin ko ta yaya za a iya shari’ar kashe mutumin da ya riga da ya mutu tun shekaru 29 da suka gabata?
Ina Matsalar Take?
Yayin da aka nemi Safwan sama ko ƙasa ba a gan shi ba har na tsawon wasu kwaki, sai mahaifiyarsa Amina ta matsa wa mahaifinsa game da nemo inda yake. Domin har ta fara fatan ina ma ace masu garkuwa da mutane ne suka sace shi, a tunaninta ko ba komai za su ji yana raye kuma su san nawa za su biya. Babban abinda ya fi tayar wa da mahaifin Safwan hankali shi ne irin yadda ya ziyarci ofisoshin ‘Yansanda har biyar amma babu inda aka yi mishi tarbar kirki, sai ma tayin kuɗi da suke masa. To ina matsalar take?
Hoton Mijina
Muka amsawa da amin muna sakar wa juna murmushi. Tun daga ranar duk wasu makaman yaƙina na zubar da su, har mamakin kaina nake yi da tambayar kaina anya kuwa ni ce Rashida? Zaman lafiya ya samu matsuguni a tsakaninmu tamkar ba kishiyoyi ba.
Fudayl
Abbu ya yi wa ‘yarsa Hamna Nuhu Alƙali aure da mijin da ko sunan shi ba ta iya riƙewa ba saboda ba auren soyayya ba ne. Amna za ta bi shawarar Ammi ta zauna da mijinta lafiya ne ko kuma za ta biyewa son zuciya da ra’ayinta?
Zinariya
Tashin hankalin da ya afku a ƙauyen su Hamida ne ya sa ta rasa ‘yanuwanta gaba ɗaya kuma ta koma rayuwa a daji. A cikin wannan yanayi ne ta haifi Zinariya, kuma ba da jimawa ba ta rasu. Sarauniya Jahiyana wadda ke mulkin masarautar aljanu ta Gimatuwa ce ta tsince ta a dokar daji ta kai ta gidanta kuma har ya aiyana ta a matsayin wadda za ta gaje ta. Sai dai kuma wannan shiri bai yi wa gimbiya Juhaina daɗi ba. Shin ko yaya za ta ƙarke a tsakaninsu?
Ma'aurata
Habibu mijin Ruƙayya ne, kullum cikin yi mishi masifa take saboda in ya fita gida ba ya dawowa sai dare sosai, hakan kuwa ya faru ne saboda ƙazantarta da rashin girki da gyaran jiki, wani lokaci ma hana shi haƙƙinsa take yi ta ce sai ya biya. Fahad shi ma ba ya wani zaman gida, kuma a buge yake dawowa Fatima, wani lokaci ma ya haɗa mata da duka da zagi. Shin ko za su samu mafita?
Nima Matarsa Ce
Taufiq ya shiga gagarumar damuwa sakamakon irin bita-da-ƙullin surikarsa wato Hajiya Murjanatu. Tun da ya nuna yana son ‘yarta Mujaheeda, shikenan ta shiga kawo tsirfa iri-iri duk don ta ga an fasa, domin a cewarta bai dace ya auri ɗiyarta ba. Shi kuma yana son Mujaheed, ita ma kuma tana sonsa. Anya kuwa ko da sun yi auren Hajiya Murjanatu za ta bar su su zauna lafiya?
Waye Zabin Munibat?
Munibat natsattsiyar yarinya ce, maraici ya sa ta shiga cikin uƙuba a hannun matar mahaifinta wadda a kullum take nuna mata ƙauna a fili, a ɓoye kuma tana gasa mata gyaɗa a hannu. Shin wane zaɓi Munibat take da shi? Yaya za ta yi wajen ganin ta fita daga wannan ƙangi?
Rayuwata
Zuwan ‘Yan Bindiga rugar su Naja’atu ya yi sanadiyar mutuwar mafi yawa daga cikin ‘yan’uwanta. Yayin da ita kuma garin gudun neman ceton rai ta faɗa hannunsu har shugaban ‘Yan Bindigar ya mayar da ita tamkar matarsa.
Na Sake Ta
Hamshaƙin matashin mai kuɗin da ake ji da shi, wato Usman One boy ya samu Kamal mayen kuɗi da batun wani irin kasuwanci mai ban mamaki. Usman ya yi alƙawarin ba wa Kamal kuɗi naira na gugar naira har miliyan biyar, matuƙar dai ya yarda zai saki matarsa Hajir domin ya aure ta. Ashe Kamal na gab ne da fahimtar cewa ba komai bane kuɗi ke iya yi wa mutum.
Izina
Aisha (Ma’isha) da Abdul’aziz ‘yan’uwan juna ne, kuma dukkansu lauyoyi ne. Sai dai a karo farko za su kara da juna a gaban ƙuliya domin kare mutane biyu. Iya Aisha tana ƙoƙarin ƙwato wa wata mata da ‘yarta
‘yancinsu ne a hannun wani mugun mai kuɗi. Shi kuma Abdul’aziz yana kare shi. A wani ɓangaren kuma, yayansu jami’in ƙasa da ƙasa, Deputy Commissioner of Police Abdulmalik Ibrahim Ahmad ya zo Nijeriya domin ya gudanar da bincike na musamman akan kisan da aka yi wa wani babban jami’in tsaro, kwatsam kuma sai ƙaddara ta haɗa shi da ‘Yar Jarida Intasar Mahmood Abdullahi.
Indo A Birni
Indo ta gallabi mutanen ƙauyensu baki ɗaya. Kowa ƙorafi yake yi da ita, abu ya yi tsamari dai har da kai ta ƙara gaban Mai Gari, kullum iyayenta mutanen kirki suna zarya wajen magance matsalolin da take jawo musu amma kamar ba sa yi. Sai dai duk da wannan hauka da rashin kan gado nata, Allah ya jarrabe ta da soyayyar Muhammad Mustapha wanda ke zuwa daga birni. Anya kuwa za ta samu shiga a wurinsa? Musamman da yake akwai wata ‘yar uwar tasa ma a birni da take son shi amma ba ya ko kula ta.
Ta Ki Aure
Sawwama da Kawwama yaya da ƙanwa ne da suka jima basu yi aure ba. Shekarar Sawwama talatin da biyar ba ta yi aure ba, yayinda ita kuma Kawwama shekararta talatin da biyu ba ta yi aure ba. Hakan ya sa kowa a dangi ke ta faman yi musu surutu. Kwatsam sai ga Jalil ya zo neman auren Kawwama, an sha biki an gwangwaje, sai dai kuma Jalil na ɗauke da wani ɓoyayyen lamari da ba kowa ya san da shi ba.
Laifin Wa?
Ladidi matashiya ce mai ji da ƙuruciya, hakan ya sa ta faɗa harkar bin maza domin ta hucewa kanta haushin rashin ɗauke mata ɗawainiya da iyayenta suka kasa. Duk da cewa sun san irin abin da ɗiyarsu ke aikatawa, amma ba su da ta cewa. Saboda wani lokaci ma wurinta suke zuwa su yi ‘yar murya.
Amnah
Amnah nutsattsiyar matashiya ce mai kyau da kamala, domin har sauka ta yi. Sai dai mummunan halin da ta tsinci kanta a ciki ne ya sa ta shiga harkar karuwanci, a harkar karuwancin ma har tarihi take ƙoƙarin kafawa na ganin cewa duk mutumin da ya yi tarayya da shi ba ta ƙarawa. To sai dai kuma ta kamu da soyayyar matashi Taufiq. Shin ko za ta samu cikar burinta?
Kasaitar So
Zaid sangartaccen matashi ne wanda ke ji da kansa da kuma taƙama da kuɗi. Yana da yaransa ‘yan daba da ke masa aiki, su ne Gaye, Mugu da kuma Wizzy. Ƙaddarar rayuwa ta sa Gaye ya fara bibiyar Jidda, wadda ƙanwar Ibteesam ce wato Maryam, zafin rai irin na Ibteesam ya sa ta yi musu kaca-kaca, shi kuma tun daga nan ya sha alwashin sai ya lalata mata rayuwa.
Lullubin Biri
Hankalin Yusuf ya yi matuƙar tashi sakamakon halin da matar da aka kwantar a asibitin take ciki, matsananciyar damuwa ce take fama da ita wadda har ta kai ta ga fita hayyacinta. A gefe kuma, Fillo (Halimatu) da masoyinta Amir suna ci gaba da more soyayyar su, har ma maganar aure ta shiga tsakani. Kwatsam sai Turaki, wanda ke ɗauke da wani ɓoyayyen sirri ya shigo cikin rayuwar Halima. Shin ko menene wannan sirrin.
Allah Daya Gari Banban
Yayin da matar Abdullahi masunci ta haihu a karo na goma a rayuwarta, sun yi farin ciki sosai. Hakan ne ma ya sa Abdullahi tafiya bakin kogi domin ya yi su ya samo abinda zai ciyar da iyalansa. Amma wani abin mamaki shi ne, sai da ya yi kwanaki arba’in yana zuwa su ba tare da ya kama ko da kwaɗo ba, ga shi yana matuƙar jin kunyar mai gurasa wanda ke binsa bashin da yake ta bashi a kullum ba tare da gajiya ba.
Na Cancanta
Sumayya Abdullah Khalil mace ce mai hakuri da tarbiyya daidai gwargwado. Talakawa ne su, wannan ya sa a dangi ake ƙyamar su, ake gudun su kuma ba a son ganin su. Domin da an gansu za a fara tunanin wani abu suka zo nema. Babban abin da ya fi ci wa Sumayya tuwo a ƙwarya shi ne irin yadda dangi ke zargin halin da suke ciki ya ta’allaƙa ne da ‘ƙashin tsiya’ irin na mahaifiyarsu.
Birnin Sahara
Haidar ya farka daga suman da bai san ya yi ba, yayin da ya tsinci kanshi a wani babban birni da duniya kaf ba ta san da wanzuwarsa ba. Abin ya bashi mamaki ƙwarai da gaske da ya ga tsohuwar budurwar da yake so Nadiya ita ce ke mulkin wannan birnin. Sai dai mamakin shi ya ƙara nunkuwa ne bayan ya fahimci cewa yana da alaƙa ta asali da wannan birni, kuma ya zama wajibi a gare shi ya tsallake wasu matakai domin ya zamo sarkin wannan birni matuƙar yana so ya ceci rayuwar ‘yan uwansa.
Kaddarar Mutum
Tun bayan mutuwar mahaifinta, wato Malam Tanimu, Asma’u da mahaifiyarta Inna Hauwa suka shiga cikin tsangwama a wurin mutanen ƙauyen Somayi. Hakan ko ya samo asali ne sabo da ta ƙi amincewa da batun auren duk samarin garin, musamman Muntari da yake ɗan Maigari. Ba zato ba tsammani kuma sai wani ya yi wa Asma’u fyaɗe har ta samu ciki. Wannan dalili ne ya tursasa mata barin ƙauyen ba don tana so ba. Ko za ta samu mafita a inda ta nufa?
Matar Bahaushe
Ruqayya Manaf ƊanGambo ‘yar majalisar wakilai ce mai tausayi da ganin ta taimaki al’umma. Captain Anwar Sarari da Honorable Bamanga Jafaru, na daga cikin mazajen da ke mararin ganin sun mallake ta a matsayin matar aure. Sai dai kuma, tuni ta daɗe da yi wa mazan duniya gaba ɗaya kuɗin goro, hakan ya sa ba ta da lokacin su.
Nawa Bangaren
Gimbiya Naheela ita ce ‘ya guda ɗaya tilo a wurin sarkin aljanun Zuwatu, wato Zawatunduma. Naheela ta jarabtu da soyayyar Yarima Naheel ɗan sarkin aljanu Zimba, sai dai shi kuma baya son ta, ya tsane ta matuƙa. Wannan dalili ne ya sa ta aika Zamzila domin ya nemo mata inda Yariman ya ɓoye.
Kukan Kurciya
Ana gobe ɗaurin auren Mujahida da masoyinta da suka yi shekaru biyar suna soyayya, wato Nura ya ce ya fasa. A gigice ta shiga gida da taimakon ƙanenta Mujtafa, sai dai shigarta cikin gidan ya yi daidai da furta kalmar saki da mahaifinta wato Habibu ya yi ga mahaifiyarta wato Bilkisu.
Muradin Rai
Alhaji Kasim Banazir ƙasurgumin ɗan kasuwa ne a fili, a ɓoye kuma gogaggen ɗan safarar miyagun ƙwayoyi. Yana da wata kyakkyawar ‘ya guda ɗaya da yake matuƙar ji da ita, sunanta Nooreyn. Nooreyn da Ekram tare da Saleym sun je River Kaduna domin yin wani shagali, kwatsam sai ta ci karo da wani mutum ruwa ya jawo shi daga wani wuri, jikinsa duk tabbai.
Kudi Ko Rai
Alhaji Ahmad Mukhtar na ta faman kashe kuɗi wajen ganin ya samar wa ɗansa guda ɗaya tilo wato Mashkur lafiya amma abu ya ci tura. Sai dai duk da haka ya sha alwashin ƙarar da dukiyarsa gaba ɗaya wajen nema wa ɗan nasa lafiya. Abinda bai sani ba shi ne, matarsa Zinatu na da hannu dumu-dumu bisa rashin lafiyar ɗan nasa.
Labarin Asiya
Ba tare da tunanin komai ba Asiya A Baba ta shiga asibiti domin karɓar sakamakon gwajin da ta yi ranar Larabar da ta wuce. Sai dai hankalinta ya yi matuƙar tashi da jin cewa tana ɗauke da cutar ƙanjamau. Hakan ya sa ita da mijinta Hassan zuwa wani asibitin suka yi wani gwajin, sai dai a nan ɗin ma dai sakamakon iri ɗaya ne, ita da shi duka suna ɗauke da cutar. Babban tashin hankalin Asiya shi ne ba ta taɓa zina ba, don haka kai tsaye ta fara tunanin Hassan ne ya saka mata cutar.
Wata Rayuwa Ce
Alhaji Buhari hamshaƙin mai kuɗi ne na gaban kwatance, sai dai matarsa Hajiya Jamila ta hana shi saƙat saboda neman abin duniya. Wannan dalili ne ma ya sa ta sa Maza da Alamz suka sace Sadiya da ‘yarta suka jefar da ita. Ya zama dole Alhaji Buhari da amininsa Alhaji Saleh su nemo Sadiya matuƙar suna so burinsu ya cika.
Daurin Huhun Goro
Halin yunwa, talauci da kuma matsatsin rayuwa da ake ciki ne suka tunzura Tabawa har ta kai ga tana bin layi da lunguna tana zagin shugabanni, ‘yan siya da kuma ‘yan kasuwa. Domin ita a ganinta, duk su ne sanadin faruwar hakan a cikin al’umma. Ta kuma ƙudiri aniyar kawo sauyi game da wannan lamari.
Wa Ya Kashe Zahra'u?
Matakin tashin hankali da ruɗanin da ya ɓarke a gidan Alhaji Aliyu Ibrahim MD ya kai maƙura, yayin da aka wayi garin ranar ɗaurin auren ‘yarsa guda ɗaya tilo a duniya aka same ta a mace. Angon nata, wato Zayyan ya suma sakamakon jin wannan mummunan labari. APC da DCP Sardauna suna ta bincike domin gano wanda ya shigo har cikin gidan ya kashe Zahara’u duk kuwa da tarin matakan tsaron da ke gidan.
Alkawarin Allah
Alhaji Usman Ibrahim Matawalle ba ya barin kowa zuwa zance wajen ‘ya’yansa, watau Maryam da Fatima saboda mutum ne shi mai zafi sosai. Soyayyar Maryam ta kama Nuraddeen, kuma sai bibiyarta yake yi har sai da ya gano gidansu. Shin ko zai dace da samun soyayyar Maryam tare da amincewar mahaifinta?
Sirrin Boye
Mairo yarinya ce mai kaza-kazar, bata da son jiki ko yanƙwana. Talakawa ne su masu rufin asiri. Tana da yayye guda biyu, Amadu da Kabiru. Tana matuƙar tsoron Yaya Amadu, sannan ta shaƙu sosai da Yaya Kabiru. Babban abin da ke ɗaure wa Mairo kai shi ne irin yadda ba sa so Kulu tana raɓar inda take, ta kasa fahimtar wane irin ɓoyayyen sirri ne ke tattare da Kulu wadda tun tana ƙarama take fama da cuta mai kama da ta hauka.
Inuwa Daya
Fadila ta shirya tsaf domin ganin ta auri Uban riƙonta ko da kuwa duniya za ta yi Allah-wadai da ita, matuƙar dai za ta samu damar zama inuwa ɗaya da mai tarin arziƙi. Alhaji ya dage kan cewa lallai zai ƙara aure, kuma budurwa zai aura. Wannan dalili ne ya Hajiya Amina ta kasa zaune ta kasa tsaye wajen ganin ta samu mafita dangane da wannan ɗanyen aikin da yake ƙoƙarin jawo mata. A gefe kuma, babbar aminyarta Hajiya Baratu ba ta da burin da ya wuce ita ma ta aure mata miji. Tsakanin Fadila da Baratu wa zai yi nasarar aure Alhaji?
Ummu Hani
Rayuwar Ummu Hani ta sauya cikin dare ɗaya, bayan mahaifiyarsu ta rasu ta barta da ƙanne biyar ba tare da wanda zai kula da su ba, ciki kuwa har da jariri sabon haihuwa. Sai dai ta ɗauki aniyar kulawa da ƙannen nata ko ana ha maza ana ha mata.
Ya'yanmu
Rayuwar zaman marina ake yi a Unguwar Hayin Talaka. Unguwa ce ta talakawan da basu san ciwon kansu ba ballanta na ‘ya’yansu. Rayuwa ce ake yi cikin rashin tsafta, nutsuwa da sanin yakamata. Ko yaya rayuwar yara masu tasowa a wannan Unguwar za ta kasance a gaba? Shin ko za su samu mafita?
Kwamin Nadama
Baƙin kishi ya sa Ladiyo cakumar wuyar mijinta tana mai sauke masa kayan rashin mutunci tare da tabbatar mishi da cewa bai isa ya yo mata kishiya ba. Shi kuwa Kabiru, don ya gwada mata lallai ya haifu bai yi wata-wata ba ya danna mata saki biyu. Tun daga nan ta shiga tashin hankali da ruɗani, musamman da ta tuna cewa za ta bar gidan kuma zai kawo wata.
Dare Daya
Salim ya shiga cikin jarrabawa babba. Shekaru uku kenan da kammala karatunsa amma har yanzu bai samu aikin yi ba. Kwatsam! Ana cikin haka kuma sai wani mai mota ya bige mahaifiyarsa, inda har ta samu karaya bakwai a jikinta. Likita ya bayyana za a yi mata aiki, amma ana buƙatar Naira miliyan uku domin yin aikin. Ga shi Salim ba shi da kosisi.
Zuciya Da Hawaye
Rumana tana cikin wani irin mummunan hali sakamakon farmakin da mahaifinta ke yawan kai mata don ganin ya cimma burinsa. Alhaji ya damu sosai bisa mafarkin da ya yi da masoyinsa Jabir, yayin da ita kuma Zully take fusace da mahaifinta sakamakon irin azabar da yake gana wa mahaifiyarta. Shin me ke faruwa ne a cikin zukatansu? Me ke hana duk wanda ya yi yunƙurin keta wa Rumana haddi damar cimma burinsa?
Ranar Birthday
Ruƙayya Mohammed (Rukky) ta shirya tsaf domin tunkarar ranar zagayowar haihuwarta da wani irin bazata. Ta sha alwashin kawo gyara, sauyi da kuma canji a zukatan mutane game da yadda aka ɗauki bikin zagayowar ranar haihuwa (wato Birthday Party) a cikin al’ummar Hausawa. Shin ko za ta yi nasara?
Wa Gari Ya Waya?
Tahir yana cikin matsananciyar damuwa, ba komai ya jawo mishi wannan damuwa ba kuwa face matansa guda huɗu. Basma na fama da ciwon ƙwaƙwalwa, Halima na da yawan cin bashi, Latifa amarya kuma yawon bin malamai. Ummul Khair ce kawai mutuniyar kirki a cikinsu. Shin ko Tahir zai iya magance matsalolin da ke ci gaba da tashi a gidansa?
Abinda Babba Ya Hango
Okasha Sani Sa’id matashi ne mai taƙama da kuɗi da kyawun halitta. Hakan ya sa yake wasa da hankulan ‘yanmata tare da ɓata musu rayuwa. Ƙaddara ce ta haɗa shi da Jameela, wadda ta bijirewa shawarar mahaifinta ta auri Okasha ba don suna so ba. Kash! Da ta san abin da zai biyo baya da ba ta yi wannan aure ba.
Ba Kauyanci Ba Ne
Alhaji Abdulƙadir mutum ne ɗan zamani wanda kiyaye haƙƙoƙin addini bai dame shi ba, to amma ‘yarsa Salma da mahaifiyarta Hajiya Bilkisu suna da kyawawan halaye kuma suna matuƙar kiyaye dokokin shari’ar Musulunci. Alhaji Sameer da Hajiya Samira suna da ɗa guda ɗaya da suka haifa mai suna Kamal. Duk iya ƙoƙarin da Alhaji Sameer yake yi na ganin Kamal ya shiryu, ita mahaifiyarsa gani take takura ce. Kamal ya kama hannun Salma a wurin wani taro inda ta wanke shi da mari. Sai daga baya yake jin ashe mahaifiyar Salma mahaifinsa ya fara so ya aura kafin mahaifiyarsa.
Mafarkin Deluwa
Malam Shitu, Malam Lawal, Malam Tsalha da Malam Zaidu ma’aikatan wata maƙabarta ce da ke ƙauyen Ɗanduƙus. Tsananin firgici ne ya ziyarce su a lokacin da suka ga wata ‘yar wada ta shigo maƙabartar da suke kula da ita tana neman taimakon su binne mata gawar. Saratu, wadda aka fi sani da Deluwa ta yanke shawarar kashe masoyinta Chibunzu, kamar yadda Alhaji Labaran ya umurta domin cika burinta na zuwa Makka.
Sa'adatu
Zarah da Ahmed masoyan juna ne, soyayyarsu har ta kai ga an saka ranar aurensu. Ana saura sati biyu bikin ne sai aka sace Zarah, ba kowa ne ya sace ta ba face Aljana Zainab da masoyinta Safwan ɗan sarkin aljanu. Sun yi hakan ne kuma domin su cimma wani mummunan ƙuduri nasu da suke da shi akan waɗannan masoya.
Duniyar El-Dorado
Bayan shuɗewar lokaci mai tsawo da rabuwarsu, Khadija Muhammad Lamiɗo, wadda aka fi sani da Deejah, ta kawo wa Abou Adem ziyarar bazata a gidan yarin Kirikiri Maximum Security Prison da ke Apapa, Lagos State, Nigeria. Wa ya faɗa mata an kama shi? Me ya kawo ta? Waɗannan na daga cikin tambayoyin da yake buƙatar sani a hanzarce.
Nisfu Deeniy
Nadeefah Yusuf Yerwa, wacce a gidansu ake kira da Lele, kyakkyawar budurwa ce ajin farko. Allah ya jarrabe ta da son Burhan Abdallah Yerwa wanda ake kira da Islaam, son da take yi masa ya yi ƙarfin da har sai da ta fito fili ta faɗa mishi abinda ke cikin zuciyarta. Sai dai shi kuma ba ya sonta, bai ma ɗauketa da muhimmancin da zai iya ko kula ta ba, a madadin hakan, Suliem Aliyu Yerwa yake so, ita kuma bata ma san yana yi ba. Wannan soyayya ta mutane uku kuma ‘yan ahali ɗaya tana ɗauke da jimirɗa sosai. Waye zai yi nasara?
Jini Ya Tsaga
Hafsat bazawara ce da ke zaman zawarci a gidansu. Mahaifiyarta ta rabu da mahaifinsu mai suna Kamaluddeen, amma sauran matan nasa guda uku suna zaman lafiya sosai da junansu. Hafsat ta sha alwashin kai mahaifinta ƙara ofishin ‘Yansanda bisa zargin nuna rashin adalci a tsakanin matansa. Shin ko za ta ci nasara?
Tsinin Harshe Ya Fi Na Mashi
Al’amura sun dagulewa Zainab tun bayan da bakinta ya jawo mata jalli-joga sakamakon sharrin maita da ta yi wa Jummai a gidan suna. Lamarin ya kai matuƙa a fagen tsamari ne ya yin da aka aiko mata da takardar sammaci daga kotu a bisa wannan zargi, ana tsaka da wannan kuma sai mijinta Auwal ya sake ta.
Na Kamu Da Kaunar Matacce
Rayuwar Munaya ta birkice tare da wuntsulawa wata duniyar sabuwa tun daga lokacin da ta ga hoton tsohon mijin Zuwaira, wato Zayyad Muhammad Hashim. Tafiyar da ta yi zuwa garin Kaduna da nufin shiga makarantar KASU domin ta ɗora karatun gaba da Sakandare sai ga shi yana neman komawa karatun binciken rayuwar matacce.
Abbakar
Abbakar Malami ne da ke koyarwa a jama’ar B.U.K. Allah ya jarrabe shi da matsanancin son wata ɗalibarsa mai suna Ummulkhairi, sai dai ya kasa faɗa mata. Kwatsam watarana sai ya gano cewa ashe matar aure ce, har ma tana da ciki. A gefe kuma ga ƙawarta Aisha da take matuƙar son Abbakar ɗin.
I Am Not Your Punching Bag
I Am Not Your Punching Bag And Other Stories is a collection of short moral and interesting stories depicting the daily struggles of African woman.
Mutum Da Kaddararsa
Bilkisu matashiyar mace ce mai ƙarancin shekaru, sai dai ƙaddarar rayuwa ta sa zaman aure ya gagare ta. Da farko ta auri Aminu wanda suka samu ɗaa guda ɗaya da shi wato Amir. Bayan sun rabu ne sai ta auri Malam inda suke zaune tare da uwargidarsa Hajja. Kisisinar amaryar Malam ne tai ta jawo musu damuwa har aurenta ya mutu a karo na biyu. Bayan ta koma gidan gwaggo Maryam ne masoya biyu suka fito neman aurenta. Hassan mai shagon siyar da kayayyaki da kuma Ɗan Majalisa Hashim Bello. Kowa na mata kwaɗayin auren Ɗan Majalisa, sai dai ita kuma tunaninta daban.
Munafukin Miji
Ridayya na matuƙar son mijinta Zameer. Ta mallaka mishi dukkan rayuwarta da duk wani abu da ta mallaka. Saboda shi ta rabu da iyayenta da ‘yan’uwanta. Sai dai shi kuma a nashi ɓangaren, Zameer cin amanarta yake yi, ha’intarta yake yi6, kuma amfani da ita kawai yake yi wajen cimma muradansa. Duk irin yadda Mardiyya ta so ta nuna wa Ridayya gaskiyar abinda mijinta ke yi ta kasa fahimta saboda makauniyar soyayyar da take yi mishi.
Su Ne Sila
Tsananin raɗaɗi da zogin da ciwukan jikin Zainab ke yi mata ba su kai rabin wanda zuciyarta ke yi mata ba sakamakon tsintar kanta da ta yi a gidan yari. Duk irin tsusayinta da Safiya ke ji bai sa ta saki jiki da ita ba. Daga ƙarshe ma dai yanke shawarar kashe kanta ta yi. Domin a tunaninta hakan kaɗai mafita a gareta.
Aminaina Ko Ita?
Nafisa, kyakkyawar matashiya mai tashe da ji da kanta, ta ɗana wa ɗaya daga cikin ‘ya’yan Ambasada Ahmad Ɗangiwa mai suna Haidar tarkon soyayyar ƙarya domin ta samu maƙudan kuɗaɗe a wurinsa. Abin da ba ta sani ba shi ne, rikicin da ke kewaye da ahalin su Haidar ya sha gaban tunaninta, domin kuwa akwai waɗanda suka fi ta son kuɗin da take hangen samu, kuma har kisa za su iya yi domin su cimma burinsu.
Kuskuren Waye?
Halima da Zarah maƙwafta ne kuma ƙawaye. Makarantarsu ma ɗaya. Suna tsaka da rayuwarsu mahaifin Zahra ya ba da ita ga Hafiz. Babbar matsalar ita ce, mahaifiyar Hafiz ba ta son wannan haɗi da za a yi duk kuwa da cewa su yaran sun fara kamuwa da son juna. Ko ya za ta kaya a tsakaninsu?
Lokaci
Alhaji Yusuf na kwance yana barci sai ga kiran ƙaninsa Khamis cewa ya zo ofishin C.I.D cikin gaggawa ya fitar da shi daga komar wata azababbiyar mace da ta jawo mishi jarfar da bai san yadda zai yi da ita ba. Wace ce ita? Kuma wanene mai gaskiya a cikinsu?
Barrister
Burin Yazid na zama Barrister ya cika, dukkan ‘yan’uwansa kowa sai taya shi murna yake yi. Ita kuwa Nadiya, ta ƙwallafa rai akan Yazid, babu abinda take so face ganin ta aure shi, duk kuwa da cewa shi ba sonta yake yi ba. Zahra na cikin matsanancin tashin hankali sakamakon ciwon da mahaifiyarta ke yi wanda take buƙatar kuɗin kai ta asibiti. Ga kuma yayarta Zainab da kullum ba ta da aiki face musguna mata.
Wata Kaddara
Mubarak Yusuf Maikuɗi matashin mai kuɗi ne da ya taso da taka-tsan-tsan da kuma jajircewa akan tarbiyya. Babban abin da ya fi tsana a rayuwarshi ita ce sata. Sai dai kash… Ƙaddara ta sa ya auro ‘yar wani ƙasurgumin ɓarawo ba tare da ya sani ba.
Siradin Rayuwa
Karatu ne ya zama sanadin haɗuwar Al’Ameen Bello Maƙarfi da Ihsan a America. Bayan sun sheƙe ayarsu na wani lokaci sai suka yi aure ba tare da sanin iyayensu ba. Yanzu shekaru kusan goma kenan, rashin nutsuwa ya sa dole sun dawo gida Nijeriya. Babbar matsalar da ke gabansu ita ce, ba su san da wani ido za su kalli iyayensu ba.
Alkalamin Kaddara
Altaaf Tafida ya daɗe da yin aure amma har yanzu bai samu haihuwa ba, gashi kuma Allah ya jarabce shi da son yara. Kwatsam watarana sai ƙaddara ta sa ya ci karo da wasu ‘yan biyu waɗanda ko tantama babu nashi ne, sai dai karɓarsu daidai yake da neman jaki mai ƙaho. Rafiq ya kasa fahimtar dalilin da ya sa ba ya iya tuƙi, alhali kuwa yana iya tuna lokutan da yake tuƙa kansa a mota, tashin hankalinsa ya hauhawa ne ya yin da ya fahimci sabuwar amaryarsa Tasneem ta zo gidan shi ba tare da budurcinta ba. Kafin kuma ya gama ji da wannan, sai ga wani sabon asirin da ka iya rusa komai na rayuwarsa ya fara fitowa fili.
Hukuncin Allah
Salim matashi ne da bai yarda da cewa abubuwa suna faruwa ba ne a bisa yadda Allah ya ƙaddara za su faru ba. Abinda ya aminta da shi kawai shi ne, duk wani mummunan abu da ka ga ya faru, to sakacin wanda abin ya faru gare shi ne ya ja mishi.
Tsakaninmu
Habibu shi kaɗai ne namiji tilo a cikin ‘ya’ya biyar da suka rage a ahalinsu. Kowacce daga cikin sauran ‘yan uwanshi mata ba ta da burin da ya wuce ya samu nasara a rayuwa su ci a huce. Ga mahaifiyarsa Hajiya wadda ita ma ke da nata burikan akansa. A gefe kuma ga yarsa Talatu wadda sau uku tana yin aure tana fita saboda masifa. Shin ko Habibu da ahalinsa za su iya fita daga tarkon da ƙaddara ta ɗana musu?
Ina So
Halima mace ce mai kamun kai da shiga ta kamala a kowane lokaci, ba ta taɓa bayyana fuskarta hatta a wurin aikinta. Kullum cikin saka niƙabi take. Rayuwarta ta canza ne sakamakon dawowar ɗan mai kamfanin da take yi wa aiki daga ƙasar waje. Shin ko izzar Ali za ta yi tasiri akan Halima?
Kwaya Tushen Tsiya
Ƙalubalen rayuwa ya sa wani matashi yanke shawarar shan miyagun ƙwayoyi domin su taimaka mishi wajen ɗaukar fansa. Abinda bai sani ba shi ne, su ma ƙwayoyin tasu rigimar ta musamman ce.
Rayuwarmu
Hajiya Beeba ta asirce Auwal domin ganin ta mallake shi ko ta halin ƙaƙa. A sanadiyar wannan asiri ne har ta raba shi da matarsa ta farko, kula da su ya dawo hannun Dawud duk da ƙarancin shekarunsa. Tashin hankali ya yi wa Labeeb yawa, abubuwa sun cukurkuɗe mishi. Dukkan ‘yan gidansu sun canza mishi. Ga Dawud na fushi da shi saboda cikin da ke jikin Zulfa, ga yaro an kawo mai da bai san daga inda ya fito ba, ga matarsa na neman rabuwa da shi, babban abokin shi ba sa ko magana, kwatsam kuma sai ƙaramin ƙanin shi ya mutu.
Abul-Khair
‘Yan biyu masu matuƙar kama da junansu wato Abul da Khair kyawawa ne na gaban kwatance. Saboda tsabar kamanninsu ma ba kowa ke iya bambance su ba. Sai dai kuma akwai wani ɓoyayyen lamari game da su. Shin ko wane irin lamari ne?
Bakar Tafiya
Basma, Jafar, Salma, Rabson Guy da Biba sun shirya tsaf domin yin wata doguwar tafiya, sai dai kafin su isa inda suka nufa dole sai sun bi wata shu’umar hanya wadda ta ratsa ta cikin wani baƙin daji da ake yi wa laƙabi da ‘Kai Ka Zo.’ Kowa a cikinsu tana da babban dalilin da ya sa zai yi wannan tafiya. Sai dai tun kafin a yi nisa kowannensu ya fara da na sanin yin tafiyar a lokacin da kwatsam direbansu ya mutu ba tare da sun san dalili ba.
Mu'azzam
Irin biyayya da kuma soyayya da Mu’azzam ke yiwa mahaifiyarsa, Goggo, ya sa duniya ke kallon shi a matsayin da nagartacce. To amma a badini kuma yana da wata rayuwa da ko makiyinsa ne ba zai yi farin ciki da ganin sha a ciki ba. Wannan ya hada da rashin adalcin da yake tafkawa a tsanin matansa uku. A hakan kuma Goggo ta umurce shi da kara auren Husna, wacce ta ke kamar kanwa a gare shi, adalilin wani mummunar kaddara da ta fada ciki. Shin ko rikicikin da ke cikin gidan Mu’azzam zai barshi ya zauna lafiya?
Rumfar Kasuwa
Alhaji Isah mutum ne da ke ƙoƙarin sauke nauyin gidansa daidai gwargwado a koyaushe. Sai dai hakan bai sa matarsa ta gode wa Allah ba, domin kuwa tana yi wa ‘yarsa awara tana siyarwa bai sani ba. Maryam kuwa tsula tsiyarta take yi yadda ta ga dama matuƙar za ta siyar da kayan siyarwarta, duk kuwa da irin nasihar da ‘yar uwarta take yawan yi mata.
Sanadin Kenan
Engineer Ma’arouf Ji-Ƙas zaɓaɓɓen gwamna ne, yana da ‘ya guda ɗaya mai suna Amina wacce ke fama da ciwon shanyewar ɓarin jiki. Bayan ya lura da cewa matarsa Lailah ba za ta iya kula mishi da ‘yarsa ba sai ya nemi likitar da za ta zo har gida ta kula da ita. A sanadiyar haka ne ya haɗu da Dr. Amina, ko yaya haɗuwar za ta kasance?
Daga Karshe
Fatima budurwa ce ‘yar kimanin shekaru goma sha bakwai. Shiririta, rashin hankali da tsiwa bayyanannu ne daga cikin halayenta. Kowa na ƙorafi da ita game da wannan, domin ko waye mutum za ta iya ɗaga ido ta kalle ka ta faɗa maka duk maganar da ta ga dama. Kafiya, kuwa sai ka ce kuturu. Jamilu ɗan uwan mahaifiyar Fatima ne, kuma shi take so ta aura, Mustafa kuma malamin Fatima ne na Islamiyya. Jamilu ya daɗe yana son Fatima amma bai faɗa wa kowa ba, ita kuma ta ce wa Mustafa ya turo manyan gidansu neman aurenta.
Siddabaru
Ko da yake yasan ba a mutuwa a dawo, bayyanar hotunan gayyatar auren Maryam da ya gani a Facebook tare da cikakken sunanta da ya gani sun ƙara tabbatar wa da Isah cewa lallai akwai wani ɓoyayyen al’amari game da mutuwarta. Ita kuma Jalila ko ya za ta yi da irin halin ko in kula da mijinta ke nuna mata?
Shirin Allah
Wanda Allah Ya so da shiriya, babu wanda ya isa ya sauya shi. Duk da irin ƙalubale na rayuwa da Hamida ta fuskanta har zuwa aurenta da Abdurrashid, da kuma harin da babban amininsa Usman kai mata tare da nuna sha’awarsa akanta basu canza ta ba. Shin ko Hamida za ta ba wa Usman dama wajen saɓa wa Allah, me zai faru idan Abdurrashid ya gane Usman na neman matarsa?
Our Friendship
When Zainab caught her best friend Sa’ada with her husband naked on their matrimonial bed, a ruckus ensured which ended the marriage shortly after. But is that really the solution she sought? Are things going to happen the way Sa’ada planned?
Cikin Baure
Auren Asma’u da Abbas ya kusa, sai dai ko kaɗan ba ta son shi. Hankalinta na kan wani matashin mai kuɗi da ake kira Alhaji Nas, alhali kuwa shi bai san ma tana yi ba. A haka dai aka ɗaura auren ba don tana so ba. Kwaɗayin dukiyar Alhaji Nas da fafutukar ganin ta shiga rayuwar daula suka sa soyayya ta makantar da ita har sai da ta kashe aurenta ta fito domin ta auri Alhaji Nas. Burinta ya cika ta aure shi, sai dai irin halin da ta tsinci kanta a rayuwar zaman gidan ko a mafarki ba ta hango wa kanta hakan ba.
Soyayya Da Rayuwa
Safina da Nabila matan Hassan Hassan ne da Hussaini. Suna zaman lafiya tare da nuna wa juna tsantsar soyayya. Kwatsam rana guda sai Hassan da Hussaini ke faɗa wa matansu cewa za su ƙara aure nan da wata uku. Shin ko matan za su ɗauki wannan labari da sauƙi kuwa?
Tsaka Mai Wuya
Umar Bin Ally ba shi da aikin yi a kullum face kula ‘yanmata a shafin sada zumunta na facebook. Kusan kullum sai ya yi sabuwar budurwa, bisa tsautsayi wata rana sai ya fara soyayya da matar ministan tsaro na ƙasa ba tare da ya sani ba.
Martabarmu
Ahmadi cikakken ɗan boko ne, auren soyayya suka yi shi da matarsa Maimuna wacce kuma ‘yar danginsu ne. Sai dai rikici ya ratso cikin zaman lafiyar da suke yi da juna ne daga lokacin da ya sa ɗambar auren Maryam wadda ita ma ‘yar danginsu ce.
Fadime
Bayan Uwale ta yi wa ‘yar mijinta Faɗime asiri ta haukace,’ yarta Hainsai na ganin cewa ta fidda ita kawai daga ƙauyen kowa ya huta. Sai dai Uwale ba za ta iya ba saboda sharuɗɗan da aka gindaya mata. Kuma a shirye take ta bi takan ko waye domin cikar burinta. Sai dai ƙaddarar da ke cikin rayuwarsu duka mai girma ce.
Rigar Siliki
Mujahid da Binta ‘yan dangi ɗaya ne. Akwai kyakkyawar fahimtar juna sosai a tsakanin su, domin ya zamo mai share mata kukanta a kowane lokaci. Abinda ba ta sani ba shi ne, Mujahid na matuƙar ƙaunarta fiye da komai na duniya. Sai dai kuma ta zaɓi Shukuranu a matsayin miji ba tare da ta san yana da wata gagarumar matsala ba.
Rai Da Kaddara
Shin ko Daada za ta iya riƙe amanar Nawfal da Madina kamar yadda ta yi alƙawari? Sai zuwa yaushe ne Nawfal zai samu sauƙin halin kaɗaicin da ya riga ya saba da shi a gidan Julde? Matuƙar da rai, to ƙaddara za ta biyo baya. Yadda za su yi da wannan ƙaddara kuwa zaɓinsu ne.
Gidan Gado
Kakan su Habiba ya mutu ya bar wa mahaifiyarsu wani makeken gida, sai dai ɗan uwansa Malam Umaru ya yi kane-kane akan wannan gida ya ƙi bari a raba a ba wa kowa haƙƙin shi. Duk wanda ya taso da maganar ma sai ya yi mishi barazanar ganin bayan shi. Magada dai sun sha alwashin ƙwato haƙƙinsu, shi kuma Malam Umar da matarsa Saude sun sha alwashin tauye wannan haƙƙi ta kowane hali.
Hakabiyya
Yayin da fafutukar nemawa mijinta magani ya kai Zawwa zuwa ga tone kabarin wata budurwa mai ciki, hakan ya zamo matakin farko na cukurkuɗewar rayuwar Haƙabiyya tun kafin ta fito duniya. Hameedu, wanda ya canza sunan shi zuwa Huzaif yana ɗauke shi ma da wani ɓoyayyen sirri wanda ka iya fayyace komai ko ruguza komsi. Makirci ya haɗu da makirci, tsafi ya haɗu da mugunta, sirri ya ci karo da sirri, shin ko gaskiya ita kuma za ta yi halinta daga ƙarshe?
Kaddarata
Rayuwa takan zo wa wasu da sauƙi, wasu kuma takan zo musu da akasin haka. Rayuwar Fatima Zahra cike take da ƙalubale, kuma ga dukkan alamu ba ta gama fuskantar ƙalubalen ba.
Abdulkadir
Kowa ya sha mamakin yadda aka yi har soyayya ta ƙullu a tsakanin Abdulƙadir da Waheedah saboda bambancin da ke tsakanin halayensu tamkar na ruwa da wuta ne. Yayin da wasu kuma ke tunanin halin da za ta shiga a zamantakewar aurenta da shi. Sai dai sun ba mara ɗa kunya sosai na tsawon wani lokaci kafin babbar ƙawar Waheedah da ake kira Nuriyya ta kutso kanta jikin Abdulƙadir tare da ƙoƙarin ganin ta aure shi.