Kwaya Tushen Tsiya
Ƙalubalen rayuwa ya sa wani matashi yanke shawarar shan miyagun ƙwayoyi domin su taimaka mishi wajen ɗaukar fansa. Abinda bai sani ba shi ne, su ma ƙwayoyin tasu rigimar ta musamman ce.
Hukuncin Allah
Salim matashi ne da bai yarda da cewa abubuwa suna faruwa ba ne a bisa yadda Allah ya ƙaddara za su faru ba. Abinda ya aminta da shi kawai shi ne, duk wani mummunan abu da ka ga ya faru, to sakacin wanda abin ya faru gare shi ne ya ja mishi.
Tsanin Nasara
Duk da cewa amaryar ta jima a gidan mijinta har ma ta tara yara. Gwalagwalan shawarwarin da mahaifinta ya ba ta sun zamo mata tsanin hawa matakin nasara a gidan aurenta da ma rayuwarta baki É—aya.
Fatalwar Sinu
Katoɓara da ɓarin baki suka sa Haiman bayyanawa duniya irin abubuwan da yake so a bashi a matsayin kyautar barka da sallah. Sai dai ya samu kyautar da ta fi ƙarfin shi, yayin da wata kyautar ta fito daga lahira kuma daga hannun wani gagarumin maƙiyin da bai san yana da shi ba.
Bakar Kaddara
Wasu lokutan ba sai ka aikata mummunan aiki ba kafin baÆ™ar Æ™addara ta afko maka. A wasu lokutan kuma, halayen mutane ne ke kaisu ga faÉ—awa cikin bala’i.
Tun A Duniya
Alhaji Garba ya shiga wani irin mummunan hali na ban mamaki. Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci duk dukiyar da ya tara ta salwanta, sannan lafiyarsa ma kanta ta fara ƙoƙarin ƙaurace masa.
Baba Dattijo Dan Bursin
Yayin da wani É—an jarida ya je gidan yarin Kurmawa da ke Kano ya gamu da wani dattijo mai ban mamaki da ke rayuwa a wannan gida na kaso. Shin ko ta yaya za a iya shari’ar kashe mutumin da ya riga da ya mutu tun shekaru 29 da suka gabata?
Hoton Mijina
Muka amsawa da amin muna sakar wa juna murmushi. Tun daga ranar duk wasu makaman yaÆ™ina na zubar da su, har mamakin kaina nake yi da tambayar kaina anya kuwa ni ce Rashida? Zaman lafiya ya samu matsuguni a tsakaninmu tamkar ba kishiyoyi ba.Â
Na Sake Ta
Hamshaƙin matashin mai kuɗin da ake ji da shi, wato Usman One boy ya samu Kamal mayen kuɗi da batun wani irin kasuwanci mai ban mamaki. Usman ya yi alƙawarin ba wa Kamal kuɗi naira na gugar naira har miliyan biyar, matuƙar dai ya yarda zai saki matarsa Hajir domin ya aure ta. Ashe Kamal na gab ne da fahimtar cewa ba komai bane kuɗi ke iya yi wa mutum.
Izina
Aisha (Ma’isha) da Abdul’aziz ‘yan’uwan juna ne, kuma dukkansu lauyoyi ne. Sai dai a karo farko za su kara da juna a gaban Æ™uliya domin kare mutane biyu. Iya Aisha tana Æ™oÆ™arin Æ™wato wa wata mata da ‘yarta
‘yancinsu ne a hannun wani mugun mai kuÉ—i. Shi kuma Abdul’aziz yana kare shi. A wani É“angaren kuma, yayansu jami’in Æ™asa da Æ™asa, Deputy Commissioner of Police Abdulmalik Ibrahim Ahmad ya zo Nijeriya domin ya gudanar da bincike na musamman akan kisan da aka yi wa wani babban jami’in tsaro, kwatsam kuma sai Æ™addara ta haÉ—a shi da ‘Yar Jarida Intasar Mahmood Abdullahi.
Ta Ki Aure
Sawwama da Kawwama yaya da ƙanwa ne da suka jima basu yi aure ba. Shekarar Sawwama talatin da biyar ba ta yi aure ba, yayinda ita kuma Kawwama shekararta talatin da biyu ba ta yi aure ba. Hakan ya sa kowa a dangi ke ta faman yi musu surutu. Kwatsam sai ga Jalil ya zo neman auren Kawwama, an sha biki an gwangwaje, sai dai kuma Jalil na ɗauke da wani ɓoyayyen lamari da ba kowa ya san da shi ba.
Laifin Wa?
Ladidi matashiya ce mai ji da Æ™uruciya, hakan ya sa ta faÉ—a harkar bin maza domin ta hucewa kanta haushin rashin É—auke mata É—awainiya da iyayenta suka kasa. Duk da cewa sun san irin abin da É—iyarsu ke aikatawa, amma ba su da ta cewa. Saboda wani lokaci ma wurinta suke zuwa su yi ‘yar murya.
Kukan Kurciya
Ana gobe ɗaurin auren Mujahida da masoyinta da suka yi shekaru biyar suna soyayya, wato Nura ya ce ya fasa. A gigice ta shiga gida da taimakon ƙanenta Mujtafa, sai dai shigarta cikin gidan ya yi daidai da furta kalmar saki da mahaifinta wato Habibu ya yi ga mahaifiyarta wato Bilkisu.
Daurin Huhun Goro
Halin yunwa, talauci da kuma matsatsin rayuwa da ake ciki ne suka tunzura Tabawa har ta kai ga tana bin layi da lunguna tana zagin shugabanni, ‘yan siya da kuma ‘yan kasuwa. Domin ita a ganinta, duk su ne sanadin faruwar hakan a cikin al’umma. Ta kuma Æ™udiri aniyar kawo sauyi game da wannan lamari.
Alkawarin Allah
Alhaji Usman Ibrahim Matawalle ba ya barin kowa zuwa zance wajen ‘ya’yansa, watau Maryam da Fatima saboda mutum ne shi mai zafi sosai. Soyayyar Maryam ta kama Nuraddeen, kuma sai bibiyarta yake yi har sai da ya gano gidansu. Shin ko zai dace da samun soyayyar Maryam tare da amincewar mahaifinta?
Kwamin Nadama
Baƙin kishi ya sa Ladiyo cakumar wuyar mijinta tana mai sauke masa kayan rashin mutunci tare da tabbatar mishi da cewa bai isa ya yo mata kishiya ba. Shi kuwa Kabiru, don ya gwada mata lallai ya haifu bai yi wata-wata ba ya danna mata saki biyu. Tun daga nan ta shiga tashin hankali da ruɗani, musamman da ta tuna cewa za ta bar gidan kuma zai kawo wata.
Abinda Babba Ya Hango
Okasha Sani Sa’id matashi ne mai taÆ™ama da kuÉ—i da kyawun halitta. Hakan ya sa yake wasa da hankulan ‘yanmata tare da É“ata musu rayuwa. Ƙaddara ce ta haÉ—a shi da Jameela, wadda ta bijirewa shawarar mahaifinta ta auri Okasha ba don suna so ba. Kash! Da ta san abin da zai biyo baya da ba ta yi wannan aure ba.
Ba Kauyanci Ba Ne
Alhaji AbdulÆ™adir mutum ne É—an zamani wanda kiyaye haƙƙoÆ™in addini bai dame shi ba, to amma ‘yarsa Salma da mahaifiyarta Hajiya Bilkisu suna da kyawawan halaye kuma suna matuÆ™ar kiyaye dokokin shari’ar Musulunci. Alhaji Sameer da Hajiya Samira suna da É—a guda É—aya da suka haifa mai suna Kamal. Duk iya Æ™oÆ™arin da Alhaji Sameer yake yi na ganin Kamal ya shiryu, ita mahaifiyarsa gani take takura ce. Kamal ya kama hannun Salma a wurin wani taro inda ta wanke shi da mari. Sai daga baya yake jin ashe mahaifiyar Salma mahaifinsa ya fara so ya aura kafin mahaifiyarsa.
Mafarkin Deluwa
Malam Shitu, Malam Lawal, Malam Tsalha da Malam Zaidu ma’aikatan wata maÆ™abarta ce da ke Æ™auyen ÆŠanduÆ™us. Tsananin firgici ne ya ziyarce su a lokacin da suka ga wata ‘yar wada ta shigo maÆ™abartar da suke kula da ita tana neman taimakon su binne mata gawar. Saratu, wadda aka fi sani da Deluwa ta yanke shawarar kashe masoyinta Chibunzu, kamar yadda Alhaji Labaran ya umurta domin cika burinta na zuwa Makka.
Tsinin Harshe Ya Fi Na Mashi
Al’amura sun dagulewa Zainab tun bayan da bakinta ya jawo mata jalli-joga sakamakon sharrin maita da ta yi wa Jummai a gidan suna. Lamarin ya kai matuÆ™a a fagen tsamari ne ya yin da aka aiko mata da takardar sammaci daga kotu a bisa wannan zargi, ana tsaka da wannan kuma sai mijinta Auwal ya sake ta.
I Am Not Your Punching Bag
I Am Not Your Punching Bag And Other Stories is a collection of short moral and interesting stories depicting the daily struggles of African woman.
Addininmu
Abduljabbar wanda aka fi sani da AJ, matashi ne É—an talaka jikan talakawa, sai dai kuma ya Æ™wallafa wa ransa zama hamshaÆ™in mai kuÉ—i. A dalilin hakane yake yaudarar budurwarsa Zahra tana sato kuÉ—in iyayenta tana kawo mishi. Abdallah shi kuma ya tubure fafur kan cewa shi fa Æ™anwarsa Maryam ba za ta auri É—an bidi’a ba. Zainab Ambato kuma na shirin yin fito-na-fito da wani matashin mai wa’azi da ke sukarta.
Munafukin Miji
Ridayya na matuÆ™ar son mijinta Zameer. Ta mallaka mishi dukkan rayuwarta da duk wani abu da ta mallaka. Saboda shi ta rabu da iyayenta da ‘yan’uwanta. Sai dai shi kuma a nashi É“angaren, Zameer cin amanarta yake yi, ha’intarta yake yi6, kuma amfani da ita kawai yake yi wajen cimma muradansa. Duk irin yadda Mardiyya ta so ta nuna wa Ridayya gaskiyar abinda mijinta ke yi ta kasa fahimta saboda makauniyar soyayyar da take yi mishi.
Uban Da Ba Namu Ba
Tanimu Sambo wanda aka fi sani da Baban Nawwara malamin makaranta ne da ke koyarwa a wata makarantar mata. Jajircewa da ƙwazonsa a ɓangaren koyarwa tare da tsayuwa akan gaskiya suka sa ya ƙi yarda ɗalibansa su ba da kuɗi domin a basu amsar jarabawar fita daga Sakandare. Maimakon haka, sai ma dagewa da ya yi wajen horas da su yadda za su amsa tambayoyin yadda ya kamata.
Akwai Ciwo
Akan ce ‘naka shi ke ba da kai’, Jidda ta ga gaskiyar hakan a zahiri yayin da ta tsinci kanta a matsayin marainiyar da ‘yan’uwa suka yi watsi da ita. Ƙuncin rayuwa tare da tunanin yadda za ta ciyar da kanta da Æ™annenta ne ya sa ta faÉ—awa ashararanci ba tare da ta yi tunanin abinda zai biyo baya ba.
Almajirai Ma 'Ya'ya Ne
Sa’idu da Halliru sun zamo tsayayyu kuma bayyanannun misalai na irin mummunan halin da al’majirai ke faÉ—awa a cikin rayuwarsu ta al’majiranci. Duk da cewa an nuna irin yadda mugun halin mutanen zamani yake game da al’majirai har suke cutar da su, Hajiya Maryam ta fita zakka tare da zamowa misalin da kowa zai so zama kamarta.
Kisan Boko
Kyawun fuska da kyawun dirin jiki tare da dakakkiyar niyyar ganin ta yi karatun boko mai zurfi ne suka sa ake yi wa Sa’adatu inkiya da ‘Yar Boko. Tabbas ta yi bokon, domin har ta kai ga samun digiri na biyu. Ga gida da aiki duk ta mallaka. Babban tashin hankalinta shi ne rashin samun mijin aure. Ƙawayenta da yawa tuni sun tara ‘ya’ya, samarinta duk sun kama kansu, ga shi ita kuma auren take so.
Nakasar Zuci
Abubuwa sun taru sun yi wa Badi’a jingim a ka, sakamakon sakin da mijinta Adamu ya yi mata da tsakar dare bayan da ya gano cewa tana da cikin wata uku a jikinta, alhali ba su wuce wata É—aya da ‘yan kwanaki da yin auren ba. Ga shi mahaifinta ya ce in har ta baro gidan miji kada ta zo mishi gida, ko yaya za ta yi?
Rule Of The Soil
In the arid fields of Danja, Balarabe is a farmer of exceptional skill, bound by the absolute “Rule of the Soil” and the rigid traditions of his father, Malam Isa. He is ready to marry Rukayya, the light of his life, but his father demands an impossible wait: the marriage must be postponed until the final, spiritual purity of the harvest, a time that perpetually refuses to arrive.
​Rukayya waits in silence, trapped between her devotion to Balarabe and the obedience required by her father. But when a wealthy, modern merchant offers a dowry so spectacular it blinds her father with vanity, the very custom that commanded Balarabe’s patience becomes the swift, brutal instrument of her loss.
​Trapped in a heartless contract, Rukayya faces a choice between dishonoring her family and denying her heart. Her final, devastating act of defiance leaves behind a single, unshakeable message for the village to find.
​Shattered by grief and his father’s catastrophic certainty, Balarabe flees to the wild country, a man ruined by his own virtue. He must abandon the iron grip of the old order and the sacred calendar to forge a new legacy, one built on resilience, action, and the enduring memorial to the woman who taught him that obedience has a cost.
Death on Motorbikes
A fourteen-year-old boy, haunted by news of bandit attacks on motorbikes in Northern Nigeria, questions his uncle about the root causes. His uncle reveals that banditry is a million-dollar business fueled by powerful financiers, politicians and businessmen who use violence to destabilize governments. The riders are mere pawns, including brainwashed children. The only solution, his uncle argues, is to imprison the financiers, though their immunity makes this nearly impossible.